Table of Contents
A cikin 1983, Ahmed Deedat ya wallafa wani ɗan littafi mai suna “Almasihu a Cikin Islama”. Ko da shike an ɗauka cewa marubucin yana da niyyar samar da safiyo na gaba ɗaya na yadda Islama take ɗaukar Yesu, ba mamaki, a sami cewa yawancin littafin gardama ce kawai gāba Kristanci. Kamar dai yawancin rubuce rubucensa, sabon littafin nan na Deedat gardama ce zalla gāba da bangaskiyar Kirista. Mun ga ya dace a cikin waɗannan al’amura mu tantance al’amuran da ya yi batun su a cikin ɗan littafin nan, mu kuma ba da ƙaƙƙarfan martani a kan gardandaminsa. Ba nufinmu ne mu dubi dukan abubuwan da ke cikin ɗan littafin ba, amma za mu dubi abubuwan da suka danganci wasu gaskatawar Kirista kaitsaye kawai.
Tun da fari ba za mu ɓata lokaci ba, za mu ce, ƙoƙarin Deedat na ƙasƙantar da labarin rayuwar Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma mutuntakar Yesu, ba shi da wani tasiri. Kyakkyawan misalin irin rashin tasirin nan za a gan shi a farkon shafi shida na ɗan littafinsa, inda ya yi iƙirari cewa, ainihin sunan Yesu shi ne “Isa” (kamar dai yadda ake kiransa a cikin Kur’ani) kuma an samo sunan daga Ibrananci, “Isuwa”. Ya ce Isuwa “ana morarsa ko’ina cikin Yahudanci” kuma an mori sunan fiye da sau sittin” a cikin littafi na farko na Littafi Mai Tsarki, wanda a ke kira Farawa (Almasihu Cikin Islama: A turance ana kiran ɗan littafin “Christ in Islam” shafi na 6). Deedat ya nuna jahilinsa a game da Littafi Mai Tsarki da kuma tarihin Yahudawa, za a ga wannan tun farkon ɗan littafinsa, domin kuwa akwai Isuwa guda ɗaya kaɗai da aka ambata a cikin Littafin Farawa da ɗan’uwansa Yakubu, wanda shike anihin uban al’ummar Isra’ila. A kan kowanne ɗayan waɗannan fiye da su sittin ɗin wannan Isuwan ne kaɗai ake magana, a cikin Littafi Mai Tsarki kuwa babu inda aka ambaci wata Isra’ila da ake kira ta Isuwa. Yahudawa ma ba sa kiran ’ya’yansu da sunan nan.
Yawancin rayuwar Yakubu da Isuwa ta magabtaka ce, da su da zuriyarsu. Isr’ilawa da Edomawa sun sha gabza yaƙi da junansu. Babu yaran Yahudawa da suke da sunan ɗan’uwan Yakubu wanda shike uban Isra’ilawa, don kuwa ya yi gāba da Yakubu, Allah kuma ya ƙi shi (Ibraniyawa 12:17). Saboda haka, ruɗarwa ce, a ce asalin sunan Yesu shi ne Isuwa.
Ba shakka, kwaɓen tarihi da Deedat ya yi a cikin ɗan littafinsa a sarari yake, ko da shike kuskure ba duka ne nasa ba. Larabawa Kirista a koyaushe suna kiran Yesu Yasu cikin Aramanci shi ne Yashuwa wanda yake da Hellenanci “Iesous” da Ingilishi kuwa Jesus wato “Yesu”. Saboda wasu dalilai marasa ganuwa, sai Muhammadu ya zaɓi ya kira shi Isa. Yadda Deedat ya fassara sunan nan da “Isuwa” ya samu ne daga shawarar wasu Yahudawa a cikin ƙasar Arabia, waɗanda suka yaudari Muhammadu don su ɓadda shi daga sunan Yesu na asali, sai suka fassara shi da sunan ɗan’uwan kakansu, marar addini. Idan a ƙarshen batun Deedat daidai ne, to, ya yi gāba ƙwarai ke nan da ainihin allahntakar Kur’ani.
Ba shakka cewa, ko kusa, Isuwa ba ainihin sunan gaske na Yesu ba ne fiye da Isan Muhammadu. Tushen kuskuren nan ne ya kafa tushen gardamar Deedat wajen kwatanta, ko gwamawa tsakanin Almasihu cikin Islama da Kristanci, yana kuma da wuya a ƙi ƙarshen batunsa na cewa Yesu na cikin Littafi Mai Tsarki shi ne gaske a maimakon Isa na cikin Kur’ani. Za mu ci gaba mu tantance wasu fannoni cikin rubutun Deedat da suka danganta Isa na cikin Kur’ani ga Yesu na gaske cikin Kristanci.
Deedat yana da abin faɗi da dama, ba a kan koyarwar Kur’ani a game da Yesu kaɗai ba, amma har da koyarwar Kur’ani a kan mahaifiyar Yesu, wato Maryamu. A ƙarƙashin kan magana mai suna “Haihuwar Maryamu” yana cewa:
Ga yadda labarin yake, kakar Yesu, wato Hannatu, bakararriya ce. Ta tsiyaye zuciyarta a gaban Allah: muddin Allah zai ba ta ɗa, to, za ta keɓe shi domin yi wa Allah hidima cikin haikali (Deedat, Christ in Islam P.9, wato ɗan littafin Deedat Almasihu cikin Islama, shafi na 9).
Kowane yaro Kirista mai zuwa Sunday School ya san labarin Hannatu, da yadda ta yi addu’a da naciya ga Allah don ta sami ɗa, ta kuma yi alkawarin ba da shi ya yi wa Allah hidima muddin ransa idan Allah ya amsa addu’arta. Sai dai matsalar ita ce, ɗan da ta haifa sunansa Sama’ila, wanda ya zama annabi, ya kuma shafe Dawuda ya zama sarkin Isra’ila tun wajen shekara dubu kafin zamanin Maryamu da Yesu! An ba da labarin addu’ar Hannatu a cikin 1Sama’ila 1:11, daga bisani kuma muna karanta cewa:
“Ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, ta raɗa, masa suna Sama’ila, wato ‘Na roƙo shi daga wurin Ubangiji’”. 1Sama’ila 1:20.
To, yaya ke nan, Mr Deedat, wanda ake gani “Ƙwararren Musulmi masanin Littafi Mai Tsarki” (kamar yadda yake nuna kansa), ya zo ya yi irin wannan kwaɓe, yadda ya gauraye mahaifiyar Sama’ila da mahaifiyar Maryamu? Dalili shi ne, Kur’ani ma ya ruɗar da labarin matan nan biyu (Suratu Al Imrana 3:35-36). (Wasu ayyukan Hadisi a sarari su ke cewa, sunan mahaifiyar Maryamu lalle Hannatu ne, duka masharhantan Kur’ani na dā da na yanzu sun yarda cewa wannan ne ainihin sunanta).
A shafi na gaba cikin ɗan littafinsa, Deedat yana cewa, “Labarin ke nan. Amma a ina ne Muhammadu ya samo saninsa? Domin bai iya karatu da rubutu ba” (Christ in Islam, p.10; wato “Almasihu Cikin Islama” a shafi na 10). Da shike tabbatacce ne an yi kuskure, wannna kam kyakkyawar tambaya ce ƙwarai da gaske! Deedat ya nuna gaskiyar cewa Muhammadu bai iya karatu da rubutu ba don ya kāre ikirarin cewa Kur’ani maganar Allah ne amma, da shike ya gauraye batun matan nan biyu, ba shakka, gaskiyar cewa Muhammadu bai iya karatu da rubutu ba ƙarin tabbaci ne cewa lalle shi ne ya ƙaga littafin. Idan da a ce ya san Nassoshin Yahudawa sosai da bai aikata irin wannan kuskuren ba.
A ƙashin gaskiya, dukanin labarin haihuwar Maryamu da kēɓe ta a cikin Kur’ani sabuwar ruɗarwa ce ga sassa dabam dabam na Littafi Mai Tsarki. Tun da fari ma a fili yake an rikita Maryamu kanta da Iliya, annabin da ya ɓuya, hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci daga bisa (1Sarakuna 17:6 – Kur’ani kuwa ya ce, Maryamu ma hankaki sun ciyar da ita a cikin Suratu Al Imrana 3:37). Duk da haka, sunan da aka ba mahaifiyar Maryamu ke nan, Hannatu, wannan ya ba mu haske a game da inda mai ƙagawan nan ya sami labarun da ya harhaɗa. Ya kamata a wannan wuri mu ambaci cewa, ainihin labarin an fara samun sa ne daga cikin Afokirifa mai suna, “Protevangelium of James the Less” (Wato Bisharar Yakubu Ƙarami), sai kawai Muhammadu ya kwasa ya zuba cikin Kur’ani ba tare da sanin asirtaccen mafarin ba.
Labarin ya taso ne daga ruɗami tsakanin batun addu’ar Hannatu domin neman ɗa, da kuma labarin dake cikin Bishara daga hannun Luka:
Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, ’yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci, da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu’a da azumi. Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima. Luka 2:36-38.
Mutum zai iya gani a sarari yadda wannan kuskuren ya auku. Har yanzu muna da macen da ainihin sunanta na Ibrananci Hannatu ne, kuma mun gane cewa wannan matar ce ta zauna cikin Haikali shekaru masu yawan gaske, tana bautar Allah ta wurin addu’a da azumi. An rikita batun Maryamu, ba da Iliya da Sama’ila kaɗai ba, amma har da annabiya Hannatu kuma! A sarari yake cewa Hannatun nan su biyu wato Hannatu-mahaifiyar Sama’ila, da kuma Hannatu ’yar Fanuyila – an gauraye su da juna, labarin cikin sura ta 3 ta Kur’ani kuma ba shakka kwaɓe ne aka yi na labaru biyu da suna nan daban suke da juna a cikin Littafi Mai Tsarki a kan matan nan su biyu.
A sarari yake cewa, Deedat ya yi babbar kwaɓawa ta wurin gauraya mahaifiyar Maryamu da macen da ta yi rayuwa tun ƙarni wajen goma kafin ta. Amma kamar wannan bai isa ba, sai ya kamo wata aya kuma daga cikin Kur’ani a cikin ɗan littafin nasa wanda yake gauraya Maryamu kanta da wata macen wadda ta yi rayuwa kusan ƙarni ashirin kafin ta. A shafi na 15 cikin ɗan littafinsa mai suna a Turance “Christ in Islam” ya faɗo waɗannan kalamai waɗanda maƙwabtan Maryamu suka gaya mata:
Yaa Ukhta Haaruuna – Ma’ana. “Ya ’yar’uwar Haruna!” (Suratu Maryam 19:28).
A shafi na gaba cikin ɗan littafinsa, Deedat ya kwaso daga sharhin Yusuf Ali a kan wannan faɗin “Ya ’yar’uwar Haruna” inda ma fassara ya ke cewa, “An tuna wa Maryamu irin zaman tsarki da mutunci na mahaifinta da mahaifiyarta”. Matsalar a nan ita ce, Harunan da aka ambata kaɗai a cikin Kur’ani shi ne Firist na Lawiyawa, wanda shike ɗan’uwan Musa, wanda kuma ya yi rayuwa kusan shekara dubu biyu kafin zuwan Yesu! A bayyane, an faɗo Musa yana maganar Haaruuna akhi, ma’ana - “Haruna ɗan’uwana” – a cikin Kur’ani (Suratu Ɗ.H. 20:30). Saboda haka, ta yaya Maryamu mahaifiyar Yesu za ta zama ’yar’uwar Haruna da Musa kuma?
Cikin wannan al’amari, kuskuren Muhammadu ba za a ɗora shi a kan rubutun Afokirifa ba, kamar yadda batun Hannatu da Sama’ila yake. A wannan karon dukan ruɗamin a kansa yake, nasa ne. Lokacin rayuwarsa, Kirista sun tunkare shi dangane da wannan kwaɓen da yake yi, sai ya amsa da cewa, ai, mutanen dā su su ka riƙa ba mutanensa sunayen manzanni da masu ibada da suka rigaye su (wani littafi mai suna Sahih Muslim kundi 3, shafi na 1169). Yana da wuya a yarda da lauɗin irin wannan tunanin, tun da ma babu inda aka kira wani haka a cikin Kur’ani. Ba shakka, ba wuya an kira Haruna (Akha) ɗan’uwan Musa a cikin Kur’ani, kamar dai yadda haka ɗin yake, kai tsaye haka batun yake idan an kira Maryamu ’yar’uwarsa (Ukhta) a zaurance. A wani wuri a cikin Kur’ani kalman nan ukhtun (’yar’uwa) a koyaushe ta shafi ’yar’uwa wadda ake bi, ko wadda take biye, babu wani a tsakani (kamar yadda yake a Suratun Nisa 4:12,23,176), yadda kuma aka mori kalmar a game da Maryamu, tana nufin “’yar’uwar Haruna ta jini”. Da gaske, yana da wuya a bayyana cewa ma’anar ita an ba ta sunan kakanta Haruna kamar yadda aka ce Muhammadu ya shawarta.
Ko ma da an yi niyyar karɓar wannan ma’ana, duk da haka da za mu fuskanci wahalolin gaske, domin za su kai mu ga gardama marar kāriya, marar tushe. A wancan zamani mutane suna ba ’ya’yansu maza da mata sunayen mutane daga zuriyarsu (amma ba na ’yan’uwa, wato ƙanne ko yayye maza da mata ba). (Yana nan kamar yadda yake a Matiyu 1:1 inda aka kira Yesu “ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim”, da kuma cikin Luke 1:15 inda aka kira Alisabatu ɗaya daga cikin “’ya’ya mata na Haruna”). Matsalar ita ce, Maryamu ba daga zuriyar Haruna ba ce, ko kusa!
Haruna dai firist ne na Lawiyawa, shi da ɗan’uwansa Musa daga zuriyar Lawi, ɗaya daga cikin ’ya’yan Yakubu. Wajen Maryamu kuma daga zuriyar Yahuza take, guda daga cikin ’ya’yan Yakubu, ta wurin layin Dawuda (Luka 1:32). Ba ma daga zuriya ɗaya take da Haruna ba. Dangantakar da ta haɗa su kaɗai ita ce zama al’umma ɗaya da tsabi’a ɗaya. Gaskiya ne, an kira Alisabatu “’yar’uwarta” a cikin Luka 1:36, amma in har akwai wata dangantakar aurayya a tsakanin kakanninsu, dole daga dangin Alisabatu ne. wani daga cikin kakanninta dole ya yi aure daga zuriyar Yahuza (wanda da wuya a yi mamaki, da shike bayan bautar talala a Asuriya da Babila, wannan kabilar ce ta kafa babbar ƙungiyar ringin Isra’ila da a ƙarshe suka komo zuwa ƙasar alkawari ta Falisɗinu). A gefe guda kuma bayyananne ne a cikin Littafi Mai Tsarki cewa, Yesu madawwamin babban firist ne bisa ga ka’idar Malkisadik, saboda haka, ba shi yiwuwa ya zama daga zuriyar Lawi ta wurin Haruna. Haka kuma mahaifiyarsa Maryamu, ba ta da jinin Lawiyawa, don haka ko kaɗan ba ta fito daga zuriyar Haruna ba, ko haɗa dangi da shi:
Gama da a ce kammala na samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama’a suka karɓi Shari’a) wace bukatar kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatankwacin ɗabi’ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatankwancin ɗabi’ar Haruna ba? Domin in an sauya matsayin firistoci, sai tilas a sauya Shari’a kuma. Domin kuwa shi wannan da aka faɗi waɗannan abubuwa game da shi, ai, na wata kabila ne dabam, wadda ba waninta da ya taɓa hidimar bagaden hadaya. Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba game da kabilan nan kan zancen firistoci. Wannan kuma ya ƙara fitowa fili sosai, sa’ad da wani firist dabam ya bayyana kamar Malkisadik, wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka’ida ta al’adar ’yan adam ba, sai dai ta ikon rai marar gushewa. Ibraniyawa 7:11-16.
Saboda haka babu wata tantama, Maryamu ba ta da wani mahaɗi da Haruna ko kaɗan, maƙamin kuma da aka ba ta a cikin Kur’ani ko kaɗan bai dace ba. To, ta yaya wannan kuskure ya taso? Dole mu juya cikin Littafi Mai Tsarki inda muke karanta cewa:
Sai Maryamu, annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki kuru cikin hannunta. Fitowa 15:20.
Macen nan da ake magana a kanta ainihin ’yar’uwar Haruna ce wadda ta yi rayuwa ƙarni masu yawa kafin mahaifiyar Yesu, don haka ruɗarwa ta taso ne saboda sunayen matan nan biyu abu ɗaya ne cikin Ibrananci, ana cewa Miriyam (da Larabci kuwa ana cewa Maryam).
Mun ga cewa ukhta cikin Kur’ani dole nufin ’yar’uwa-ta jini ce ta Haruna, alhali kuwa haka abin yake ga Miriyam. Ba shakka, Muhammadu ya ruɗe, ya gauraye Maryamu mahaifiyar Yesu da wannan macen. Bugu da ƙari, ƙaƙƙarfar shaidar wannan tana nan ga sunan da aka ba mahaifin Maryamu a cikin Kur’ani. A cikin Littafi Mai Tsarki muna karanta cewa, “Wanda ya auri Yokabed ’yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yakobed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, ’yar’uwarsu” (Littafi Ƙidaya 26:59). Saboda haka, mahaifin Haruna da Maryamu sunansa Amram - haka kuma sunan mahaifin Maryamu, mahaifiyar Yesu, a cikin Kur’ani! Ana kiran sa Imrana cikin Larabci daidai ke nan da Amram (Kamar yadda ake kiran Abram Ibrahim da Larabci). Maryama kuma, a bayyane ana kiran ta Maryamabnata Imrana – wato “Maryamu ’yar Imrana” – a cikin Kur’ani (Suratul Tahirim 66:12). Don haka, ba kiran ta ’yar’uwar Haruna kaɗai aka yi ba, amma kuma ’yar Imrana (Amram). Saboda haka muna da tabbaci har riɓi biyu na gaskiyar cewa an gauraye batunta da na Miriyam, ’yar’uwar gaske ta Haruna, kuma ’yar Amram.
Ba wuya kuma a yi tambaya cewa, don me aka kira Maryamu “’yar’uwar Haruna” a cikin Kur’ani idan ba a gauraye ta da Miriyam ba? Mun nuna cewa ko kaɗan ita ba daga zuriyarsa ba ce, ba su kuma haɗa dangi da shi ba baya ga haɗuwar kakannin farko, ba ko wani muhimmin mutum na Isra’ila. Haka kuma, wace dacewa ke cikin sunan ko muƙami? Don me ake kiran ta da Haruna a maimakon Musa, ko Iliya, ko Sulemanu, ko Yusufu, ko kuwa annabi? Ba rashin dacewar maƙami kaɗai za mu samu ba, sashin da aka ambata a nan sama daga littafin Ibraniyawa kuma ya bayyana a sarari cewa, yana akasi, mugun - nufi ne wanda kuma bai dace ba.
Saboda haka, Kur’ani ba gauraye Hannatun nan biyu kaɗai ya yi ba, amma har da Maryamun nan biyu kuma. Deedat ya sha raɗaɗin ƙoƙari a cikin ɗan littafinsa don ya nuna cewa labarin da Kur’ani ya ba da ya fi wanda ke cikin Littafi Mai Tsarki a kan rayuwar Maryamu, amma tun da ya ƙunshi shirme marar tushe kamar yadda muka riga muka duba su, ai, tabbatacce ne cewa labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki shi ne na ainihin gaskiyar.
A ƙarshe za mu bi ciki a taƙaice cikin batu uku a game da Maryamu waɗanda Deedat ya kawo. A wani shafi na ɗan littafinsa, ya ambato Suratu Al Imrana 3:42 inda ya kwaso abin da mala’iku suke faɗa wa Maryamu cewa “Allah ya zaɓe ki, kuma ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan matan talikai” Ya kuma yi sharfi haka: Wannan irin girmamawa ba za a samu an ba da ita ga Maryamu ba ko a cikin Littafi Mai Tsarki na Kirista! (Za a sami wannan cikin ɗan littafin Deedat, Christ in Islam p.8.)
Wannan batu ba shi da tushe ko kaɗan, don kuwa Littafi Mai Tsarki ya yi wannan batu a zahiri kamar yadda Kur’ani ya kofe cikin ayarsa lokacin da yake ambato Alisabatu sa’ad da take ce wa Maryamu:
“Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne!” (Luka 1:42).
A gaskiya, cikin ayan nan ne muka sami dalilin da ya sa Maryamu ta sami tagomashi gaba da dukan matan al’ummomi. Batun cewa an zaɓe ta haka a cikin Kur’ani duk da Littafi Mai Tsarki, ya nuna lalle an bayyana da ƙarfi cikin mahallin alkawarin cewa za ta haifi ɗa, ɗa mai tsarki Yesu, Masihin da ake ta jiran zuwansa (Suratu Al Imrana 3:45; da Luka 1:31-33). “Dan cikinki kuma mai albarka ne”, Alisabatu kuwa ta faɗi daidai. Maryamu ce mafi girma a cikin mata duka, an zaɓe ta sama da matan dukan al’ummomi, domin ta haifi mafi girma duka a cikin maza, zaɓaɓɓe sama da mutanen dukan al’ummomi a matsayin Mai Ceton duniya, Shi ne kuwa Yesu Almasihu.
Batu na biyu da Deedat ya gabatar wanda ya cancanci a duba shi, shi ne, akwai sura guda gaba ɗaya a cikin Kur’ani: Suratu Maryam 19 “an ba ta sunan don girmama Maryamu, mahaifiyar Yesu Almasihu (Phub)”, ana samun wannan a cikin ɗan littafin Deedat Mai suna Christ in Islam shafi na 11). Da zai fi masa kyau, idan da ya buɗa cewa, Maryamu ce kaɗai macen da a bayyane aka ambace ta da sunanta a cikin Kur’ani, da kuma a wasu lokatai da dama. Babu wata mace da aka faɗi sunanta kamar Maryamu. Muhammadu ya yi daidai da ya ba ta wannan martabar, amma ba shakka a sarari yake cewa, Maryamu ce kaɗai ta cancanci samun irin wannnan girmamawar domin kuwa ita ce mahaifiyar mutum mafi fice da aka taɓa yi, shi ne Yesu Almasihu.
A ƙarshe Deedat, a koyaushe yana neman laifi ga Littafi Mai Tsarki, yana sūkar muƙamin da Yesu ya kira mahaifiyarsa da shi, wato “Mace” lokacin da ya yi magana da ita a cikin Yahaya 2:4. Deedat yana nuna Yesu ya yi rashin ɗa’a” (Christ in Islam shafi na 19). Yana ba da shawara cewa, da ya fi kyau ya kira ta “Mama” (ko Iya).
Deedat kuma ya bayyana jahilcinsa a game da Littafi Mai Tsarki, da kuma lokacin da aka rubuta shi, domin a wancan zamani in an ce “mace” babban muƙamin girmamawa ne, kuma duk lokacin da Yesu yake magana da mata wannan kalmar ya ke mora. A wani sashi muna karanta yadda shugabannin Yahudawa suka nemi jajjefe wata mace da aka kama cikin zina, suka kuma tambayi Yesu ko wane hukunci zai yanke a game da wannan matsala. Ya amsa musu ya ce: “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse” (Yahaya 8:7). Bayan da dukansu sun sulale, a natse ya ce mata, “mace, ina suke? Ba wanda ya kāshe ki da shari’a” (Tsohon Juyi Yahaya 8:10). Da ta ce, “Babu, Ubangiji”, sai ya ce, “Ni ma ban kāshe ki ba: ki tafi, daga nan gaba kada ki ƙara yin zunubi” (Tsohon Juyi Yahaya 8:11). Sa’ad da cikin juyayi ya miƙa mata hannun jinƙai sai ya ce mata, “Mace”. Wannan ne “rashin hankali”? Wannan muƙami zallan girmamawa ne , kamar “Madame” cikin Faransanci, ko kuma “Dame” cikin Jinsin da ake kira Afrikaans.
Yesu kuma ya mori muƙamin nan lokacin da yake ta’azantar da macen nan ta Samariya (Yahaya 4:21), lokacin kuma da ya ke mutuwa a kan gicciye, ya kira mahaifiyarsa da wannan muƙami da ya ganta da ƙaunataccen almajirinsa Yahaya da yake a tsaye kusa da ita:
“Mace, ga ɗanki” (Tsohon Juyi Yahaya 19:26).
Sa’an nan ya ce wa Yahaya, “Ga uwarka!” (Tsohon Juyi Yahaya 19:27). Ko da shike yana fama da azabar gicciye, bai manta da mahaifiyarsa ba, ya danƙa ta ga shaƙiƙin almajirinsa, ɗaya daga cikin mazan da suka bi shi. Bayan ya tashi daga matattu ya mori muƙamin nan “mace” lokacin da yake magana da Maryama Magadaliya, almajirar da ta fi kurkusa da shi daga cikin matan da suka bi shi (Yahaya 20:15 Tsohon Juyi). Duk mai karanta labaran nan da gaskiya ba zai taɓa tunanin rashin ɗa’a ko rashin hankali a game da ambatar muƙamin nan ba, wato “mace”, amma muƙami ne na girmamawa.
A ƙarshe dai abin da kaɗai za mu ce shi ne, Deedat ya kwaɓe abubuwa cikin batun rayuwar Maryamu da muƙamin da aka ba ta a cikin Kur’ani da kuma Littafi Mai Tsarki. Akwai ’yar shakka cewa labarin Littafi Mai Tsarki a game da girmamawa, da sassalarta da kuma rayuwarta a ce Deedat ya ba da na gaskiya.
Deedat ya nuna ƙarancin saninsa a game da Littafi Mai Tsarki cikin maganganunsa a kan mahaifiyar Yesu, ba wannan kaɗai ba, amma rashin saninsa ya tabbata a fili cikin taƙaitaccen la’akarinsa ga muƙamin da aka ba Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki, muƙanin shi ne “Almasihu” (Kristi). Ya nuna cewa, ainihin Kalmar Ibrananci “masaha” (daga nan “Mashiah” ya fito, wato Masihi, ko Almasihu (Kristi) ba wata kalmar musamman ba ce, ta shafi kowace irin shafewa da mai, a kan more ta a kan firistoci, da ginshiƙai, da masujadai, da dai sauransu, waɗanda aka kēɓe domin sujada.
Gardamarsa ta nufi cewa, kiran Yesu da muƙamin Masihi a cikin Littafi Mai Tsarki, ko yadda ake kira da Hallenanci Christos, wannan bai sa Yesu ya zama na dabam ba ta kowace hanya, kamar dai yadda “kowane annabin Allah yake shafaffe ko naɗaɗɗe” (Christ in Islam p.13).
Ya ci gaba da nuna cewa, a cikin Islama an ba da wasu muƙamai ga wasu annabawa waɗanda suka shafi dukan annabawa. Ya ce, da aka kira Muhammadu Rasulullah (manzon Allah) Musa kuma Kalimullah (kalmar Allah), waɗannan muƙamai sun shafi dukan annabawa don kuwa kowanne manzon Allah ne wanda Allah ya riƙa magana da shi a kan kari. Ƙarshen batunsa shi ne, muƙamin nan Christos, wato Masihi ko Almasihu, ko kaɗan bai sa Yesu ya zama wani annabi na dabam ba, don haka Yesu bai bambanta da sauran manzannin Allah ba.
Jahilcinsa kuma ya ƙara bayyana a kan muƙamin da aka ba Yesu a cikin Littafin Mai Tsarki; ainihi (a cikin Hellenanci na asali) ho Christos, wato “Christin” (ko Masihin). Laƙanin shi Masihin ya sa ya bambanta da sauran, ya zama ainihin Shi, wannan ya nuna zahiri Yesu shi ne Masihin, Shafaffe na Allah, yadda babu wani annabi daga cikin annabawa da yake haka, sai Yesu kaɗai. Haka kuma abin ya nuna a cikin Kur’ani inda aka kira Yesu Al-Masih, wato Masihi, ko Almasihu, a kansa ne kaɗai aka mori wannan muƙami.
Ba shakka Deedat, ya ƙuduri ƙasƙantar da Yesu ya zama daidai da sauran annabawa, ta haka ya ƙi wannan muƙami Masihi (ko Kristi), ya zamar masa a hagungunce, kuma abin laifi. Duk da haka, gardamarsa ta kafu ne a kan zato na ƙara marar tushe mai nuna cewa muƙamin bai shafi Yesu ba da zai zama mabambanci.
Kur’ani ya kira Yesu Al-Masih daidai, amma bai yi ƙoƙarin bayyana muƙamin ba. To, me ke nan, ko ma’anar gaskiyar ke nan? A nan, mutum ba zai bukaci ƙoƙarin Kirista ba don ya canja “baƙin ƙarfe ya zama zinariya mai haske” (Christ in Islam, shafi na 13), kamar yadda Deedat yake begen shayi, ɗaukaka muƙaman Masihi gaba da na sauran annabawa. Domin Yahudawa ne suka yi maganar zuwan mai iƙirarin nan wanda suka ba suna Masihi bisa ga bayanin morar wannan muƙami cikin Littattafansu kamar yadda yake a cikin (Daniyel 9:26). Cikin dukanin Littattafan annabawan farko ana samun annabce-annabce a kai-a kai a game da zuwan shafaffen nan na Allah, wannan da ba annabi ne kawai ba, amma matuƙar Mai Ceto na dukan duniya. (Ga misalai: Ishaya 7:14; 9:6,7; 42:1-4; Irmiya 23:5,6; Mika 5:2-4; da kuma Zakariya 6:12,13). Zai kafa mulkin Allah har abada cikin gaskiya da adalci, zai kuma yi mulkin al’ummomi. Da fari za a ƙasƙantar da shi (Ishaya 53:1-12), za a datse shi daga ƙasar masu rai (Daniyel 9:26), amma a komowarsa a ƙarshen lokaci zai kawo ceto da hukuncin Allah, yana yin mulki da gaskiya da ɗaukaka a kan mabiyansa adalai, zai kawo maƙiyansa kuma daga ko’ina a duniya su zama matashin sawayensa (Zabura 110:1).
Yahudawa sun san cewa wannan ɗaukakakke, Masihi, yana zuwa, lokacin da ya zo kuwa sai suka yi ta wuswasi ko shi ne (Yahaya 7:31,41-43; 10:24; Matiyu 26:63). Sau da dama ya yi ta nunawa a sarari cewa shi ne Masihi (Yahaya 4:26; Matiyu 16:17; Markus14:62) Ya kuma faɗa wa Yahudawa cewa zai komo ta cikin gajimarai da iko da ɗaukaka mai girma, za su kuma gan shi zaune a hannun daman Allah (Matiyu 26:64). Wanda yake Kirista ba ya bukatar “Canje-Canjen maganganu” (Christ in Islam, shafi na 13) don ya ɗaukaka Yesu zuwa muƙaman madawwamin Mai Ceto da Masihi. Yahudawa da kansu sun san cewa Masihi ba zai zama mai “goge baƙin ƙarfe” don ya yi ƙyalli ba, amma ainihin “zinariya ne mai haske” wanda tabbatacce haka Yesu yake!
Abin takaici, Yahudawa sun ƙi Masihinsu, wanda yake cikar begensu, don haka nan da nan aka datse su (70 AD), har ya zuwa yau addininsu ya rasa dukan ma’ana da darajarsa na ainihi. Haka yake faruwa kuma a duniyar Musulmi wanda a gefe guda sun san cewa ba shakka Yesu Masihi ne, amma a gefe guda kuma suna iƙirarin cewa shi annabi ne kawai. Dukan ma’anar muƙamin ta ɓace gaba ɗaya a cikin Islama.
Yesu Almasihu shi ne makaɗaicin Mai Ceton duniya, mabambancin Masihi wanda Allah ya aiko domin warkar da al’ummomi. Muƙamin nasa ne shi kaɗai, an kuma ɗaukaka shi zuwa matsayin da sai shi kaɗai ne a kai daga cikin dukan mutane – Sarkin Ɗaukaka wanda zai yi mulki har abada abadin.
Nukurar Deedat gāba da Littafi Mai Tsarki na Kirista ta ƙara samun ƙaimi cikin maganarsa a kan ɗaukar ciki da haihuwar Yesu. Ya faɗo Luka 1:35 inda aka sami kalmomin mala’ika Jibra’ilu zuwa ga Maryamu inda ya ambaci cewa Ruhu Mai Tsarki zai “sauko” mata, kuma ikon maɗaukaki zai “lulluɓe” ta. Ya yi sharhi a kan waɗannan kalmomi:
Lafazin da aka mora a nan abin banƙyama ne – ruɓaɓɓen lafazin - Ko kun yarda! (Ɗan littafin Deedat Christ in Islam, shafi na 22)
A cikin ɗan littafin Deedat, kalmomin nan “ruɓaɓɓen lafazi” ya ƙarfafa su ta wurin ƙara ƙarfin alƙalami. Wani ya ce, “Kyau yana cikin idon mai dubawa”. Haka fa abin yake. Deedat yana ɗauka cewa akwai abin da ba kyau, marar tsarki a cikin labarin da ke a Littafi Mai Tsarki a game da ɗaukar cikin Yesu. Da nufi ne ya tsallake sauran abin da ke cikin ayar: “Saboda haka Mai Tsarki nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah” (Luka 1:35). Dukan ayar an dasa ta ckin girman mahallin tsarki ne. Domin wannan yaro an ɗauki cikinsa ba ta wurin tsakantar jiki marar tsarki ba, amma ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki, saboda haka yaron ba zai zama mara tsarki ba cike da zunubi kamar dukan sauran mutane, amma zai zama mai tsarki, har ma shi Ɗan Allah ne. Yadda wani zai ga cewa wannan ya zama abin banƙyama, to, abin ya wuce gaban ganewa. Kur’ani yana koyar da cewa dalilin ɗaukar cikin Yesu ta wurin ikon allahntaka kaɗai shi ne mabambancin tsarkinsa (Suratu Maryam 19:19). Waɗannan kalmomi sun shiga:
Ga masu tsabtar rai dukan abu da tsabta; amma ga waɗanda ke ƙazantattu da marasa bangaskiya babu abin da ke da tsabta; amma hankalinsu duk da lamirinsu sun ƙazantu (Tsohon Juyi Titus 1:15).
Cikin Bishara ta Luka sau da dama mutum zai karanta yadda Ruhu Mai Tsarki yake saukowa a kan mutane, kuma a kowane lokaci ya sauko yana nuna shafewa ta mallakinsa mai Tsarki. Saminu mutum “adali mai bautar Allah, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi” (Luka 2:25), lokacin da aka yi wa Yesu baftisma, Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa” (Luka 3:22). Haka kuma muka karanta cewa lokacin da ɗaukakar Allah ta bayyana a kan Yesu lokacin da kamaninsa ya sāke, “sai wani gajimare ya zo ya rufe su” (Luka 9:34). Ta yaya wani zai iya cewa, lokacin da aka yi irin wannan bayani a game da ɗaukar cikin Yesu (alal misali, cewa Ruhu Mai Tsarki “Ya sauko wa” Maryamu, kuma ikon Allah ya “lulluɓe” ta), sai a ce da wannan “abin banƙyama ne - ruɓaɓɓen lafazi”?
A sarari yake cewa kalmomin da aka mora domin bayyana yadda za a ɗauki cikin Amasihu, an mori irinsu cikin Littafi Mai Tsarki wajen bayyana al’amari inda ake ainihin shafewa ta iko da tsarki na Allah suke saukowa a kan mutum. A gaskiya, ba mu ga dalilin gardamar Deedat ba, sai dai kawai yana nuna irin ɓatancinsa gāba da bangaskiyar Kirista da zarge-zarge gāba da Kristanci. Ƙoƙarin Deedat na kwatanta labarun haihuwar Yesu da rashin daidaita, da labarun da ke cikin Kur’ani ya tabbatar da ƙoƙarin nasa na banza ne lokacin da ya ce:
Idan Allah zai halicci Yesu, ba tare da uba na jiki ba, Allah zai nufa kawai sai ya kasance. Idan Allah yana so ya halicci Yesu har miliyan guda ba tare da uba ko uwa na jiki ba, Allah zai nufa kurum sai su kasance. (Dan littafin Deedat, Christ in Islam, shafi na 24).
Wannan ya taso da tambaya – don me Allah bai halicci “miliyoyin Yesu ba, ba tare da ubanni ko uwaye na jiki ba”? Tabbacin gaskiyar ita ce mutum ɗaya da aka ɗauki cikinsa ta wannan hanya ya nuna cewa ba nufin Allah ba ne a ɗauki cikin mutane da dama ta wannan hanya ba tare da ubanni na jiki ba. A akasin wannan, a fayyace yake cewa wannan bayanin nufinsa cewa mutum guda ne mabambanci aka ƙaddara a haife shi ta wannan hanya. Wannan kuma yana nuna cewa akwai wani abu mabambanci ƙwarai a game da mutumin nan Yesu da aka ɗauki cikinsa ta wannan hanya. Dukan sauran mutane suna da ubanni da uwaye na jiki duk da annabawa. Akwai dalili guda kaɗai da ya sa Yesu ba shi da uba na jiki. Kasancewa Ɗan Uba Madawwami muhimmin abu ne a ɗauki cikinsa da kamannin ɗan Adam ta baƙuwar hanya, wato ba tare da hannun ɗan Adam ba, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki na Allah kaɗai. Tabbatace haka yake.
Deedat ya rewaito abin da ba zai taimake shi ba daga juyin Yusuf Ali na Kur’ani da kuma sharhinsa a kan Kur’ani daga Suratu Al Imrana 3:59 in da mai sharhin ya ke nuna cewa Adamu ba shi da uwa ko uba, don haka yana da babban ’yancin a kira shi Ɗan Allah (kamar yadda Deedat ya shawarta a cikin ɗan littafinsa mai suna Christ in Islam, shafi na 26). An halicci Adamu balagagge tun da babu iyaye na jiki da za su haife shi. Dole a halicci wani da fari. Amma an haifi Yesu ta wurin mace kaɗai a lokacin da ka’idar halitta ta riga ta fara aiki tun ƙarni da dama da suka gabata. Ba shakka akwai dalilin da ya sa Adamu ba shi da uba ko uwa, amma ina dalilin da ya sa Allah ya katse hanzarin ka’idar halitta/haihuwa don a iya haifar Yesu daga uwa kaɗai? Babu wata hanya dabam da ta bi bayan bayanin da aka ba da a cikin Littafi Mai Tsarki da za ta gwama Yesu da Adamu daidai:
Mutumin farko daga ƙasa yake, na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama yake. (I Korantiyawa 15:47).
Adamu mutum ne kawai wanda Allah ya busa numfashin rai. Yesu kuwa madawwamin mutum ne, ruhu mai – ba da rai, wanda ya zo daga sama, wanda kuma ɗaukar cikinsa dole ta katse hanzarin ka’idar haihuwa ta duniya, da zuriyar ɗan adam. Shi ne numfashin rai, waɗanda kuwa suka gaskata da shi su sami rai madawwami, za a kuma sāke su zuwa cikin kamanninsa basamaniye a nan gaba.
Mu ci gaba da la’akari da halayyar Deedat a game da yadda ya ke batun kamanni tsakanin Yesu da wanda ya riga shi zuwa, wato Malkisadik. Yana cewa Malkisadik “wani mutum ne wanda ya fi Yesu girma” (Ɗan littafin Deedat mai suna Christ in Islam shafi na 26), ya kuma faɗo Ibraniyawa 7:3 mai cewa Malkisadik ba shi da mahaifi, ba shi da mahaifiya ko zuriya, ba shi kuma da farkon kwanaki ko kwanakin ƙarshe na rayuwa. Bayan wannan bayani sai ya ci gaba da ƙarasawa da wasu ɗigo-ɗigo marasa ma’ana a cikin littafin nasa (Shafi na 26). Wannan ba sabon abu ba ne a cikin wasu ’yan littattafai da Deedat ya rubuta (dubi lamba ta 1 cikin wannan jerin, Gicciyen Almasihu: Gaskiya, ba almara ba) da kuma cikin wasu ’yan takardu da aka buga daga Cibiyar Farfagandar Islama. Ɗigo-ɗigon nan guda uku suna a madadin wasu kalmomi da Deedat ya tsallake da gangar, domin suna sūkar ainihin batun da ya ke ƙoƙari ya gabatar. Babbar magana! Za mu faɗi dukan abin da sashin ya ke faɗa daga Ibraniyawa. Za mu mayar da kalmomin da Deedat ya tsallake ya maye gurbinsu da ɗigo-ɗigo:
Shi wannan Malkisadik, Sarkin Urushalima, firistin Allah Maɗaukaki, ya gamu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim ke dawowa daga kisan sarakuna, ya sa masa albarka. Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma’anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa’an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato sarkin salama. Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haihuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, firist ne har abada (Ibraniyawa 7:1-3).
Sheɗara ta ƙarshe ta ayoyin nan, kalmomin sun doke ƙoƙarin Deedat a sarari inda ya ke cewa, Malkisadik “ya fi Yesu girma” domin suna nuna cewa shi kwatanci ne kawai na Ɗan Allah. Ta haka ne kaɗai ya zama wanda ya riga Yesu zuwa, kwatanci, kuma inuwa, da kuma taƙaitaccen misali na madawwamin Babban Firist da ya ke zuwa.
Batun da aka yi a cikin sashin nan da aka faɗo daga Ibraniyawa shi ne, Nassoshin ba su ƙunshi asalin Malkisadik ba, ba su ambaci mahaifinsa ko mahaifiyarsa ba, balle asalinsa, ba su kuma faɗa mana lokacin haihuwarsa da na mutuwarsa ba. An ambace shi sarkin Salem wanda ya tarbi Ibrahim da ya ke komowa daga kisan mutanen da suka kama ɗan ɗan’uwansa wato Lutu. An bayyana shi a sarari cewa shi “firist ne na Allah maɗaukaki” (Farawa 14:18), amma baya ga waɗannan ’yan matuni, ba inda aka ambace shi kuma.
Gardamar da ke cikin wasiƙa zuwa ga Ibraniyawa ita ce, Yesu ba firist na Lawiyawa bisa ga ka’idar Haruna ba ne, amma Madawwamin Babban Firist bisa ga ka’idar Malkisadik. Ana nufin cewa kamar yadda ba a ambaci farko da ƙarshen Malkisadik ba a cikin Littafi Mai Tsarki, ta haka ne kawai ya kwatanta Yesu wanda ainihi daga sama yake, madawwami ne shi, wanda a zahiri ba shi da mafari ko ƙarshe a ainihin ma’ana. Malkasadik kwatanci ne kawai – batun da Deedat cikin mugun wayo yake rikitarwa – kuma taƙaitaccen bayanin halin Malkisadik a matsayin firist na Allah, wanda Ibrahim ya bai wa ushiri misali ne na mai hidimar gaskiya na Allah da ya ke zuwa, wato Yesu Almasihu.
Sashin ƙarshe na ɗan littafin Deedat ya ƙunshi muguwar sūkar Deedat gāba da Rukunan Kirista da koyarwar Littafi Mai Tsarki mai cewa, Yesu Ɗan Allah ne. Amma duk da haka ya zamar masa dole ya yarda da a ƙalla batu guda cewa, “Shi mafificin Ɗan Allah ne” (Ɗan littafin Deedat mai sunan Christ in Islam shafi na 29). A shafi na 28 ya faɗo matanai da dama don ya nuna bayanin nan mai nuna “ɗan Allah” sau da dama ana samun su a cikin Littafi Mai Tsarki inda aka riƙa bayyana mutane gaba ɗaya a matsayin ’ya’yan Allah. Sai ya ƙarasa da cewa, lokacin da Yesu ya yi iƙirarin zama Ɗan Allah yana magana a zaurance, sai Kirista suka ɗauka cikin kuskure suka ce shi ne madawwamin Ɗan Allah.
Babu wanda zai yi irin wannan ƙarashen batu, sai dai idan ya ƙi yarda da ɗumbim shaidar da ke cikin Littafi Mai Tsarki mai nuna cewa babu wata tantama Yesu Ɗan Allah ne. Sau da dama ya sha yin magana da fayyace wannan batu a sarari. Yi la’akari da wannan aya:
“Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san kowanene Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san kowanene Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa” (Luka 10:22).
Kamar yadda Yahudawa suka taɓa shaidawa, “A’a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan” (Yahaya 7:46). Babu annabin da ya mori irin lafazin nan don ya bayyana kansa. Yesu ya faɗa, dukan abu an mallaka masa, ba kuwa wanda zai iya sanin Uban sai dai wanda Ɗan ya so ya bayyana wa. Ga kuma wani abin da aka faɗo mai nuna cewa Yesu ya ɗauki kansa Ɗan Allah ne babu wata tantama magana kamar sauran irin wannan duka Deedat ya kauce ma rubuta su a cikin ɗan littafinsa:
“Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan, domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan” (Yahaya 5:22,23).
Idan dukanmu ’ya’yan Allah ne, kamar yadda Deedat yake shayi (shafi na 29 cikin ɗan littafinsa), to, don me Yesu ya ce ya kamata dukan mutane su girmama shi a matsayinsa na Ɗan Allah har ma kamar yadda suke girmama Uban? Ba shakka, a cikin dukan Bisharu muna samun koyarwa da ke nuna mana cewa Yesu ya nuna kansa a shi ne mabambanci, madawwamin Ɗan Allah. Wani lokaci ya faɗa masu wani misali a kan mai garkar inabi, wanda ya dasa ta, ya danƙa wa masu sufuri don su yi hayar ta. Lokacin ɗibar ’ya’yan inabin ya yi, sai ya aiko da barorinsa don su sami ’ya’yan inabin amma suka wulakanta su bi da bi, suka kore su hannu – wofi, suka daddoki guda, ɗayan kuma suka ji masa rauni. Daga nan sai mai garkar ya ce wa kansa:
“Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa”(Luka 20:13)
Amma da masu sufurin garkar suka gan shi, nan take suka ƙi shi, suka jafar da shi a bayan garkar suka kashe shi. Sa’an nan Yesu ya ƙarasa maganarsa da cewa, mai garkar zai halakar da masu sufurin nan, ya kuma ba da garkar ga wasu. Nan da nan sai Yahudawa “sun lura a kansu ne ya ba da misalin” (Luke 20:19). Ganewarsu daidai ne, fassarar misalin kuma tabbataccen abu ne.
Allah ya yardar wa Yahudawa su zauna cikin ƙasar da ya ba su gādo, duk da haka sun yi ta yi masa tawaye. Ya aiko bayinsa annabawa amma su ma suka ƙi su, suka wulakanta su. A ƙarshe bayan da suka fitar da Yesu daga tsakiyarsu suka kashe shi, Allah kuma ya kawo halaka a kansu, aka tumɓuke su daga ƙasar Falisɗinu, Urushalima kuma ta zama kufai (wannan ya faru shekara arba’in bayanYesu ya hau zuwa sama, Titus wakilin Romawa ya aiwatar da wannan kisan).
Muhimmin batu a cikin misalin nan shi ne fayyace manzo na ƙarshe zuwa ga masu lura/sufurin garkan nan a matsayin ƙaunataccen ɗan mai garkan nan, ya sha dabam ainun daga manzanni na fari waɗanda borari ne kaɗai. A fili Yesu ya bambanta kansa daga annnabawan farko a cikin wannan misali, inda yake nuna cewa su barori/bayin Allah ne kawai, shi ne ƙaunataccen Ɗan. An ƙarfafa wannan a ƙalla sau biyu lokacin da Allah kansa ya yi magana daga sama inda ya yi magana a game da Yesu:
“Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai” (Matiyu 3:17).
A wani lokaci Yesu ya tambayi almajiransa ko mutane suna tsammani shi wanene. Suka amsa cewa, yawanci sun gaskata shi ɗaya ne daga cikin annabawa. Daga nan sai ya tambaye su wa suke tsammani shi ne, Bitrus kuwa ya amsa, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye” (Matiyu 16:16). Yesu kuwa ya amsa da cewa an yi wa Bitrus albarka ta masamman, don kuwa ba fahimin ɗan adam ne ya bayyana masa wannan ba, amma ta wurin wahayi daga sama. Yana da wuya a ƙarasa da gaskiya daga nazari na ainihi na koyarwarsa, cewa har kullum Yesu yana ɗaukar kansa a shi ne madawwami, mabambancin Ɗan Allah. Waɗannan kalmomi sun taƙaice koyarwarsa:
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami” (Yahaya 3:16).
Allah ya aiko da tilon Ɗansa, koyarwar da ake ta samu ke nan a cikin Littafi Mai Tsarki. (Bi cikin morar kalman nan “haifaffe” da kuma gardandamin Deedat a game da wannan, sai ka duba lamba ta 3 cikin wannan jeri, Tarihin Mahallin Kur’ani da na Littafi Mai Tsarki).
Waɗancan da suke ’ya’yan Allah a duniya, ’ya’yansa maza da mata sun zama haka ne domin Allah ya zama Ubansu, ya kuma zaɓi ya yi da su daidai da ’ya’yansa. Amma Yesu madawwamin Ɗansa ne, wanda ya zo daga gare shi zuwa cikin duniya domin wasu su zama ’ya’yan Allah. Dukanin bambancin da ke tsakanin Yesu da yake haƙƙun, madawwamin Allah, da Kirista da suka zama ’ya’yan Allah, an sa shi tattimin a cikin kalmomin nan:
“Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma ƙarƙashin Shari’a” (Galatiyawa 4:4).
Allah ya aiko da Ɗansa domin da yawa su sami tallafin ’ya’ya. Yesu ya koyar da wannan a sarari kuma, yana cewa, “Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni” (Yahaya 8:42). Wata aya kuwa ta fayyace wannan sarai:
Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya yă yanka mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa (Yahaya 3:17).
Yesu ne Makaɗaicin Ɗan daga wurin Uba (Yahaya 1:18) ya kuwa ɗauki kansa a haka yake cikin dukan koyarwarsa. Bai taɓa ɗaukar cewa ya zama ɗan Allah ta hanya guda cewa dukan masu bi ’ya’yan Allah ne ba. Da ya ke magana a kan ranar komowarsa sai ya ce ba wanda ya san ranar, “Ko mala’iku da ke sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai” (Matiyu 24:36). A nan akwai fayyataccen ci gaban iko, mutane da mala’iku, Ɗa da Uba. A sarari yake sarai, Yesu yana magana a kan kansa cikin wannan mahalli kaɗai – gaba da mala’iku a matsayinsa na makaɗaicin Ɗan na madawwamin Uba. Ya bayyana muƙamansa yadda suka danganci kasancewarsa ta Allahntaka kaɗai.
Deedat ya ci gaba da magana a game da faɗin Yesu, “Ni da Uba ɗaya muke” (Yahaya 10:30) yana cewa mahallin ya nuna cewa wannan ba ana nufin cewa Yesu da Ubansa ɗaya suke ba cikin sanin abu dukka, da cikin hali ko zama mai iko dukka, amma “ɗaya cikin manufa” (Ɗan littafin Deedat mai suna Christ in Islam, shafi na 37). Don ya sa faɗin cikin mahalli sai ya faɗo aya ta 27-29 gabaninta, ya kuma ce:
Ta yaya mutum zai makance da ba zai ga daidaicin ƙarshen ayoyi biyu na ƙarshe ba. Amma maƙiftan ruhaniya sun fi rikitarwa fiye da naƙasassun na jiki (Christ in Islam shafi na 37).
Mutum zai yi mamaki a kan ko ina ne makamtar take a zahiri, kuma wanene idanun ruhaniyarsa maƙiftan suka hana shi gani, domin Deedat a hankali yana rufe muhimmin batun da Yesu ya yi a cikin ɗaya daga ainihin ayoyin da yake nufi inda Yesu ya ke magana a game da waɗannan da suke masu binsa na gaskiya:
Ina ba su rai madawwami”. (Yahaya 10:28).
Allah ne kaɗai ya ke ba da rai, ba rai kaɗai ba, amma rai madawwami. Ya kamata mutum ya riƙa karanta irin maganan nan ba daga rabin mahalli ba amma dukan mahallin koyarwar Yesu a game da kansa. A wani lokaci ya ce:
“Yadda Uba ke ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma ke rayar da wanda ya nufa” (Yahaya 5:21).
Wannan magana tana nuna cewa, tabbatacce ne Ɗan yana da dukkan iko irin na Uban. A ƙarshen aikin Yesu a duniya ya sāke yin maganar Uban ya ba shi “iko a kan dukkan ’yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi” (Yahaya 17:2). Magana mai cewa, “Ni da Uba ɗaya muke” (Yahaya 10:30) wadda Yesu ya faɗa, ita ce wadda bai yi ƙoƙarin ya cancance ta ba, ba ta kuma hana wani mai fassara ya hana ma’anarta ga “wanda ake nufi” ba. Daga gani a waje, a sarari yake cewa tana nufin “wanda yake cikin dukkan abu” Yesu kuwa ba zai yi irin wannan i’kirari ba idan bai cancanci yin sa ba, idan bai yi niyyar nuna cewa akwai tabbataccen ɗayanci ba a tsakanin Uban da Ɗan, kuma saboda haka ne yake da allahntaka. Ashe ba mamaki da Yahudawa suka gane da iƙirarin nasa (Yahaya 10:33).
Bugu da ƙari kuma, abin mamaki ne a ga cewa Deedat ya sa wasu kalmomi da manyan harufai a cikin ayoyin da aka ambata a baya, wato inda Yesu ya yi magana mai cewa, babu mai iya fizge masu binsa daga hannunsa, ko daga hannun Ubansa. Yaya Yesu zai yi irin wannan iƙirari in ba yana da irin ikon da Uban yake da shi ba, na tsare masu binsa? Tabbatacce a sarari yake, ga waɗanda zato bai makamtar da idanunsu ba gāba da koyarwar Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki cewa Yesu bai yi iƙirarin cewa shi da Uba ɗaya suke a cikin manufa kaɗai ba, amma kuma a cikin mallakar cikakken madawwamin ikon da ake bukatar zartas da wannan manufa ta kammala aikinta.
Babbar matsalar Deedat ita ce, kasancewarsa Musulmi, yakan fuskanci Littafi Mai Tsarki da zaton cewa Yesu ba madawwamin Ɗan Allah ba ne, don haka ba zai taɓa yin irin iƙirarin nan ba. Saboda haka Deedat ba zai iya karanta Littafi Mai Tsarki da zuciya ɗaya ba ya kuma fassara shi dai dai bi da bi. Duk lokacin da ya haɗu da wasu batu da suke nunawa a sarari cewa Yesu ya yi iƙirarin zama Ɗan Allah, Deedat sam ba zai iya yarda da haka ba. Zace- zacensa sukan tilasta shi ya kau da kai ya ƙi kulawa da su ko kuwa ya fassara su a karkace lokacin da ya ga sun gagare shi.
Wajen ƙarshen ɗan littafinsa ya ambaci al’amari biyu a cikin rayuwar Yesu waɗanda suka tabbatar da wannan batu daidai. Ya sami wani wuri inda Yesu ya koyar da cewa, don mutum ya shiga rai madawwami dole ya kiyaye dokokin Allah (Matiyu 19:17) ya kuwa dāge ƙwarai a kan wannan don wannan irin koyarwar kamar ta zo daidai da irin ta Islama. Duk da haka, a nan ya fāɗa cikin tarkon da yake kauce wa a wasu wurare cikin ɗan littafinsa ta wurin ɗaukar wasu batutuwa ba daga cikin mahallinsu ba. Abin da ya biyo baya bai shiga daidai da gardamarsa ba don haka sai ya ƙi komawa ta kansa. Yesu ya ci gaba da nuna wa saurayin da yake magana da shi cewa, ba mai iya kiyaye dukan dokokin Allah daidai har ya iya shiga rai ta wannan hanya. Matashin mai arziki ne ƙwarai, sai Yesu ya ce masa:
“In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni” (Matiyu 19:21).
Zai yiwu ya zama gaskiya ne a yau cewa “babu wanda yake cikakke” sai Allah kaɗai, kuma zai shar’anta mu ta wurin ma’aunansa na kammala. Taƙaitaccen ƙoƙari na kiyaye dokokinsa ba zai karɓa ba, kuma wanene zai iya kiyaye su cikakku? Lokacin da Yesu ya sa matashin nan ya gane cewa lalle ba zai iya ba, sai ya nuna masa wata hanyar samun rai: In za ka zama cikakke ... ka biyo ni.
Karo na biyu ya shafi batun tashin Li’azaru daga matattu. Saboda Yesu ya nisa a cikin ruhunsa, sai ya yi addu’a ga Ubansa a game da wannan al’amari. Sai Deedat ya ƙarasa da cewa, Yesu ba zai iya zama madawwamin Ɗan Allah ba. Duk da haka, a nan ma ya ƙarasa da kauce wa mahallin wannan addu’a, cikin dabara sai ya kauda kai daga muhimmin iƙirarin da Yesu ya yi a ainihin wannan lokaci na aikin al’ajabin banmamaki da aka yi:
“Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu” (Yahaya 11:25).
Kalmomi a cikin ainihin Hellenanci suna gabatar da wannan batu suna da ƙarfi ainun, ma’anarsu, “Ni, Ni ne tashin matattu da kuma rai”, ko “Ni kaina ne tashin matattu da kuma rai”. Ana nufin cewa Yesu kansa, cikin mabambancin kasancewa kuma cikakke, shi ne tashin matattu da kuma rai. Ba mamaki da aka kira shi “Tushen Rai” (Ayyukan Manzanni 3:15) a cikin Littafi Mai Tsarki. Babu mahalukin da zai iya yin wannan iƙirari in ba wanda yake madawwami ba. Mai allahntaka kaɗai zai iya yin irin wannan magana.
Babban kuskuren da Deedat yakan yi a lokacin da ya karanta Littafi Mai Tsarki shi ne, ba ya ƙoƙarin gane gaskiyar abin da ya karanta, amma sai ya ɗauki zace- zacen zuciyarsa kawai. Kirista kuwa suna karanta Littafi Mai Tsarki da gaske, da muradin sanin abin da Yesu ya ce a kan kansa, kuma cikin dukan tarihi a duniya duka sukan kammala da cewa Yesu ya koyar cewa shi ne madawwamin Ɗan Allah wanda ya zo cikin kamannin mutum domin ya fanshi duniya. Wannan tsucewar da suka samu ce daga tamanin da ke ƙunshe cikin littattafan da su ke karantawa. Amma wasu mutane kamar Deedat, tun kafin su ɗauki Littafi Mai Tsarki su karanta, sun riga sun yanke shawara a kan abin da zai ce a game da Yesu. Domin ya gaskata cewa Yesu annabi ne kaɗai, ba Ɗan Allah ba, sai su fuskanci Littafi Mai Tsarki da zato kurum cewa zai goyi bayan wannan gaskatawa, duk kuma lokacin da iya zai yi ƙoƙarin ɓatarwa ko ya karkatar da koyarwar don ya samar da zatonsa.
Ta haka ne Deedat ya zama wanda bai cancanci isa ya fassara Littafi Mai Tsarki ba sam. Ta yaya za a ce Ikilisiyar Kirista a duniya gaba ɗaya ta yarda cewa Yesu madawwamin Ɗan Allah ne idan da Littafi Mai Tsarki bai koyar da wannan ba? Ƙoƙarin Deedat na ƙaryata wannan bai taso daga kintata gaskiyar koyarwar Littafi Mai Tsarki ba, amma daga zato ne kawai cewa ba zai iya samar da irin wannan rukunai ba. A sarari yake ga mai karanta littafi da “ido a buɗe”. Mai farfagandar Islama ne wanda iyawarsa ta karanta Littafi Mai Tsarki da gaskiya, kuma da nufin gane gaskiya zatonsa ya makantar da idonsa da cewa bai kamata a koyar da cewa Yesu Ɗan Allah ne ba.
A ƙarshe muna iya cewa kawai Deedat ya fallashi kansa cikin rashin tabbas a lokacin da ya yi ƙoƙarin bayyana Yahaya 1:1 ta hanyar ilimin zatonsa a shafi na 40,41 na ɗan littafinsa. Dukan ayar tana cewa:
“Tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne” (Yahaya 1:1).
Deedat yana cewa Kalman nan Allah a cikin Hellenanci a sashi na fari “Kalman nan kuwa tare da Allah yake”, sashi na biyu kuma ya ce, “Kalman nan kuwa Allah ne”. ya bambanta Allah a shashi na fari da Allah a sashi na biyu a cikin ayar. Yana danganta tattaunawarsa tsakanin shi da kansa da Rev. Morris a inda a cikin ƙuƙumin saninsa na harshen Hellenanci ya ƙure Rev. Morris gaba ɗaya. Abin ya ba mu matuƙar mamaki, wanda ake zaton “Musulmi masanin Littafi Mai Tsarki” bai yi kome ba sai fallasa jahilcinsa a kan matanin Hellenanci. A sashin farko na ayan nan da Hellenanci an ce ton theos, a sashi na biyu kuwa aka ce Theos, duk ana nufin Allah ne. A kan wannan kuskuren ne Deedat ya kafe gardamarsa mai rinjayarwa a cikin ɗan littafinsa!
Yana cewa, saboda haka ton theos ana nufin “wani allah” don haka kuma ya ce Yahaya 1:1 yana koyar da cewa “Kalman nan kuwa wani allah ne”. Wannan yana musuntar allahntakar Yesu Almasihu ke nan. Hellenanci na ainihi cewa ya yi ho logos, shi ne “kalma”, Theos, shi ne “Allah”. Ayar ta faɗi daidai “Kalman nan kuwa Allah ne”, maganar da a fahimce tana tabbatar da allahntakar Almasihu. Ta haka ne gardandamin Deedat suka zuba ƙasa warwas ta wurin kuskurensa wanda ya yi da kansa, ta wurin jahilcinsa a game Littafi Mai Tsaki. ’Yan littattafansa gāba da bangaskiya Kirista a kai – a kai suke bayyana matuƙa biyu – na ƙarfin halin amincewarsa cikin batutuwansa a gefe guda suka dace kaɗai ta wurin rashin wani tasiri a cikinsu a guda gefen!
Ba shakka shaida kaɗan kawai za a bukata don a nuna cewa, cancantar Deedat ’yar kaɗan ce da za ta iya sa shi zama “Musulmi masanin Littafi Mai Tsarki”. Gardandaminsa da irin amincewarsa za su iya sa Musulmin da ba su da sani, waɗanda suke da jahilcin Littafi Mai Tsarki su fāɗa cikin tunani cewa Deedat wani mashahurin sukar littafi ne, amma kamar yadda Yesu ya ce “Kada ku yi hukunci da zato” (Yahaya 7:24). Da shike wannan ya ba da amsa ga ɗan littafinsa Christ in Islam yana nuna cewa Kirista mai isasshen sanin Littafi Mai Tsarki zai iya ƙaryata gardandamin Deedat ba tare da wata wahala ba. Duban kurakuran da Deedat ya yi, da ɓata koyarwar Littafi Mai Tsarki da ya ke yi suna nunawa a ƙarshe cewa yaƙinsa gāba da Kristanci tabbatacce ne cewa, ƙoƙarinsa na fallasa Littafi Mai Tsarki, sai ya yi cikakkiyar nasarar fallasa kansa.
Cikin 1983 Cibiyar Farfagandar Islama ta wallafa wani ɗan littafi mai suna Allahn da bai Taɓa Kasancewa ba wanda aka fara wallafa shi a matsayin labari a cikin wata jarida ta Musulmi mai suna Al-Balaagh a 1980 don mai da martani ga amsar da na rubuta a kan wasu laccoci gāba da bangaskiyar Kirista da Ahmed Deedat ya gabartar a cikin kaset-kaset. Ɗan littafin ya ƙunshi ayoyi masu yawa daga Littafi Mai Tsarki, mafiya yawa daga Bisharu huɗu, dukansu kuwa sun danganta ga rayuwar Yesu a duniya ta shekara tatalin da uku cikin kamannin mutum. Kowacce daga ayoyin nan da ya ɗauko tana da suna wanda aka maye sunan Yesu da “Allah”, da kuma sharhin da aka yi a kan mutuntakarsa wadda aka sa ta zama abin ba’a ga gaskatawar Kirista cikin allahntakarsa. Marubucin wannan ɗan littafin ya kafa manufarsa cikin kalmomin nan:
A cikin kawunan maganarmu, da ƙananansu muna sa Yesu “Allah” a cikin ’yan shida da ’yan tara don mu nuna wawancin iƙirarin wannan mutum cewa Yesu Allah ne! (The God that Never Was wato Allahn da Bai Taɓa Kasancewa Ba, shafi na 2,3).
Zaɓen wasu sassa daga Bisharu da aka ɗauko aka sa cikin ɗan littafin nan, da kuma kanun maganar da aka sa a samansu yana nuna irin yadda marubucin ya fito muraran don yin ba’a ga allahntakar Almasihu:
Kakannin “Allah”: “Tsararrakin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim” (Matiyu 1:1). (shafi na 3 na ɗan littafin).
“Allah” yana da shekara Goma sha Biyu da Haihuwa Lokacin da Iyayensa suka tafi da shi Urushalima: “To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa. Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi bisa ga al’adarsu a lokacin Idi” (Luka 2:41,42) (shafi na 6 na ɗan littafin).
“Allah” dan Kabilar Yahudawa ne: “Zakin Kabilar Yahuza” (W. Yah 5:5) (shafi na 9)
Kamar yadda duk makarancin ɗan littafin nan zai iya gani, ayoyin da aka ɗauko duk sun danganta ne ga mutuntakar Yesu, da taƙaitacciyar rayuwarsa a duniya. Labarin dai ƙoƙari ne mai nuna cewa Yesu ba zai iya zama Allah ba saboda shi mutum ne, yana da dukan gajiyawa irin na ’yan adam (yana da kakanni, ɗan ƙasƙanci, hankalin tunani na ɗan adam, rashin ƙarfi na jiki, da sauransu).
Ba a ambaci sunan marubucin labarin ba a cikin ɗan littafin, amma an ce wani ne mai suna Mohammed Seepye cikin jaridar Al-Balaagh wadda ke ɗauke da labarin, inda da gangar ya rufe kuma bai kula ya bi ta kan rukunana Kirista na Tirniti (murhunniya) ba, amma a maimakon haka sai ya nuna gaskatawar Kirista cewa Yesu Allah ne, abin da ko kaɗan ba zai taɓa yiwuwa ba (wato ya kauce wa Uba da Ruhu Mai Tsarki, babu ma matsayin Yesu a shi Ɗan Allah ne). Ya san cewa lokacin da Kirista suka ce Yesu Allah ne wannan yana nufin cewa yana da rabo cikin halin allahntaka na Uban da kuma Ruhu Mai Tsarki a cikin Tirnity uku ciki ɗaya. (Ni ne na tsara wannan batu a hankali a cikin ainihin nassoshin da labarin jaridar ya ƙunsa daga amsa ga kaset na Deedat). Amma da wayo ya birkita rukunan Kirista, ya tsara shi ya zama kamar gaskata cewa, Allah ne Yesu, ba Yesu Allah ne ba, ya kuma kafa dukan gardamarsa a kan wannan zaton.
Daidai ne Musulmi suke iƙirari cewa Duniyar Yamma ba su fahimci Islama ba, kuma suna fassara a karkace. Gaskiya ne, amma kuma haka yake, Musulmi ma haka suke yi da gaskatawar Kirista a game da Yesu Almasihu, kuma dagangar suke karkatar da shi don ya dace da manufofinsu. Jigon rukunan Kirista shi ne, Yesu Ɗan mutum ne, kuma shi Ɗan Allah ne. Babu halacci ko kaɗan cikin kowace irin gardamar da ke gāba da allahntakar Yesu, gardamar da ta kahu a kan ɗaukar Yesu yana ckin gajiyawa irin ta ɗan adam kaɗai lokacin da yake a duniya. Zai zama canji abin karɓa idan aka gano rubuce-rubucen Musulmi a kan gaskatawar Kirista cikin Yesu a shi Ɗan Allah ne, sun kuma yi da gaskiya a kan rukunai daidai kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, ba a kan karkatacciyar fassara ba kamar yadda muke gani a cikin labarun Seepye da aka buga a jarida. Akwai wani sashi na Littafi Mai Tsarki da yake dukanin tsaikon wannan labarin jarida daidai-wadaida a fayyace:
Ku ɗauki halin Amasihu Yesu, wanda, ko da ya ke surar Allah yake, bai mai da daidaitakan nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba, sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam. Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye (Filibyawa 2:5-8).
Cikin harshen Hellenanaci, kalman nan “sura” a cikin nassin nan yana nuna ma’ana “ainihi”, wato Yesu na ainihin mafari ne. Ba kamar Adamu ba, mutum na fari, wanda ya so zama kamar Allah ta wurin ci daga itacen sanin nagarta da mugunta, Yesu kuwa ko da shike shi na allahntaka ne, ainihin ta Uba madawwami a cikin sama, bai mai da wannan ɗaukaka da yake da ita a can sama wani abu ba. A maimakon haka, cikin cikakken tawali’u sai ya zaɓi ya zama mutum, ta haka a kan sami “sura” (wato ya zama zahirin mutum). Kamar bisa ga halitta mutane bayi ne ga Allah, ta haka shi ya ɗauki “surar” bawa ko da shike bisa ga halitta shi ba bawan Allah ba ne. Maganar ita ce, da yardar kansa ya tuɓe ɗaukakar allahntaka saboda dalili guda, ya ɗauki surar mutum domin ya fanshi maza da mata, ta haka ya cike gāɓar dake tsakanin Allah da mutum wadda zunubi ya haddasa. Wannan ne tushen dalilin zuwansa a duniya cikin surar mutum.
Cikakken tawali’unsa da tausayin alherinsa ya kai shi ga zama fiye da Adamu nesa, kamar halittaccen bawan Allah. Ya zama mai biyayya har ga mutuwa, mutuwa ma ta gicciye. Daga kursiyin sama ya sauka domin a ɗaga zunubabbun mutane zuwa muƙamai na ’ya’yan Allah ta wurin aikinsa na fansa. A sakamakon shiga zurfafan taɓarɓarewar ɗan adam sai Allah ya ɗaukaka shi a saman sammai:
Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da ke birbishin kowane suna, domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa, kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba. (Filibiyawa 2:9-11).
A zamanu masu zuwa, a cikin madawwamiyar ɗaukakarsa wadda yake a ciki yanzu, dukan mutane da dukan mala’iku za su rusuna su kuma girmama shi, cikin yabo da mubaya’a ga muƙamansa na gaskiya.
Bisa ga hasken wannan batu cewa ya ɗauki surar ɗan adam, kuma da yardar ransa ya zaɓi ya zama ƙarƙashin dukan gazawa, da kumamancin ɗan adam (amma banda zunubi). Mutum zai iya gani hakika cewa babu wani aibu ga allahntakarsa saboda mutuntakarsa (haɗe da sassalar da ya zaɓi ya ɗauka, da ’yan ƙasanci da ya shiga, da zama irin na ɗan adam da ya ɗauka). A duk inda labarin jarida inda Seepye ya sa kan maganarsa “Allah”, ba tare da wahala ba mutum yana iya maye shi da Ɗan mutum ba tare da sa ’yan tara da ’yan shida ba, kuma suna/kan magana ya yi ma’ana mai kyau. (Na ce kusan a kowane wuri dagangar aka karkatar da ma’anar wasu ayoyin da aka kwaso).
Kirista ba su ce “Allah shi ne Almasihu ɗan Maryamu” ba kamar yadda Kur’ani yake zargin Kirista sun ce (Innallaaha huwal Masiihubnu Maryam 5:72). wato Allahn nan Yesu ne. Mun gaskata Allah ne Mafi Girma a cikin murhunniya, Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, kuma Ɗan ne kaɗai ya ɗauki surar mutum, shi ne Almasihu Yesu.
Mun gaskata Ɗan yana a ƙarƙashin ikon Uban (muƙaman da suka shafi ainihi da hali a tsakaninsu a gefe guda, gefe guda kuma zama a ƙarƙashin juna). Mun kuma gaskata cewa an aiko Ɗan cikin duniya bisa ga nufin Uban, kamar yadda Yesu kansa ya faɗi: “Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni” (Yahaya 8:42). Haka kuma mun yarda cewa bai yi kome domin kansa ba, amma abin da yake nufin Uban kaɗai ya ke yi, kuma domin shi madawwamin Ɗan Allah ne, yana da dukkan iko ya sa nasa nufin allahntaka da aikinsa su yiwu (Yahaya 5:19). Waɗannan ne jigon koyarwar Kirista.
Babban bambancin da ke tsakanin ra’ayoyin Kirista da na Musulmi a game da Almasihu ba a kan fahimtarsa ba ce a game da zamansa a ƙarƙashin iko na gaba da nasa, ko haƙƙaƙewarsu cewa shi mutum ne ta kowane hali lokacin da yake a duniya. Tare da Musulmi mun yarda cewa ya yi magana yadda aka umarce shi kaɗai (Yahaya 12:49) kuma akwai wanda ya fi shi girma (Yah.14:28). Da fari dai mun bambanta cikin gaskatawarmu a game da yadda yake, domin Islama ta yardar masa ya zama mutum kaɗai, kuma annabi kaɗai, Kristanci kuwa yana koyar da cewa Allah ya yi magana ta wurinsa, ba a matsayin annabi ba, amma a matsayin Ɗa, wanda ta wurinsa a ka yi dukan abu, wanda ya nuna ɗaukakarsa wanda kuma “yake ɗauke da ainihin hatimin kamanninsa” (Ibraniyawa 1:3).
’Yan littattafai kamar Allah da Bai Taɓa Kasancewa ba, wanda ke nuna Yesu cikin rukunan Kirista a matsayin shi Allah ne tattibin, ba tare da nuna matsayin Uba da Ruhu Mai Tsarki ba, ko zamansa a ƙarƙashin ikon Allah, wannan ya kauce wa manufa ko ma’anar Kristanci gaba ɗaya. Irin waɗannan ’yan littattafai ba su amfana wa manufar. Idan da Musulmi za su auna wannan rukunai a ainihin yadda yake, da za su ga bai yi nisa ƙwarai daga nasu ba kamar yadda suke zato, da zai yiwu kuma su kusato ga gaskiyar sanin kowane ne ainihin Yesu - ba “allahn” da “bai taɓa kasancewa” ba, amma madawwamin Ɗa daga sama, wanda ya tabbata “babu sā, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma” (Ibraniyawa 13:8).
In ka karanta ɗan littafin nan a hankali, za ka iya amsa tambayoyin nan, waɗanda suke sashi ne na Kososhinmu na Gida a game da Littafi Mai Tsarki:
Wanene Isuwa a cikin Littafi Mai Tsarki? Don me Yahudawa ba su raɗa wa ’ya’yansu sunan Isuwa?
Wacece Hannatu bakararriya da ta yi addu’ar roƙon ɗa aka kuwa amsa mata? Ina sunan ɗan da ta haifa?
Yaya za ka bayyana Kur’ani da ya ke kiran Maryamu mahaifiyar Yesu wai “’yar’uwar Haruna”?
Yaya Kur’ani yake girmama budurwa Maryamu, kuma me Sabon Alkawari/Linjila ke faɗi a game da ita?
Yaya za ka bayyana cewa Yesu “manzon Allah” ne?
Don me Yesu ne kaɗai budurwa ta haifa ba tare da uba na jiki ba?
Ina bambanci a tsakanin Adamu da Yesu?
Ta yaya Malkisadik ya zama kwatancin Almasihu da yake zuwa?
Yaya za ka bayyana cewa Yesu Ɗan Allah madawwami ne rayayye?
Don me Yesu ya ke kiran mu mu bi shi?
Ka bayyana: “tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne” (Yahaya 1:1).
Ta yaya Yesu yake mutum da gaske, kuma Allah da gaske a lokaci guda?
Ka rubuta amsoshin tambayoyin nan a wata takarda dabam, ba tare da wani sharhi ba. Idan ka amsa mafiya yawa da kyau, za mu aiko maka ɗaya daga cikin littattafanmu, domin ka ƙarfafa kanka cikin bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna.
P.O.Box 66
CH - 8486
Rikon
Switzerland