TA YAYA ZA MU IYA SANIN GASKIYAR LINJILA / BISHARA?

TA YAYA ZA MU IYA SANIN GASKIYAR LINJILA / BISHARA?

Iskander Jadeed

All Rights Reserved

1990

2000


TAMBAYOYI:

Ta yaya za ka iya tabbatar da matsayin Ubanci na Allah ga Almasihu?

An ce wai an sassauya Attaura da Sabon Alkawari. Menene ra’ayinka a game da wannan?

Ko kana da wata shaida mai nuna cewa Almasihu ya mutu a kan gicciye?

Ashe, ko ba kasancewar “Bisharu huɗu” shaida ce ba mai nuna cewa an sassauya Linjila, wato sabon Alkawari?

M. Z. S. TRIPOLIS - LEBANON

Zuwa ga Abokina,

Na ji daɗi ƙwarai da na lura cewa ka ƙuduri niyyar bincike a game da gaskiyar Linjila/Bishara. Yana da kyau da kake da wannan irin muradi, domin mun ga yadda Bulus, manzo kuma gwarzon Bangaskiya yana cewa: “Ku jarraba kome, ku riƙi abin da ke nagari kankan” (1 Tasalonikawa 5:21).

Daga farkon maganar cikin wasiƙarka, daga dukan alamu kana so ne ka tattauna a game da wasu gaskatawar Kirista. Amma duk da haka, ɗokinka ya kai ka cikin filin jayayya da “mutanen Littafi”, a akasin umarnin Kur’ani mai cewa, “ ...sai fa da magana wadda ta fi kyau” (Suratul Ankabut 29:46).

Amma ka manta da kashedin da Kur’ani ya yi, inda ya ce, “kuma yaya suke gabatar da kai ga hukunci, alhali a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah?” (Suratul Maida 5:43). Cikin ƙoƙarinka na ƙin wasu gaskatawa na Kirista waɗanda suke muhimmai, suke kuma ji da su, ka yi amfani da wasu nassoshi daga Kur’ani a maimakon na Littafi Mai Tsarki wanda Kur’ani kansa ya sa don su zama sasantawa a kan kowace irin jayayya da taka taso tsakanin Kirista da Musulmi. Tabbatar wannan gaskiya ita ce, Muhammadu da kansa an umarce shi da ya je wurin “Mutanen Littafi” domin ya tabbatar da gaskiyar kowace gaskatawa. Kur’ani ya ce: “To idan ka kasance a cikin shakka daga abin da muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littafi daga gabaninka” (Suratu Yunus 10:94).

Wannan umarni ya shafi kowane Musulmi dangane da sasantawa a game da kowace muhawara da taka taso dangane da rukunai/ koyarwa, tare da mutanen Littafi, sai su amince da hukuncin Littafin kansa. Kamar yadda yake a wata aya ta Kur’ani, mai cewa: “Lalle ne, mu, mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shirya da haske, annabawa waɗanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da malaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littafin Allah, kuma sun kasance, a kansa, masu ba da shaida... Wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to waɗannan su ne kafirai” (Suratul Maida 5:44).

Abin dake biye da wannan shi ne, babu abin da ya wajabci Kirista daga cikin ayoyin Kur’ani ko ta kowane hali. Akasin haka, Kur’ani yana kira ga Kirista ya manne wa Littafinsa, ga abin da ya ce: “Kuma sai mutane su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a aikinta, kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to waɗannan su ne fasiƙai” (Suratul Maida 5:47).

Yanzu kuma zan ba da amsa ga sukar da kake yi a game da wasu koyarwa da dama na Kirista:

I. ÅIYANCIN ALMASIHU

A ƙoƙarinka na ƙalubalantar ɗiyancin Almasihu, ka mori wasu ayoyi biyu na Kur’ani, cikin Suratul Ikhlas da Suratu Maryam, amma ba ka kula ka taɓo ayar da ke cikin Suratul An’am ba, wadda take cewa; “Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yaya ɗa zai kasance a gare Shi, alhali kuwa mata ba ta kasance a gare Shi ba, kuma ya halitta dukan kome kuma Shi, game da dukan kome, Masani ne?” Suratul An’am 6:101).

Nufina da kawo ayan nan, shi ne, don in jawo hankalinka ga rashin ƙarfin jayayyar da Islama yake kawowa lakacin da ya ke ƙalubalantar ɗiyancin Almasihu. Kafin isowar Islama, wasu mabiya addinin Kirista, daga asalin arna ne yawancinsu, sun yaɗa wata irin koyarwar ƙarya wadda take cewa, Budurwa Maryamu allahiya ce. Zai yiwu sun ɗauke ta daidai da allahiyarsu “Al-Zahra” (Zara matar wata). Wannan ƙungiya mai karkata, suna kiran kansu “Maryamiyawa” ko kuwa mabiya Maryamu. Shehin malami Ahmad Al-Makreezy ya ambace su cikin littafinsa mai suna, “Al-kawl-Al-Ibreezy” (shafi na 26). Haka kuma wani marubuci mai suna, Ibn-Hazm, ya ambato wannan karkacewa cikin littafinsa mai suna “Al-milal Wal-Ahwaa Wal- Nihal” (shafi na 47). A yanzu haka babu ko da Kirista guda ɗaya da ya gaskata wannan. A zahirin gaskiya, wannan babban cin mutunci ne ga ɗaukakar Allah Mai Tsarki, wanda yake gaba, nesa da abubuwan da suka jiɓanci jauharansa. Malaman tauhidin Kirista sun yi yaƙi tuƙuru da wannan karkacewa, suka mori nassoshin Littafi Mai Tsarki, da kuma bin diddiƙi, har sai sun ga bayan wannan karkatacciyar koyarwa gaba ɗaya kamin ƙarshen ƙarni na bakwai.

Daga abubuwan nan da aka ambata, muna iya ganin cewa, Kur’ani bai soki koyarwar Kirista ba, sai dai wannan kaɗai, wato ta karkatattun Maryamiyawa, waɗanda ainihin asalinsu arna ne. Domin arnanci a wacan lokaci ya zama game- gari ne a ƙasashen Masar da Sa’udi Arabiya da kuma Girka wato Helas, waɗanda suka gaskata cewa allolinsu sukan yi aure su haifi ’ya’ya. Kirista kuwa ba su gaskata ɗiyancin Almasihu ta wurin haihuwar jiki ba ne, wato wadda take samuwa ta wurin haɗuwar namiji da mace cikin jima’i. Sun dai gaskata shi ɗan Allah ne bisa ga yadda ya fito daga Allah kansa a cikin kasancewarsa ta Ruhaniya (Uluhiya). “Shi Kalman Allah ne, kuma daga Ruhunsa.”

Manzo Bulus ya ambato wannan gaskiyar lokacin da ya ce: “Daga Bulus bawan Yesu Almasihu manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah, wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa cikin Littattafai masu tsarki. Bishara ɗin nan a kan Åansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne, amma ga tsarkinsa na ruhu shi Åan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu.” (Romawa 1:1-4)

Cikin sāke duba faɗar Almasihu, a sarari za mu ga shaidar da ke tabbatar da ɗiyancinsa na allahntaka, alal misali: “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da ke cikin sama” (Matiyu 16:17).

“Haka kuma Ubana da ke Sama zai yi da kowannenku... ” (Mat. 18:35).

“Me ya sa kuka yi ta nema na? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha’anin Ubana ba?” (Luka 2:49).

“Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, ‘Ubana na aiki har yanzu, ni ma ina yi” (Yahaya 5:17).

Mun kuma karanta daga Linjila/Bishara, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?” (Yahaya 10:32).

Labarin da ke cikin Linjila/Bishara a game da baftismar Almasihu cikin Kogin Urdun, aka ce an ji murya daga sama cikin wannan lokacin tana cewa, “ ...Wannan shi ne ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai” (Matiyu 3:17).

Yanzu bari mu komo ga ayar Kur’ani mai cewa: “Ba a haife shi ba, bai kuwa haifa ba.” Ga yadda Iman Al-Baudawi ya fassara ayan nan: “bai haifa ba” bisa ga fahintar cewa, ba ta wurin haɗuwar namiji da mace cikin jima’i ba, kuma ba shi da bukatar mataimaki (ko mataimakiya), ko magāji – sa’an nan “Kuma ba a haife shi ba”, ma’ana, bai rasa kome ba, kuma ba babu a gare shi. Saboda haka “haihuwa” (ko a haifa) kamar yadda aka mora cikin Suratul Al-Ikhlas ba a nufin kome sai haihuwa irin wadda take aukuwa cikin tarawar namiji da mace cikin jima’i. A kan wannan, babu wata tantama ko kaɗan, ba gaskatawar Kirista ke nan ba, sam!

II. FIFIKON MUHAMMADU

Musulmi sun ɗauka cewa Muhammadu ya fi dukan sauran annabawa.

Inda a ce Almasihu annabi ne, da sai in yi muhawara da kai don mu ga ko wane ne mafi girma. Amma duk da haka, babu kokanto, Almasihu shi ne mafi girma a kan dukan annabawa, da dukan mala’iku, da dukan manyan mala’iku. Yana kan dukan talikai cikin sama da cikin duniya; a kan dukan abubuwa masu ganuwa da marasa ganuwa. Saboda haka bai ma zama dole ba a ce mu yi wata tattaunawa a game da wannan. Mun karanta a cikin Yahaya 1:1-5 cewa: “Tun fil azal akwai Kalma, Kalman kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. Shi ne tun fil azal yake tare da Allah. Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. Haske na haskakawa cikin duhu, duhu kuwa bai rinjaye shi ba.” Ibraniyawa 3:1-6 tana cewa, “Saboda haka ya ku ’yan’uwa tsarkaka, ku da kuke rabe a kiran nan basamaniye, sai ku tsaida zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa, shi da yake mai aminci ga wannan da ya sa shi, kamar yadda Musa ya yi ga duk Jama’ar Allah, Amma kuwa an ga Yesu ya cancanci ɗaukaka fiye da ta Musa nesa, kamar yadda mai gina gida ya fi gidan martaba. Kowane maigida, ai, da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abubuwa Allah ne. To, shi Musa mai aminci ne ga dukan jama’ar Allah a kan shi bara ne, saboda shaida a kan al’amuran da za a yi maganarsu a gaba, amma Almasihu mai aminci ne, yana mulkin jama’ar Allah a kan shi ɗa ne, mu ne kuwa jama’arsa, muddin mun tsaya gabanmu gaɗi, muna taƙama da begenmu ƙwarai.”

Muna kuma karantawa cikin Ibraniyawa 1:1-6, cewa, “A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa, amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi magana ta wurin Åansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya. Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗa tasa. Bayan ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna dama ga Maɗaukaki a can Sama. Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku, kamar yadda sunansa da ya gāda yake da fifiko nesa a kan nasu. Domin kuwa, wanene a cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, ‘Kai Åana ne, Ni Ubanka ne yau’? da kuma, ‘Zan kasance Uba gare shi, Shi kuma zai kasance Åa gare ni’? Amma da zai sāke shigo da magāji a duniya, sai ya ce, ‘Dukkan mala’ikun Allah su yi masa sujada.’” Zabura 2:7 kuma tana cewa, “Sarkin ya ce, ‘Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta. Ubangiji ya ce mini, “Kai ɗana ne, yau ne na zama mahaifinka.”’” Mun kuma karanta cikin Kolosiyawa 1:15, “Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba”.

III. Sassāke ABIN DA LINJILA/BISHARA TA ƘUNSA

Zai yiwu a zargi kowane littafin addini a kan sassāke abin da ya ƙunsa. Amma akwai bambanci a tsakanin yin zargi da samar da abin shaida mai tabbatar da zargin naka. “Tabbacinka” na fari shi ne, Linjila ta hana kisan aure, Kur’ani kuwa ya ce a kashe aure; Kur’ani ya hana shan ruwan inabi, Linjila kuwa ba ta hana ba. Ba shakka, wannan zargi ba shi da wani tasiri, domin kuwa ba a kan fahimtar gaskiya yake ba saboda dalilai guda biyu:

1. Linjila/Bishara ba hana kisan aure ta yi ba, amma don ta taƙaice gardandamin Marubuta da Farisiyawa ne cikin fassarar shari’ar/dokar Attaura a game da kisan aure da a ka yi batunsa a cikin (Maimaitawar Shari’a 24:1). Almasihu ya ƙarfafa mutane da su koma a kan abin da Allah ya kafa tun da farko (Farawa 2:24), shi ne cewa, namiji da ta mata su zauna tare muddin ransu. Wannan domin a tsare mutuncin iyali da walwalarsu, da halin kirki, a kuma tsare mutuncin matar aure a matsayinta na uwa da mai tarayya cikin ruhaniya da mijinta. Saboda haka, Almasihu ya yarda da kisan aure saboda laifin yin zina kaɗai daga ɗayansu, wannan ne kaɗai yake kwance igiyar aure (Matiyu 5:31). Mun gani a ’yan shekarun da suka gabata yadda wasu masanan Musulmi kuma shugabanni suka tilasta kawar da dokoki masu yawaita yarda da kisan aure, domin a tsare mutuncin inyali da na al’ummar ƙasa. Zai yiwu wannan ya faru ne saboda takalidan/al’adun nan na annabci masu cewa, “Abin da ya fi muni a gaban Allah shi ne sassauci a kan batun kisan aure” (Sunan Abi Davood, Littafi na 13, sashi na 3).

2. Linjila/Bishara ba ta ƙarfafa shan ruwan inabi ba, amma kashedi ta yi a game da sha, “Kada kuma ku bugu da giya hanyar masha’a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu” (Afisawa 5:18). Ta kuma ce, “Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo, ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah” (1 Korantiyawa 6:9,10).

Bugu da ƙari kuma, bambance-bambancen da ke tsakanin Linjila/Bishara da Kur’ani cikin al’amuran doka, ba su kai yadda za ka yanke hukunci cewa an sassāke Linjila/Bishara ba. Idan kuwa har za mu fara a kan wannan matakala, to kuwa ba abin da zai hana Kirista su ce an sassāke Kur’ani don kuwa ya amince da kisan aure a kan dalilan da Linjila/ Bishara ba ta amince da su ba. IV. LINJILA/BISHARA TA CE AN GICCIYE ALMASIHU (ISA), AMMA KUR’ANI YANA CEWA BA A GICCIYE SHI BA.

Bisa ga dukan alamu, kai ma, kamar mutane da yawa da suke ƙoƙarin kama dukan abin da suka karanta cikin Kur’ani, kana kuma mantawa cewa, Kur’ani kansa ya ba mu labarin shaidar da al’ummar Yahudawa suka yi mai nuna su da kansu suka gicciye Almasihu, don kuwa Kur’ani ya ce, “Da faɗarsu ‘Lalle mun kashe Masihi Isa ɗan Maryama, Manzon Allah”’ (suratul Nisa 4:157).

Al’ummar Yahudawa sun yi ta miƙa wannan takalidai (al’ada) na kisan Almasihu, daga uba zuwa ga ɗa tun daga ƙarni na fari har ya zuwa yau. Amma ba shaidarsu kaɗai ake da ita ba a game da gicciye Almasihu. Ga rahotannin waɗansu nan masu shaida wannan babban al’amari kuma:

1. Annabce-Annabce: Wannan shaida ce wadda ba ta musuntuwa. Ƙarnoni da dama na farko aka hura annabawa su rubuta cikakkun bayanai dangane da mutuwar Almasihu a kan gicciye; alal misali:

a) Sayar da Almasihu a kan kuɗi azurfa talatin- “Sai na ce musu, ‘Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakkina, idan kuwa ba haka ba ne, to, ku riƙe abinku!’ sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana” (Zakariya 11:12).

b) Sayen gonar mai tukwane da kuɗin - “Ubangiji kuma ya ce mini, ‘ka zuba kuɗin a baitulmalin Haikali.’ Sai na ɗauki kuɗin da suka kimanta shi ne, tamanina, na zuba su a baitulmalin Haikalin Ubangiji” (Zakariya 11:13).

c) Wulakanta Almasihu, da yi masa ba’a kafin su gicciye shi - “Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni, suka taso mini kamar garken karnuka, suka soke hannuwana da ƙafafuna. Ana iya ganin ƙasusuwana duka. Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido” (Zabura 22:16, 17).

d) Mugayen raunukan da aka yi masa – “Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hunkuncin da ya sha ya ’yantar da mu, dèkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke” (Ishaya 53:5).

e) Bai ce ƙala ba cikin shan wahalarsa – “Aka ƙware shi ba tausayi, amma ya karɓa da tawali’u, bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, bai ko ce uffan ba” (Ishaya 53:7).

f) Aka yi masa bulala, a ka tofa masa yau – “Na tsiraita ga masu dukana. Ban hana su ba sa’ad da suke zagi na, suna tsittasige gemuna, suna tofa yau a fuskata” (Ishaya 50:6).

g) Suka yi masa dariya – “Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai, dukansu suna kewaye da ni, kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan. Sun buɗe bakinsu kamar zakoki, suna ruri, suna ta bi na a guje” (Zabura 22:12,13).

h) Suka rarraba tufafinsa a tsakaninsu, suka kuma jefa kuri’a a kan rigarsa – “Suka rarraba tufafina a tsakaninsu, suka jefa kuri’a a kan babbar rigata” (Zabura 22:18).

i) Ya yi tambaya don me Uba ya yashe shi – “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako, amma har yanzu ba ka zo ba!” (Zabura 22:1).

j) Mashi zai soki kwiɓinsa – “ ...Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu” (Zakariya 12:10).

k) Za a gicciye shi a tsakanin ɓarayi, za a kuma binne shi tare da masu arziki – “Aka yi jana’izarsa tare da masu mugunta, aka binne shi tare da masu arziki ko da yake bai taɓa yin laifin kome, ko ƙarya ba” (Ishaya 53:9).

l) Ba ko ɗaya daga ƙasusuwansa da zai karye – “Ubangiji yakan kiyaye shi sosai, ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye” (Zabura 34:20).

Idan muka karanta labarun cikin Sabon Alkawari, za mu ga cewa dukan annabce- annabcen nan sun cika.

2. Alamar Gicciye: Kirista na farko sukan yi amfani da alamar gicciye domin su riƙa gane junansu a lokacin da ake tsananta musu. Sukan sassaƙa alamar gicciye a jikin kaburburansu, da wuraren da sukan ɓuya su yi taro a asirce, suna ɓuya daga mugun tsananin mai mulkin Roma, wato Nero. Duk wanda ya kai ziyara zuwa Roma to, zai ga irin waɗannan alamomi.

3. Wa’azin Almasihu Gicciyayye da Almajiransa suka yi: Bitrus ya ce wa Yahudawa, “Ya ku ’yan’uwa, Isra’ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu’ujizai, da abubuwan al’ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani – shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi. Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi” (Ayyukan Manzanni 2:22-24).

4. Shelar da Almasihu ya yi da kansa: Marubutan Bisharun nan huɗu sun ba da labarin/rahoton cewa, Almasihu ya sha faɗar gicciye shi da za a yi, da kuma mutuwarsa, da kuma ambatar cewa ceton su daga zunubi ya bukaci mutuwarsa a kan gicciye. Ga ɗaya daga cikin lokatan da ya riƙa yin wannan faɗi: “Yesu na tafiya Urushalima, ya ɗauki almajiran nan goma sha biyu waje ɗaya. Suna tafiya ke nan sai ya ce musu, ‘To, ga shi, za mu Urushalima, za a kuma ba da ɗan mutum ga mayan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bashe shi ga al’ummai, su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi” (Matiyu 20:17-19).

5. Tsayayyar Shaida Cikin Takalidan/Al’adun Kirista: Tun farkon ɓullowar Kristanci, masu bin Almasihu suke aiwatar da hidimar ‘Jibin Ubangiji’ ana kiran wannan ‘Zumuntar Jiki da Jinin Almasihu’. Almasihu kansa ya kafa wannan doka a daren da aka bashe shi. Ya faɗa wa almajirinsa su yi wannan domin tunawa da shi. Almasihu ya ce “Ina so ƙwarai ko da ma in ci Jibin nan na ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya. Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulki Allah.” Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan ku shassaha. Ina gaya muku, daga yanzu ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.” Sai ya ɗauki gurasa, bayan ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni” (Luka 22:15 -19).

Almasihu ya ba da tabbaci cewa, ya mutu ne domin kafarar zunubanmu, kuma an ba da shi hadaya domin ’yan adam. Almajiran suka riƙa yin wannan hadima, su kuma suka miƙa ga na biye da su har ya zuwa yau ɗin nan: “Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya ɗauki gurasa, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura ya ce, ‘wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.’ Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo,ya ce ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da jinina. Ku yi haka duk sa’ad da kuke sha, domin tunawa da ni” (1Koranitiyawa 11:23- 25).

6. Shaidar Tarihi: Tarihi ma ya ba da labarin mutuwar Almasihu. Marubutan tarihi sun ba da labarin wannan al’amari, sun yi dogon bayani a game da wannan cikin labarunsu. Wasu daga cikin waɗannan masana tarihi su ne: Tacitus, shi daga cikin arna yake, cikin shekara ta A.D 55 ya yi nasa rubutun; Lucian Bahelene ya yi nasa rubutun cikin A.D. 100; sai kuma Josephus, Bayahude wanda ya yi rayuwarsa shekaru kaɗan bayan an aikata gicciyewar. Dukan rubuce-rubucensu sun yi muwafaka da labarun da Linjila/Bishara ta ƙunsa dangane da haihuwar Almasihu, da koyarwarsa, da gicciye shi da kuma tashinsa daga cikin matattu.

7. Shaidar Rubutattun Labarun Hukumomin Romawa: Mafi muhimmanci duka daga cikin rubutattun labarun hukumomin Romawa shi ne rahoton da Bilatus ya rubuta zuwa ga Kaisar Tibariyas. Cikin rahoton, Bilatus ya bayyana dalla-dalla a game da ayyukan Almasihu, da zarge-zargen Yahudawa gāba da Almasihu, da kuma yadda ya zamar masa wajibi ya yanke hukincin kisa a kan Almasihu ta hanyar gicciyewa don ya kauce wa tawaye daga Yahudawa. Wannan rubutacciyar takarda tana ɗaya daga cikin muhimman rubutattun abin shaida da masanin nan Kirista, mai suna Tertullian ya mora cikin fitacciyar kāriyarsa ta Kirista.

8. Shaidar Littafin Al’adun Yahudawa da ake kira Talmud: Sanin kowa ne cewa Yahudawa al’umma ce mai bin Attaura wadda Musa ya rubuta. Mutane kaɗan ne su ka san muhimmin littafi guda na al’adun Yahudawa da aka sani da suna ‘Talmud’. Wannan littafi yana ƙunshe da al’adu/takalidan Yahudawa, tun daga kakannin kakanninsu, wanda sau da dama yakan maye gurbin Dokar Allah. Yesu ya taɓa tsauta musu a kan wannan, inda ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al’adunku?” (Matiyu 15:3).

Mukan karanta a cikin littafin Talmud shafi na 42 cewa, “An gicciye Almasihu kwana ɗaya kamin Idin ƙetarewa, an kuma faɗa kwana 40 kafin gicciyewar cewa za a kashe shi saboda shi mai sihiri ne, ya kuma ƙuduri ruɗin Isra’ila don ya ɓad da su”.

9. Shaidar Kur’ani: A ƙalla akwai wurare biyar a cikin Kur’ani da suke tabbatar da mutuwar Almasihu. Uku daga cikinsu sun mori kalmomin nan ‘Mutuwa’ ko ‘Ƙarewa’:

1) Suratu Maryam 19:33

2). Suratu Al Imrana 3:55

3). Suratul Maida 5:116,117.

Sauran kalmar ita ce ‘kashewa’ ko ‘kisa’

1). Suratul Baƙara 2:87

2). Suratu Al Imrana 3:183

10. Tashin Almasihu daga cikin matattu: Tashin Almasihu daga cikin matattu ita ce shaida mafi ƙarfi a game da mutuwarsa a kan gicciye, domin kuwa Linjila/Bishara mai tsarki tana faɗa mana: “Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus iznin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izni, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu. Nikodimu kuma, wanda farkon zuwansa wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al’ul a gauraye wajen awo ɗari. Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lilin game da kayan ƙanshin nan, bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa ba. Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa sai suka sa Yesu a nan” (Yahaya 19:38-42. Amma a rana ta uku, kamin ketowar asuba, sai aka yi babbar girgirar ƙasa, domin mala’ikan Ubangiji ya sauko daga sama, ya mirginar da babban dutse daga ƙofar kabarin. Wannan ya tsoratar da masu tsaro, waɗanda Bilatis ya umarta su tsare kabarin bayan da aka hatimce shi. Zai yiwu ƙyallin walƙiyar mala’ika ta hana masu tsaron su iya ganin yadda Yesu ya tashi har ya fito daga kabarin. Amma duk da haka, mala’ikan ne da kansa ya sanar da Maryamu Magadaliya cewa Almasihu ya tashi, a lokacin da ita da abokanta suka iso wurin kabarin tun da sassafe.

Daga wannan fa, Tashinsa daga cikin matattu babu wata tantama, Yesu Almasihu ne aka gicciye, domin Yesu kansa ya faɗa wa Yahudawa cewa: “Ku rushe haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku” {Yahaya 2:19). Duk wanda ya musunci wannan gaskiyar to, yana zargin Allah ke nan, da Almasihu da kuma mala’iku cewa sun haɗu don su ruɗi ’yan adam.

Nufin Yahudawa cikin ƙoƙarinsu na kawar da Yesu daga doron ƙasa shi ne, don su hana yaɗuwar Kristanci, domin sun gane a cikin jawabansa, ƙarshen tsananin kishinsu na addini ya zo, duk da na kabilancinsu. Saboda haka, da suka yi nasarar rinjayar hukumomin Romawa don a kashe shi, aka kuwa kashe shi, aka kuma kwantar da jikinsa cikin kabari, sun zaci sun cika burinsu ke nan.Amma Bisharar Allah babu miyagun ikokin da za su iya tsai da ita. Ba da ɓata lokaci ba ta mamaye kowace kusurwa ta duniya. Dubban mutane sun juyo ga gicciyen Almasihu.

Don haka, Yahudawa ba su cim ma burinsu ba, sai dai shayi suke yi cewa sun cika burinsu ... Sa’an nan Kur’ani ya iso da nasa maganganun bayan shekara ɗari shida. Waɗanda suke jayayya a kansa ba su da tabbas a hannuwansu, suna kuma tsammani tunaninsu gaskiya ne. A zahiri ba su kashe shi ba, domin “Ya tashi a kan rana ta uku!” Sa’an nan kalaman Kur’ani suka zo suna ƙarfafa wannan babban al’amari: “Kuma aminci ya tabbabta a gare ni a ranar da aka haife ni da ranar da nake mutuwa da ranar da ake tayar da ni ina mai rai” (Suratu Maryam 19:33). Da kuma cewa, “Ya Isa! Lalle Ni mai karɓar ranka ne, kuma mai ɗauke ka ne zuwa gare ni, kuma mai tsarkake ka daga waɗanda suka kafirta... ” (Suratu Al Imrana 3:55).

Yanzu kuma ka yardar mini in taɓo batun tatsuniyan nan mai ban dariya wadda ka ambata a cikin wasiƙarka, wadda ta yaɗu cikin Musulmi. A taƙaice, tana iƙirarin cewa, wani ne aka gicciye a maimakon Almasihu. Bari in faɗi maka cewa, faɗar annabci ba ɗaya ba, ba biyu ba, tun kamin a haifi Yesu cikin jiki, da kuma faɗar Almasihu kansa sun sa wannan batun “madadi” ya zama tatsuniya kawai, ba ma ƙage marar tasiri kawai ba, amma mafarki marar ma’ana. Mafi muni duka shi ne, wannan yana mai da Allah-Maɗaukaki, Mafifici, ya zama marar adalci ke nan, kuma mai ruɗi. Wane irin mugum rashin adalci ke nan, a ce an lanƙaya kamannin Almasihu ga wani mutum, wanda zai mutu a madadin Almasihu, ba tare da mutumin ya ce ƙala ba a game da al’amarin! Wane irin mugun ruɗi ke nan, a ce Allah ya hura annabawa su yi faɗin zuwan Almasihu domin ya fanshi duniya ta wurin mutuwarsa ta hadaya , don ya kawar da zunubansu. Sai a ce da lokaci ya yi sai Allah ya sāke shirinsa, ya sa wani ya mutu ba tare da bayyana dalilai ba, sai ya bar mutane suna shakkar amincinsa? Ashe, ba za ka yi tunanin cewa, wannan da aka gicciye a kuskure ba zai cika duniya da ihu ba ya na cewa, shi fa bai yi laifin kome ba kafin a kai shi inda za a kashe?

Ba shakka, irin wannan labari, babu mai cikakken hankali da zai yarda da shi, saboda haka ne ma wasu manyan malaman Islama ba su yarda da wannan labari ba, babba daga cikinsu shi ne Fakhr-Ed-Deen Al-Razi. Shi ne ya yi cikakken bincike a kan wannan batu, ya ƙare da cewa, wannan ƙage ne na ɓatanci kawai, aka ƙara gishiri a kan abin da ya wakana. Kana iya karanta sharhinsa a game da wannan, a kan aya nan Suratu Al-Imrana 3:55.

V. Sākiyar ABUBUWAN DAKE CIKIN NASSOSHI

A cikin wasiƙarka ka ce: “Na gaskata cewa Isa, (Salama ta kasance a gare shi), da ya gane makircin da suka ƙulla na su gicciye shi ‘sai ya bar littafinsa a duniya’. Lokacin da aka gicciye wannan mai ɗauke da kamanninsa, sai aka ƙone dukan littattafan nan. Don haka, sai wasu mutane suka sāke rubuta abubuwan da suka sani, suka ƙaƙƙara abubuwwan da suka ƙaga don kansu. Wannan yake bayyana mana yadda aka sami bishara da yawa, kowacce kuma ta bambanta da sauran. Kur’ani kuwa a dunƙule yake, kuma ba a yi sākiya a cikinsa ba. Attaura ma an yi sākiya a cikinta, ba kamar yadda aka saukar wa Musa take ba.”

Ba ni so in shiga musu da kai, a kan cewa Kur’ani ma ai, gutsattsari ne aka tattara, ko kuma an yi sākiya a cikinsa; babu ruwana da wannan. Amma duk da haka, da farko dai ina da ’yanci in biɗa daga gare ka, waɗanne littattafai ne aka ƙone su ƙurmus? Idan kana batun littattafan Linjila/Bishara ne, to, ba zai taɓa yiwuwa ba, don kuwa ba a kai ga rubuta su ba tukuna a wancan lokaci. Idan kuma kana nufin littattafan Attaura ne, waɗannan ana matuƙar tsaronsu cikin haikali da majami’u. Ban sani ba, ko kana nufin cewa, a zahiri Yesu ya rubuta littafi ya bari a duniya har ya shiga hannun masu ƙone-ƙonen littattafai; ko kuma suka yi sākiya a cikin dukan abin da ya ƙunsa, ko kuma cikin wani sashi na littafin.

Ban tsammani akwai wani Musulmin kirki ko da guda ɗaya a duniya da zai yarda da wannan batu naka ba, muddin dai mutumin yana cikin hankalinsa sosai. Musamman tun da shike Kur’anin Musulmi ya shaidi gaskiyar Bishara; da yake cewa, “Ya ku mutanen Littafi! Ba ku zama a kan kome ba, sai kun tsayar da Attaura da Linjila da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku” (Suratul Maida 5:68). Da kuma cewa, “Kuma sai mutanen Linjila su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fasikai” (Suratul Maida 5:47).

Idan muka ƙara ayoyin nan a kan umarnin da aka yi wa Muhammadu da ya yi imani da abin da ke a rubuce cikin Littafi Mai Tsarki, (dubi Suratush Shura 42:15, tana cewa, “Na yi imani da abin da Allah ya saukar na littafi, kuma an umarce ni da in yi adalci a tsakaninku. Allah ne Ubangijinmu”). To, kuwa za ka fuskanci wata tambaya da za ta kunyatar da kai, ga tambayar: Ko daidai ne a ce bayan ɗaruruwan shekaru haka, bayan hawan Almasihu zuwa sama, a ce Allah ya kira Muhammadu don ya yi imani da littafin da aka muzanta?

Ban zaci kana da jahilci a game da gaskiya cewa Musulmi na kowace tsara da zamani, Kur’ani ya umarce su da su gaskata Littafi Mai Tsarki. Gama ya ce, “Ya ku waɗanda suka yi imani! ku yi imani da Allah da Manzonsa, da Littafin da ya sassaukar ga Manzonsa da Littafin nan wanda ya saukar daga gabani” (Suratun Nisa 4:136). Kuma, “Ya shar’anta muku game da addini, abin da ya yi wasiyya da shi ga Nuhu da abin da muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da muka yi wasiyya da shi ga Ibrahim da Musa da Isa, cewa ku tsayar da addini sosai, kuma kada ku rarrabu a cikinsa” (Suratush Shura 42:13).

Idan muka shiga da zurfi cikin nazari a game da Kur’ani, za a samu a cikin sassa, da shafuka ba goma kaɗai ba, suna nan da yawa da suke shaidu a game da gaskiyar Attaura da Linjila/Bishara, da kuma alkawarai masu yawa daga wurin Allah don a kula da maganarsa, a tsare ta daga yi mata shisshigi da sākiya. Ga wasu daga cikinsu:

“Lalle mu ne, muka saukar da Ambato kuma lalle mu, hakika, masu kiyayewa ne gare shi” (Suratul Hijr 15:9).

“ ...Ba za ka sami musanyawa ba ga hanyar Allah” (Suratul Ahzab:62).

“Kuma babu mai musanyawa ga kalmomin Allah” (Suratul An’am 6:34).

Cewa an sauya kalmar Allah, to, daidai da a yarda ne da cewa alkawaransa da ke a rubuce cikin Kur’ani don su tsare/kāre wannan kalma sun kāsa ke nan. Haka kuwa ba zai yiwu ba tun da yake Allah mai aminci ne kuma mai adalci, mai kuma iya kiyaye kalmarsa ne. Wannan gaskiya ce musamman tun da shike gaskiyar da tsarkinsa sun bukaci haka. A ƙarshe fa abokina, sai me za ka yi da Kur’ani da yake cewa, “Ka ce, ‘To, ku zo da wani littafi daga wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bi shi, idan kun kasance masu gaskiya’” (Suratul Ƙasas 28:49).

Yanzu kuma, don a faɗi gaskiya, ba abin da zan yi illa in tambayi masu zargin cewa an yi sākiya cikin maganar Allah su faɗi ko wane lokaci ne a ka yi waɗannan sāke-sāken.

Idan an yi sāke-sāken kafin ɓullowar Islama, to, don me Kur’ani ya shaidi Littafi Mai Tsarki, ya tabbatar da abin da ya ƙunsa, yana kuma ƙarfafa gaskiyarsa. Idan sāke-sāken da ake zargi sun auku bayan yaɗuwar Islama, to, wannan iƙirari kuma ba shi da amfani ko tasiri, tun da shi ke akwai daɗaɗɗun rubutun littattafan Littafi Mai Tsarki a adane cikin gidajen tara kayan tarihi waɗanda sun girmi Islama da ƙarni uku. Ayoyi/matanin rubutattun takardun nan ba su bambanta ba ta kowace hanya daga ayoyi/matanin littattafan da ake aiki da su yanzu haka.

A kan wannan kam, ba zan iya yin shiru ba, sai na yi tambaya idan zai zama daidai a ce, Kur’ani ya shaidi Littattafai masu daraja haka a Gaskiya ne da Allah ya saukar domin jagora da jinƙai ga ɗan adam, sai kuma daga baya a ce an yi sākiya a ciki? A aikace, in irin haka ya faru, to, wato ke nan Kur’ani ya kāsa cikin aikinsa na tsaron lafiyar Littafin. Gama yana cewa, “Kuma mun saukar da Littafi zuwa gare ka da gaskiya, yana mai gaskatawa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littafi... ” (Suratul Maida 5:48).

Akwai tambaya guda ta ƙarshe a game da wannan batu: Ina matsayin masu cewa an yi sāke-sāke, da shike akwai tsararrun abubuwa tabbatattu da suka ƙure gardandamin da ake yi a game da batun cewa an yi sākiya cikin Attaura? Babu yadda za a ce Yahudawa sun sassāke Attaura kamin bayyanar Almasihu. In ba haka ba, da Almasihu bai tabbatar da ita ba, da kuma bai riƙa faɗo nassi daga cikinta ba. Haka kuma ba yadda za a ce sun sassāke ta bayan zuwan Almasihu, in haka ne da sun sami suka ƙwarai da gaske daga wurin Kirista. Ba shakka, da babu yadda za a yi a ce Yahudawa da Kirista su yarda da juna a kan sāke-sāke da ke cikin Littattafai Masu Tsarki, da farko dai, waɗannan mutane ne da suka sha bambam da juna ƙwarai da gaske, na biyu kuma domin Littafi Mai Tsarki ya bazu ko’ina a dukanin duniya, kuma cikin harsuna masu yawan gaske. Babu yadda za a yi a iya tattaro dukan waɗannan kofe na Littafi Mai Tsarki masu ɗumbin yawan da ba su ƙidayuwa don kawai a zo a yi sākiya cikin nassin/matanin.

VI. BISHARU DA YAWA

Iƙirarinka na cewa, kasancewar Bishara da wasiƙu fiye da ɗaya yana tabbatar da cewa an sassāke abubuwan da su ka ƙunsa, wannan kuwa ya zama abin kaico. Bisa ga dukan alamu, ba ka gane cewa, Bisharu guda huɗu, da wasƙu, da littafin Wahayin Yahaya, da Littafin Ayyukan Manzanni, su ne suka haɗu suka zama “Sabon Alkawari” wato Linjila ke nan. Saboda haka, samun littattafai da dama cikin Sabon Alkawari ba yana nufin cewa an lalatar da Linjila/Bishara ba ne, kamar yadda surori 114 suke a cikin Kur’ani ba zai sa a ce an tabbatar cewa an lalatar da Kur’ani ba

AKWAI AMSA GA KOWACE TAMBAYA:

Idan a cikin fassarar da muka yi cikin littafin nan ba ta taɓo ayar da kake muradin bayani a kanta ba, ko kuma kana da ƙarin wata tambaya a game da Maganar Allah, in ka yarda, sai ka rubuto mana. Mu kam, cikin ƙauna, nan take za mu amsa ko waɗanne tambayoyi da kake da su a zuciyarka. Ka aiko da tambayoyin zuwa ga:

KACINCI-KACINCI

Zuwa ga mai karatu:

Idan ka iya ba da amsar mafiya yawan tambayoyin nan da kyau, za mu aiko maka da wani ɗan littafi daga cikin littattafan da muke da su.

 1. 1. Me ka fahinta daga Suratu Yanus 10:94?

 2. 2. Ko Kur’ani ya yi suka ga masu koyarwar Maryamiyawa, kuma don me?

 3. 3. Ko Kiristan farko sun yarda, ko kuma sun musunci gaskatawa da koyarwar ƙarya ta Maryamiyawa?

 4. 4. Ko soke - soken da Kur’ani ya yi masu tsanani, a kan masu aikin kafirci yana yi ne da Kirista ko Maryamiyawa?

 5. 5. Ka nuna bambancin da ke a tsakanin gaskatawar Kirista a game da Almasihu da kuma na Maryamiyawa.

 6. 6. Ka bayyana hanyar da Kirista suke ɗaukar Almasihu ya zama “Åan Allah”.

 7. 7. Ka ba da wasu batutuwa na Yesu da suke tabbatar da ɗiyancinsa na allahntaka.

 8. 8. Wace irin haihuwa ake nufi a cikin Suratul Ikhlas?

 9. 9. Ko Yesu Annabi ne kaɗai? Ko mun yi daidai idan mun gwada shi daidai da sauran?

 10. 10. Ka rubuta abin da ka fahimta a taƙaice a game da ayoyin nan: Ibraniyawa 1:1-6, da kuma Zabura 2:7.

 11. 11. Yaya Yesu ya bayyana doka a kan kisan aure cikin Linjila?

 12. 12. A kan wane irin al’amari ne Almasihu ya yarda a kashe aure?

 13. 13. Menene koyarwar Linjila/Bishara a game da kayan sha masu sa maye?

 14. 14. Ko bambance-bambancen da ke tsakanin Kur’ani da Linjila/Bishara sun isa mu ce an sassāke ɗaya daga cikinsu ko ma dukansu?

 15. 15. Menene shaidar Yahudawa wadda Kur’ani ya ba da labarinta a game da gicciyen Almasihu?

 16. 16. Ko shaidar Yahudawa ce kaɗai take tabbatar da cewa lalle an gicciye Almasihu?

 17. 17. Ka ambaci wasu annabci dagane da mutuwar Almasihu.

 18. 18. Me Kirista na farko suka mora don shaidar da suke gane juna?

 19. 19. Me yake ƙunshe cikin Ayyukan Manzanni 2:22-24?

 20. 20. Ko Almasihu ya hurta cewa za a gicciye shi tun kafin ya mutu? A ina ne?

 21. 21. Wane farali ne masu bin Almasihu suke kiyayewa domin su nuna mutuwarsa, da tashinsa, da kuma komowarsa?

 22. 22. Ko akwai abin da ke goyon bayan Linjila daga cikin tarihi a game da ikirarinta a game da gicciyen Almasihu?

 23. 23. Ina sunan Littafin Yahudawa na biyu? Ko ya ambaci gicciyen Almasihu?

 24. 24. Ayoyi nawa ne cikin Kur’ani da suke goyan bayan mutuwar Almasihu?

 25. 25. Wace ce shaida mafi ƙarfi mai nuna cewa Almasihu ya mutu a kan gicciye?

 26. 26. Wanene ya roƙi Bilatus a bar shi ya ɗauke jikin Yesu daga kan gicciye?

 27. 27. Me ya faru, kwana uku bayan mutuwar Almasihu?

 28. 28. Me ka fahimta a game da faɗar cewa, “Kamannin wannan ne kaɗai aka nuna musu”?

 29. 29. Wanene masanin nan Musulmi wanda ya yi sukar ra’ayin nan na “kamanni” da kuma cewa wani ne aka gicciye a madadin Almasihu?

 30. 30. Ko Kur’ani ya shaidi gaskiyar Linjila/Bishara?

 31. 31. Ko Kur’ani ya yi kira ga mutanen Littafi su tabbatar da abin da ke cikin littafinsu na dokoki, ko abin da ke cikin sauran?

 32. 32. Ko an yi kira ga Muhammadu da al’ummarsa da su yi imani da Littafi Mai Tsarki?

 33. 33. Me ka fahinta daga Suratul Ƙasas 28:49?

 34. 34. Ko Kur’ani shi ma zai kuɓuta idan a ka ci gaba da iƙirarin cewa an sassāke Littafi Mai Tsarki?

 35. 35. Ko zai yiwu a iya tattara dukan kofen Littafi Mai Tsarki daga ko’ina a duniya don a daddagula shi? (wato a sassāke).

 36. 36. Me yake ƙunshe a cikin Sabon Alkawari? (wato Linjila/Bishara).

Ka aiko da amsoshinka tare da cikakken adireshinka, da rubutu mai kyau, zuwa ga adireshin nan:


KIRAN BEGE
P.O. Box 14555
KANO
NIGERIA

Internet: www.the-good-way.com -