DALILIN ZAMANA KIRISTA

DALILIN ZAMANA KIRISTA

DAGA SULTAN MUHAMMED PAUL

All Rights Reserved

1996

2004


ROƘO

Ana kira ga mai karatu da ya yi la’akari da waɗannan, lokacin da ka ke karatun littafin nan:

1. Waɗanne ne bukatun ruhaniya a kan ɗan adam?

2. Wane addini ne zai iya biyan waɗannan bukatu?

3. Wace hanya ce yanzu ta karanta Littafin Mai Tsarki?

GABATARWA

Mutumin zamani yana nishi da nauyin tunanin abubuwan da ba gaskiya suke ba a game da iyali, da zamantakewa, da kuma ingancin al’ummar ƙasa. Waɗannan irin tunani marasa gaskiya akan gane da su cikin sauƙi a cikin kowaɗanne irin mutane, da kuma a kowane-kai wanda a addinance ana ce da wannan “muguntar mutum.” Wannan lalacewa ta cikin mutum tabbatacce ne ta kafu a cikin gāba da Allah Mai Tsarki Rayayye. Lahanin dafin zunubi ya lalatar da zukatan mutane, yadda duk da sanin muguntar zunubin, su na jin daɗi, su na fādawa ciki a sake. Wannan riƙaƙƙen jangwan na zunubi da biɗar ’yanci daga laifin zunubi da ƙanginsa, shi ne ya fuskanci Sultan Muhammed Paul.

Mai yiwuwa ne akwai waɗanda ba su kula da matsalar zunubi da hanyar ceto ba. Sun gwammace su lulluɓe matsayin zuciyarsu daga gare su da kuma ga sauran mutane, ko da shike su na sane sarai cewa, ɓoyayyun abubuwa cikin zuciya a bayyane suke domin Allah ya duba. Irin waɗannan mutane, wannan labari ba zai daɗe kome a gare su ba. Duk da haka, akwai wasu da suka damu ƙwarai a kan zunubi da ceto a cikin rayukansu, da rayukan sauran mutane. A gare su, wannan ɗan littafi zai yi taimako wajen auna nasu abin da suka sani daga hasken waɗannan na Sultan Muhammed Paul. Muna fata zai zama sanadin samun bishewa da labarka daga wurin Allah Rayayye ga dukan waɗanda su ka karance abin da ke cikin ɗan littafin nan.

MAWALLAFA

II. FARKON RAYUWA DA NAZARI

Ƙasar haihuwata ita ce Afganistan. Mahaifina ya na da zama babban birnin Logar, wajen mil hamsin kudu da birni Kabul.

Mahaifina mai suna Payanda Khan, yana da matsayin da ake kira, “Bahadur Khan.” Duk ƙasar an san shi da muƙamin “Kanar Bahadur Khan.” Mahaifinsa ne na kurkusa. Ta haifa masa ’ya’ya uku duka mata. Don kada iri ya ƙare, sai ya auri ɗiyar Sayyid Mahmud Aga, ɗaya daga cikin manyan iyali masu faɗi aji na Afganistan. ‘Kanena, Taj Muhammed Khan da ni, matar ta biyu ce ta haife mu. An haife ni a 1881.

Ba da daɗewa ba bayan da Abdur Rahman Khan Amir (wato mai mulki), ya komo daga Russia a karagar Mulkin Kabul, sai ya kama shida na manyan mutanen ƙasar, ya tura su zuwa wani wurin da ba a sani ba. Daga baya sai aka kashe su. Mahaifina yana daga cikinsu. Daganan sai bala’i na biyu ’ya’uwan mahaifiyata su biyu, daga baya aka kawar da su zuwa India. Ba da jimawa ba bayan wannan, sai ɗan’uwan mahaifiyata na uku, tare da mahaifiyarsa, da bayinsu, suka zo India, da iznin Amir, sauran dangina mafiya kusa kuwa su ka yi zamansu a Kabul. Da su ka isa India, sai suka zauna a Hasan Abdal.

Saboda ƙarin wahalolin siyasa, sai dukan iyalinmu suka ƙaura Hassan Abdal. Bayna watanni da dama, sai mamata ta rasu. A ƙarshe, bayan sulhu tsakanin iyalinmu da Amir, Abdur Rahman Khan, sai dukan iyalinmu in ban da ’yan’uwan mahaifiyata su uku da ni kaina, duk suka komo ƙasar haihuwarmu.

Daga baya na tafi Delhi na shiga makaranta, Madrsasa-i-Fateouri, don in ƙware cikin binciken larabci. A wancan lokaci, malamin shi ne Mawlana Abdul Jalil ɗan asalin babban jinsin Afganistan. Malami na biyu shi ne, Fateh Muhammed Khan na Quandahar. Ta wurin alherin mutum biyu nana a kaina, sai da nan na kammala nazarina, na juya da takalidai da sharfofi. Da rana sai in yi karatu tare da ’yan ajina. Da dare kuwa, nakan ɗauki ki\oyarwa ta musamman daga Mawlana Abdul Jalil. Ta haka, tawurin Alheri, Allah, na iya waɗannan fannoni.

III. FARKON SADUWATA DA KIRISTA

Wata rana ina komowa tare da abokina zuwa Chadni Chowk, sai muka ga babban taron mutane sun tare kusa da makarantarmu, Da mu ka iso wurin, sai muka lura ana ta gardama a game da batun Tirnit tsakanin wani Mai wa’azin Kirista da wani dalibinmu. Kiristan ya sami goyon bayan wata ayar Kur’ani:

“Mun fi kusa da shi jijiyar wuya” (Alkur’an 50:16).

Yana cewa mutum ɗaya da ya zama jama’i “Mu” an yi amfani da shi a nan yadda idan zamantowar guda na Allah Tabbatattu ne “Ni” da shi aka mora maimakon “mu”. Da shike ɗalibin ya na ba da amsar da ba a kan hanya take ba, sai abokina su ka iza ni don in amsa wannan gardamar mai fari da ake ambato da jama’i, to, bisa ga Larabci, bayanin salon magana ne, ana morarsa domin girmamawa ba ana nuna jam’i ba ne.

Wannan ne zarafi na fari gare bi na saduwa da Kirista cikin muhawara. A wannan rana, sai wani hali ya shuku marar bayyanuwa a cikina na yi muhawara da Kirista, wannan ɗoki ya tura ni in yi zurfi ƙwarai, da kuma damuwa game da waɗannan asirai. A sakamakon haka, sai na shiga tare sanannnun littattafai gwargwadon iko don sukar Kristanci. Na yi nazarin littattafai masu yawa, sai na fara zuwa a cibiyar Kirista a wasu azazzun ranaku domin ci gaba da tattaunawa da masu wa’azi Kirista.

Wata rana, sa wani malamin Kirista Ba- Ingilishi, wanda ya ke zuwa tare da masu wa’azin, sai ya ba ni katinsa na ziyara, ya gayyace ni zuwa gidansa. Yana da kirki, har ya ce in zo tare da abokina. Haka kuwa a ka yi, na je tare da abokai biyu ko uku. Lokacin da muke shan shayi, sai mu ka fara wata tattaunawa mai bansha’awa a kan al’amaran addini. Ya tambaye ni, ko na karata Littafi Mai Tsarki. Sai na ce, “Don me zan karnta Littafi Mai Tsarki? Wa zai karanta wannan irin littafin da aka daddagula, wanda mutane suke sassākewa shekara?” Sai baturen nan ya bude ni cike da tausayi saboda amsar da na ba shi, ya na murmushi, sai ya ce “Kana ɗauka dukan Kirista marasa gaskiya ne? A ganinka, ba ruɗin duniya ta wurin Attaura da Linjila, sun ɗauka dukan Kirista su na ta daddagula matanin Attaura da Linjila, sun ɗauka dukan Kirista ba su da gaskiya, kuma masu ruɗin mutane ne. Yanzu wannan zargi mai tsanani ne, marar tushe kuma. Kirista sun gaskata Kur’ani. Haka yadda Musulmi ba su iya sāke matanin Kur’ani, ta yaya Kirista za su iya sāke matanin Littafi Mai Tsarki, Littafin Allah mai dukan hikima? Idan wani maɓarnacin musulmi ya yi wauta ya canja matanin wata aya ta Kur’ani,ashe da ba dukan Musulmi za su ɗauke shi ya fita daga hanyar Musulunci ba, a kuma fallasa ainihin gaskiya a kansa? Haka kuma, idan wani maɓarnacin Kirista zai canja matanin wata ayar Maganar Allah, ashe da dukan Kirista na gaskiya a kansa? Ba shakka da sun yi! Daga wannan za ka iya ganin cewa irin Zargin da Musulmi su ke yi wa Kirista cewa sun dagula maganar Allah, ba shi da tushe ko kaɗan. Na tabbata cewa, wannan jayayyar da Musulmi su ke yi wadda yawanci suna da rashin sanin Littafi Mai Tsarki, da bangaskiya da kuma rukunan Kirista.” Daga nan, sai malamin nan bature ya ba ni Littafi Mai Tsarki guda biyu, ɗaya daga cikin Faisanci, ɗaya kuma cikin Larabci, ya kuma iza ni in karanta su. Mu ka gode masa mu ka tafi. Ban kula da shirin da mutamin nan ya bada shawara ba. Nufina cikin karatun Littafin Mai Tsarki shi ne, neman aibu daga ciki, don daga ciki in tabbatar da gaskiyar Islama, in kuma iya kwaɓe bakin Kirista cikin muhawara. Ban ma karanta Littafi Mai Tsaki daga farko zuwa ƙarshe duka ba, amma wuraren da Musulmi masu gardandami sukan karanto, su sa rubuce-rubucensu, su nake karantawa. Muddin ina cikin Delhi, ba abin da na fi maida hankali illa yin muhawara da Kirista.

IV. ZURAFAFA KARATU

Ana nan, sai na yi shawarar tafiya Bombay. A can ne na yi sa’ar saduwa da Mawlavi Hidayat Ullah, wani shahararren malamin da ake girmamawa a duk lardin, ya na kuma da iko. Gidansa yana a Kabul, ya kuma saba da iyalinmu sosai. Da dai mu ka san juna a nan Bombay, da farin ciki ya yi mini alkawari zai ƙara karantar da ni. Ya ga na kusa gama fannin hankali ga nazarin sha’anin littattafai. Ya kuma yarje mini in mori ɗakin takardunsa. Wannan malami ya yi yawancin rayuwarsa a Istanbul. Ya yi koyarwa da harshen Farisanci, harshen dukanmu biyu, wannan ya kawo mini sauƙi cikin karatun.

A wannan lokaci, sai ga wani shahararren malami mai kirki, ya zo daga Masarar, aka naɗa shi shehin malami a cikin Madrasa-i-Zakariyya. Sunansa Malam Abdul Ahad na Lardin Jalalabad a ƙasar Afganisatan. Da na ji irin shahararsa, sa na shiga Madrasa-i-Zakariyya, na ƙara karatun manyan littattafai a kan dabaru da ussan ilimi. Malamin nan ya yi ni kamar ɗansa, ya ba ni ɗaki kusa da nasa, yadda zan iya zuwa gare shi a koyaushe don neman taimako.

V. ZURARA MUHAWARA DA KIRISTA

Wata rana tafiya ta kai ne zuwa Dhohi Talab (wata gunduna cikin Bombay) ni da abokan makarantana. A can muka sami wasu masu wa’azi Kirista su na magana da mutane. Nan da nan sai tsohuwar ƙiyayyan nan ta taso mini, na tuna da karawar karawarmu da su a Delhi. Na yunƙura don in je mu kafsa, sai abokina ya riƙe ni, ya ce, “Malam Sahib kada ka kula da su, rabu da su. Gardama da su ɓata lokaci ne kawai. Ba suma san yadda ake tattaunawa ba, ba su san ka’idodin muhawara ba. An dai biya su kuɗi ne don wannan aikin, shi suke cikawa, don haka babu amfanin yin muhawara da su.” Sai na amsa cewa, “Na san mutanen nan sarai, ba su san ka’idar muhawara ba, amma sun san yadda za su ɓad da mutane. Aikin kowane Musulmi marasa tunani daga tarko da ruɗin mutanen nan.” Sai na shiga, ina kawo rashin yarda da abin da masu wa’azin su ke faɗi. Sai su ka maida martani da rawar jiki suna s:ukar abin da na faɗa a gigice.

Tattaunawar ba ta yi tsawo ba saboda ƙaracin lokaci. Labarin karawarmu ta bazu nan da nan a cikin ɗaliban makaranta. Su ma suka harzuƙa don shiga cikin muhawarar. Mun yi ta zuwa sau biyu a mako, don mu gamu da Kirista nan mu yi muhawara. Cikin haka ne, sai wasu Turawan Mishan na CMS suka gayyace mu ta wurin Mr. Josepj Bihari Lal zuwa gidansu. Muna tare ke nan sai suka ce mana Dhohi Talab tana da nisa gare mu ƙwarai, ba za mu iyakaiwa can da sauƙi ba, don haka su ka yarda su buɗe ɗakin karatu domin mu, don mu iya ci gaba da bincikenmu sau ɗaya a mako bisa ga yadda ranmu ke so, muddin dai mu na so mu gane da gaskiyar Kristanci. Na karɓi wannan shirin da murna. Da aka buɗe ɗakin karatun, sai mu ka riƙa haɗuwa a can bisa ga lokacin da muka shirya.

Da na gane cewa ɗaliban makarantar da wasu abokina ba su san kome game da addinin Kirista ba, sun kuma saba da muhawara, sai na yi hayar wani gida bisa ga whawarar Malam Abbas Khan Sahib. A nan mu ka kafa ƙungiyar da muka kira ta “Nadwatul Mutakallimin,” da nufin shirya gwanayen ’yan muhawara gāba da duk addinin da ba na Islama ba, Kristanci musamman. Lokacin da malamina ya lura cewa a koyaushe ina cikin muhawara, har ma ba na marmarin kome a rayuwata, sai ya zo ɗakina wata rana bayan an gama sallar dare. A lokacin kuwa ina karatun Linjila. Ya tambaye ni ko me nake karatu. Na gaya masa sai ya mayar mini cikin fushi cewa, “Ina jin tsoro, ba harzuka, ina ko da shike ba na so in masa rashin ladabi, duk da haka sai na ce masa, “Don me zan zama Kirista? Karanta Linjila kaɗai zai sa ni in zama Kirista? Ina karanta Linjila ne don in lalatar da Kristanci daga tushensa har rassansa. Ya kamata ka ƙarfafa ni a maimakon neman laifi a kaina.” Ga abin da ya ce, “Na faɗi haka ne, don na ji cewa wanda ya karanta Linjila zai zama Kirista. Ba ka ji abin da wani wāƙe ya ce ba: “Lokacin da ya karanta Linjila, sai zuciyar amintacce ta juya ta rabu da bin Islama” Sai na ce, “Wannan ba gaskiya ba ne.” Bayan ƙara bani shawara sai malamin ya koma ɗakinasa.

VI. TAFIYA ZUWA ARABIYA

Mu ka ci gaba da wannan karo na addini shekaru da dama, abin da ban sha’awa, ba labari sai na ji marmarin tafiya aikin hajji a Makka. Nan da nan na yishirye shiryen da suka dāce, na shiga jirgin ruwa da aka kira “Sha-i-Nur,” mai zuwa jeddah daga nan na wuce Makka. Daga Makka na rubuta wa Malam Hassamud Din, wani edita na Kashful Hagaig. A ranar aikin hajji, sai na tufafin aikin hajji, na kama hanya zuwa Dutsen Arafat. A ranar nan, na ga abin mamaki: attajirai da talakawa, manya da ƙanana, duk sun yi ado iri ɗaya da fararen riguna. Sai na ga kamar duk matattu ne suka fito daga kabari nannaɗe da likafani, su na jiran ba da lissafin kansu. Wannan ya sa na yi hawaye. A lokaci guda kuma sai wani tunani ya zo mini: “Idan Musulunci ba addinin gaskiya ba ne, me zai zama matsayina a Ranar Tashin Kiyama?” Daga nan sai na yi wannan addu’a ga Allah, “Ya Allah, ka nuna mini addini na gaskiya, da kuma Hanyarka ta gaskiya. In musulunci addinin gaskiya ne, ka riƙe ni daƙarfi a cikinsa, ka ba ni alherin da zan iya rufe bakin mahassadan Islama. Idan kuwa Kristanci ne addini na gaskiya, to, ka bayyana gaskiyarsa a gare ni. Amin.”

Bayan na kai ’yar ziyarsa a Madina, sai na komo Bombay. Da ba ni nan, sai ƙungiyar “Nadwatul Mutakallimin” ta watse. Da komowata, sai na kafa wata ƙungiyar, Abdur Rauf ne Sakatare. A gidansa kusa da titin da ake kira Grand Road, nan mu ke taruwa. Muka sa kowane mako mu gayyaci wanda ba Musulmi ba ya zo ya yi mana jawabi, ɗaya daga cikinmu ya amsa wa baƙon mai jawabin muhawararsa. Munshi Mansur Masih shi yake zuwa koyaushe don ya yi magana a madadin Kirista. Sauran sukan zo a Arya Samaj (wato mabiya addinin Hindu).

VII. MUHIMMIN AL’AMARI

Wata rana, sai Munshi Mansur Masih ya yi mana jawabi mai rinjawarwa cewa, babu ceto cikin Islama. “’Yan ƙungiyarmu su ka ce in amsa masa, Na yi iyakar iyawata don in tabbatar masa cewa akwai ceto, kuma tabas a cikin Islama. Jama’ar dake a wurin sun yaba da jawabin, duk da haka daga ƙarƙashin zuciyata, na sani sarai amsata ba ta rinjaya ba. A ƙashin gaskiya, ya zama dole in amince da kāsawata. Ko da shike na yi surutai da yawa fiye da abokin hamayyarsa tana da daka tsawa a cikin zuciyata da wani irin ikon da ba zan iya bayyana shi ba.

Kusan wajen ƙarfe 11 na dare muka gama wannan shirin, Na komo gidana ina ta tunani a hankali a kan abin da Munshi Mansur ya faɗa. Bisa ga yawan tunanin dana yi, bisa ga ƙarin zama tabas a gare ni cewa ceto si ne. Bugu da ƙari kuma na gane cewa, mutum tarin mantuwa ne kawai, cike da rashin biyayya, mai ƙetare shari’a. Bai taɓa zama da cikakken tsarki don ya zama ;yantacce daga zunubi ba. Zunubi ya zama halittar mutum ta biyu. Abin da aka gāda gaskiya ne, cewa, “Kuskure halin mutum ne.” Muhimmiyar tambaya ita ce: Ta ya ya mutum zai tsere wa ba da lissafi da kuma hukunci? Ta yaya mutum zai sami ceto? Ya zamar mini aiki in bincike wannan matsala da gaskiya ba tare da son zuciya ba. Idan na gane cewa ceto ya tabbata a cikin Islama, to, sai in gode wa Allah. Da zan haskaka in yi farin ciki! Amma idan babu tabbas a cikin Islama, to, zai zamar mini dole in biɗi addinin da ke da gamsasshen shirin ceto. Da na kai ga wannan shawara, sai na durƙusa na yi addu’a a gaban Allah da kuka mai zafi.Na yi alkawari ba zan karanta Littafi Mai Tsarki kamar yadda na yi a dā ba. Zan iya gane hanyar ceto a cikinsa

VIII. FATAWA A KAN CETO

Daga ranan zuwa gaba, halina ya sāke,na zama mai biɗar gaskiya na gaske, ya fara gwama Littafi Mai Tsarki da Ƙur’ani in karantawa. Don in ƙara samun salama a zuciyata sai na yi aron kofen Avesta (Wani irin Littafi ne ɗauke da tsarkakan rubuce-rubuce) daga wani abokina na ’yan Parsi, na kuma sayi kofen Satyarth Prakash. Daganan na fara gwama waɗannan Littattafai. Bayan karatun Avesta a hankali, ina kuma taɗi da malaman Parsi, sai baƙin ciki ya ƙara kama ni a game da hanyar ceto, donbabu wata hanya mai ma’ana ta ceto da aka sa cikin wannan adiini.

Na juya wajen nazarin Satyarth Prakash wanda Swani Dayannand Sarasvasti ya rubuta, wanda ake gani mafi iko cikin kafa rukunana Arya Samj. Na karanta shi da begen samun abin da nake nema a cikinsa. Amma sai na sami wani baƙon rukunai wanda ya ta da tsikar jikina. A ciki an koyar da cewa Allah ba ya iya gafarta zunubai. Na yi mamaki, ya rufe da cewa ba amfani ko kaɗan mutum ya shiga Arya Samj da begen samun ceto. Bisa ga koyarwar Arya Samaj da begen samun ceto. Bisa ga koyarwar Arya Samj, Allah ba zai gafarta zunuban mutum ba, zunuban da mutum ya aikata kafin ya shiga Arya Samaj da na bayan ya shiga, saboda haka babu damar tsira daga hukunci.

Bugu da ƙari, sai na gano cewa ba madawwami ba ne a wurin Arya Samaj. Ya zama a sarari babu ceto a cikin Arya Samaj, in ma an sami ceton, sai ta wata hanya nan da can, kuma ceto ba na har abada ba ne. A sakamakon haka da shike ceton ba mai ɗorewa ba ne, ashe, mutum ba zai ji tsoro ba kullum don ana iya jefar da shi a kowane lokaci? Da na kai ga haka, na ga babu ceto a nan domin mai zunubi kamar ni, sai na daina binciken Satyarth Prakash. Aiki mai nauyi da ya sha mini kai shi ne na auna Kur’ani da kuma yardaddun Hadisai. Kafin fara wannan bincike domin rukunan ceto cikin waɗannan ayyuka, sai na ɗaga hanuwana cikin addu’a ga Allah:

“Ya Allah, ka sani ni Musulmi ne, ciki kuma aka haife ni tsararraki da yawa da suka gabata an haifi kakannina cikin Musulunci, sun kuma mutu cikin addinin nan. A ciki ne aka goye ni har na sami ilimina. Saboda haka ka kawar da kowane kangi da zai hana in gane hanyarka ta gaskiya. Ka kuma nuna mini hanyar cetonka, yadda lokacin da na bar wannan duniya, ba zan zama abin ƙi a gare ka ba. Amin.”

Abin da na samu cikin binciken Kur’ani, abin da na riga na sani ne tun dā: Samun ceto ya danganta ga ayyuka masu kyau. Na sami ayoyi da dama da suke nuna wannan rukunan, amman zan faɗi guda biyu a nan:

“Amma domin waɗanda su ka yi imani, suka kuma yi ayyuka masu kyau an ba su Lambunan Shaƙatawa (lada) domin abin da su ka saba yi. Amma ga waɗanda su ka aikata mugunta, shaƙatawarsu cikin gidan wuta ne. Duk lokacin da su ka so fitowa sai a komar da su. A gare su a ka ce: Ku ɗanɗana azabar wutan nan, wadda ku ka yi musun ta” (Kur’ani 32:19,20).

“Duk wanda ya aikata nagarta kome ƙanƙantarta, zai gan ta wanda kuma ya aikata mugunta kome ƙanƙarta zai gan ta” (Kur’ani 99:7,8).

Da gani waɗannan ayoyi su na da kyau ƙwarai, masu banta’aziyya, amma a cikin tunanina sun taso da tambaya: Zai yiwu a gare mu mu aikata nagarta kaɗai ban da mugunta? Akwai mutumin da yake da wannan ikon? Da na yi la’akari da wannan, na kuma san irin ikin tunanin ɗan adam, da yanayinsa, sai ya zama a sarari gare ni cewa, ba zai yiwu mutum ya kasance babu zunubi ba. Ba shi da iko ya aikata nagarta kaɗai kullayaumi.

Wani masanin ussan ilimin halin kirki na Arabiya, ya yi ikirari cewa akwai ikon tunani guda huɗu a cikin mutum waɗanda su ke tado da dukan ayyukansa. Uku daga cikin huɗun nan su na aiki gāba da marmarin ayyukansa na ruhaniya. Ɗaya ne kaɗai ya ke mala’ika maiikon tunani, wanda ya ke kawo mutum ga Allah, ya na taimakon sa ya yi biyayya da dokokin Allah, amma ayyukansa ɓoyayyu ne ga ganin mutum. A gefe guda kuma, akwai haɗin gwiwa na ƙarfin tunanin nan guda uku, ayyukansu sukan sa mutum jin daɗi, su zuga shi yinabu gaba ɗaya. Saboda haka, tunanin mutum yakan ga abin da ke daga sama-sama ne kawai, yana damuwa da abin da yake na yanzu kaɗai, ya fi maida hankali ga abubuwan duniya, ya kāsa kula da abubuwa na Ruhu da na Allah. Wani fitaccen Musulmi ya bayyana al’amarin kamar haka:

“Abu huɗu sun kame ni, ikon da ya sa na tagayyara. Waɗannan abu huɗu su ne, Shaiɗan, da duniya, da muguwar sha’awa da kuma zāri. Ta yaya zan kuɓuta daga waɗannan ga shi, dukansu magabtana ne? Muguwar sha’awa ta mamaye ni, ta jefa ni cikin rami mai duhu na nishaɗi da jin daɗin duniya.”

Bisa ga masana ussan ilimi na Larabci, ikokin nan guda uku, sukan fi ƙarfin ikon nan na mala’ikanci, har Adamu ya yi abin nan da Allah ya hana shi kada ya yi. An bayana sakamakon cikin zuriyarsa har zuwa gare mu yau. Bisa ga Hadishi:

Abu Huraira ya riwaito cewa Manzon Allah ya ce: “Lokacin da Allah ya halicci Adamu, sai ya daki bayan Adamu, sai dukan mutane su ka fāɗo daga bayan Adamu, wato dukan mutanen da Allah ya halitta daga zuriyar Adamu har zuwa Ranar Tashin Kiyama. Ya sa haske a gaban idanunsu. Bayan haka ne ya kawo su ga Adamu idanunsu. Bayan haka ne ya kawo su ga Adamu. Sai Adamu ya ce: “Ya Ubangijina, su wane ne waɗannan? Sai ya amsa: “Zuriyarka ne.” Sai Adamu ya ga mutum guda daga cikinsu akwai haske a tsakanin idanunsa, sun ba shi mamaki: Ya ce: “Ya Ubangijina, shekara nawa ka sa ya rayu?” Ya amasa cewa: “Shekara sittin.” Adamu ya ce: “Da aka gama ran Adamu banda shekara arba’in sai mala’ikan mutuwa ya zo gare shi. Sai Adamu ya ce: “Ashe, ba akwai sauran shekar arba’in ba da su ka ragu na rayuwata?” Sai mala’ikan ya amsa: “Ai, ka ba da su ga ɗanka Dawuda?” Sai Adamu ya yi musu, zuriyarsa ma suka yi musu, Adamu kuma ya manta, ya ci daga ’ya’yan itacen, zuciyarsa sun manta, Adamu ya yi zunubi, zuriyarsa ma sun yi zunubi.” (Tirmidhi)

Daga wannan, Hadishin, ya zama a sarari cewa dukan ’ya’yan Adamu sun yi zunubi tabbas, domin zunubin Adamu ya shiga cikinsu duka. Bisa ga haka, tsarkaka da shugabanni cikin annabawa, Hauwa’u kuma ta ce:

mana ka yi mana jinƙai ba, babu shakka mun ɓata!” “Suka ce: ’Ya Ubangijinmu: Mun yi wa kanmu laifi. In ba ka gafarta (Kur’ani 7:23).

“Ya Ubangiji! Ka yi gafara gare ni, kuma ga mahaifana, kuma da mummunai, a ranar hisabi yake tsayawa” (Kur’ani 14:41).

Annabin Islama ya yi wanna addu’a:

“Ya Allah, ka wanke laifofina da ruwan dusar ƙanƙara” (Buhkari).

Abubukar, halifa na farko na Annabin Islama, yana faɗi a cikin sanannen wāƙensa:

“Ya Allah, ya ya zan iya tsira, don babu wata nagarta a cikina? Laifofina sun sha kaina, amma kuma na kāsa cikin aiki nagari.”

Ƙari a kan dukan wanna shaida wannan aya ta biye, daga cikin Kur’ani ta dāge da cewa dukan mutane masu zunubi ne:

“Lalle mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa, lalle kuma mashaidi ne a kan laifisa” (Kur’ani 100:6,7).

Haɗe da wannan, sai was tunani su ka karaiko mini: Annabi Isa shi ma mutum ne. Kur’ani ya ambaci zunuban sauran annabawa. Amma don me Kur’ani bai ambaci zunubi a kan Isa ba? Na ga kuma rashin zunubi kaɗai Kur’ani ya faɗa a game da Isa, saboda haka sai na juya cikin Linjila. A nan na ga waɗannan ayoyi:

“ A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi?” (Yahaya 8:46).

“Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi mai zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurisa” (2 Koratiyawa 5:21).

“Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, a’a, shi ne wanda aka jarraba shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba” (1 Ibraniyawa 4:15).

“Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba” (1 Bitrus 2:22).

“Kun dai sani an bayyana shi domin ya ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi” (1 Yahaya 3:5).

Saboda haka akwai ƙaƙƙarfr shaida mai tabbatar da cewa, in ban da Annabi Isa, dukkan ’yan adam zunubabbu ne. Cikin waɗannan al’amura, wane ni da zan yi ikirarin iya samun ceto ta wurin nagarin ayyuka, sa’ad da shugabannin addini masu yawan gaske, da masannan usan ilimi, da tsarkaka duk sun kāsa ga wannan mawuyancin aiki.

Sai na sāke komawa ga Kur’ani don in auna koyarwa, ko rukunan ceto ta wurin ayyuka. Zan faɗi ayoyi biyu a nan waɗanda su ka fanyace cewa babu mahalukin da zai iya tsera wa hukunci, kome girman muƙaminsa:

“Amma ba ko ɗaya daga cikinku da zai tunkure shi. Wato Faralin Ubanginka. Sa’an nan za mu kuɓutar da waɗannan da suka keɓu daga mugunta, suka bar masu aikata mugunta suna ta noƙewa a can.” (Kur’ani 19:71,72).

Ni kaɗai cikin tsoron, da mayata, da surewa na san kaina, na karanta kalmomin nan. Ni da nake marar lafiyar ruhaniya, ina karatun Kur’ani kamar mai zuwa wurin likita, don ya bani magani domin zumuncina. Amma maimakon ya ba ni magani, sai ya ce: “Kowanne ɗayanku zai lalace, gama wannan aikin Ubangijinkane kaɗai.”

Amma ƙaunar da nake da ita da kuma shaƙuwa a game da Islama sun hana ni sauri yanke shawara. Na ga zai fi kyau in nemi sarfi a kan ayan nan a cikin Hadisai, don in iya ganin abin Annabin Islama da kansa zai faɗi a kan wannan Hadishin a cikin Mishkat (wani sanannen littafi na Sunnin Hadisai):

Ibnu Masud ya ce, Annabin Islama ya ce: “Dukan mutane wuta za su shiga. Sa’an nan za su fito daga ciki bisa ga ayyukansu. Waɗanda za su fito su yi kamar walƙawar walƙiya, na biye kuma kamar iska mai ƙarfi, sai kuma doki mai gudun gaske, daga nan sai kamar mahayi mai saurin gaske, da kuma kamar mutum mai tsalle, a ƙarshe, kamar tafiyar mutum? (Tirmidhi da Darimi).

Ma’anar ayar nan yanzu ta fito sarari. Babu makawa cewa kowa da kowa zai shiga wuta, sa’an nan ya fito bisa ga ayyukansa. Ma’anar Kur’ani fayyatacciya ce, maganar Annabin Islama kuma ta tabbatar da ita. Da so samu ne, da na tsaida binciken nan a nan, amma na ga zai gi kyau in biɗi fassara a cikin Kur’ani kansa. Ta haka bayan bincike mai zurfi, sai na kawo kan wannan ayar:

“Da Ubangijinka ya so, da ya sa mutane su zama al’umma guda, duk da haka ba su daina bambanta da juna ba, sai wanda Ubangijinka ya yi wa jinƙai, domin haka ne kuma ya halicce su. Maganar Ubangiji kuma ta cika: Hakika zan cika gidan wuta da aljannu da ’yan adam” (Kur’ani 11:118,119).

Abin ya soke ni, bayan karatun ayan nan, sai na rufe Kur’anin, na nutsa cikin zurfin tunani. Ko ina barci ban sami hutawa ba, tunanina suna a farke, ina zama kamar da mafarkai, na kāsa jin daɗi. Da wuya ƙwarai a gare ni in rabu da bangaskiya irin ta iyayena; har zai fi mini sauƙi in rasa raina. Gama wani lokaci, na yi ta ƙoƙari in yi tunani a kan wata hanyar rabuwa da wahala, ko wata hanya ta kuɓuta, yadda ba zan bar Isalama ba. Da wannan niyya, sai na fara neman taimako a cikin Hadisai. Wannan ma ba abu mai sauƙi ba ne, domin Hadisan ma su na nan cikin manyan kundi ba ne, domi Hadisan ma su na nan cikin manyan kundiguda shida. Bugu da ƙari aiki ne mai wuya ka yi aiki da ka’idodin kimiyar Hadisai a kan kowane Hadishi. Amma duk da waɗannan wahaloli, na yi wannan aiki da taimakon Allah.

Bisa ga Hadisai akwai hanyoyi uku na samun ceto. Na fari shi ne, babu mahaɗi ko kaɗan a game da ayyuka da ceto. Mummunan mafi zunubi duka, wanda ya gama dukan rayuwarsa cikin s:ɓon Allah, zai yiwu ya shiga aljanna, Haka kuma, mutum mafi kirki duka, wanda ya gama rayuwarsa duka yana kyawawan ayyuka zai yiwu ya shiga gidan wuta. Waɗannan Hadisai za su yi magana don kansu:

Hazrat Anas ya ruwaito cewa, Annabin Islama ya na haye da babba, Madh yana biye. Lokacin da Annabi ya maimaita sau uku cewa, “Duk wanda ya gaskata ya kuma maimaita: ‘Ba wani Allah, sai Allah ɗaya kaɗai da kuma annabinsa Muhammadu,’ ba zai taɓa hallaka cikin gidan wuta ba”, Madh ya ce, “Ya Annabin Allah, ba zan yi shelar wannan albishir/” Annabi ya amsa, “A kan wannan, ba za su yi imani cikin kome ba sai wannan.” (Mishkat).

A kan wannan batu, akwai Hadishin da Abu Dharr ya saukar wanda kalmomin sun ƙarfafa ƙarshen magana shi ne, ceto ta wurin ayyuka ba shi da ma’ana, domin har da fasiki da ɓarawo su na iya samun ceto ta wurin maimaita kalmomin shaidar Musulmi kawai. Ga yadda Hadishin yake:

Ubadah bin Samit ya ruwaito cewa, Manzon Allah ya ce: “Duk wanda ya shaida cewa ba bu wani Allah sai Allah kaɗai ba shi da abokin tarayya, Muhammadu kuma bawansa ne kuma manzonsa, Isa kuma bawan Allah ne da manzonsa kuam ɗan baiwarsa kalmarsa kuma ita ce ya saka a cikin Maryamu, ruhu kuma daga gare shi, aljanna da gidan wuta kuma gaskiya ne. Allah zai ɗauke shi zuwa cikin gidan jinƙai ko da yaya ayyukansa suke! (Musulmi, Bukhari)2

Lokacin da na karanta Hadisan nan, sai wata tambaya ta zo mini, ko mutumin da ya gama dukan rayuwarsu cikin aikata mugunta, bai taɓa tunanin yin wani abin kirki a ce zai shiga aljanna bayan ya mutu, wanda kuma ya gama dukan rayuwarsa cikin tsoron Allah, mai kamun kai, mai kyawawan ayyuka daga baya a jefa shicikin gidan wuta.

Abu na biyu, aka nuna cikin Hadishin shi ne, ceto ya danganta a kan jinƙan Allah – har yadda Annabi da kansa ma mabukaci ne, yana bara don samun wannan jinƙai. Idan Allah bai yi masa jinƙai ba, Annabi da kansa fa ba zai sami ceto ta wurin ayyuka ba. Wani Hadishi kuma a cikin Mishkat ya faɗi hak:

Abu Hurarira ya ruwaito cewa, Annabin Islama ya ce: “Ba ko ɗaya cikinku da zai shiga Gidan jinƙai.” Su ka ce: “Har da kai ma ya Manzon Allah?” Sai ya amsa “Har ni ma, sai dai in Allah ya rufe ni da Alherinsa. Saboda haka ku ƙarfafa, safe da maraice da a kowane lokaci ma, ku yi ƙoƙari aikata nagarta.”

Haɗa kuma da wannan Hadishin:

Jabir ya ruwaito cewa Annabin Islama ya ce: “Babu ayyuka masu kyau da za su ko samar muku wuri cikin aljanna, ba kuma za su iya ceton ku daga gidan wuta ba – har ni ma idan ba tare da lherin Allah ba.”

Daga waɗannan Hadisai, na gane cewa babu wanda zai iya samun ceto, sai in jinkan Allah ya na kansa. Wannan ya ɗan ta’azantar da ni, amma kuma sai na fara tunani: Idan Allah mai jinƙai ne, to, mai adalci ne. Idan Allah zai gafarta ta wurin aikata jinƙasa kaɗai, to, yana kauce wa Gaskiyarsa da Adalcinsa ke nan. Irin wannan bauɗewa ta Gaskiyarsa za ta yi lahani ga kasancewarsa Allah. Ba shakka irin wannan tunani bai dāce da ɗaukakar Allah ba.

Abu na uku da ya zamar mini a sarari daga Hadisai shi ne, har Annabin Islama da kansa ba zai iya ceton kowa ba, ko ’yarsa Fatima, ko danginsa da zai iya ceton su ba. Don haka ra’ayin nan na cewa, Annabi zai yi roko domin mumminai, wanda na yi tsammani tabbas daidai ne, yanzu ya tabbata ba daidai ba ne. Ga yadda wani Hadishi ya nuna:

Abu Huraira ya ruwaito cewa, lokacin da ake bayyana ayan nan ga Annabin Islama “Ka sa danginka na kusa su ji tsoro,” sai Annabi ya tashi ya fara shela: ‘Ya mutanen Kuraisha, da ku ’ya’yan Abdul Man, da kai Abbas ɗan Abdul Muttalib, da ke Safiyyah innata, ba zan iya cetonku daga hukuncin Ranar Tashin Kiyama ba. Ki kula da kanki ya ’yanta Fatimah, kina iya morar dukiyata, amma ba na iya ceton ki daga hannun Allah. Ki kula da kanki’” (Bukhari).

Saboda haka, bayan bincike mai zurfin gaske na Hadisai, ba sauran abin bincike kuma. Bayan wannan cikkaken tsoron da fargaba, sai na rufe littattafan Hadisai, na yi addu’a ga Allah:

“Ya Allah mahalicina da Ubangijina, ka san asiran zuciyata fiye da yadda na sun su. Ka san tsawon lokacin da nake biɗar Addininka na gaskiya. Na yi bincikena iyakar iyawata. Saboda haka, yanzu, ka buɗe mini ƙofar saninka da cetonka. Ka yarje mini in shiga ayarin jama’arka waɗanda suke abin yarda a gare ka, domin in ɗaukaka, in wadatu, a lokacin da na shiga cikin Ɗaukakarka. Amin.”

Cikin wannan halin dugunzuma da narkewar tunani, sai na fara karatun Linjila Mai Tsarki da nufin gyara ga lahanin da zai yiwu na yi a cikin bincike bincikena. Da buɗe Linjila Mai Tsarki a wannan lokaci, sai idanuna suka kai a kan waɗanan kalmomi

“Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya,ni kuwa zan hutasshe ku” (Matiyu 11:28).

Ban san yadda ya faru ba, har na kai ga wannan nassi a cikin Bishara daga hannun Matiyu. Ban nemi nassin da nufi ba. A gefe guda kuma bai faru kamar tsautsayi ba ne yi da binciken shaida ce ta albishir mai daɗi. Wannan aya mai ba da rai tana da gaggarumar nasara a kaina. Ta kawo mini salama, da ta’azziya, da murna, nan take kuma ta kawar mini da dukan rashin kwanciyar rai da rashin tabbas daga zuciyata. Masiha ya yi ikirarin: “Zan hatasshe ku.” Ya nuna yadda ceto ya danganta gare Shi. Ba nuna hanya kaɗai ya yi ba wadda ta fi ƙarfinsa, amma cewa ya ke yi ba wadda ta fi ƙarfinsa, amma cewa ya ke yi: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya nine kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yahaya 14:6).

Duk da haka, sai tambaya ta zo a tunanina: Ko mutum zai iya amincewa da wannan ikirari na Almasihu? Na dai daddale cewa mutum zai iya jingina a kansa, da fari dai, Musulmi sun yarda Almasihu ba shi da zunubi, maɗaukaki ne cikin wannan duniya, da duniya mai zuwa kuma, Kalman Allah, da Ruhun Allah. Waɗannan, da sauran wasu bayyanai, da suka shafi Isa sun nuna kammala. Na biyu, bisa ga Kirista shi cikakken Allah ne, cikakken mutum kuma, ba ruwansa da wani yayi, da ƙawazuccin duniya. Ta haka, ba shi yiwuwa Almasihu wanda bisa ga faɗar Kirista duk da Musulmi yana da inganci mafi duka, a ce yana da zunubi, ko ya yi wani abin da bai dāce da shi kansa ba.

Na fara bambinin yadda Almasihu ya yi alkawarin ba da ceto. Don hutar da raina, sai na fara biɗa ta wurin Linjila Mai Tsarki, har na zo a kan wanna aya:

“Kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa” (Matiyu 20:28).

“Daga karatun ayan nan, na gane yadda Allah ya ke ba da ceto. Almasihu ya ba da ransa domin mu masu zunubi. Wannan hanya mai banmamaki, wadda duniya ba za ta iya nuna wata kamar wannan duniya, amma babu ko daya daga cikinsu da ya yi ikirarin cewa mutwarsa za ta iya kawo gafarar zunubai. Almasihu kaɗai, ba ikarari kaɗai ya yi ba, amma har ya cika.

A wannan tunani, sai na cika da murna a ruhunce Sai hoton Almasihu da ƙaunarsa suka a kafu daram a zuciyata. Amma lokacin da na shera a cikin wannan murna, sai wata tambaya ta zo mini: Don me ake bukatar hadayar Almasihu da aikinsa na kawo gafara? Ba zai iya kawo ceto ba sai ya ba da ransa? Bayana na kara tunani, sai na sami amsar wannan:

Allah mai jinƙai ne kuma mai adalci. Idan Almasihu ya yi alkawarin kawo ceto ba tare da ya ba da ransa ba, da bukatar jinƙai ta cika babu shakka. Amma domin a gamsar da bukatun alci, sai Almasihu ya biya fansa – Jininsa mai daraja. Ta wannan hanya ne Allah ya bayyana kaunarsa a gare mu.

“Ta haka ƙauna take, wato ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.” (1 Yahaya 4:10).

Na ci gaba da bincikena a cikin Sabon alkawari ina kuma karanta shi sau da dama daga farko zuwa ƙarshe. Na same ɗaruruwan ayoyi, da misalai masu tarin yawa waɗanda su ka tabbatar mini, babu wata tantama, cewa ceto-cibiya da manufar addini-yana samuwa kaɗai ta wurin ba da gaskiya ga Ubangiji Isa Almasihu. Na faɗo wani nassi a nan don tabbatar da wannan batu:

“To, mun sani duk abin da shari’a ta ce, ya shafi waɗanda ke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma ta sani ƙarƙashin hukuncin Allah take. Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan shari’a, tun da ya ke ta Shari’a ne mutum ke ganin laifinsa.” Amma yanzu ba kuwa gamed da Shari’a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa ke yi wa Shaida. Adalcin nan na Allah wanda ke samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambanci, gama ’yan adam duka sun yi zunubi sun kāsa kuma ga ɗaukakar Allah. Amma ta alherin da ya yi musu kyauta sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi. Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin ya nuna adalcinsa ne, domin da saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da a ka gabatar” (Romawa 3:19-25).

IX. TUBA DA SHAIDA

Bayan kammala bincike-binciken da na bayyana, sai na ƙarasa da cewa zan zama Kirista. Cikin dukan al’amuran nan, sai na ga zai fi mini daraja in gabatar da dukan batun a gaban ƙungiyarmu, don su yi la’akari da shi, ni kuma in zama kuɓuttacce daga zargin gudanar da bincike-bincikena cikin asiri.

Na je wurin taro kamar yadda na saba. Zarafin Munoshi Mansur Masih ne don ya yi magana. Kafin ya fara, sai na yi katsalandan da cewa, a wannan karon ni da kaina ne zan yi magana akasin Islama. Sai na ci gaba da bayanin sakamakon binciken da na yi shekaru da dama. Jami’an ƙungiyar su ka yi mamakin kalmomina, amma suka ta’azantu don su na begen ko zan soki jawabin nawa (wato in musance shi.) Da na gama, ma je na zauna, sai mataimakin shugaba ya ce: “Muna fata shugaba da kansa zai tasji ya soki wannan jawabi nasa, marar daɗin ji.” Sai na sāke tashi na ce: “Ku saurare ni, ’yanuwa. Abin da na bayyana muku ba wani abu ne na bisa-bisa ba, ko na ƙage. Abu ne tabbatacce yankakke, a kan bincike na shekaru da dama. Don zama takamaimai, wannan ya faro ne daga ranar da Munshi Mansur Masih ya yi mana jawabi a kan batun ceto. A wannan lokaci, na yi alkawair ga Allah cewa daga ranan nan zan karanta Littafi Mai Tsarki, ba kamar yadda na riƙa karanta shi a dā ba, amma a matsayin mai biɗar gaskiya don a bayyana mini hanyar gaskiya da adalci. Bisa ga haka ne, na jingine son kai da duk wasu hanyoyin ussan ilimi, na gwama Avesta, da Satyarth Prakash, da Littafi Mai Tsarki, da kuma Kur’ani. Sai na ƙarshe batun da cewa, sai ta wurin Alamsihu kaɗai za a iya samun ceto. Iyakar abin da na faɗa ke nan. Idan na yi lahani cikin bincikena, zan gode idan waninku ya nuna mini. A gefe guda idan ku da kanku kuna so in yi s:uka a kan waɗannan muhawarori, zan faɗa muku muraran cewa ba zan amsa su ba; ko wani begen samun amsa daga wurin wani dabam.”

Na bar taron, don ba zai haske ba in ci gaba da kasancewa a wurin. Munshi Mansur Masih nan da nan ya biyo ni. Da ya tarar da ni, sai ya rungume ni, ya fara kuka don murna, yana magana cikin tsoro: “Da daren nan ka zo mu tafi gidana cikin tsoro ne ka kwana a ɗakinka kai ɗaya.” Na amsa cewa jami’an ƙungiyata masu ilimi ne, ba abin tsoro daga gare su.” Na ƙara da cewa, “Gaskiya ne, akwai wasu da dole mutum ya ji tsoron su. Zan zo gidanka kafin gari ya waye. Idan ban zo ba a wannan lokaci, sai kai ka zo masukina.”

Bayan mun yi wannan shiri sai muka rabu. Na tafi ɗakina, na kulle ƙofa daga ciki, na kashe fitila. Na zauna, na nutsa cikin zurfin tunani. Ba zan taɓa mantawa da zace-zace na tsoro ba, da kokawa ta runaniya a wannan dare. Dare ne na yanke shawara dare mafi gwaji mai kawo ƙasawa. Wasu lokatai, sai tunani ya karaiko mini cewa, idan na zama Kirista, zan rasa ƙasata, da gādona, da ’yancina/hakkina, da iyalina, da abokina – a taƙaice duk zan rasa kome da kome. Ina kuma damuwa da ra’ayin nan cewa, zama Kirista yana nufin shiga duniya inda ɗa’a da sauran abubuwa za su bambanta da waɗanda na saba. Ban iya barci ba a daren nan.

A ƙarshe na ce wa kaina: “Sultan, ka lura cewa kai ɗan wannan sa’a ne, duniya kuma ta na wucewa. Idan ka mutu, ƙasarka da gādonka ba za su amfana kome ba, iyalinka da abokanka kuma ba su taimake ka ba. Dukan waɗannan na duniya ne kaɗai. Bangaskiyarka kaɗai za ta wuce kabari. Saboda haka wauta ce ka rabu da rai na har abada, da farin ciki na ruhaniya saboda wannan rai mai shiga canji.” Daga nan sai na durƙusa a gaban Allah na yi wannan addu’a:

“Ya Allah madawwami, Mai Iko Dukka, mai binciken zukata, na miƙa kaina a gare ka. Ka karɓi wannan baiko, ka kuma kiyaye ni daga kan tarkon ibilis da hatsarorin ruhaniya. Ka kawar da duniya da sha’awace sha’awacenta dagazuciyata. Ka ba ni ƙarfin zuciya da ƙarfi don in iya shaida Ɗanka Yesu Almasihu a bainar jama’a. Ka jini, ka karɓi addu’ata sabili da Yesu Almasihu. Amin.”

Da na gama wannan addu’a, sai jiri ya kama ni, daga nan sai barci na ɗan lokaci kaɗan. Da na farka, sai na ji murna gaba ɗaya ina farin ciki. Babu alamar damuwa irin ta dā da matsuwar da suka dame ni.

Gari yana wayewa. Nan da nan na yi wanka, na nufi gidan Munshi Mansur Masih. Da na isa can, na tarar ya damu ƙwarai don ban zo ba. Ya san ni mai son shan shayi ne a daidai lokacin nan, har an riga an shiya mini. Da na gama shan shayi, sai muka tattauna a kan wasu abubuwa na ɗan lokaci, daga nan sai mu ka shiga addu’a. Bayan addu’a, sai muka tafi gidan Padre Lrdgeard.

Padre ya yi mamakin isarmu gidansa tun da safe haka. Munshi Mansur Masih ya ci gaba ya faɗa masa cewa na zo ne a yi mini baftisma. Da fari, ya na tsammani ba da gaske mu ke yi ba. Amma da ya ji abin da ya gudana a daren jiya, sai nan da nan ya tashi ya rungume ni, ya na cewa: “Na sani in ka karanta Littafi Mai Tsarki da gaske ba shakka za ka zama Kirista. Godiya ga Allah da shike ka yarda.” Daga nan ya yi alkawarin yi mini Baftisma nan da kwana uku, ya shawarce ni in haddace Dokokin Ubangiji kafin ranar baftisma. Ya kuma shawarce ni kada in riƙa tsayawa cikin Musulmi. Sai ya gayyace ni in zauna tare da shi ko kuma tare da Munshi Mansur Masih, sai na zaɓi zama da Manshi Mansur Masih.

Ran Lahadi, sai majami’a ta cika da Musulmi. Ganin hatsarin da ke nan sai Mr. Ledgeard ya fāsa yi mini baftismar. A ƙarshe dai, ta wurin alherin Allah da jinƙasa, a ka yi mini baftisma ran 6 ga watan Augusta 1903, cikin Majami’ar St. Paul, Bombay. An yi mini baftisma a gaban waɗannan mutane: Rev Canin Ledgeard, shi ya yi mini baftismar Munshi Mansur Masih, da wasu mutum biyu, waɗanda ban riƙe sunansu ba. Bayan wannan, sai nan da nan aka aika da ni Kampur, dan akwai hatsarin gaske in na zauna a Bombay.

Lokacin da na zama Kirista, sai wani canji mai banmamaki ya faru a cikin rayuwata. Maganata, da ayyukana, da kowane fanni na rayuwa duk suka sāke, har shekara guda daga baya, lokacin da na ziyarci Bombay naɗan lokaci, abokaina Musulmi sun yi ta mamakin abin. Sun yi mamakin sauƙin halina, don sun sanni da saurin fushi. Kafin in zama Kirista, na gane zunubi, zunubi ne, amma ban gane kamar yadda na gane a yanzu ba, yadda yake da hatsarin gaske, mai hallakarwa. Har yanzu ni mutum ne rarrauna, ƙura kawai, lokacin da kuma na yi zunubi, ba zan iya bayyana kunya da baƙin cikin da na ji ba nan take, na fāɗi a fuskata, da hawaye, na tuba, na roƙi gafara. Wannan hali yana samuwa kaɗai ta wurin ganewa da hadayar aikin ceto na Ubangiji Yesu Almasihu. Zunubi bai kawuwa ta wurin tuba kaɗai. Dole sai an share shi da jini mai daraja na Mai Cetonmu. Shi ne, saboda ainihi dalilin zunubi ya sa kullayaumu duniya tana ta gabatowa kurkusa da hallaka.

Ko da yake Shaiɗan zai yi ta yaƙi gāba da ni da iyakar ikon da yake da shi, ko ƙanƙani ba zan damu ba, domin na gaskata cewa Almasihu, ko ya yi nasara a kan su ba. Bari Allah, Mahaliccin sama da ƙasa mai binciken zukata, ya juye zuciyata, ya ba su wahayi, yadda su ma tunanin Ranar Hukunci, zai fahimtar da su game da zurfin bukatarsu ta Almasihu.

Ni ne, ’yan’uwana Musulmi kaunatattu, mai yi muku fatar alherin ruhaniya,

Sultan Muhammed Paul

KACINCI-KACINCI

Kana iya amsa tambayoyi nan cikin sauƙi daga ɗan littafin nan, idan ka yi bincikensa a hankali. Ka aiko da amsoshinka zuwa gare mu za mu aiko maka da ɗaya daga cikin littattafanmu kyauta.

  1. 1. Mene “lalacewar mutum” ta yaya kuma take bayyana kanta cikin ’yan adam?

  2. 2. Wace matsalar ra’ayin riƙau ce ta ke damun Sultan Muhammed Paul?

  3. 3. Faɗi abin da Faston nan Bature ya amsa wa tambayar Sultan Muhammed Paul da ya ce, “Don me zan karanta Littafin Mai Tsarki? Wa zai karanta littafin da aka daddagula, wanda mutane suke sassake shi kowace shekara?

  4. 4. Yaya Sultan Muhammed Paul ya ji a ransa bayan da Munshi Mansur Masih ya ƙalubalance shi a game da ceto cikin addinin Islama?

  5. 5. Da wane nufi Sultan Muhammed Paul ya shawarta shiga binciken Littafin Mai Tsarki bayan da kalmomin Munshi Mansu Masih suka ratsa zuciyarsa?

  6. 6. Me Sultan Muhammed ya zama mai biɗa lokacin da ya fara gwama Kur’ani, da Littafi Mai Tsarki, da Avesta, da kuma Satyarth Prakash?

  7. 7. Me Sultan Muhammed Paul ya gano a kan mutane da ceto a cikin Kur’ani (32:19;7,8)

  8. 8. Me Sultan Muhammed Paul ya koya a game da Adamu, da Ibrahim, da Annabin Islama, da Abu Bakr da dukan ’yan adam a cikin bincikensa na Kur’ani, yaya kuma Yesu ya yi dabam da dukan sauran mutanen nan?

  9. 9. Ka rubuta cikakke jawabi guda biyar na Sabon Alkawari da Sultan Muhammed Paul ya samu, da su ke selar rashin zunubin Yesu. Ka haɗa da surori da ayoyi cikin amsarka.

  10. 10. Ka taƙaita a cikin sheɗaru kaɗan, ka’idodi manya guda biyu waɗanda Sultan Muhammed Paul yakoya daga waɗannan: Kur’ani 19:71,72 da kuma sharfinta a cikin Mishkat, da Kur’ani 11:118,119.

  11. 11. A taƙaice ka rubuta abu uku da Sultan Muhammed Paul ya gano a game da ceto, bisa ga Hadisai. Menene matsayin tunaninsa bayan bincikensa?

  12. 12. Ka faɗi aya a cikin Bishara ta hannun Matiyu wadda Sultan Muhammed Paul ya gano bayan bincikensa cikin Hadisai. Me wannan ya jawo masa?

  13. 13. Ka faɗi Yahaya 14:6, ka kuma bayyana muhimmancinta.

  14. 14. Waɗanne abu biyu Sultan Muhammed Paul ya tantance, waɗanda su ka goyi bayan iƙirarin nan wanda babu kamarsa da Yesu ya yi?

  15. 15. Ka faɗi Matiyu 20:28, ka kuma bayyana yadda Allah yake ba da ceto.

  16. 16. Wace amsa Sultan Muhammed Paul ya samu a kan tambayarsa: "Menene ya sa bukatar Almasihu ya yi hadaya da aikin gafara? Ba zai iya ba da ceto ba in bai ba da ransa ba?

  17. 17. Ka faɗi aya daga Sabon Alkawari wadda ta ke bayyana yadda ya bayyana ƙaunarsa domin mu.

  18. 18. Menene ainihin cibiya da manufar addini, ta waɗannen hanyoyi ne kuma yake damuwa? Ka faɗi nassi daga Romawa wanda ya goyi bayan amsar.

  19. 19. Bayan da Sultan Muhammed Paul ya yi jawabi na ƙarshe ga ƙungiyarsa, sai ya kulle kansa cikin ɗakinsa. Faɗi kalmomin da ya faɗa wa kansa, da kuma addu’ar da ya yi a durƙushe gaban Allah.

  20. 20. Waɗanne canje-canje abokan Sulatan Muhammed Paul suka lura a cikin rayuwarsa bayan ya miƙa ransa ga Yesu?

Idan kana da wasu tambayoyi a game da bangaskiyar Kirista, za mu yi murna mu amsa maka su. Kada ka manta ka rubuta cikakken sunanka da adireshinka a cikin wasiƙar, da kuma a kan ambulon.


KIRAN BEGE
P.O. Box 14555
KANO
NIGERIA

Internet: www.the-good-way.com