Littattaffen da muke da su | Almasihu

Murfi Taƙatchen bayani Yadda yake
Almasihu Cikin Islama Da Kristanci
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Almasihu cikin Islama``. Littafi ne wanda aka yi nazari game da koyaswar Christa da koyaswar Musulmai akan mutantakar Yesu Christi. Marubucin ya tattauna abubuwa game da Maryamu a cikin Ku´rani da Littafi mai Tsarki, da kuma matsayin Yesu Kristi. Ya kuma yi bincike akan haifuwar Yesu da sauran battutuwa game Yesu Dan Allah da sauransu.
HTML
GICCIYEN ALMASIHU GASKIYA NE, BA ALMARA BA
Na John Gilchrist
Da gaskiya ne wai an gicciye Yesu? Wannan muhimiyar tambaya ce, domin, an gina Kristanci akan gicciyewar Kristi da tashin sa daga Mattatu. Littafi mai Tsarki wanda ya zama tushen bangaskiyar Krista na tabbatar mana da cewa Yesu Kristi ya mutu akan Gicciye. Wannan littafi na kuma nuna cewa Yesu bai taba yin shiri domin ya hambarar dad a wata gwanati ba. Bai ma taba yin kokarin karekansa daga wani zargi ba.
HTML
KO ALLAH YA BAYYANA CIKIN JIKI?
Na Iskander Jadeed
Ko zai iya yi wu wa cewa Allah ya bayyana kansa cikin sifan mutum? Ma rubucin wannan littafi ya yi nazari da bayani akan yadda Maryamu ta haifi Yesu (an haife shi a kamanin mutum). Ya zauna a cikin wanan duniya, ya yi irin rayuwa na dan´adam. Ya ji yunwa, ya ji kishin ruwa, ya gaji da tafiya, har ma ya yi barci a cikin jirgin ruwa. An wulakanta shi ko da shike shi Allah ne cikin jikin mutum. Ko da shike ya zo cikin sifar mutum, ikonsa ya cika sama da kasa. Wannan shine asirin halayensa kamar yadda aka bayana a cikin littafin Matiyu 11:27 da kuma 1 Timatawus 3:16.
HTML