TIRNITI [MURHUNNIYA] DA ƊAYANTAKA

TIRNITI [MURHUNNIYA] DA ƊAYANTAKA

Laccar da Papa Shenuda III ya bada a Babbar Majami’ar Markus a Alƙahira


TIRNITI [MURHUNNIYA] DA ƊAYANTAKA

Ɗaya daga cikin abubuwan sa tuntuɓe ga Musulmi wajen gane Allah na gaskiya daidai da fahintar Kirista shi ne batun Tirniti [Murhunniya]. Musulmi suna zargin Kirista da bauta wa Allah uku, wato Allah Uba da Uwa Maryamu da kuma Yesu Almasihu Ɗa. Bai yi nisa da gaskiya ainun ba.

Wannan batu a kan Tirniti [murhunniya] da Ɗayantaka na Allah zai taimaka wajen kawar da dukan kuskuren tunani a game da wannan. Muna sa zuciya duk wanda ya karanta ɗan littafin nan zai kai ga fahintar gaskiyar Tirniti [Murhunniya] cikin Allah ɗaya Na Gaskiya.

Matsalar masu sūkar Tirniti ita ce, sun sa batun Tirniti cikin akasin ɗayantaka. Suna shayin cewa Tirnitin Kirista wani salo ne na bauta wa Allah fiye da ɗaya, wato Kirista suna da alloli uku. Duk da haka, mu Kirista mun ce muna gaskata Allah ɗaya tak, ba shi da abokin tarayya, ba shakka kuma ba mu gaskata alloli uku ba. Bugu da ƙari dukan soke -soke sun tarke a kan gaskata alloli uku ne, alhali kuwa ko ta ƙaƙa ba inda wannan ya haɗu da gaskiyar Kirista mai riƙe da Allah ɗaya kaɗai. Ba shakka mun lura cewa gaskata fiye da allah ɗaya wani abu ne da ko Iblis ma ba zai yi wannan ba: “Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro” [Yakubu 2:19].

Daga can ciki, aljannu sun gaskata da Allah ɗaya. Idan sun yaɗa alloli da yawa cikin mutane, ba’a suke yi wa tunanin mutane, su da kansu kuwa suna gaskata Allah ɗaya ne, babu wani sai Shi.

Daga cikin matanin Sabon Alkawari [Linjila] wadda take nuna gaskatawar Kirista ga Allah ɗaya, su ne kalaman Almasihu ga almajirinsa, lokacin da ya aike su zuwa yin wa’azi: “Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki” [Matiyu 28:19]. Ya ce “cikin suna,” bai ce “sunaye” ba. Wannan batu ya fito cikin wasiƙar Yahaya ta fari inda ya ke cewa: “Akwai shaida uku, wato Ruhun da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce” [1 Yahaya 5:8]. Haka yake kuma ga Dokar Kirista ta duniya gaba ɗaya wadda ta fara da: “Ina ba da gaskiya ga Allah. ɗaya.”

Saboda haka, muna gaskatawa da Allah ɗaya babu ƙari. Muna ɗaukar kasancewa da allah fiye da ɗaya kafirci ne, duk kuma wanda ya gaskata fiye da allah ɗaya ko allah uku, to, kafiri ne: Ta wane hali ne Allah, wanda mu duka muka gaskata yake “ɗaya cikin uku”? Me kalman nan “Ɗa” take nufi, me kuma ake nufi da “Ruhu Mai Tsarki”, ko wannan ya musunta zamantowar Allah guda ɗaya tak?

Bari mu fara tattaunawarmu ta fannin “Tirniti [Murhunniya] da Ɗayantaka” a natse wanda ya fi ta yin fushi da ɓatanci. Gama ’yan’uwanmu Musulmi Kur’ani ya hore su cikin Surat Al Ankabout 29:46 cewa: “Kada ku yi jayayya da mazowa Littafi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zalunci daga gare su, kuma ku ce, ‘Mun yi imani da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautawarmu da Abin bautawarku Guda ne, Kuma mu masu sallamawa ne a gare Shi.’” Kuma cikin Suratu Al Imrana 3:113-114 mun karanta cewa: “Ba su zama daidai ba; daga mutanen Littafi akwai wata al’umma wadda take tsaye, suna karatun ayoyin Allah a cikin sa’o’in dare. Suna imani da Allah da Yinin Lahira... ” Cikin Suratul Maida 5:82, ya ce, “Lalle ne kana samun mafiya tsananin mutane a adawa ga waɗanda suka yi imani, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kana samun mafiya kusantarsu a soyayya ga waɗanda suka yi imani su ne waɗanda suka ce: “Lalle mu ne Nasara; Wancan kuwa saboda akwai ƙissisuna [wato firistoci] da ruhubunawa [wato ’yan zuhudu] daga cikin su... ” A nan an gabatar da ƙungiya uku: Yahudawa, da masu bautar gumaka da kuma Kirista.

Haka kuma cikin Suratul Baƙara, 2:62 aka ce: “Lalle ne waɗanda suka yi imani, da waɗanda suka tuba, da Nasara da Makarkata, wanda ya yi imani da Allah da kuma Yinin Lahira, kuma ya aikata, akin ƙwarai, to, suna da ijararsu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.”

Bugu da ƙari, cikin Suratul Hajj 22:17 aka ce: “Lalle ne waɗanda suka yi imani da waɗanda suka tuba [Yahudu] da waɗanda suka karkace [Saba’awa] da Nasara da Majusawa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah yana yin hukunci a tsakaninsu a Ranar Ƙiyama. Lalle ne Allah mahalarci ne a kan dukan kome.”

A sarari yake cikin waɗannan matani cewa, bambanci yana nan tsakanin Kirista da masu bautar gumaka. Haka kuma Islama da kanta ta bambance tsakanin ƙungiyoyin nan biyu, don kuwa ta hana Musulmi ya auri mai bautar gumaka, alhali kuma ta yarda ya auri Kirista. Islama kuma ta yarda a yanka masu bautar gumaka, amma banda Kirista masu biyan gandu. Kirista mutane ne da suka san Allah, ba su haɗa Shi da wasu alloli ba, mun kuma yarda da wannan. Idan kuwa yana da abokin tarayya, to, ya nuna ke nan ba shi da dukkan iko, domin ba shi da iko a kan abokin tarayyarsa. Haka yake kuma, Allah ne Mahaliccin dukka; idan akwai wani allah, to, Allah ne ya halicce shi? In haka ne, wannan halittaccen taliki ba sauran ya zama Allah, domin ba zai iya halittawa ba.

Hakika, muna gaskata Allah ɗaya ne Mai Iko Dukka. Kowane abu yana a ƙarƙashin ikonsa. Babu abin da ke kasancewa wanda ba a ƙarƙashin wannan Allah ɗaya yake ba.

Uku Cikin Ɗaya da Ɗaya Cikin Uku

Tambaya: Cikin Suratul Maida akwai matanin da ya nuna waɗanda suka gaskata da Tirniti Mai Tsarki kafirci ne. Me Tsarkinka ya faɗa a kan wannan?

Amsa: Cikin Suratul Maida 5:73 muna karanta cewa: “Lalle ne, haƙiƙa, waɗanda suka ce: ‘Allah na ukun uku ne; sun kafirta, kuma babu wani abin bautawa face Ubangiji Guda.” Mu ba mu gaskata cewa “Allah shi na ukun uku” ne ba, kamar yadda Suratul Maida ta nuna. Ga abin da muke cewa, Allah Ɗaya ne, kuma za mu sa wando ƙafa ɗaya da duk wanda ya ce Allah “Ɗayan ukun uku” ne. ƙiyasi mafi kyau domin gaskiyar Tirniti shi ne mutum kansa wanda aka halitta “Cikin siffar Allah”. Shi ne mutumin da ya mallaki hankali da ruhu. Mutuntaka, da tunani, da ruhu sun haɗu sun samar da taliki guda. Haka yake, Uba da Ɗa da Ruhu Mai Tsarki mutum guda ne kansa. Ba wanda zai ce Allah ba shi da tunani da ruhu. Allah, cikin tunaninsa da ruhu Allah Ɗaya ne, ba “Ɗayan Uku” ba. Daidai kamar yadda muka ce, wuta tana samar da zafi da haske. Wuta ke nan, da haskenta da zafi, ita abu guda ne, abin da a ka faɗa a game da wuta ana iya faɗi kuma a game da rana.

Allah rayayye ne, mutum mai allahntaka, mai basira, ya ƙunshi tunani, rai da kuma kansa. Tunani da kuma rai, rayuwa guda ce. Haka yake, mutum ba zai iya rabawa tsakanin Uba, da Ɗa da Ruhu Mai Tsarki ba. Muna ce da wannan mai allahntaka, rayayye da kuma basira. Tirniti Mai Tsarki. Manufarmu a nan ita ce bayani a maimakon rabawa.

Tunanin Allah – “Kalman”

Fayyatacce ne cewa Ruhu Mai Tsarki Ruhun Allah ne, babu damuwa a kan wannan... A game da maganar “Kalma” kuwa, ta wane hali ne yake tunanin Allah?

Fayyatacce ne cewa Ruhu Mai Tsarki Ruhun Allah ne, babu damuwa a kan wannan... A game da maganar “Kalma” kuwa, ta wane hali ne yake tunanin Allah?

Allah ya halicci duniya ta wurin tunani mai bisara, ta wurin Ɗansa, ko hankalinsa ko hikima – dukan waɗannan abu guda ne. Allah da tunaninsa abu guda ne. Misalin wannan shi ne lokacin da muka ce, “Na magance matsalar da tunanina”. Kai ne ka magance matsalar ko tunaninka ne? Duk biyu abu guda ne. Wannan rabewa tsakanin kai da tunaninka bisara ne kawai amma bai shafi rabuwa ba. Haka kuma, lokacin da muka ce Uba da Ɗa, ba raba su muke yi ba, amma fayyace batu ne kawai mu ke yi. Idan Allah ba shi da tunani, to, bai zama Allah ba ke nan; ko kuma a ce ba shi da Ruhu, to bai zama Allah ba ke nan. Saboda haka wajibin Allah ne ya kasance da tunaninsa da Ruhu Tirnitin ɗayantaka.

Uba da Ɗa:

Mun gaskata da Allah ɗaya, Shi ne Allah Uba. Daga nan me ake ta magana a game da Ɗa? Mutuntakar ɗan ba ta jikin ɗan adam ba ce, wato ba kamar yadda miji da mata sukan yi jim’i har su haifi ɗa ba ne, a’a. Wata irin haihuwa ce dabam ɗiyanci ne na mutum, da fahimi, da ruhaniya wanda ba shi da wani gami da jiki mai nama da jini. Misali a kan wannan shi ne, lokacin da muka ce tunani ya haifi manufa. Gaskiya ne cewa tunani ya haifi manufa, amma haihuwar ta nama da jini ce? Ko kaɗan, ba haka ba! Kamar yadda tunani ya haifi manufa, kamar haka Uban ya haifii Ɗan. Cikin haihuwa ta nama da jini akwai rabuwa. Amma haihuwa ta Tirniti [Murhunniya] Mai Tsarki babu rabuwa. Kamar yadda Almasihu ya faɗa a cikin Bishara ta hannun Yahaya, “Ni da Uba Ɗaya muke” [Yahaya 10:30]. Ɗan ya zo daga wurin Uba ba tare da ya rabu da shi ba. Ya fito daga wurinsa, duk da haka yana nan a cikinsa, wannan ya kawo tambaya, ta yaya? Zan bayyana maka ta wurin masali: Lokacin da kake tunani, tunanin kuma ya fito kamar sauci, har tunanin nan ya kai kunnuwan mutane, duk da haka tunanin yana nan cikin hankalinka. Yana yiwuwa tunaninka ya bar ka ya shiga littafi wanda a ka rarrabar cikin Amerika inda mutane da yawa suka karanta shi. Ta haka tunanin ya fito daga cikinka duk da haka yana nan a cikinka.

Mun fahinci kalman nan “Ɗa” cikin hanyoyi da dama. Kalmar ta na maganar lokaci da fili kamar lokacin da muka ce cikin misali: Wane ya shiga soja lokacin da yake shekara ashirin da haihuwa, kamar yadda yake a larabci “Ibn Ishreen” ɗan shekara ashirin. Mukan kuma ce, “ɗan Nilu” - Ɗan garinmu - na al’amuran bisara kuma da mukan ce :Wane bai furta “’yar leɓu” ba [“Bint shafa”, ma’ana ɗiyar leɓuna, wato kalma]. Akwai kuma ɗiyancin ruhaniya tsakanin malami da almajiransa, zai kira su: “’ya’yana, almajirai!” Cikin harshen kimiyya mukan yi maganar sāɓani ya haifi zafi... haka kuma cikin Bishara daga hannun manzo Yahaya ƙaunatacce ya ce, “’Ya’yana ƙanƙanana, ina rubuta muku domin kada ku yi zunubi”.

An kuma ce da Ɗa “Hikima” cikin Karin Maganar Sulemanu a Tsohon Alkawari [Kafin zuwan Almasihu cikin jiki]. Wannan yana da azancin hikima da sani... Littafin ya ce: “Cikinsa aka ɓoye dukan taskar hikima da sani...” Haka yake lokacin da mu ka ce ya halicci duniya ta wurin Ɗan, ana nufin cewa ya halicci duniya ta wurin Tunaninsa, Hikimarsa, Hankalinsa da kuma Saninsa. Ta haka ne ya zama Uba ya yi halitta, Ɗa kuma ya yi halitta, su biyun nan Ɗaya ne.

Tirnitin [Urhunniyia ] Arna

Tirnitin da Islama ta ke yaƙi da shi ba Allah na Kirista ba ne. A sarari yake cewa maƙasudin sūkar da Islama ta ke yi cikin matanin Kur’ani yake: “Mahaliccin sammai da ƙasa – ta yaya zai kasance da ɗa, ganin cewa ba shi da mata, shi ne kuma ya halicci dukan abu, shi ne kuma masanin abu duka” [Suratul An’am 6:100]; wannan kuskure ne wanda Islama ta ke ƙi, mu Kirista kuma mu ke yaƙi da shi. Wanda ya ce Allah yana da ɗa ta wurin auren mace, to, wannan kafiri ne ga dokokin Islama da na Kirista ... Tirnitin [Murhunniya] da Islama duk da Kristanci su ke yaƙi da shi, shi ne tirnitin arna. Ana samun misalin wannan cikin addinin Fir’aunanci wanda yake da Isis, da Osiris, da ɗansa Horus, tirnitin da Kristanci ya yi ta yaƙi da shi ke nan tun kafin zuwan Islama. Duk da haka, Islama tana zargin Kirista, a sarari aka yi wannan cikin ayarsu a kan Tirnitinsu, cewa, sun gaskata ya ƙunshi Allah da Almasihu da kuma Budurwa, tun da an ce cikin Suratul Maida: “Kuma lokacin da Allah ya ce, ’ya Isa, Ɗan Maryamu, ko ka ce wa mutane, “Ku ɗauki ni da mahaifiyata a matsayin alloli rabe da Allah”? Ya ce, “Ɗaukaka ta tabbata gare ka! Ba zan faɗi abin da ba ni da ’yancin faɗa ba”’. Mu ma, mun yi musun faɗin wannan, mun ƙi Tirnitin Allah, da Almasihu da kuma Budurwa... Ba shakka muna yaƙi da wannan tare da Musulmi. Ba mu koyar da cewa Budurwa allahiya ce. Akasin wannan, muna ɗaukar wanda ya mai da Budurwa ta zama allahiya shi kafiri ne.

Mutum uku da ke cikin Tirnitin Kirista daidai da juna suke cif: Uba daidai yake da Ɗa, daidai yake kuma da Ruhu Mai Tsarki; babu bambanci ko rabuwa. Masu tarayya ne cikin dawwama, wannan ya bambanta Tirnitin Kirista da tirnitin arna.

Cikin Tirnitin arna akwai su uku – Isis, da Osiris, da Horus – su ba abu ɗaya ba ne, ba kamar Tirnitin Kirista ba wanda yake Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki abu Ɗaya suke.

Tirnitin arna yana da alamun farfagandar jima’i, abin da babu shi cikin na Kirista. Lokaci ma ya bambanta: Cikin labarin arna, akwai lokacin da Osiris da Isis tun kafin su yi aure. Bayan aurensu ne Horus ya samu, Shekarunsa sun kāsa na Osiris da Isis... Cikin Kristanci kuwa babu wannan bambancin a tsakanin mutanen nan uku, domin Allah yana nan tun fil azal, cikinsa ne akwai tunani (Ɗa) da Ruhu (Ruhu Mai Tsarki).

Manufar Tirnitin Kirista ba ta batun yau ko jiya ba, ba kuma Kirista suka ƙaga ba, don wannan yana nan tun fil azal [adun-adun].

Tirnitin [Murhunniya] Kirista da Karkatattun Koyarwa

Cikin karkatacciyar koyarwar Arian, sai Arius ya ce, an halicci Ɗan ne, ta haka ya nuna jahilcinsa a kan ainihin Tirniti Mai Tsarki. Don in da ya gane cewa Ɗan tunanin Allah ne, da ya gane cewa ba zai yiwu Allah ya halicci tunanin kansa ba; domin da wannan ya zama ke nan bai kasance kafin halittarsa ba. Ba zai taɓa yiwuwa ba Allah ya kasance ba tare da tunaninsa ba ko da sau ɗaya ne, sam! Saboda haka, ba shi yiwuwa Ɗan ya zama halittacce. Allah da Tunaninsa suna nan tun fil azal. Ko da shike gaskiya ne cewa akwai lokacin da ya zama jiki, duk da haka Ɗan ya kasance tun kafin ya zama jiki.

A game da Ruhu Mai Tsarki kuwa, waɗannan da suka ce halittar sa aka yi, to, ba su fahinci Tirniti Mai Tsarki ba. Ta yaya Allah zai kasane kafin Ruhunsa Mai Tsarki? Abin da ke nan shi ne, Allah cikin tunaninsa da Ruhu ya kasance tun fil azal. Kalman nan kuma “Allah” tana iya shafar kowane ɗayan Ukun nan. Daga nan muke cewa: Allah Uba, Allah Ɗa, da Allah Ruhu Mai Tsarki.

Wanda ya ƙago ƙungiyar da ake kira a turance, “Neo-Platonist Philosophies” yana mai ra’ayin cewa ba zai yiwu ba Allah ya yi hulɗa ta kai tsaye da al’amari. A sakamakon haka sai ya halicci matsakaici wanda yake da mahaɗi da al’amari. Wannan matsaikaci yana tsakanin kansa (Allah) da al’amari (mutum). Amsar Kirista ga irin wannan ussan ilimi ita ce, ba mu ga wata matsala ba ko kaɗan a game da halittar da Allah ya yi wa al’amari, wato mutum. Idan halittaccen allah (matsakaici) ya kasance, ba daidai ba ne a kira shi Allah domin dole akwai lokacin da allahn nan bai kasance ba. Daga wannan muna iya ganin cewa, irin allahn nan ana iya yin abu ba tare da shi ba, tun da shike duniya ta kasance, an kuma sarrafa ta ba tare da shi ba ... Saboda haka, Uba da Ɗa (Allah cikin jiki) ɗaya suke, abu guda ne kuma.

Allah Ruhu ne da Hikima (ko tunani) kuma Shi mutum ne na allahntaka. Ta haka muna iya magana a kan allahntakar Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, da Uba kuma; duka uku su Ɗaya ne. Babu bambanci a tsakanin mutum ɗaya na Tirniti da sauran biyun.

KACINCI KACINCI

Idan ka karanta ɗan littafin nan a hankali, za ka iya amsa tambayoyin nan cikin sauƙi:

  1. Ta yaya za ka iya tabbatar da cewa Kirista sun gaskata Allah ɗaya ba alloli uku ba? Ka ba da ayoyi daga Littafi Mai Tsarki!

  2. Yaya za ka iya bayyana ɗayantakar Tirniti Mai Tsarki?

  3. Ina ma’anar kalman nan ta Helenanci wato “Logos”, don me kuma akan more ta a kan Allah?

  4. Yaya za a fahinci ɗiyancin Almasihu cikin dangantakarsa da Allah Uba?

  5. Ina bambanci a tsakanin tirnitin arna da Tirnitin Kirista?

  6. Mecece amsar Kirista ga karkatacciyar koyarwar Arius da sauran masana ussan ilimi?

Ka aiko mana da cikakken adireshinka, muna a shirye mu aiko maka da ɗan littafi biye da wannan.


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland