Littattaffen da muke da su | Mafari

Murfi Taƙatchen bayani Yadda yake
Almasihu Cikin Islama Da Kristanci
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Almasihu cikin Islama``. Littafi ne wanda aka yi nazari game da koyaswar Christa da koyaswar Musulmai akan mutantakar Yesu Christi. Marubucin ya tattauna abubuwa game da Maryamu a cikin Ku´rani da Littafi mai Tsarki, da kuma matsayin Yesu Kristi. Ya kuma yi bincike akan haifuwar Yesu da sauran battutuwa game Yesu Dan Allah da sauransu.
HTML
BISHARA TA HANNUN BARNABA <<SHAIDAR KARYA>>
Na Iskander Jadeed
Wannan dan littafi ya shaida cewa an karyata wannan Bishara ta hannun Barnaba. Bishara ta hannun Barnaba na cike da kurakure masu yawa. Marubucin yana zaton cewa wani dan kasar Italiya ne wanda ya shiga musulci ne ya rubuta Bishara ta Hannun Barnaba.
HTML
GICCIYEN ALMASIHU GASKIYA NE, BA ALMARA BA
Na John Gilchrist
Da gaskiya ne wai an gicciye Yesu? Wannan muhimiyar tambaya ce, domin, an gina Kristanci akan gicciyewar Kristi da tashin sa daga Mattatu. Littafi mai Tsarki wanda ya zama tushen bangaskiyar Krista na tabbatar mana da cewa Yesu Kristi ya mutu akan Gicciye. Wannan littafi na kuma nuna cewa Yesu bai taba yin shiri domin ya hambarar dad a wata gwanati ba. Bai ma taba yin kokarin karekansa daga wani zargi ba.
HTML
TIRNITI [MURHUNNIYA] DA ƊAYANTAKA
Na Laccar da Papa Shenuda III ya bada a Babbar Majami’ar Markus a Alƙahira
Wannan lacca ya nuna wadansu kurakure da Musulmai suke dashi cikin tununin su game da Triniti.
HTML
Ta YaYa Za Mu Iya Sanin Gaskiyar Linjila / Bishara?
Na Iskander Jadeed
Wannan littafi ya yi nazari akantushen bangaskiyar Krista. Marubucin yak are martabar Littafi mai Tsarki, da martabar Dan Allah, da gicciye, da wadansu battutuwa da ba mutane wahala.
HTML
Tarihin Matanin Kur’ani Da Na Littafi Mai Tsarki
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Littafi mai Tsarki Kalmar Allah ne?``. Ya kuma yi nazari akan wadansu shaidu daga cikin Kur`ani da Littafi mai Tsarki. Marubucin littafin ya kuma tattauna wadansu irin shaidu uku. Shaidu daga Littafe masu Tsarki, daga littafin Apokrifa da``Babbar nakasa``, kurakure dubu hamsin, da abubuwan da ke lalata Littafi mai Tsarki. Akwai kuma tarihin Yesu Kristi.
HTML