KO ALLAH YA BAYYANA CIKIN JIKI?

KO ALLAH YA BAYYANA CIKIN JIKI?

ISKANDER JADEED


BABI NA I

TAMBAYA:

Me kake nufi lokacin da ka ce Yesu Allah ne yake bayyana cikin jiki? Idan abin da ka gaskata ke nan, don me kasancewa cikin jiki ya zama wajibi?”

F. K. Tripoli, Lebanon

1. Abu na fari da za mu ɗaga a kai shi ne, ran ɗan Adam da kansa ba zai iya kaiwa ga matsayin kammalar da ake bukata ba domin dokar zunubi tana nan kamar abin sa tuntuɓe a kan hanyarsa.

Manzo Bulus ya bayyana mana wannan gaskiyar lokacin da ya ce, “Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin dake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu. Nagarin abin da nake niyya kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa. To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yin sa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne. Sai na ga, ashe, ya zamar mini ka’ida, in na so yin abin da ke daidai, sai in ga mugunta tare da ni. Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da Shari’ar Allah. Amma ina ganin wata ka’ida dabam a gaɓoɓina, wadda ke yaƙi da ka’idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ka’idan nan ta zunubi, wadda ke zaune a gaɓoɓina” (Romawa 7:18-23).

2. A nan, maganar manzo ta misalta sāɓanin dake cikin ran ɗan Adam tsakanin alheri da lalacewa, tsakanin shari’ar Allah wadda mutum yake farin ciki, wadda kuma yake so ya kamantu da ita, da kuma dokar zunubi mai neman ta bautar da mutum, ta kuma tilasta shi ya yi abin da ba ya son yi, duk da haka, manzo, ya matsu da ya kuɓutar da kansa daga dokar zunubi da mutuwa, sai ya yi sanannen kukan nan nasa zuwa sama: “Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan wanda ke kai ni ga mutuwa?” (Romawa 7:24). Da ya ɗan gimtsi ganin Mai Fansa na Kalman nan cikin jiki sai ya yi murna yana cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu!” (Romawa 7:25).

An riga an buɗe asirin nan ga mutumin Allahn nan, Ayuba lokacin da ya ci gaba da fama da shan azaba. A tsakiyar babbar bukatarsa ta matsakanci tsakaninsa da Allah, sai ya bayyana kukansa haka: “Amma ga shi, ba wanda zai shiga tsakaninmu, ba wanda zai shar’anta tsakanina da Allah. Ka daina hukunta ni, ya Allah! Ka daina razanar da ni. Ba ni jin tsoro, zan yi magana, domin na san zuciyata” (Ayuba 9:33-35). Daga nan ɓangare na biyu na Allah (Ko mutum daga cikin Kai na Allah, da Larabci shi ne: UKNUM) ya ɗauki siffar jikin ɗan Adam. Ya biya matsananciyar bukatar fansa, a maido shi, ya kuma sulhunta shi da Allahnsa.

3. Kowane mutum daga abin da ya saba da shi ya san cewa, akwai niyyar lalaci a cikinsa, wadda ya ba da wuya cikin baƙin ciki. Mu tuno da faɗar manzo: “Gama ’yan Adam duka sun yi zunubi, sun kāsa kuma ga ɗaukakar Allah” (Romawa 3:23), da kuma cewa “In mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta tare da mu” (1 Yahaya 1:8). Islama ta yarda da wannan gaskiyar, kamar yadda aka ce cikin Kur’ani: “Kuma da Allah yana kama mutane da zaluncinsu, da bai bar wata dabba ba a kan ƙasa” (Suratun Nahl 16:61). Saboda haka ya zama tabbas a gare mu, ba cikin tarihi kaɗai ba, amma har a hankalce ɗan Adam ba zai iya kaiwa a matsayin ruhaniya da ake so ya kai ba, in ba a haɗe da wani da ya fi shi iko ya bi da shi ba, wato ikon da ya fi shi.

4. Don haka, mun tsaida nazarinmu a kan fayyace kāsawar mutum da fāɗuwarsa daga kaiwa ga matsayin da Adamu ya sha daɗinsa kafin shi ma ya fāɗi. Tsayawa a nan kaɗai ya zama daidai da fāɗuwa, ko an yi nasara da mu. Ba za mu iya shayin cewa irin wannan abin takaici zai aikata manufar Allah Mai Iko Dukka. A akasin wannan, Ubangiji Allah nagari ne, jiye-jiyenƙansa kuma madawwama ne. Allah cikin nagarinsa ba zai bar mutum, wanda ya halitta cikin Kamanninsa, cikin taɓarɓarewa ba, wadda mutum ya shiga ita ta kai shi ga hallaka. Tun da mutum ya kāsa cika nufin Allah, sai Allah ya ƙaddara wani mahaluki don ya maida mutum cikakke. Wanene wannan mahalukin? Ko shi taliki ne mai cikakken tsarki? Ko Allah ne Kansa?

5. Bari mu yi ƙoƙari mu dāge a hanyar dake daidai, kada a janye hankalinmu ta wurin dabarun kanmu, ko da shike suna kan wasu ka’idodi ne da suke kafe a kan wasu addinai. Dalilin wannan kuwa shi ne domin sabawa da irin ra’ayoyin nan ba shakka zai sa a kauce wa hanyar gaskiya. Bari kuma mu tuna da abu guda, shi ne kuwa cewa babu wani addini da zai musunci cewa mutum ya karkace daga zumunta da Allah. Ga Allah mutane suke yin addu’a, daga gare Shi suke neman taimako da bishewa. Hakika, yana taimako, yana kuma bi da ƙafafun masu ba da gaskiya gare Shi cikin hanyoyin salama; bugu da ƙari, dukanmu mun gane cewa manufar dake bayan alamomi, waɗanda wasu lokatai aka maida kamar asirai, cikakkiyar haɗewa ce ta ran ɗan Adam da Allah. Mutumin Allah, mai suna Augustine, wani masani, cikin addu’arsa ya ce: “Ya Ubangiji! Kai ka halicce mu domin kanka, rayukanmu ba su hutawa har sai sun sami hutawa cikanka.”

Saboda haka, babu dalilin da zai sa mu yi tunanin cewa, akwai wani halittaccen matsakanci dake a tsakanin Allah da mutum, ko da an zubo masa fifiko a kan mutum. A ƙashin gaskiya, akwai tulin tabbas a game da akasin wannan. Idan talikai za su iya kaiwa ga kammala wadda Allah ya so su kai, idan kuma za a fanshi mutum, ya zama wajibi a cika wannan ta wurin ainihin aikin Allah, wanda yabo da ɗaukaka sun tabbata a gare Shi har abada.

Don a kai ga maƙasudin wannan manufa, an ƙaddara cewa Allah zai ƙunshi abu ko mutum uku (Larabci: AKANIM), domin a cika zamansa mutum ta wurin zaɓin guda, ba wani dabam ba. Wannan abin da Allah ya so ne: cewa, Ubangiji zai fanshi al’ummarmu da ta fāɗi cikin zunubi, ta zama ba bege, ko taimako in banda daga Allah cikin mutum, domin Shi kaɗai yake da ikon da ya isa domin yin ceto. Abin bukata domin zama cikin mutum a gabam Allah, shi ne, ɗaya daga cikin abu ukun nan na Allah (Larabci: UKNUM) ya ɗauki jikin ɗan Adam.

Ko kaɗan, ba ina ƙoƙarin amsa tambayan nan ba ne a nan mai cewa: “Ko Allah bai iya ceton fāɗaɗɗen mutum ba sai ta wurin zama cikin jikin ɗan Adam kawai?” Amma ina ƙarfafa ko tabbatarwa cikin hasken maganar Allah, cewa zama cikin jiki da Allah ya yi ita ce hanyar da ya ga ta fi dacewa, ba shakka ta dace, kuma mabambanciya cikin hikima domin cika bukatar manufar. Gaskiya ita ce, zama cikin jiki ta faru domin ita ce ta zama jazaman don cikar nufin Allah cikakke cikin aikin fansa; kuma matsayin fāɗaɗɗen ɗan Adam yana bukatar wannan.

6. Wani batu kuma da ya zama dole in ambata shi ne, cewa, Allah wanda ɗaukaka ta tabbata a gare shi, yana son ya kawo talikansa su kai ga matsayin da ya ke so, zai bi ta wata hanya ya haɗa su da shi Kansa; zai yi wannan ba ta wurin umarnin allahntaka daga waje ba, kamar cewa, “Bari ya kasance, ya kuwa kasance,” amma wannan ta wurin zamansa cikin mafificin halittarsa ne, ko mu ce, ta wurin bayyana Kansa cikin Kamannin cikakken mutum.

7. In mun yi la’akari da koyarwa a kan fansa da ke cikin maganar Allah, za mu ga cewa matsakanci tsakanin Allah da ’yan Adam dole ya kasance da waɗannan halayya:

(a) Dole ya zama mutum, Manzo ya bayyana cewa dalilin da ya sa ɗaya daga cikin ukkun nan na Allah (Larabci: UKNUM) ya ɗauki siffar mutane a maimakon ta mala’iku, shi ne, don ya zo ne domin ya fanshe mu. Ya zama wajibi a haife shi a ƙarƙashin dokar da muka karya domin a cika dukan adalci, yadda zai sha wuya ya kuma mutu a matsayin hadaya don biyan fansar zunubanmu, don ya ɗauki rayuwarmu ta ’yan Adam don ya sha irin kumamancinmu (Ibraniyawa 2:14).

(b) Dole ya zama marar zunubi. Hadayar da aka riƙa miƙawa a kan bagade dole ta zama marar aibi bisa ga doka. Wato ba zai yiwu ba mai ceto daga zunubi ya zama shi kansa mai zunubi ne, don ba zai sami isa ga Allah ba; ba kuwa zai iya zama sassalar tsarki da rai madawwami ga mutanensa ba, da shike shi kansa ba adali ko mai tsarki ba ne. Saboda haka, ya zama wajibi ga Babban Firist namu ya zama mai tsarki, salihi, marar aibu, rababbe daga zunubi (Ibr. 7:26).

(c) Dole ya zama Allah, domin babu abin da zai iya kawar da zunubi sai dai jinin shi wanda yake mafi girma a kan wanda yake taliki kawai. Saboda haka, Almasihu, da shike Allah, ta wurin miƙa kansa haɗaya sau ɗaya tak domin dukka, ya kammala har abada waɗannan da suka tsarkaka (Ibr. 7:27 da 10:14). Haka kuma sai mai ikon allahntaka kaɗai zai iya lalatar da ikon Shaiɗan, ya ceci waɗanda ke cikin ƙangin bautar Shaiɗan. Ba mai iya kammala babban aikin fansa, sai Shi da yake Mai Iko Dukka, Dukkan Hikima Dukkan Sani, don ya zama Babban Firist na Ikilisiyarsa da Alƙalin dukka. Ba wanda zai iya zama sassalar rayuwar ruhaniya domin fansassu, sai wannan da dukkan kammalar Allah take zaune cikinsa cikin jiki.

8. Dukan waɗannan inganci da Maganar Allah ta zayyana sun zama jazaman ga cancantar matsakanci don aikin matsakanci tsakanin Allah da ɗan Adam, duka sun haɗu cikin Almasihu bisa ga aikin da ya zo ya kammala.

Wannan yana gudana daga bukatar waɗannan halaye Cikin Almasihu domin tsakantarsa, wadda ta haɗa da duk abin da ya yi da wanda zai ci gaba da yi domin ceton ’yan Adam, aikin ikon allhantaka ne. Dukan ayyuka da shan wuyar Almasihu cikin aikata tsakantarsa sun zama ayyuka da shan wuya na ikon allahntaka. Shi wanda aka gicciye Ubangijin Ɗaukaka ne; wanda ya tsiyaye Kansa ga mutuwa, shi ne na biyu cikin uku ɗin Allah (Larabci: UKNUM).

Tabbacin Tarihi

9. Duba tarihi kaɗan zai nuna mana cewa, akwai mutumin da ya taɓa zama a fuskar duniyan nan wanda rayuwarsa ta zama fayyatacciyar shaida ce ta abubuwan da ɗan Adam ya ƙunsa; waɗannan abu biyu su ne zaunanniyar dangantaka da Allah da kuma ƙaunarsa marar kwatantuwa ga ’yan’uwansa mutane. Ya yi ta zagawa yana wa’azin albishir mai daɗi, yana warkar da marasa lafiya, yana yin ayyuka nagari, yana kuɓutar da waɗanda aljannu suka ɗaure. Ya bayyana wa ’yan Adam sabuwar manufa a game da Allah, cewar Allah yana kula da kowane mutum da guda-guda, kamar yadda uba yake kula da ’ya’yansa; Allah yana karɓar kowane mai zunubin da ya tuba kamar yadda uba ya karɓi ɓataccen ɗan da ya komo gida da tuba.

10. da ll: Ƙari a kan koyarwarsa a game da ƙauna, da ayyukan jinƙai da ya yi, ya kira almajiransa su kansance tare da shi, su koyi maganarsa, da samun ikon bin gurbinsa. Yau da gobe, almajiran nan suka ƙaru da sanin sa, suka yi zurfi cikin ganewa da hanyar tunaninsa, da fahimtar ma’anar misalansa. Sun ƙaru daga falalar Ruhunsa, sun koya daga amincewarsa da kuma zumuntarsa da Allah. Duniya kuwa ta girgiza don jin tsoron sa. Waɗanda suka ƙi gaskiya, suka dogara ga adalcin kansu, suka tayar masa, suka ja shi zuwa shari’a, suna zargin sa da yin sāɓo, da karya doka. Suka zartar masa da hukuncin kisa. Amma yaya ya ji da wannan? Bai yarda ya kāre kansa ba, don ya sani sarai yana da ikon ya yi umarni rundunar mayaƙa mala’iku su sauko su kame maƙiyansa. Ya zaɓi ba zai yi kowane abu da zai kuɓutar da kansa ba. Don ya yi shelar ma’anar ƙauna, ƙaunar Allah, sai ya ba da Kansa matuƙa. Saboda girman zunubi da muninsa a gaban Allah, ya kuma zama da nauyi a zukatan mutane, sai ya yarda hukuncin zunubi ya hau kan cikakken jikinsa na ɗan Adam, jikin da yake marar aibu ko cikas. Don dai ya yi nasara da mugunta, sai ya jure wa dukan wulakanci, har ya kai shi ga mutuwa, don haka ya sha duk irin gwagwarmayar da ’yan Adam suke sha, ya share hanya domin tabbatacciyar nasara. Ta haka ya zama mai nasara.

12. Ya tashi a rana ta uku. Ya riga ya faɗi cewa: “- - -Domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma. Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma” (Yahaya 10:17, 18). Ainihin abin da ya yi kuwa ke nan. Ya kammala aikin, wahayin allahntaka kuma ya kammala. Ya kwararo da matuƙar ƙauna, duk da ikon mugunta ya yi nasara da ita. Nasarar nagarta a kan mugunta ta tabbata.

13. Bayan wannan sai me? An lura da sakamakon wannan a cikin almajiransa, waɗanda suke da shaƙiƙin sani a game da shi. Wannan ya ɓullo lokacin da ya bayyana gare su bayan tashinsa daga matattu. A gare su Shi ba ɗan Adam kurum ba ne. Sun ga jauharin Allah a cikin sa. Ya yi iƙirarin abubuwan da suke sāɓo ga wasu. Kowane iƙirarin da ya yi, ya tabbata cikin gaskiya, duk da gaskiyar cewa ya cancanci su yi masa sujada, hakika kuma shi Allah ne yake rayuwa irin ta ɗan Adam, a lokaci guda kuma, yana mulkin dukan duniya daga kan Kursiyinsa a sama.

14. Ba almajiran kaɗai suka sami wannan sani ba, wato su da suka yi hulɗa da shi kaitsaye, amma sanin ya yaɗu da saurin gaske zuwa ga wasu mutane da yawa ainun, almajiran kuma suka yi shelar albishir mai daɗi ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda ya aiko a madadinsa.

Tabbacin cewa Yesu Banazare shi Allah ne da mutum kuma, bai shuɗe tare da mutuwar waɗannan da suka san shi cikin jiki ba. Don me? Domin bai danganta a kan kuskuren addini ko ka’idar addini ba, amma a kan sanin da Kirista kansu suke da shi shekara da shekaru, a kan kuma tabbacin cewa har yanzu Yesu yana da rai, yana kuma da dangantaka da dukan waɗanda suke biɗar sa. Wannan dangantaka ba ta zama hani tsakanin su da Allah ba amma a ainihi zumunta ce da Allah Kansa.

15. Wannan Mutum da yake Allah (Larabci:UKNUM), Yesu Almasihu, shi ba taliki ne marar hankali ko rashin kammala ba, amma ya cika dukan duniya; yana nan da can da ko’ina. Ya taɓa mutum ya ce, “Bi ni!” Mutumin ya tsorata ya ce: “Ya Ubangiji! Bautarka da wuya, mai nauyi kuma ba zan iya ba, ba kuma zan iya bin sawunka ba, ka bar ni, ya Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.” Yesu ya amsa masa ya ce: “Ka ba ni ranka, ka dogara gare ni, ka ba da gaskiya gare ni, gama alherina ya ishe ka.” Zai yiwu mutum ya amsa wa Kiransa ya zama almajiri. Har yanzu Almasihu yana a hanya yana kira: “Ku zo gare ni, dukanku da kuke fama da kaya mai nauyi, zan ba ku hutawa - - -Ku dube ni ku ƙarshen duniya ku sami ceto.” Da yawa sun ji Kiransa, sun kuma zo gare Shi alherin allahantakarsa ya jawo hankalinsu. Yana da farin jini a yau cikin baƙaƙe ’yan Afrika, inda ɗumbin mutane sun bi shi, sun kuma sami kuɓuta daga ikon miyagun ruhohi, da ƙangin masihirta, da matsibbata. Cikin kowace al’ummar ƙasa, da kabila, da jinsi akwai mutane waɗanda Yesu ya sāke su. Rayuwarsu ta yi dabam. Dā suna zama cikin zunubi, da muguwar sha’awa, da girmankai. Yanzu suna zama bisa ga Bishararsa, cikin adalci da tsarkin gaskiya. In ka tambaye su a game da tushen wannan canji, za su amsa cewa: “Dukan wannan ya samu ne ta wurin sanin Yesu Ubangijinmu”

Saboda haka muna iya faɗa da cikakkiyar amincewa cewa, Yesu Banazare ya naɗa aikin Allah cikin halitta, ya kuma ɗaga shi zuwa ƙolin duka na fifiko da kammala. Aikin nan ya kai ga cikakkiyar kammala cikinsa. Cikinsa rai da ruhu suka sami nufin Allah; kuma cikinsa, dukan waɗanda suka karɓe shi cikin ƙauna an kafa su, an kuma cika su zuwa ga cikar Allah. Wato ran da ya gaskata Shi ya kai ga babban maƙasudi na kasancewarsa, wato haɗuwa da Allah Kansa, da ɗaguwar halitta zuwa ga Allah Mahalicci.

16. Wannan ne hukuncin da tarihi ya yanke da kuma ƙarshen batunsa. A game da Yesu Almasihu kuwa, ma’anar “Kammalallen mutum” ba ainihin allahntakar dukan duniya kaɗai ba ne, ƙyallin ainihin allahntaka da kuma mahaɗi tsakanin Allah da halittarsa ne. Amma shi cikakke ne domin a lokaci guda shi Allah ne cikakke, “Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar allahntaka ke tabbata” (Kol. 2:9). Shi ba madubi ba ne kawai, mai sa wani abin allahntaka ya haskaka ta wurin rayuwar ɗan Adam ba ne, amma “Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗa tasa” (Ibraniyawa 1:3). Shi ne Kalma wanda yake tun farko tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne - - -ta wurinsa aka yi dukkan abu; in ba ta wurinsa ba, ba abin da aka yi (Yah. 1:1-3). Saboda haka ya cancanci karɓar dukan iko, mulki, hikima, ƙarfi, girma, ɗaukaka da yabo. Amin!

BA SHAKKA ASIRIN ADDININMU MUHIMMI NE ƘWARAI AN BAYYANA ALLAH DA JIKI (1 TIMOTI 3:16)

BABI NA II

TAMBAYA:

“Sanin kowa ne cewa, Allah ba ya bukatar duniya ko waɗannan da ke zama cikin ta; kowace dangantaka da yake da ita a game da talikansa ta taƙaice Shi, Shi da yake Mai Iko Dukka, an taƙaice shi ke nan a game da lokaci; da wuri saboda dangantakan nan; a sakamakon dangantakan nan an rage jauharinsa, wannan kuwa ya zama sāɓo. Saboda haka, ashe, zamansa cikin jiki kamar yadda Kristanci ya gaskata ba yana nufin sāke wa wani sashi na Allah wurin zama ba ke nan zuwa jikin Almasihu?”

A. S. Beirut, Lebanon

17. Zuwa ga mai tambaya, idan ka yi tsai, ka yi tunani za ka ga cewa, Islama wadda ka yi imani cikin ta, ta sa Allah cikin mahallin dangantaka da talikansa, haka yake kuma dangane da lokaci da kuma wuri. Ka gaskata cewa, Allah ya aiko manzonsa ga mutane. Wannnan yana nufin cewa, Allah ya kafa dangantaka ke nan da talikansa. Kur’ani ya ce: “Lalle ne Mu; Mun aika, zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda muka aika wani Manzo zuwa ga Fir’auna, sai Fir’auna ya sāɓa wa Manzon, saboda haka Muka kama shi, kamu mai tsanani” (Suratul Muzzammil 73:15, 16). Gaba da wannan kuma, Kur’ani ya gargaɗi mutumin da ya kafa dangantaka da Allah, mahaliccinsa, ya nuna cewa Allah yana ƙaunar haka, kamar yadda aka misalta cikin Suratu Al Imrana 3:159, wadda ta ce: “- - - Sa’an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, dogara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son masu tawakkali”.

Zai yiwu ka ja da cewa, irin wannan bayanin ai, na alama ne. Wannan yana iya zama yadda aka karanta fassara ne, amma a ainihi wannan hujja fāɗaɗɗiya ce a gaban batutuwan gaskiya. Akwai lokatai da dama irin wannan inda aka ambaci wasu mutane da Allah ya umarta da su yi wasu ayyuka, alal misali, bisa ga faɗar Kur’ani: “Lalle ne, hakika, Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: ‘Ya mutanena! Ku bauta wa Allah! Ba ku da wani abin bauta wa waninsa. Lalle ni ne, ina yi muku tsoron azabar wani yini mai girma.’ Mashawarta daga mutanensa suka ce: ‘Lalle ne mu, hakika, muna ganin ka a cikin ɓata bayyananniya.’ Ya ce, ‘Ya mutanena! Babu ɓata guda gare ni, kuma amma ni, Manzo ne daga Ubangijin halittu! Ina iyar muku da saƙonnin Ubangijina: Kuma ina yi muku nasiha, Kuma ina sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba.’” Irin waɗannan ayoyi ba za a ɗauke su a matsayin alamomi ba, domin suna magana ne a kan al’amura na zahiri.

18. Me za ka ce a game da hadisan annabci da suke magana a kan ka’idodin addu’a/salla da aka ɗora wa Musulmi? An ji Ibn Ishaka yana faɗar abin da ya ji Ibn Mas’ud ya ce manzon Allah (Muhammadu) yake faɗi cikin labarinsa na daren hawansa cikin samaniya: “A ƙarshe dai, sai Jibra’ilu ya kawo ni a gaban Ubangijina wanda ya ɗora mini yin salla sau hamsin kowace rana. Da ina komowa, sai ina wucewa ta kusa da Musa ɗan Imrana, aboki ne na ƙwarai! Ya tambaye ni, Salla sau nawa Ubangiji ya ɗora mini, sai na amsa masa cewa: ‘Sau hamsin kowace rana.’ Sai ya ce: ‘Sallolin suna da nauyi ainun, mutanenka kuwa ba su da ƙarfi; ka koma wurin Ubangijinka, ka roƙe Shi ya rage nauyin dake kanka, da a kan mutanenka.’ Sai na komo na roƙi Ubangijina don ya rage nauyin daga kaina da a kan mutanena, Ya rage mini goma. Na tafi, ina wucewa kusa da Musa, wanda ya sāke maimaita shawarar da ya fara ba ni. Na koma na roƙi Ubangijina, ya kuwa ƙara rage mini goma. Sai na komo, ina bi ta kusa da Musa, ya kuma sāke maimaita shawararsa a gare ni. Na koma, na roƙi Allah, ya kuwa ƙara rage mini goma. Musa ya yi ta maimaita shawararsa a gare ni duk lokacin da na komo ta wurinsa: ‘Ka koma ka roƙi Ubangijinka.’ A ƙarshe dai Ubangijina ya ɗauke mini nauyin, ya bar ni da guda biyar a kwana guda, dare da rana. A wannan lokaci, sai na amsa na ce: ‘Na roƙi Ubangijina sau da dama har ina jin kunyar Sa. Ba zan koma ba! Saboda haka, daga cikinku duk wanda ya yi sallolin nan ta wurin bangaskiya da aikatawa, zai sami ladan salloli hamsin’” (Labarin Annabi daga Iban Hisham 3:276).

19. Na bar ka da hadisan annabci kawai don ka tsaida tunaninka a kan hasken da hadisan suka ba da, wato a kan ko Allah yana da dangantaka da halittunsa, haka kuma ko su halittun suna da dangantaka da Shi. Bugu da ƙari, cikin bayyana ƙauna, bari in sa maka shi haka: In kana riƙe da gaskatawar “Cikakkiyar rashin dangantaka tsakanin mutum da Allah” (Larabci: TANZIH), to, ke nan kana ba da gaskiya ga Allah wanda ba ka san kome a game da shi ba, wanda kuma kake a rabe da shi gaba ɗaya. In kuwa haka ne, ya zama kana musuntar Annabci da Kur’ani ke nan. Ba za a kira mutum annabi ba, sai dai wanda aka hure, aka kuma aiko domin ya zo ya kafa dangantaka tsakanin Allah da halittunsa.

20. Wasu faɗi na hadisan annabci su na cewa: “Albarka da ɗaukaka su tabbata ga sunan Allah; kowane dare yakan sauko zuwa sama ta ƙasa duka, inda yakan kasance har kashi na uku na ƙarshen dare, yana kuma kira: ‘Ko akwai wanda ke yin addu’a gare ni zan kuwa amsa masa? Duk wanda yake roƙo na zan kuwa ba shi? Duk mai tuba a gabana zan gafarta masa’” (Bukhari 4:68).

Na gaskata cewa, “cikakkiyar rabe kome na mutum daga dangantaka da Allah” (Larabci TANZIH) wanda ya raba Allah ƙaƙaf daga talikansa, ya sa shi ya zama Allah da yake a ware (ɗaukaka ga sunansa). Wannan ya kai ga sāke wuri cikin al’amuran ruhaniya. Mutum ba zai iya tuba ya sami sabuwar haihuwa ba in yana a rabe can nesa da Allah. Ana sane sarai da cewa dukan ƙoƙarin da mutum zai yi don ya tashi daga matsayinsa na zunubi zuwa na adalci duk a banza ne idan mutum ba shi da wata hulɗa da Allah. Almasihu, cikin “Wa’azinsa a kan Dutse,” ya ce, “Wanene a cikinku, don damuwa tasa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwa tasa?” (Matiyu 6:27). Sai a yi la’akari cewa, “ɓalle kome na mutum daga Allah gaba ɗaya” (Larabci: TANZIH), yana zama kamar hani ga mutane da yawa ga hanyar karɓar manufar Allah cikin jiki. Saboda haka, mutanen nan sun hana wa kansu fa’idar fansa. Cikin kāriya ta hujjar ƙin koyarwar Allah Cikin jiki, suna ba da hujjoji da yawa na ƙi, sun haɗa da waɗannan:

21. Suna jayayya cewa, ra’ayin Allah cikin jiki yana nuna Allah ga canza matsayin Allahntakarsa a wani lokaci da wani wuri na musamman, ta haka suna auna Allah da ma’aunin tunani na rashin kammala. A gaskiya, a fakaice suna mai da Allah bai zama Mai Iko Dukka ba ke nan, ba shi kuma iya zama Allah cikin jiki ya kuma kasance ba tare da ya canza ainihinsa ba. Gaskiyar ita ce, zaman Allah cikin jiki bai zama dole sai ya canza cikin allahntakarsa ba.Tabbacinmu a game da wannan shi ne kashi na biyu cikin Allah ko cikin ukunin Allah (Larabci:UKNUM), lokacin da yake haɗe da ɗan Adam bai rasa ko yi hasarar Allahntakarsa ba, amma ya kasance a matsayinsa na Allah mai iko wanda ya tada matattu, ya warkar da makafi, da kutare, ya gafarta zunubai, ya kwantar da hadirin teku da umarninsa. Bishara Linjila tana gaya mana cewa ya bayyana cikin jiki ta ikon allahntaka, domin shi ne mahaliccin jikunan ’yan Adam, ba shi da wahala wajen haɗewa da su. Duk gaskatawa mai akasin wannan ta zama yarda da cewa mahaliccin jikuna da talikai ba Allah ba ne, wani abu ne dabam.

22. Muna da sanin cewa duk mutum mai hikima da hankali yana iya kintsa kansa ga kewayensa da kuma al’amuran dake tattare da shi. To, in ya zama haka ga mutum, ina ga Mai Dukkan Hikima, Allah Mai Iko Dukka, da zai iya zama cikin jiki ba tare da ya canza ainihinsa ba?Ka tuna da rana tana aiko da tsirkiyoyinta, da ɗuminta zuwa duniya, cikin kuma haɗuwa da wasu talikai a duniya, su ba su rai, da taimakon su su yi girma ba tare da sun yi wani kowane irin canji ya auku ga harhaɗuwar rana ba. Ko akwai ma’ana a ce rana tana da ikon haɗuwa da sauran abubuwa, tana rinjayar su ba tare da ita kanta ta lahantu ba, amma Allah da shike Mahaliccin rana da sauran abubuwannan ya rasa wannan iko?

Ka gaskata cewa Allah ne ya halicci mutum na fari daga “laka, kamar maginin tukwane” (Suratur Rahman 55:14). Wannan ya nuna cewa Allah ya tsaya a iyakancin lokaci domin kuma ya riƙe yumɓu da hannunsa a ƙayyadadden wuri wanda ya yi mutum a iyakancen lokaci. Idan ka ce tsayawarsa a iyakancen wuri da iyakancen lokaci bai tauye shi ba domin Shi Mai Iko Dukka ne, to, zan ce maka Kasancewarsa cikin jiki a iyakancen lokaci, da wuri, ba zai tauye Shi ba domin Shi Mai Iko Dukka ne. Saboda haka Almasihu ya ce: “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah” (Luka 18:27).

23. Hadishi ya riwaito Muhammadu ya na cewa: “Lokacin da masu bi suka roƙi taimakon Allah a ranar tashin kiyama, sun zo gare ni, sai na ja gabansu zuwa ganin Allahna a gidansa, aka kuma yarje mini. Da na ga Allahna, sai na fāɗi a gabansa” (Bukhari 4:18).

Ga wata tambaya: “Don me ake zargin Kirista da yin sāɓo idan ya ce, Allah ya bayyana cikin jiki, amma ba a zargin wanda ya ce Allah yana zaune cikin gida ba?”

Cikin Suratul Hadid 57:29 an ce: “Kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yana bayar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah mai falala ne mai girma.” Cikin Suratul Fath 48:10 aka ce: “Lalle waɗanda ke yi maka mubaya’a, Allah kawai ne suke yi wa mubaya’a. Hannun Allah na bisa hannuwansu.” Cikin Suratul Mulk 67:1 an ce: “(Allah), Wanda gudanar da mulki yake ga hannunsa (ikonsa), Ya tsarkaka, kuma Shi Mai iko ne a kan kome.”

An rubuta cikin Suratu Hud 11:37 cewa: ‘Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau bisa ganinmu da wahayinmu.” An rubuta kuma cikin Suratuɗ Ɗur 52:48 cewa: “Sai ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kana idanunmu.” An kuma rubuta cikin Suratu Ɗ.H. 20:39 cewa: “Ki jefa shi a cikin akwatin nan, sa’an nan ki jefa shi cikin kogi, sa’an nan kogin ya jefa shi a gāɓa, wani maƙiyi Nawa kuma maƙiyi nasa ya ɗauke shi. Kuma Na jefa wani so daga gare Ni a kanki. Kuma domin a riƙe ka da kyau a kan ganina.”

Hadishi ya kwaso abin da Abu Hurairah ya ji Muhammadu yana cewa: “Allah ya halicci halittu, kuma lokacin da dangantaka a sashin mace ta tsaya, sai suka riƙe kuturin Wannan Mai Jinƙai” (Bukhari 3:114).

Dukan abubuwan da aka ambata nan sama cikin ayoyi sun ambaci Allah yana da fuska, da ido, da kuturi, dukan waɗannan sassa ne na jikin mutum. Idan zaman Allah cikin jiki ya zama sāɓo, to, ta yaya za a fassara ayoyin nan?

25. Ta yaya Allah Mai Tsarki zai zauna cikin mahaifar mace, cikin jini, da ƙazantar junabiyu da na haihuwa? Ta yaya kuma zai zauna cikin jikin ɗan Adam yana cin abinci, yana jin yunwa, yana shan ruwa yana kuma jin ƙishirwa, yana yin fitsari da bayangida?

Zai yiwu su da ke faɗar haka ba su fahimci faɗar mala’ikan Allah ba: “Shi da Maryamu ta ɗauki cikinsa ta wurin Ruhu Mai Tsarki.” Idan Allah mafi tsarki har ya fi gaban ya zo ya yi cuɗanya da jinin mace, yaya suka gaskata cewa Allah ya ɗauki haƙarƙarin Adamu ya yi mace da shi? Yaya za su bayyana hadishin annabci mai cewa: “Annabi yakan kwanta a ƙirjina lokacin da nake al’ada, yana haddace Kur’ani?” (Bukhari 1:44).

Idan jini rashin tsarki ne, Kur’ani kuma madawwamiyar maganar Allah ne, yana da asali daga ainihin Allah, ba shi kuma rabuwa daga gare Shi, ta yaya Muhammadu ya halatta wa kansa Karanta shi sa’ad da yake kwance a ƙirjin A’isha a lokacin da take cikin al’ada, amma aka haramta Kalma ta zauna ta kuma zama jiki cikin mahaifar Tsattsarka Maryamu? An rubuta cikin Suratul Hijr 15:28 cewa: “Kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce wa mala’iku ‘Lalle Ni, mai halittar wani jiki ne daga ƙeƙasasshen yumɓu wanda ya canja.” Jalalaini ya fassara wannan irin yumɓu da “baƙar laka.” Idan cuɗanya da baƙar laka ba a ɗauke shi ƙasƙanci ne ga tsarkin Allah ba, bai kuma ƙazantar da Shi ba, to, ina da gami, bayan Allah ya yi mutum daga yumɓun, ya ɗora shi kan dukan halittunsa, sai kuma a ce ba zai sauko ya zauna cikinsa ba? Yabo ya tabbata ga Allah gama maganarsa ta bakin manzo Bulus ta ce: “Ashe, ba ku sani ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma na zaune a zuciyarku?” (1Korantiyawa 3:16). Idan Allah Mai Tsarki bai ga lahanin zamansa cikin mai bi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ba, to, ina da gamin dacewarsa da zama cikin jikin Yesu wanda bai san zunubi ba, wanda aka haifa ba daga iri na ɗan Adam ba?

26. An rubuta cikin Suratul Kasas 28:29, 30 cewa: “To a lokacin da Musa ya ƙare adadin kuma yana tafiya da iyalinsa, sai ya tsinkayi wata wuta daga gefen dutse (Ɗur).Ya ce wa iyalinsa, ‘Ku dakata, lalle ne ni, na tsinkayi wata wuta, tsammanina ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani labari, ko kuwa da guntun makamashi daga wutar don ko ku ji ɗumi.’ To, a lokacin da ya je wurinta (wutar) aka kira shi, daga gefen rafin na dama, a cikin wurin nan mai albarka, daga itaciyar (cewa) ‘Ya Musa! Lalle Ni ne Allah, Ubangijin halittu.’”

An maimaita labarin nan cikin Suratu Ɗ. H. 20:9-13 cewa: “Kuma shin, labarin Musa ya je maka? A lokacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyalinsa, ‘Ku dakata. lalle ne ni, na tsinkayi wata wuta, tsammanina in zo muku da makamashi daga gare ta, ko kuwa in sami wata shiriya a kan wutar.’ Sa’an nan a lokacin da ya je mata, aka kira shi, ‘Ya Musa! Lalle ne, Ni ne Ubangijinka, sai ka ɗebe takalmanka. Lalle ne kana a rafin nan abin tsarkakewa, Duwa. Kuma Ni, Na zaɓe ka. Sai ka saurara ga abin da ake yin wahayi.’”

Ga yadda Imam Fakhruddin ya bayyana labarin:Musa, salama ta tabbata a gare shi, ya nemi iznin barin Shu’aib don ya koma wurin mahaifiyarsa, aka kuwa yardar masa. Yana kan tafiya ke nan sai matar ta haifa masa yaro a wani daren Juma’a a lokacin tsananin sanyi ne kuwa. Ya yi ɗan tattaki. Musa, salama ta kasance tare da shi, ya ƙyasta ƙyastu amma ba wuta. Ya yi ta fama, can, sai ya lura ga wata wuta can nesa a gefen hagu na hanyar.” Ga abin da aka ji Assaddi yana cewa: “Musa yana zaton wasu makiyaya ne suka hura wutar.” Wasu suka ce Musa ya ga wutar a jikin wani itace. “Lokacin da ya ga wutar, sai ya nufe ta, ya faɗa wa iyalinsa: ‘Su jira! Ga shi! na ga wata wuta, watakila zan kawo muku garwashi ko bakin wuta ko ƙyastu.’ Ibn Abbas ya ce: “Da ya isa can Sai ya ga itace kore daga jikinsa har ressan kamar farar wuta. Ya tsaya yana mamakin hasken wutar da itacen kore shar. Wutar ba ta canza itacen ba, itacen kuma bai canza wutar da ɗanyen jikinsa mai ruwa ba; sai Musa ya ji mala’iku suna raira waƙoƙin yabo, ya ga haske mai ƙarfi. Da Musa ya ga wannan, sai ya rufe fuskarsa da hannuwansa, aka kira shi: ‘Ya Musa! Ni ne Allahnka.’ Ya amsa da ladabi ya ce: ‘Na ji muryarka amma ba ni iya ganin ka. Ina kake?’ Sai Allah ya ce: ‘Ina tare da kai, a gabanka, da bayanka, da kewaye da kai, ina kuma kurkusa da kai - - - Ka tuɓe takalmanka, domin kana a kwari mai tsarki ne’” (Tafsirin Al Kabir Kundi na 22:Shafi na 14, 15).

Cikin Littafi Mai Tsarki kuwa ga yadda aka ba da labarin: “A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ya ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba. Musa kuwa ya ce, ‘Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba.’ Sa’ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, ‘Musa, Musa.’ Musa ya ce, ‘Ga ni.’ Allah kuwa ya ce, ‘Kada ka matso kusa, ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne’” (Fitowa 3:2-5).

Abokina! Idan har Allah, don ya yi magana da Musa, ya kuma aike shi wurin mutane, ya zaɓi ya zauna cikin ɗan kurmi, ya kuma bayyana cikin harshen wuta, ashe, an kyauta ke nan da ake zargin Kirista da yin sāɓo domin sun ce sun gaskata Allah, domin ya bayyana Kansa cikin ƙauna, ya bayyana cikin Almasihu? Ko ɗan kurmin da Allah ya bayyana cikinsa ya fi Almasihu muhimmanci?

27. Na bar ka da wannan, idan Yesu, lokacin da yake cikin jiki, ya ci abinci, ya sha ruwa, ya kuma yi gyatsa, waɗannan duka ba su raunana cikakkiyar Allahntaka da ke zaune cikinsa ba. An misalta wannan cikin Littafi Mai Tsarki haka: “Na sani, na kuma tabbata, tsakanina da Ubangiji Yesu, ba abin dake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki” (Romawa 14:14).

28. Ya abokina! Duk wanda ya yi bimbini da zurfi cikin Maganar Allah ba zai kāsa yin la’akari da hanyar da Allah ya zaɓa don ya bayyana Kansa ba, ya kuma sadar da nufinsa, ta hanyar bayyana da kuma zama cikin jiki. Babu damuwa, ko irin bayyanar da kuma zama cikin jikin sun faru ne cikin gajimari, ko cikin wuta, ta wurin jikin Mala’ikan Alkawari ko jikin Almasihu wanda cikinsa ne ya bayyana cike da alheri da gaskiya kuma.

Cikin Ibraniyawa 1:1, 2 mun karanta wannan magana wadda take furci ne a game da hulɗar Allah da ’yan Adam: “A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa, amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya.” A nan ga wasu misalan bayyanar Allah ga ’yan Adam, kamar yadda yake a rubuce cikin Littafi Mai Tsarki.

Farawa 18:1-5 tana cewa: “Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana. Da ya ɗaga idonsa ya duba, sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku’u, ya ce, ‘Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima. Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gidin itace, ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da ya ke kun biyo ta wurin baranku.” Sai suka ce, ‘Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.’” A nan Allah, ya bayyana ga Ibrahim cikin kamannin mutum wanda ya zauna, ya ci abinci, ya kuma sha ruwa.

Farawa 32:22-30 ta ce Ya bayyana ga Yakubu cikin siffar mutum, ya kuma yi kokawa da shi har kusan wayewar gari, sa’an nan ya roƙi Yakubu ya bar shi ya tafi, “Yakubu ya ce, ‘Ba zan bar ka ba sai ka sa mini albarka,’” Ya kuwa albarkace shi da cewa “... ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.” Sai Yakubu ya kira wurin Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.”

Fitowa 24:9-11 tana cewa: “Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba’in na Isra’ila. Suka ga Allah na Isra’ila. Wurin da yake a ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yaƙutu, garau kamar sararin sama. Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra’ila wani abu ba.” A nan bayyanar Allah ta ɗauki kamannin mutum da hannuwa da ƙafafu, Amma bai yi wa dattawan wani abu ba, domin su masu zunubi ne, suna bukatar matsakanci, mai halin Allah da halin mutum.

BABI NA III

TAMBAYA:

“Ashe, Allah Mai Jinƙai ba shi da ikon ceton ɗan Adam in ba ta wurin aiko da ɗansa ba, idan ma har yana da ɗan kamar yadda kuke iƙirari, ya ɗauki siffar jikin mutum, a jarraba shi kamar mu, a kuma kashe shi ta hannun mugayen mutane?”

S. A. Dimashƙu Suriya

29. Littafi Mai Tsarki yana koyar da cewa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah (Farawa 1:27). Allah, Ɗaukaka ga sunansa, ya nufi mutum ya zama marar lalacewa. Amma mutum, ta wurin girmankansa ya karya dokar Allah dagangar, ya yi rashin biyayya, ya fanɗare. Ta haka ya zama mai zunubi, ya jawo wa kansa hukuncin Allah inda Nassi ya ce: “Wanda ya yi zunubi shi zai mutu” (Ezekiyel 18:20). Manzo Bulus ma ya yi magana a kan wannan, inda ya ce: “To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi” (Romawa 5:12).

Maganar Allah tana koyar da cewa, “Yan Adam, ta wurin ƙin riƙe Allah cikin saninsu, suka fāɗa cikin rashin biyayya kamar iyayensu na fari. Tun daga nan ne fa, suka rasa siffar adalci da tsarkin gaskiya wadda Allah ya halicce su ciki. Sun lalace ta wurin muryoyinsu; kamar yadda Mai hikima Sulemanu ya ce: “Wannan ne kaɗai abin da na gane, tsaf Allah ya yi mu, amma mu muka rikitar da kanmu” (Mai Hadishi 7:29); Manzo Bulus ma ya ce: “Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi kamar shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta. Suna da’awa, wai su masu hikima ne, sai suka zama wawaye” (Romawa 1:21, 22).

Yana yiwuwa ga mutum, wanda Allah ya halitta cikin siffarsa, ya kauce wa lalacewa, da ruɓewa, ya yi zamansa cikin tsarki, idan da ya riƙe Allah cikin saninsa. Allah ya halicce mu ba daga kome ba, ya numfasa mana rai, amma kuma ya sa mana yiwuwar zama cikin zumunci da Shi Kansa. Amma da shike mutane sun gusa daga ran Allah, suka yarda da jarabar Shaiɗan, su suka jawo wa kansu tāɓewa da kansu.

30. Ko ya dace da Allah ya ƙaddara mutum ga halaka ta har abada, mutumin da ya halitta cikin siffarsa da kamanninsa? Me Mahalicci zai yi, Shi da yake jauharinsa adalci ne, kuma jinƙansa madawwami ne? Ko falalar ƙaunarsa zai yardar wa lalacewa ta shafi siffarsa daga ɗan Adam? Ko allahntakarsa maɗaukakiya za ta ji daɗin halakar jama’ar ’yan Adam waɗanda ya halitta da kammala? Idan har zai bar su cikin wannan halin lalacewa, ashe, bai zama sakaci ba? Amma sakaci ya dace da ɗaukakar Allah Mai Tsarki? Ko kusa, bai dace da ɗaukakar Allah ba! Ashe, bai ce: “Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu’” (Ezekiyel 33:11).

31. Gaskiya ne cewa Allah cikin falalar ƙaunarsa, ya nufi mutum da samun ceto. Ta yaya? Ta wurin tuba ne? Amma fa tuba ba ta kawar da hukunci, a sakamako dai tana ɗaga horo, domin wannan ba zai biya bukatar adalcin Allah ba. Gaskiya ne cewa sa’ad da tuba take tsaye a tsakanin mai tubar da ƙara aikata zunubi, tubar ba ta kankare ɓarnar zunubin dake biye ba, da kuma hukuncin Allah. Bisa ga wannan mawuyacin hali, mutum zai yi tambaya kuma: Wane irin mataki Allah zai ɗauka a game da wannan, Shi, “wanda ke so dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya” (1 Timoti 2:4). A gaskiya, Allah yana so ya baratar da mutum don ya komo da shi da yake lalataccen taliki zuwa matsayin rashin lalacewa, a lokaci guda kuma, ya iya biyan bukatar adalcin allahntaka. Wannan ya haɗu da shawarar allahntaka dangane da hadaya. Saboda haka “Logos” wato Kalma, Wanda “Tun fil azal kuwa tare da Allah yake, ‘Logos’ wato Kalma kuwa Allah ne”, Shi kaɗai ya cancanta, bisa ga ainihin yadda yake, don ya kawo maya haihuwar dukan abubuwa ta wurin ɗaukar jikin ɗan Adam, da ɗaukar horo a madadin ’yan Adam, horon da yake bisa ga adalcin allahntaka. Wannan ne ainihin dalilin zuwansa cikin duniyarmu, “Ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗicin Ɗa daga wurin Ubansa” (Yahaya 1:14).

32. Hakika, tun fil azal, Kalman yana shirya Kansa domin jiki. Haka mutumin Allah, Tertulliyan ya faɗa cewa, Almasihu yana shirya Kansa don zama jiki tun zamanun zamanai kafin bayyanarsa. Gaskiyar ita ce, duk wanda yake bimbinin Littafi Mai Tsarki zai ga cewa, Ubangiji Mai Fansa yana raɗawa ta wurin izawa ga kunnuwan annabawan Allah cikin Tsohon Alkawari. Annabci ya yi batun sa ta bakin annabi Ishaya: “Yanzu fa, Ubangiji Kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel - - - (Ma’anar Immanuwel kuwa, Allah na tare da mu”) (Ishaya 7:14; Mat. 1:23).

Hurarriyar maganar tana gaya mana cewa: “Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma ƙarƙashin Shari’a, domin ya fanso waɗanda ke ƙarƙashin Shari’a, a mai da mu a matsayin ’ya’yan Allah” (Galatiyawa 4:4, 5).

Bisharar fansa ta bayyana mana cewa, dukka suna a ƙarƙashin hukuncin mutuwa wanda ba shi kankaruwa sai ta wurin mutuwar Wani adali, wanda bai san zunubi ba. Kalman, da yardar ransa ya ɗauki siffar jikin ɗan Adam, don a cika hukuncin mutuwa a kansa a madadin dukkan masu ba da gaskiya. An bayyana wannan asiri gare mu ta wurin manzo Bulus da ya ce: “Saboda haka yanzu ba sauran kayarwa ga waɗanda ke na Almasihu Yesu. Ka’idan nan ta Ruhu mai ba da rai da ke ga Almasihu Yesu ta ’yanta ni daga ka’idar zunubi da ta mutuwa. Abin da ba shi yiwuwa Shari’a ta yi don ta kāsa saboda halin ɗan Adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi cikin jiki, da ya aiko Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi. Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari’a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu” (Rom. 8:1-4). Wannan yana nufin cewa, Ubangiji, kuma Maifansa, cikin miƙa jikin nan da ya ɗauka a kan Kansa a matsayin hadaya ta ƙonawa, hadaya kuma marar aibi, ta kawar da hukuncin mutuwa dake a kan dukan waɗanda ya yi wannan a madadinsu. Ta haka ne, saboda an ɗaukaka shi a kan duka, kuma ba shi da zunubi. Ta haka ya iya biyan bukatar adalcin allahntaka.

33. Zai yiwu ka fuskanci wahala cikin fahimtar asirin fansa. Amma lokacin da ka yi bimbinin koyarwar Linjila, wato Bishara a game da ƙaunar Allah, da falalar jinƙai, za ka ga cewa irin wannan aiki ya yi muwafaka da juyayin da yake jauharin Allah ne. Nan ƙasa ga wasu matani nan cikin Sabon Alkawari hurarru, rubutattu domin koyarwa a gare mu. Ta wurin karanta su za ka ga har ina ne ƙaunar Allah ta kai domin ceton ka:

- “Wato tun da yake ’ya’yan duk suna da tsoka da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis ta mutuwarsa” (Ibraniyawa 2:14).

- “Amma ta alherin da Allah ya yi musu kyauta sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi. Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin ya nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ne ya jingine zunuban da aka gabatar” (Romawa 3:24, 25).

- “Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu. To, tun da yake yanzu an kuɓutar da mu ta jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan” (Romawa 5:8, 9).

- “Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?” (Romawa 8:32).

34. Tabbacin Annabcin Allahntaka Cikin Jiki

- “Na shirya in amsa addu’o’in mutanena, amma ba su yi addu’a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al’ummar ba ta yi addu’a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’ Kullum ina a shirye domin in marabci waɗannan mutane, waɗanda saboda taurinkansu suka yi ta aikata abin da ba daidai ba, suka bi hanyoyin kansu” (Ishaya 65:1, 2).

Wannan aya tana magana a kan Yesu Almasihu cikin jiki, domin Bulus ya faɗo batun, inda ya yi magana kamar haka: “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni. Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.” Amma a game da Isra’ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama’a marasa biyayya, masu tsayayya” Rom. 10:20, 21). Yesu ne a zahiri wanda ya miƙa hannuwansa a kan gicciye.

- “Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, ya ga girmansa da ikonsa. Ku ƙarfafa hannuwana da suka gaji, da gwiwoyin da ke fama da rashin ƙarfi. Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, ‘Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka. Makaho zai iya ganin gari, kurma kuma zai iya ji’” (Ishaya 35:2-5).

Wannan annabci ba bayyana Allah yana zama a nan kaɗai ya yi ba, amma ya nuna alamomin zuwansa, da bayyana ayyukansa kamar yadda aka zayyana su cikin Linjila, kamar haka: “Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, ‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’- - - Sai ya amsa musu ya ce, ‘Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana tada matattu, ana kuwa yi wa matalauta bishara. Albarka ta tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni’” (Luka 7:19-23).

- “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali. Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta, a yi mata tituna da kagara” (Daniyel 9:24, 25).

Cikin annabcin nan mun sani cewa ba batun Almasihu kaɗai aka yi ba, amma har da nuna Wannan da za a shafe ba mutum ne kawai ba, amma Shi Mafi Tsarki ne. Hasali, lokacin da Almasihu ya zo, wahayi da annabci suna a kan jama’ar Yahudawa ne waɗanda daular mulkinsu ta ƙare. An sa zuciyar za a dinga shafe sarakunansu har sai lokacin shafe Wannan Mafi Tsarki ya yi. Yakubu ya yi annabci cewa, Sarakunan Yahudawa za su daɗe har sai Masiha ya zo, ga yadda ya ce: “Yana riƙe da sandan Mulkinsa, ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama’o’i” (Farawa 49:10).

- “Ba ka bukatar bayebaye da hadayu. A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka. Sai na amsa, ‘Ga ni, umarnanka zuwa gare ni suna a Littafin Shari’a. Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah! Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata’” (Zabura 40:6-8).

35. Idan mun gwada ayoyin nan da abin da aka ambata cikin Ibraniyawa 10:6-10, za mu ga cewa wannan Zabura mai daraja, cikakke ne, ta shafi Yesu. Ubangijinmu maɗaukaki ya nuna hadaya da baiko na Tsohon Alkawari kamar su hadayun zaman lafiya, da na ƙonawa, da na zunubi, bayan ya dube su, duban hikima, sai ya furta cewa: “Ba su ne Maɗaukaki yake bukata ba.”

Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana cewa, shirin hadaya mafi duka yana nan cikin madawwamiyar shawarar Allah. Kamar yadda muka rusuna cikin bangirma, sai Ruhu Mai Tsarki ya ɗauke mu zuwa can baya na tun fil azal, wanda ba za mu iya ganewa cikakke ba saboda kāsawarmu ta ’yan Adam; amma abin da muka iya fahimta daga wahayan Allah cikin Littafinsa Mai Tsarki, idanunmu suka ga “ainihin abubuwan nan” na Allahntaka ko Mutanen nan uku cikin Allah Ɗaya (Larabci: AKANIM), suka dubo ƙasa a kan ’yan Adam wadda za ta kasance, da zunubin da zai shigo duniya, da mutuwar zunubin, aka kuma ƙaddara cewa za a sami fansa. Mun iya ganin Allah Ɗa, da yardar ransa zai yi aikin hadaya, yana cewa: “Ga ni zan je in yi kafara domin duniya da ta fāɗi baya.”

36. Don amfanin ɗan Adam, Ubangiji cikin Jiki bai gamsu da cewar fansa ta Allah an taƙaice ta ga al’ummar da ke ɗauka ita kaɗai ce za ta gāji Alkawaran Allah ba, amma yana so abin ya ƙunshi dukanin duniya.

Ba wuya wani ya jarabtu ya yi tambaya cewa: Don me aka kammala mutuwa ta wurin gicciye a maimakon ta wasu hanyoyi dabam? Don amsa wannan, zan ce, son Allah ne ya fanshe mu da Kansa, ba kuwa wata hanyar da ta fi domin mu, wadda kuma ta fi dacewa da Ubangiji. Ya yi kyau da Ubangiji Cikin Jiki ya yi irin wannan mutuwa sabili da mu. Don in zai baratar da mu daga zunubi wanda shari’a ta liƙe mu, ta wace hanya zai bi ya zama zunubi domin mu, in bai mutu yana ɗauke da zunubanmu ba a kan gicciye?

Idan kuma mutuwar Ubangiji Cikin Jiki ta zama kafara domin dukka, ta wurin mutuwarsa kuma, ya rushe bangon nan mai raba tsakani, wato magabtaka (Afisawa 2:14), don Kiran ya ƙunshi dukkan al’ummomi; to, da ta yaya zai yiwu a kira mu ga Sulhuntuwa da Allah, in da ba a gicciye Shi ba? Godiya ta tabbata gare Shi, da shike wannan ne murnarsa, ya kuma ga ya dace ya sha mutuwar wulakanci, yana miƙa hannuwansa sama a kan gicciye domin ya jawo tsarkaka na Tsohon Alkawarin da hannu guda, da guda hannun kuma, waɗannan daga cikin al’ummai, domin ya haɗa duka cikin Ɗaukakar Kansa: “Yesu ya amsa musu ya ce, ‘Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum’” (Yahaya 12:32).

KACINCI-KACINCI

In kana da sha’awar gane fahimtarka ga abin da ke cikin littafin nan, sai ka amsa tambayoyin da ke nan ƙasa. Idan ka amsa mafiya yawa da kyau, to, za mu aiko maka da wani ɗan littafi na Iskander Jadeed.

 1. Don me mutum ba ya iya zama nagari, kuma cikakke ta wurin ikon kansa?

 2. Wace ce hanya guda kaɗai ta yin sulhu da Allah?

 3. Waɗan ne ne tabbaci uku da aka ambata masu nuna cewa mutum mai zunubi ne?

 4. Ko nufin Allah ne mu yi ta zama masu zunubi? Menene hanyar cetonmu?

 5. Wace ce bukata mafi girma cikin zuciyar mutum?

 6. Ta wace hanya ce mutum zai iya ɗaguwa zuwa matakin Allah?

 7. Menene muhimman cancantar Matsakanci tsakanin mu da Allah?

 8. Ta yaya cancantar da suka wajaba ga matsakanci na allahntaka suka cika cikin Almasihu?

 9. Waɗanne ne abu biyu masu nuna kammala mai kyau domin ’yan Adam?

 10. Don me Almasihu ya tattara almajirai kewaye da shi?

 11. Yaya Yesu ya yi da kamun da maƙiyansa suka yi masa?

 12. Ta yaya nasarar Almasihu ta zama a fayyace?

 13. Ina sakamakon mutuwa da tashin Almasihu?

 14. Ta yaya duniya ta rinjayu da allahntakar Almasihu?

 15. Ta yaya ran mutum zai sāke tun daga tushensa?

 16. Waɗanne ne jauharin da aka ba Almasihu cikin Littafi Mai Tsarki?

 17. Ko Islama ta kafa dangantaka tsakanin Mahalicci da halittunsa?

 18. Ta yaya hadisan Annabci suka nuna dangantaka ta kai tsaye tsakanin Allah da ’yan Adam?

 19. Me ra’ayin nan ya nuna na “cikakkiyar rabewar ɗan Adam gaba ɗaya daga ra’ayin Allahntaka” (Larabci: TANZIH)?

 20. Me hadisan annabci suke faɗa a game da saukowar Allah a kowane dare?

 21. Yaya za ka iya tabbatar da cewa, zaman Allah cikin jiki bai canza ainihin ikon Allah ba?

 22. Ko Allah ya iya zama cikin jiki ya kuma gane da nufinsa?

 23. Me ake nufi da matanin hadisan annabci mai cewa Allah yana cikin ɗaki /gida?

 24. Ta yaya Allah Mai Tsarki ya zauna cikin cikin mace?

 25. Me bayyanar Allah ga Musa cikin kurmi mai cin wata take nufi?

 26. Menene rashin tsarki?

 27. Ina batun hulɗar Allah da al’amarin duniya cikin wahayansa, ba tare da ya ƙazantu ba? Ashe, wannan ba alama ba ce cewa, Allah yana iya zama cikin jiki ba tare da hasarar kome ba?

 28. Ta yaya mutane suke rasa siffar Allah?

 29. Ina azancin tunanin cewa Allah zai bar halittunsa su yi ta zama cikin lalacewa?

 30. Don me tubar mutum kawai ba ta isa ceto ba?

 31. Ina tabbaci daga hurewar allahntakar zaman Almasihu cikin jiki?

 32. Ina tabbacin annabci na zaman Ubangiji cikin jiki?

 33. A gaban Allah wace hadaya ce mafi samun tagomashi?

 34. Ko Yesu ya nufi fansarsa ga dukkan mutane ne, ko kuwa ga Yahudawa kaɗai?

Ka rubuta amsarka zuwa ga:


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland