ALHERINA YA ISHE KA

ALHERINA YA ISHE KA

Ghulan Masih Na’aman


I - GIDANA NA MUSULUNCI

Mu takwas ne a iyalinmu duka musulmi. Ina da yayye huɗu da ƙane ɗaya. An haife ni a jammu, Kashmir, inda mahaifiyata ta je hutu, amma garin kakanninmu shi ne Zaffarawal a Sialkot. Kakannina asalinsu daga Mangolia ne, kuma masu arziki ne ta fuskar mallakar gidaje. Mahaifina ma ya mallaki gidaje da ƙasar noma mai albarka.

Yana nomen alkama kusa da kogin Nala Dek, wanda lokacin domina yana cika, kuma yana gudu da ƙarfi ainun, ya na cika rigyawa. Mukan noma alkamar da ta ishe mu. Mun dai yi sa’a, muna da wadata, ba mu san rashi ba. Muna da barori masu yi mana aiki, ban taɓa ganin babana ya yi aiki da hannunsa a gona ba. Yan’uwana sun balaga, suka ɗauki aikin kula da gona da kansu.

Bayan haihuwar ’yan’uwana manyan, namata ta haife wasu yaran amma suka mutu tun suna jarirai. An haife ni, rayuwata abin mamaki ne, don haka kak yi wasu alamomi a jikina kamar hakaāka huda mini kunne. Mamata tana so ta ƙara haihuwa. Ita Musulma ce ta ƙwarai, duk da haka tana riƙe da bangaskiya cikin wata allahiya – abin da ta gāda daga kakanninta. Ta je cikin tsaunukan Kashmir inda akwai masujadar wata allahiya. Ta yi wa allahiyar alkawari cewa, idan ta sami ɗa, za ta miƙa shi gare ta, kawo shi ga masujadar alama ce ta nuna godiya. Ta haka aka huda masujadar alama ce ta nuna godiya. Ta haka aka huda kunnena da zoben zinariya don a nuna cewa na zama na allahiyan nan.

Me kake tsammani alaman nan ta yi mini a makaranta. Banda ba’a da ta sa yara suka yi ta yi mini, su ka yi ja mini kune, duk lokacin da na sami faɗa kunnen suke son kamawa. Wannan alama ta haihuwata mai banmamaki, mai kuma tsare ni daga mutuwa ta sha ba ni kunya da shan zafi. Amma daga baya na fahimta cewa, akwai hannun Ubangiji a kaina – ba hannun allahiya ba, amma na Allah mai rai.

Ɗan’uwa babana ya ji tausayi na, ya tuɓe zoben daga kunnena. Na sami saki, amma mahaifiyata ta ji haushi ƙwarai da gaske. Ta damu ƙwarai don a ganinta wannan zai jawo mutuwata. Zoben dai irin na tsatsuba ne, yana da tabbacin ba ni tsaro daga allahiya – bisa ga tsammaninta. In babu zoben nan ina cikin hatsari, har ma da mutuwa. Amma ƙanen babana ya zo yakuɓutar da ni, ya tabbatar mini da cewa, “Ba za ka mutu ba.” Mamata tana fama da camfi ne kawai. In ta ce in je wajen ɗan shekara tara. A kwana a tashi ban fāɗi na mutu ba, na kuɓuta daga tsoro na kowane iri da yake ta damu na a dā. Daga wannan lokaci ban ƙara jin tsoro ba, sai daga baya a cikin rayuwata – ko a cikin al’amura masu hatsari. Na sami fāduwar duk da haka, a lokacin da ƙanena Ramazan ya kamu da ciwon maɗaukai, cikin ’yan kwanaki kaɗan ya mutu.

Yayya na maza sun yi aure tun ina ƙarami. Dukanmu muna zama a ƙaton, gida guda mai ɗakunan kwana guda takwas da babban ɗakin hira. ’Yan’uwana ɗakunansu dabam, su na tare da matansu da ’ya’yansu. Muna raba kowane abu a tsakaninmu, kamar dai irin al’amuran zaman jama’ar India a wancan zamani. A cikin gariko ƙauye, wannan ne alamar tsaro ga dukan iyali. Kowa a cikin iyali, mai lafiya ko naƙasasshe, mai aiki ko marar aiki yana da rabo cikin kayan da ake da su, yana kuma da gādo.

Zaman iyalinmu na murna ne, da mahaifiya ta gari, da mahifi mai ƙauna da ƙauntattun surukai. Kullum nakan kira matan yayyena “yan’uwa”, babana kuma ya koya mini in ɗauke su haka, domin ba ni da ’yan’uwa mata na kaina. Muna ƙaunar juna ƙwarai. Saboda zama wuri ɗaya, da surukai, za a zaci samun yawan tashin hankali. Amma ba haka yake ba a gidanmu. Mamarmu mai sauƙin hali ce, don haka sai walawar ƙauna da fahimta mu ke sha. Daga Mamaru na koyi hidimta wa saura. Takan ce, “In yi wa kaina abu ni kaɗai wannan bai bambanta ni da dabba ba. Muna iya kaɗai tabbatar da cewa mu ba dabbobi ba ne, amma mutane ne da gaske idan muna rayuwa domin waɗansu.” Rayuwata tana da waɗannan ka’idodi koda akwai al’amuran razanarwa. Halinta da gurbinta abin koyi ne a gare ni. Duk da duhun da ya yi barazanar haɗiye cikin rayuta daga bisani, ban taɓa kaucewa daga wannan tushen ba.

Mahaifina soja ne, ya taɓa riƙe muƙamin da ake kira Viceroy’s Commission a cikin Yaƙin Duniya na Ɗaya. A wancan lokaci ƙungiyar ’yan ƙasancin India ba ta kai matakin hamayyar da za ta shiga soja a ƙarƙashin mulkin Birtaniya ba. India tana cikin mulkin Birtaniya, zuwa yaƙi a ƙasashenƙetare an ɗauke shi wani aiki ne na girmamawa. Babana yakan ji daɗin tunalokacin da suke yaƙi. Yana cike da labaru iri iri da suke cika mu da zace-zace iri iri. Muna ƙaunar saurare a game da yadda sojoji suke cin zali a lokacin da ake hada-hada cikin Afrika. Baba ya shuka mini ƙaunar labarun jaruntaka. A fakaice yana koya mana cewa, ya kamata mutum ya nemar wa kansa suna ta wurin yin abin a zo a gani a duniya. Ya kamata mutane su iya gane iyawarmu' ba za mu yi allarsu ba, amma mu yi su ta yadda za a iya duba su da gaskiya.

Wannan hali ya haifar da abubuwa a cikin rayuwata. Rashin tsoro, son in yi fice cikin rayuwata, sun sa na shiga ƙwƙwa masu hatsari.

Babana ya kula da sauran mutane. Idan ya ga an danne wani, ko matalauci ƙwarai, zai yi iyakar ƙoƙarinsa don ya ga an yi wa mutumin shari’ar adalci, a kotu. Amma shi da kansa bai taba kai kowa kotu ba. Ko sojoji ma sukan biyu ta kansa kafin su iya, saboda haka duk maƙwabta su na girmama shi ƙwarai.

Saboda babana mai hannu suke ne, baƙi da yawa sukan sauka a gidanmu. Har wata rana ya sauki masu kisan kai ba da sani ba, su ka kashe masa ɗan’uwa. ’Dan’uwan nasa ya shiga jayayya ne a game da batun ƙasa (gona), ƙungiyar wasu mutane su ka kashe shi. Daga baya sai wannan ƙungiyar suka tsere, suka nemi wurin ɓuya, suka ɓuya a wani ɗan ɗaki da babana ya gina a gona. Ba tare da sanin abin da suka aikata ba, babana ya gayyato su zuwa gidanmu suka ci abinci. Daga baya, sai abokan ɗan’uwan babana da aka kashe tone su. Da babana ya ji labarin mutuwar ɗan’uwansa, ya yi ɓacin rai. Abin da ya ba kowa mamaki shi ne, bai yi fushi da masu kisan kan nan ba. Mutum ne mai kula, kuma bai riƙe kowa ba ɓacin rai a zuci ba.

Baba ya sami wannan hali daga addininsa. Bai damu da irin ruɗaɗɗun malaman nan na addinin Musulunci ba. Ya ƙi irin sujadannan cikin jama’a don mutane su gani, yakan yi addu’a, a kaɗaice. Mai zurfin ibada.

A cikin Islama Sufi su ne masu zumunci ko sadarwa ta kai tsaye tsakanin rai da Allah. Bisa ga dukan alamuwannan solo ya sami asali daga wata ƙungiyar Kirista waɗanda su ka warwartsu ko’ina a cikin hamadar Masar da ta Arabiya. Al-Ghazzali da ya mutu a 1111 A.D. ya tabbatar da wannan a cikin Islama. Da farko dai Sufi na da halin ibada, da tawali’u, da ƙin jin kowane iri daɗi, dangane da horon kai, da musun kai. Ana iya ganin alamar yin biyayya ga Allah da zuciya ɗaya. Ana sa zuciya ga maida martanin ƙauna daga Allah, ba bin dokoki kawai ba. Saboda su na biɗar tsarkakewa ta ƙwarai, da ganewa da Allah sosai. Mutanen da masu biɗar Allah a ruhunce, sun ƙarfafa muhimmancin addu’a da ɗaura niyya, da jin daɗin ɗaguwar ruhaniya ta sanin ƙaunar Allah. Saboda ƙaunan nan ne su ke iya ƙaunartar Allah, su ke kuma yi masa biyayya. Daga bisani sai suka riƙa shan ƙwaya da wasu irin muziƙa don su bugu zuwa ɗaguwar ruhaniya. Keɓantuwar ruhanyia ta babbana ƙuduri ne da niyyar samun dangantaka tsakaninsa da Allah, amma ba ta ingantu zuwa biɗar keɓantuwar ruhaniya da shi ba. Bai shiga amfani da ƙwaya, da muziƙa, da rawa ko wasu sambatu don ya sami keɓantar ruhaniya ba. Ya kasance cikin cikakken hankalinsa mai mulkin dukan ransa.

A gida, shi mutum ne mai sauƙin kai, mai kula da jin daɗinmu da iliminmu. Yayyena da ni kaina mun sami iliminmu a wata makaranta mai nisan kamar mil biyu daga gidanmu. Babanmu ya gina gida a Zaffarawal kusa da makarantar, don kada mu riƙa makara.

Na shiga firamare tun ina ɗan shekara biyar. A lokacin nan ne na fara zuwa masallaci kusa da gidanmu. Kowane yaro Musulmi ɗan shekara biyar, ya kamata ya riƙa zuwa masallaci sau ɗaya a mako don ya koyi Kur’ani da haddacewa. Massalaci ne matattarar jama’a don yin sujada da samun koyarwa, ina zuwa kowace juma’a tare da abokina ranar ibada domin Musulmi. Sa’ad da Limin ya ke addu’a, sai mu riƙa bin duk yadda ya yi. Sau da dama yakan yi ɗan jawabi, in da yaken bayyana wasu sassa na koyarwa annabi muhammadu. Ba kullum ya ke da sauƙin ganewa ba, amma shugabanninmu na addini sukan dāge su ga mun koyi bangaskiyarmu. Tun ina ɗan yaro, shaidar Islama ta riƙa kafuwa a ciki na a hankali.

La ilaha illa Allah,

Muhammadu rasul Allah.

Babu wani Allah sai Allah kaɗai

Muhammadu kuma Manzonsa

Hedmastan makarantarmu yana da iko ƙwarai a kaina. Shi mai wāƙe ne, mai iya jawabi, marubuci kuma gwanin muziƙa ne. Saboda ƙarfafawarsa zuwa gare ni, sai na fara rubuta wāke na kaina. Wannan ya zamar mini hanyar farin ciki a duk rayuwata, a kullum kuma ɗan littafin matunina yana kusa da ni. Na kuma koyi buga kayan muziƙa mai muryoyi iri iri, amma ba a yarda mini in more su a gida ba. Amma Hedmasta ya yarda in riƙa ya a gidansa. Hannun Allah yana a kaina tun ina ƙarami. Yana ta shirya ni domin hidima a rayuwata. Hakika, shi Allah Mai Girma ne.

Na yi shekara huɗu a makarantar firamare. Lokacin da nake ɗan shekara tara, sai ’yan’uwana su ka bar gida, biyu suka tafi jammu, biyu kuwa zuwa Lahore. Ni kuma zan tafi makarantar gaba da firamare. Da ina can ban ci gaba sosai ba da marmarin ilimi, amma iyalina sun matsa su ga lalle na maida hankali ga neman ilimi. Suka zaɓar mini makaranta a cikin Jammu, Kashmir. Babbar Makarata a Maharajah Ranber.

Ya zama kyakkyawan zarafi a gare ni in tafi can, domin an gina makaratar saboda ’ya’yan rajah, wato masu hali, ko ’ya’yan sarauta. Raja su ne sarakunan da su ka ci nasara, su ka maida kansu masu mulki a sassa dabam dabam na ƙasar India. Akwai rajah ashirin da biyu a cikin Kashmir a wannan lokaci. Ni kaɗai ne Musulmi a cikin ɗalilaban wannan makarantar. Ba a yardar wa musulmi a wannan makaratar sai Hindu kaɗai. Amma tun da babana yana cikin sojoji, kuma baba ne a cikin jama’a, sai rinjayi Hedmastan ya karɓe ni. Yana da wuya mutane su ƙi karɓar roƙon babana.

Wannan makarata tana ba da horon farko na aiki soja da ta dāce da ’ya’yan mayaƙa da na sarakuna. Muna ta hawan dawaki, na kuwa kaunaci wannan harkar. Ina kuma jin sarrafa ta. Na tuna, a kullum na sami zarafi nakan ɗauki dogon lokaci da ita. Na ji daɗin wannan fiye da ɗauko madara kowace safiya, wannan karamin aiki ne da barorinmu za su yi, domin ban yarda in yi wannan aikin ba.

Na fi jin marmarin harbi fiye da karatu, don maida hankali da ƙwazon aiki bai kama ni ba tukuna. Bayan haka, ban san inda na dosa sosai ba tukuna. ‘Ya’yan su rajah ana shirya su don ƙarewarsu ta gaba, wasu an ƙaddamarsu sun zama ƙanannan hafsoshi a cikin soja, wasu kuwa sun shiga wasu ayyukan gwamnati. Amma ni ban tabbatar da inda ilimina zai kai ni ba tukuna.

Da shike makarantar ta mabiya Hidu ne, sai mu ka riƙe kiyaye ayyukan Hindu. Na koyi tashi tun da safe don yin addu’a. Dole me yi haddacewa daidai kalma-kalma na nassoshi da ayoyin Hindu, waɗanda suke shika-shikan koyarwa addinin Hindu. Ban damu da Hindu ba, amma abin da na koya ya ba ni fahimta a game da wannan addini, wanda hara a yanzu na iya faɗin sa da kyau ƙwarai da gaske.

Akwai ƙaton bambanci a cikin ilimina a makarantar sakandare. Ban koyi kome game da Islama ba. Na kuwa yi murna game da wannan, amma yayana Khuda Bakhsh bai ji daɗin haka ba. Da shike babanmu ya rasu, shi ya ɗauki nawayarilimina. Sai ya sāke mini makaranta zuwa Babbar Makaratar Islamiya a Jammu. An juya ta zama gidan marayu maimakon makarantar kwana, amma wannan bai dami yayana ba, bai damu da ko ina ne zan same shi ba.

Ni ba ɗalibi mai ƙwazo ba ne, nakan bar darasi a duk lokacin da na ga dama, in je gida don in ci abinci, musamman lokacin da yayana ba shi nan. ’Yan’uwana “mata” ba su bayyana abin da nake yi ba. Makarantar ta yi magana a kan halina, wannan ya ɓata dangantakata da yayana. Yana kashe kuɗi don ilimina, ni yi watsi da zarafin, ga shi yana aiki tuƙuru don in sami ilimi.

Al’amarin ya ƙara saboda dangantakar da na shiga da wata yarinya. Lokacin hutu, sai na je wani ƙauye kusa da Srinagar inda muke da wani fili. A can ne na sadu da Salima, na kuwa ƙaunace ta. Da dai na gan ta lura da gonarmu, ko kusa ba mu haɗa dangi da ita ba. Mun zama abokai ƙwarai, mukan sadu a kai a kai. Ban gane abin namu ya yi zurfi sosai ba, sai ran da zan tashi. Ta fara kuka. Ba ta so in tafi. Wannan ya taɓa mini rai kwarai, ƙaunarmu kuma ta yi ta ƙaruwa. Da na sāke zuwa bayan shekara guda, sai na samu ta ƙara girma da kyan gani. Amma na ga alamar sākewa. Ta riƙa yi nesa nesa da ni ba kamar yadda muke da farko ba. Ta tabbatar mini cewa ƙaunarta zuwa gare ni tana nan sai abin da ya yi gaba, ta ji kewa ta ainun. Sai na ruɗe.

In mamaki, me ya faru. Dangantakarmu ta asali ce. Muna jin dadin kasancewa tare kurum. Ba lalle sai an yi jima’i ne ake sanin zahirin ƙauna ba, Tun ina yaro na san cewa jima’i kafin a yi aure yana lalatar da dangaaka mai kyau. Mutum yana iya jira har sai sun yi aure. Amma na gane sarai cewa ni da ita aurenmu ba zai yiwu ba. Iyalinta sun lura cewa iyalina ba za su amince aure ta ba. Iyalin salima ba masu arziki ba ne, nawa kuma ba za su taɓa yarda ha ɗin ya yiwu ba. Na damu amma ba abin da zan iya yi. Dangantaka tsakanina da iyalina ta ƙara rauni.

Na komo makarata cike da ɓacin rai. Ban iya maida hankali ga aikin makaranta ba. Ban taɓa zama cike da marmarin aikin ba, amma yanzu ya zama kamar ma babu amfani. Ba na jin daɗi a can, haka kamar kuma a gida. Ina ji kamar iyalina sun yi dagangar don su ɓata mini zarafin jin ainihin farin ciki. Ba a daɗe ba, sai dangantaka tsakani na da iyalina ta raunana matuƙa. A irin lokatan nan ne, na tsallake darasi, sai yayana ya iso ba labari, ya same ni a wani shagon shayi kusa da gida. Irin shagunan nan wurare ne da ake zaman lalaci da gulmace-gulmace, amma ni ina jin daɗin zama a can ina kallon jama’a.

Nan da nan na firgita. Yayana ya na tsaye kusa da ni. Ya na so ya san ko me nake yi a nan, lokacin da ya kamata ina cikin aji. Lalle kam ba ni da amsa mai gamsarwa, sai ya husata. Ya ga wani yaro ɗan shekara bakwai ko takwas ya na aiki a shagon, sai ya mori zarafi don ya kunyatadda ni cikin jama’a. Yayana ya kira yaron nan ya fara yi masa tambayoyi. Ba a hana aikin yara ba, ilimi kuma bai zama dole ba, don haka ba sabon abu ba ne a ga yara su na aiki. Ba dama a gama matsayina da nasa, in kam mai hali ne.

Yayana ya tambayi yaron, “Sunny, wane lokaci kake tashi da safe don ka kama aiki?”

Yaron ya amsa “Nakan farka wajen ƙarfe 3 na safe, in tsabtace tasoshin da ak mora jiya da dare, in goge tukwane da farantan suya don yin fanken safe, bayan wannan in tsaya tare da mai shagon dukan yini.”

“Karfe nawa kake kwanciya da dare?”

Ya ce “Ban taɓa kwanciya kafin gome sha ɗaya ba.”

Sai yayana ya juyo waje na, cike da fushi ya ce:

“Dubi wannan yaron, bai ma isa rabuwa da mamarsa ba' sa’a huɗu kaɗai gare shi don barci. Bari ya zama misali da darasi a gare ka. Kai ba ka karatu ko aiki. Ka zama namiji mana! Rayuwa takan zama da wuya ƙwarai da gaske ga waɗanda suka yi watsi da zarafi tun da farko.” Sai ya juya a huace ya tafi.

Aka bar ni nan a ruɗe, kuma a kunyace. Na gane ragwancina, na zama da kunya. Iyalina masu arziki ne, kuma da suna mai kyau, amma ga ni nan na zamar musu ƙaya cikin jiki. Na ɗauki abin da yayana ya yi mini ya zama ƙalubala a gare ni, daga ran nan, na ƙudurta a raina cewa, zan dogara ga kaina. Ba zan yi ta zama a jinƙan wasu ba. Duk da haka, wannan ƙuduri, bai sa na ƙara kuzari ga aikin makaranta ba. A maimakon haka, sai na zama mai saurin fushi da kowa da kome. Za a yi jarrabawar shekara ta goma a watan Maris Gab da wannan lokaci sai na gudu.

II - WANENE YESUN NAN?

An fara Yaƙin Duniya na biyu ina ɗan shekara goma sha shida. India ta shiga halin ƙaƙa naka yi. Ta yaya za ta shiga yaƙi da ikon da ke mallake da ɗakwacin ƙasar India? Mulkin nazi mugu ne, ya kamata a yi tir da shi amma Indiyawa da yawa a gare su wannan ba shi da wani bambanci da mulkin mallaka da kabilanci, da tanƙwasa India. Wata jam’iya da ake, “kira, India National Congrss” ta yi ta kira da dabbar murya tana cewa, ‘Yantacciyar India kaɗai za ta iya shiga yaƙi da jamus. “Dole a shawarci mutane” abin da take kwakwazo ke nan. Shugabanin siyasa sun rarrabu. Sun tsani danniyar Hitler, amma kuma su na matuƙar ƙin ra’ayin taimakon Birtaniya. Duk da haka, ƙasar da ba ta da ’yanci, ba ta iya ƙudurta abu don kanta. Da yaƙi ya ɓark, sai India ta sami kanta yaƙi a sashin Birtaniya.

Ni ma kamar yawancin Indiyawa, na matsu da ganin mun sami mulkin kai daga Birtaniya, amma ni yaro ne ƙwarai da zan iya fahimtar dukan abin da ke wukana cikin siyasa da manugofinta. Abin da ya fi damu na shi ne, samun abin yi. Ni kaɗai ne, ban kuma sa zuciyar samun wani taimako daga iyalina ba – ba na ma bukata! Na ƙuduri kasancewa ni kaɗai, sai na shiga sojan Sama. Ban sami wata wahalar shiga Sojan Sama ba. Na amsa wasu ’yan tambayoyi, sai a ka ɗauke ni a matsayin makanike, mai kula da gyara-gyaren jiragen sama.

Na sami horarwa farko a ƙarƙashin wasu Amerikawa, a Lahore, wurin aiki na fari an sa ni a Calcutta ne. Bayan samun ƙarin koyarwa, sa a ka tura ni Burma da Rangoon. Na yi aiki irin na sojan ƙasa, ina aiki sa’a ashirin da huɗu.

Daga baya aka aika da ni Makarantar Sojan sama a Calcutta. A can na sami digiri na biyu a kan basirar aikin soja. Wani daga cikin malamanmu ya faɗi wani abin da ba zan taɓa mantawa ba: “Kullum ka sami amincewar na ƙasa da kai.” Wannan ya zama jagoran ka’idodin hulɗata da na ƙasa da ni. Na yi ta ƙoƙarin kafa kyakkyawar dangantaka da su. Duk lokacin da waninsu ya sami wata matsala, zan yi bakin ƙoƙarina in taimake shi. A gare ni darajar mutum ba ta tsaya kan launin fatarsa, ko kabilarsa, ko doka ba. Rai abu mai daraja ne a cikin kowane mutum. Abin baƙin cikin, ba kowa yake da irin wannan ra’ayi ba.

Ban taɓa rashin biyayya da na gaba da ni ba, ko in yarda na ƙasa da ni su rasa bin dokata. Lokacin yaƙi, kisa ne hukuncin rashin biyayya, amma ban taɓa morar wannan hukunci ba. Idan wani na kāsa da ni ya yi mini rashin biyayya, sai in nemi hanyar warware ta girma da arziki.

Cikakkiyar sadakarwa ga aiki, da tsare mutunci da riƙon amana – su ne ingancin da su ka ba ni nasara a cikin kowane irin muƙami da na riƙe. Ko kaɗan ban yarda da rashin aminci ba, a cikina ko a cikin wasu. Ban taɓa matsa lamba ga na ƙasa da ni ba babu dalili, nakan saurari roƙonsu na ƙwara cikin natsuwa. Na damu kawai da ganin jin daɗin walwarsu, har nakan shirya musu ɗan lokacin shaƙatawa tsakanin lokatan aiki ni da kaina. Wannan ne ya sa suke a shirye don su ba ransu saboda ni.

Bisa ga shawara da shaidar manyan hafsoshin India, manyana, aka sa na zama cikin ƙungiyar hanɗingwiwa na masu basirar aikin soja. Ni ba na gāba da Turawan Birtaniya, duk da haka ba na jurewa da ganin abubuwan rashin jin daɗi a cikin sojojin Sama. Wasu hafsoshin ’yan Birtaniya su ka riƙa wulakanta hafsoshin ’yan India. Ba su ɗauke mu da daraja ba, su na kiran mu “’Yan India masu jjub da jini” Su na yi mana kalamai marasa daɗi. Gaskiya ne, ba kullum mu ke iya rarrabe tsakanin abu mai kyau da marar kyau ba a cikin kalmominsu. Wata rana kwamanda ya kira ni, sai na amsa da yadda nakan ji su na amsawa. Kwamanda Kirista ne, sai ya saurare ni da haƙuri. Sa’an nan ya tambaye ni ya ce, “Yaro ina ka koyi wannan irin turanci mai kyau.” Na ce masa, “Daga wurin hafsoshin ’yan’uwana. Sai ya ce, “To, nan gaba kada ka ƙara morar irin waɗannan kalmomi, na zagi ne.” Sai na ji kunya.

Akwai wasu manyan matsalloli da su ka dame ni. Nakan damu ƙwarai saboda yadda ake fifita ‘yan Birtaniya. Rayuwarsu ta jin daɗi ta fi ta ’yan India nesa ba kusa ba. Wannan ya sa ƙaton bambancin tsakanin hafsoshi ’yan India da ’yan Birtaniya, ko da muƙaminsu irin ɗaya ne. Bambancin kabila ya yaɗu ƙwarai. “Yan Birtaniya ba sa cuɗanya da ’yan India. Mutane da yawa sun gaskata cewa, abu mafi farin ciki na zuwa wuri kamar su Simla, sanannen wuri a cikin Himalayas, ba guje wa zafi kaɗai ba ne, amma kauce ne daga cuɗanya da ’yan ƙasa.

Wannan irin hali ya taɓa babbana ta hanyar baƙin ciki a game da ya faru da abokina na ƙwarai, Sikwadoran Surider Singh. A ka sanr da kwamandan yankin mu sau da dama a game da wani jirgin jefa bam da yake da lahani. Wata rana, sai ya ba da umarni ga ma’aikatarmu cewa, saboda rahotannin nan, ya kamata Surinder Singh ya ɗauki jirgin nan don ya tashi da shi don gwaji. Surinder ya yi shiri ya hau, amma ya damu. Sai ya hau jirgin ya tashi ya doshi kusurwar da aka umarce shi. Bayan minti goma sha biyar sai sadarwarmu da shi ta radiyo ta tsinke. Bayan wasu mintoci goma sha biyar, sai mu ka ga jirgin ya na zuwa ta saman gāɓar Bengal. Ashe Surinder ne. Ba sanar da askarawan ƙasa su tanada masa kāriya ba, ga shi Jafanawa sun babbake rabin fuskarsa da idonsa guda.

Abu na biyu na baƙin ciki da ya taso shi ne, daga yunwar Bengal. Wannan ya nuna matuƙar muguntar mutum, cikin 1943-44. Bengal da Gabashi da kudancin India duk yunwa ta rarake su. Annobai suka biyo bayan ’yunwa, musamman kwalara da malariya. Nan da nan suka watsu cikin sauran larduna. Jita-jita ta nuna mutum 3,400,000 suka mutu, amma sanarwa hukuma ta nuna mutum 1,500,000 su ka mutu a cikin Bengal “a sakamakon yunwa zai iya tantance dubban mutanen da ke mutuwa kowace tana. Da za a iya magance bala’in yunwa nan tun da wuri, amma hukumomi su ka bayyana halin ko in-kula. Da wuya mutum ya iya gaskata labaran mugun bala’in da ya auku a fatattakakkun yankunan nan ba. Wasu hukumomin suka zargi masu watsa labaru a kan kara gishiri. Amma lokaci ya zo da ba dama a ƙara musunta labarun, da gardama a kan ko wa za a zarga, sai a ka maida hankali da agaji zuwa baratar da kai. Dubbai su na mutuwa kowace rana, duk da wannan, ga tarin abincin nan yana ruɓewa a ɗakunan ajiya na gwamnati. A wancan zamani, Malariya cuta ce mai kisa, duk da haka ga dumbin manganin malariya nan jibge ba a aiki da shi a ɗaukunan ajiyar magunguna. Kamar baƙin ciki ya sa ni ciwo saboda mugun halin da ake nunawa a gabana, sai na fara ɗaukar kayan shayi, da shinkafa da sauransu ina ranrraba wa mabukata ƙwarai kyauta. Na kuma riƙa ba da magungunana malariya.

Abin ya tsawala ƙwarai, har attajirai ’yan India, da dukan dukiyar da su ka tara, abin ya kai inda har su ma sun kāsa iya sayen abinci don kansu. Mutane sun fādo har su na sa ’ya’yansu mata su yi karuwancin don samun kayan abinci. Ba shakka, wasu sun mori wannan dama don su cuci ’yan adam ’yan’uwansu, su na sayar da maganin malariya da muguwar tsada. Akwai waɗanda babu bala’in da ke motsa su. Lokacin da yunwa da annobai su ke ta kwashe rayuka kamar ganima, a koyaushe sai gāsa ke gudana tsakanin ’yan Birtaniya da attajirai ’yan India a Calcutta. Su na nan ba sa jin tausayin kowa, sai ƙaunar jin daɗin duniya suke ta yi kamar ma babu abin da ke faruwa.

Wannan ya jefa ni cikin matuƙar damuwa, har hankalin tunanina ya tashi a kan dukan abubwan da ke faruwa a kewaya da ni, shekarun ƙuruciyata su na ta wucewa da sauri, har, shekarun ƙuruciyata su na ta wucewa da sauri, har na balaga da sauri saboda waɗannan al’amura. Wata rana ni da abokina da ake kira Puran shi ma hafsa ne dan India, mu ka tsinci wasu yara biyu da aka yar, mu ka kawo su a zangonmu. Mu ka ɓoye su har fiye da wata shida. Da kwamandanmu ya ji labari, ya tsauta mana ƙwarai da gaske.

Ni da abokina mu na a shirye don mu sha kowace irin wahala don mu ceci yaran nan, amma a ƙarshe a ka tura su zuwa sansanin ’yan gudun jijira, can cikin wani lungu Yammacin Bengal. Muka yi fatan su sādu da wasu idon sani a can da za su iya samun taimako daga gare su, don ba mu iya ci gaba da taimakon su ba.

Ya yi mini wuya ƙwarai in iya kwantar da hankalin tunanina. Don me ba a ganin darajar ran mutum? Yaya za a darajanta ran ɗan adam? Ko akwai wanda ya kula? Inda akwai Allah, to, ya na ina a ke ta yin wannan mugun abu? Tambayoyin da na yi ta yi wa kaina ke nan. Amma nan da nan na sami haske cikin duhu. Gaskiya ne cewa halin danniya na hafsoshin ’yan Birtaniya ya na nan, har yakan haifar da tozartwa' duk da haka, akwai masu halin kirki da ƙauna. Waɗannan Kirista ne, masu ƙoƙarin bin gurbin Ubangidansu, Yesu Almasihu, sun kuma bayyana haske da ƙaunar Allah. Halinsu ya shuka iri a ciki na wanda nan gaba zai yi girma zuwa cikakkiyar juyowa, wato tuba.

Ɗaya daga cikin irin mutanen nan shi ne wani hafsa matashi mai suna Kyaftin Baxter. An yi masa canji wurin aiki daga sashinmu. Kamr sauran ’yan Birtaniya, shiru yake, amma kuma yana da tsinkaya. Muna iya gani sarai ko wani irin mutum ne shi ta wurin yadda ya ke yi da na ƙasa da shi. Ba ya goyon bayan hafsoshin ’yan India ko ƙin goyon bayansu. Ya na son ganin walwalarmu. Akwai lokacin da Indiyawa su ka nemi a ware musu wurin girki da shirin cin abinci. Abincin Musulmi ya na bukatar wasu shiye-shirye na musamman, da murhu don su iya yin dahuwa yadda ya kamata. Bukatarmu da gaggawa ita ce mu sami murhun laka a sabon ɗaki. An yarda mu samu, amma ya na da wuya mu iya samun biyan bukatanmu, ga kuwa irin matsayin irin rayuwar da muke ciki. Ba a maganar irin mamakin da ya kama ni, lokacin da na komo daga wurin aiki a tarar da Baxter ya ɗauki littafin bayani ya na ƙoƙarin gina murhun da kansa. Na ƙara ganin girmansa. Da ina kallonsa, sai fara ganewa da irin girman ƙaunar da yake da ita ga sauran mutane a zuciyarsa. Ga shi nan, yana ta ƙoƙarin gina mana murhu da hannunsa. Ya gamsu da irin roƙonmu, ya kuwa ƙudurta sai ya cika mana. Ko da shike ba wani abu mai wuya ba ne, duk da haka abin ya shige ni da zurfi.

Cin abinci tare, alama ce mai auna cewa mutane sun yarda da juna, kuma abuta ce. Baƙi sun san cewa an marabce su lokacin da a ka gayyace su don cin abinci. Kowace safiya Baxter yana ƙarya kumallo tare da mu abin da hafsoshi ’yan Birtaniya ba za su taɓa yi ba ke nan. Kuma wannan ya na iya zama abu marar muhimmanci, amma a ƙarƙashin irin yanayin danniyar baƙi da muke ciki, abin taɓa rai ne. Abin da Baxter ya yi, aiki ne na abutar ainihi, mu kuwa muka karɓa da hannu biyu-biyu.

Baxter ba mutumin da ke tsauta wa mutanensa da tsananni a kan abin da bai taka kara ya kayya ba, ko abin da ya dāce a yi gyara ne. Alal misali, wasu matasa hafsoshi suka zo karin kumallo ba su yyi gyaran fuska ba. Maimakon Baxter ya tsauta musu, sai ya ciro reza daga aljihunsa ya ba su don su je su yi gyaran fuskar.

Abin da ya fi burge ni da Baster shi ne, lokacin hare-hare. Idan Japanawa sun kawo harin bom lokacin da yana nan, a maiamakon ya gudu zuwa rami don fakewa, sai ya ce wa dukan mutanen: “Samari, ku zo nan. Bari mu shiga ɗakin sujada.” Ɗakin sujada dai na alfarwa ne. Galibin lokaci mukan yi masa biyayya. Lokacin da muke cikin ɗakin sujadar shi kaɗai zai yi ta yin addu’a. Abin, da kaɗai za mu yi ta yi shi ne faɗar “Amin,” lokacin da ya gama. Haka ya faru sau biyu ko uku. Wata rana aka kawo hari mai tsanani. Sararin sama ya cika da jirage, mu ka fara gudu zuwa ramuka. Ga mutuwa ba makawa. Sai Baxter ya yi tsawa ya ce, “Samari ba amfanin gudu zuwa ramuka, ba za ku tsira a can ba, bari mu shiga ɗakin sujada.” Mu ka yi gunagunin wannan umarni na wauta. Ba laifi mu shiga can idan harin ba mai tsanani ba ne, amma a wannan karon, zuwa ɗan ɗakin nan ya zama abin ba’a. Duk dahaka Baxter yana da alamar iko da tabbas a muryarsa. Ya ce, “Zan yi addu’a ga Ubangiji Yesuƙu dai ku ce ‘Amin’ lokacin da na gama.” Ko da shiga tare da shi. Mu ka zauna, muna mamaki da irin wannan aiki nasa. Da baxter ya fara addu’a, ya yi kuka. Har yanzu muryarsa tana bugawa a cikin kunnuwana haka:

“Ya Ubangiji Yesu. Ka bayyana ƙarfinka da ikonka a yau. Ka tabbatar wa yaran nan cewa lalle akwai ka. Saboda ƙaunatattunsu da iyayensu, ka kiyaye su daga harin nan. Ka sa mutanen nan su san cewa kana da rai, kan kuwa da ikon ceto ba na jiki kaɗai ba, amma har da ceton rai daga hallaka. Amin.”

Lokacin da Baxter ya ke addu’a sai wata irin sākewa ta faru. Kowa da kowa ya yi shiru. Wani baƙon abu kuma shi ne, a waje kuma ba a jin motsin kome dai muna nan cikin affarwa kawai, kamar an jebo mana wani bargon shiru ya lulluɓe mu. Da mu ka fito daga alfarwar, sai mu ka ga duk kome ya ruɗe.

Ga gutsattsarin nama ɗan adam nan a warwatse ko’ina. Waɗanda suke a wancan hayin magudanar ruwa bom duk ya ragargaza su. Muna jin nishin wasu, abin karya zuciya ne kuwa. Wasu bom sun fāɗa cikin hanyar ruwa a bayan babban zauren shaƙatawa, ruwa yana ta tafasa. Laka tana ambaliya, ko’ina ya murtuke da hayaƙi. A tsakiyar halalaka ga mu nan mun tsira. Cike da magagi Yesun nan na Baxter lalle ya na da rai, yana kuma amsa addu’a, ya na ceton mutanensa.

Na yi mamaki, wanene Yesun nan? Bisa ga abin da na sani cikin Kur’ani, Yesu annabi ne kawai kamar sauran annabawa. Duk da haka, mutane ba su yin addu’a ga mutanen annabawa don neman kuɓutarwa. Ban taɓa jin addu’a irin ta Baxter ba. Ta nan a sawwaƙe, amma a kaitsaye. Sa’ad da ina yaro a garinmu, na riƙa zuwa gidan mishan na wasu Amerikawa tare abokaina. Abin da na fi jin daɗi shi ne zuwa gidansu mu raira ƙananan waƙoƙi, mu yi wasa da kayan wasan yaransu. Amma cikin sujada ba na ganewa da abin da suke faɗa cikin addu’a. Yakan yi magana da ƙarfi ainun. Amma Baxter ya na yi kamar yana magana da abokinsa yana tsaye kusa da shi. Yana yi a sawwaƙe. Ko lalle abin mai yiwuwa ne?

III - YAKE CIKI DA WAJE

Ba da jimawa ba bayan harin bom da Japanawa su kawo, sai na fara aiki na makanikan sama. Amma na gamu da hatsarin da ya kusa kashe ni, sai aikin ya tsaya. Mun yi gyaran wasu jirage da suka lalace, muna gwaji ke nan bayan mun gayara su. Wata rana ke nan, sai a ka umarce ni in gwada wani jirgi musamman, don aikin da aka yi bai gamsar ba, kayan sadarwa ba su aiki sosai. Nan ne fa na tuna da abin da ya faru da abokina, wanda wajen hawan gwaji aka babbake rabin fursakarsa. Amma dole in yi biyayya, don haka sai na hau jirgi, na tashi tare da wani abokina. Aka ba mu minti talatin da uku mu gama gwajin mu komo. Mun yi nisan mil talatin kurun daga wurin aiki, sai na ji an buge ni daga ƙasa. Abokina, Putan ya ture ni daga kujerar matuƙi, ya kama tuƙin. Muka dai lallaɓa mu ka sauka lafiya, a ka kai ni Babban Asibitin India na 56. Sashin dama na fuskata ya ƙone ƙwarai da gaske.

Da na iso aka yi mini jinyar farko. Ban san abin da ake yi sosai ba, amma na gane akwai wahala wajen karɓa ta a asibitin. Kwana biyu da suka wuce, bam ya fa'ɗa a sashin da a ka keɓe wa hafsoshin ’yan Birtaniya. Ina nan rabi a some, sai na ɗan ji ana magana cewa tsakanin masu jinya da babban jami’in asibitin. Da suka tambaya ko ina za a kai ni, sai jami’in ya ce ba za a sa ni, sashin kowa da kowa ba, don ina da mukamin da a ke kira “RAF Personel.” Masu jinya su ka husata don sun ga raunina mai tsanani ne. Ɗaya daga cikinsu ta tambayi jama’in, “Me ya fi muhimmanci, rai ko matsayi?” Amma ba su yi nasarar karɓa ta nan ba. Sai suka 'sauki nauyin lura da ni a wani ɗaki a gidajen zamansu na masu jinya.

Ban san inda nake ba, don an ɗaure idanuna da bandeji. Na iya sanin irin raunukana ta wurin taɗin da su ke yi a kai na. Na yi kwana ashirin a kwance cikin ɗakin nan, amma ba su bar ni ba, “Mala’ikuna” su biyu sun dāge a kaina. Da hannuwansu su ka ciyar da ni, suka biya dukan bukatuna. Ban iya tunuwa da sauran aikin jinyar da su ka yi ba a kaina. Abin da na sani kaɗai shi ne ba na gani sosai da idona na dama tun daga lokacin nan.

Tun da sassafe a ranar da zan tafi, sai masu jinyan nan su biyu su ka zo su ka gabatar da kansu. Su ne Amber da Maryamu, masu jinya ’yan India. Na matsu in san dalilin da ya sa su ka nuna mini wannan irin ƙauna haka sa’ad da sauran sha’aninsu dabam. Amasarsu ta shige ni ƙwarai da gaske. Su ka ce “Dalilin da ya sa muka lura da kai haka, ba don kana da kyan gani ba ne (da wuya ma su yi tunanin haka a kaina saboda halin da nake ciki, idanu duk a daure!) ba kuma muna neman ka biya mu ba ne, amma kawai domin Kirista ne. Ubangijimu ya sha azaba domin ceton mutane, aikinmu ne mu hidimata wa wasu.”

Wannan irin furci a sawwaƙe ya sa har na ruɗe. Na yi kuka ƙwarai kamar hawaye na za su yoye duka. Yadda masu jinyan nan biyu za su lura da ni haka cike da juyayi cikin sunan Ubangijinsu, wannan ya ƙas'antar da ni. Suka ta’azantad da ni da cewa, “Kada ka yi kuka, har yanzu raunakanka ɗanyu ne.” Na sunkuyar da kaina cikin zurfin godiya, cikin ƙauna na nemi in sumbaci ƙafafunsu. Na sāke karo da Ubangiji Yesu ta wurin almajiran nan biyu nasa. Yesu yana ta fafara ta har ba na iya tsere masa. A cikin dukan kisa da rashin kula da rayukan mutanen da nake gani kullayaumin, sai ga mutanen Allah, masu kula, su na rayuwa don taimakon wasu. Suna riƙe da wasu ɗabi’u masu daraja kamar irin waɗanda mahaifiyata ta koya mini. Na ji kasancewar Allah tare da mutanensa, har ina mamaki ko Allah yana yafuto ni.

Babu amfani ɓata lokaci kuma. An salame ni daga asibiti a ka maida ni sansani. Da isata, sai a ka gaya mini cewa za a bani aiki mai sauƙi. Aikina shi ne hana mayaƙan sama shiga sassan birni da ka haramta masu – yankunan jar wuta. A wannan matsahi na saba da mutanen da ke zama wannan yanki. Nan ne wurin da bisa ga alama ba za a sami ƙauna tainihi ba, amma abin da na tarar a wurin ke nan.

Akwai wani hafsa matashi a wurin aikinmu, sunansa Philip daga Lardi Bihar, haifaffen can ne. Shi mai bandariya ne. Babu mai makara, ana jin daɗin tarayya da Philip ƙwarai da gaske. Amma ba jin daɗin halinsa kaɗai ya kusantar da ni gare shi. Ammaa irin sadakarwarsa da ya ke son yi kullum saboda ƙaunar Mai Cetonsa.

Wata safiya ke nan, sai aka umarce ni in sanar da Philip cewa an canja shi zuwa wani sashin aiki dabam. Ya damu, ba ya so ya tafi. Sai na tambaye shi dalili. Ya ce, akwai yarinya mai suna Kumla, karuwa ce daga wasu iyali masu mutunci, ga shi yana ƙaunarta. Na yi ƙoƙarin ba shi shawara, auren irin wannan yarinya ba shi da fa’ida, amma da dire. Ya ce, ya yanke shawara tun daga birnin zuciyarsa. Ya ce: “Addinina ya kafe a kan hadaya ne. Ubangiji Yesu ya ƙaunace mugum kamar ni, ya ba da ransa hadaya domin ceton raina. Idan har Yesu yana karɓar mai zunibi kamata, to, ashe ni ma aikinane in karɓi mutane masu zunubi, waɗanda duniya ta ke ƙi.” Kalmomin nan sun ba ni mamaki. Philip ya nuna cewa akwai wani mai sauƙin hali, mai kula kuma. Yanzu ya nuna mini shi dabam yake. Manufofinsa sun haskaka kamar haske a ciki duhu. Ba abin da zan iya faɗi kuma, ya riga ya kafa tunaninsa. A gare shi wannan aure da yake shirin yi sadakarwa ce, kusan bin gurdin Ubangidansa. Kyaftin Baxter ya fahimta. Da taimakonsa na iya bayyana al’amarin ga kwamanda, sai aka soke batun canjin wurin aikin. A ka kawo Kumla ta zauna a sansanin har zuwa ranar da faston masujada ya ɗaure aure. Daga baya su ka je su ka zauna a ƙauyen su Philip. Wannan matuƙar ƙarfin zuciya ne. Da zai fi kyau su tafi wani wurin da ba wanda ya san su, amma ya zauna cikin mutanensa, inda akwai s:uka da rashin amincewa duka za a gani a fili, dole wannan sai da ƙarfin zuciya ƙwarai da gaskie.

Bayan wasu kwanaki, na yi ta tunani a kan al’amuran baya: irin rayuwar Kirista ta Baxter, da alherin su Amber da Maryamu, da ainihin misalin sadakarwa irin ta Philip. Wannan tunani ya yi ta juyawa a cikin zuciyata, ina ta duban yadda su ka auku. Daga ina mutumin nan ya sami ƙarfi da alheri har ya iya kau da kai daga soke-soke, da rainin jama’a, ya matsa ya auri yarinya kamar Kumla? Waɗannan mutane sun gaskata cewa su mabarta ne na hadayar da Ubangiji Yesu ya yi domin su, sun yardar masa ya bishe su, ya yi mulkin rayukansu' ba bain rukunai kawai su ke yi ba. Ya yi mulkin rayukansu' ba bin rukunai kawai su ke yi ba. Waɗannan irin tunani sun juyadda ni zuwa wata irin rayuwa, ina ta ganin kowa da kowa ya na ta nuna ƙauna, da kula da wasu. Wanna, ai, wahayi ne! Amma ba ni da lokaci domin irin wannan tunani. Zai yiwu tilas ne ya zama haka. A cikin duniyan nan wadda ke zama marar ma’ana, na gimtsi wata duniyar da ran ɗan adam yake da tsarki kuma mai daraja. Damuwar da na ke ji a cikin raina ba kome ba ce in an kwantata da wahalar da ke mamaye ƙasarmu. Siyasa ta mamaye rayuwar mutum ko yana so ka yana ƙi. Ƙasar India ta na gab da fādawa cikin babban juyi.

An gama yaƙin duniya II cikin 1945. Salama ta iso cikin Turai, amma a India, lokaci ne mafi zub da jini a duk kasancewar ƙasar. A wannan lokacin ba baƙin masu mulki ne suka kawo wahalar ba, amma batun addini ne. Addini ya zamar wa mutanenmu sanadin tuntuɓe, ‘Yan Hindu da Musulmi sun tare, haɗaɗɗiyar al’umma guda mai zaman salama, yanzu duk ya ƙaura. Yanzu sun sami kansu cikin baƙar ƙiyayya ga juna. Tsoro ya ƙara rura wutar ƙiyayya, har ya kai wani matsanancin matsayi. Yawan kisan kai, da tarzoma, da ƙonne-ƙone sun gagara, har waɗanda ba su damu da kome ba dukabin ya gagare su. Musulunci ba sabon addini ba ne. Ya iso cikin India a 712 AD. Duk da wasu tashetashen hankali da aka riƙa samu, an jure da shi an zauna lafiya da shi da Hindu wanda yana nan da zurfi tun kahuwarsa a ƙasar. Daga bisani ne kaɗai Musulunci ya zama makamin siyasa mai ƙarfi a arwacin India, zuciyar Jenghiz Khan ta ci Delih a cikin 1526 AD, ta kakkafa Daular Mughar. Mughal ba su yi niyyar juyar da dukan mazaunan zuwa musulunci ba. Hindu Brahmis kabila mai ƙarfin gaske ba za su yarda ba, ko da ma sun yi ƙoƙarin musuluntar da jama’ar. Sa’ad da Musulmin da suke muhimman mutane daga zuciyar Mughals ne, talakawan da suke musulmi sun tuba ne daga talakawa da ke ƙasƙantattu cikin jama’ar Hindu. A ƙarshe, sai ya zama da wuya a iya rarrabe tsakanin ’yan Hindu da Musulmi. Duka ana iya samun su daga matalauta, da waɗanda aka maida su ba kome ba ne.

Me ya sa,mutanen da su ke zama lafiya da juna, yanzu sun komo su na aman ƙiyayya da gāba da juna? Amsa tanan nan cikin harkokin siyasa. Musulmi su na tsoron cewa Hindu za su kasa yin ƙarfi. Sun gaskata ba za su amince da Hindu za su yi musu gaskiya da adalci ba. Musulmi kuma su na ƙara ganewa da kansu, a su mutane ne masu zaman kansu da a ka sani. Ta haka, Musulmi na matsakaicin matsayi su ka fara ɓullo da kansu. Aka kafa Haɗin kan Musulmi a 1906, wannan ƙuduri ne na kāre hakkin Musulmi a 1906, wannan ƙuduri ne na kāre hakkin Musulmi, da kuma sakamakon ka’idodin ’yan Birtaniya da za su sake a game da su su na ta ƙara karɓuwa.

A cikin hada-hadar siyasa da take mamaye tunanin ’yan Hindu da Musulmi, ana iya jin kiraye kirayen Musulmi da babbar murya, kuma a sarari na neman sashin ƙasarsu mai cin gishin kanta: Dole Musulmi su sami jiharsu-Pakistan. Ta haka farfagandar ‘yan kishin ƙasa ta rura wutar ra’ayin siyasa. A baya can, al’adun gargadiya waɗanda ’yan Hindu da Musulmi sukan yi tare sun isa su sa su ci gaba da zama lafiya tare. Amma yanzu, bangakiyarsu haɗe da kishin ƙasa, ta zama dutsen da su ka fāda a kai ba su kuwa rabuwa.

Aka roƙi sojojin Bitaniya su tamaki ‘yan sandan India wajen maido da aman lafiya a ƙasar. Abin da an iya yi bai ɗore ba. Yanzu Baxter ba shi tare da mu. An kaishi wani wuri dabam. Wata rana bayan mun ci abincin dare, sai a ka kama ni. Kashegari, a ka kai ni tsibirin Indo-China da a ke kira Bala Nakamatti kusa da Singapore. Ban san laifin da na yi ba, amma nan da nan na gane cewa dangane ne da Sojoji '‘an ƙasar India. Mako guda baya, sai takarduna su ka iso. Ga laifufuukan da ake zargi na da su:

1. An kama ni ina sayar da abincin sojoji ga Bangali, kafin mai gadin sashi ya busa usur, na harbe shi na yi masa rauni.

2. Ni da kofur Izhag mun gaida Mr. Mahatma Gandhi, har mun rataya masa ado lokaci da muke cikin kayyan sarki.

3. An ji ne da saje Aslam mu na jawabi a taron siyasa na Mr. Mohammed Ali Jinnah, muna tunzura a yi tawaye.

Hafsa mai kula da wannan sansani ya karanta dukan takardun, sai ya komar da su. Waɗannan zarge-zargen ba su da tabbas. Maimakon ya aika da ni zuwa Chittagong, sai ya aika da ni zuwa wata ƙungiya kusa da Barrackpur. Ko da shike an bar dukan binciken da ake yi gāba da Sojojin India, an bari a cikin watan Afril 1946, ba a karɓi shawarar sakin dukan fursunoni ba. A ƙarshe aka sake ni cikin watan Maris, 1947.

Ina nan a tsaka-tsaki. Ban san abin da zan yi da rayuwata ba. Kamar ma babu amfani in ci gaba da aikin Sojan Sama, duk rayuwa a can ta fice mini. Yaƙi da faɗa sun sa ni ciwo a rai, raunukana sun sa ba na yin matsanancin aiki. Dukan horarwar da na samu ta tuƙin jirgin sama, da ta aikin haziƙanci yanzu ba su da amfani a gare ni. Na yi begen ganin wasu ƙasashe har zai yiwu in sami lambobin ƙwazon aiki. Na ji daɗin kai ziyara a Burma da Singapore, amma muradina na samun lambobi bai cika ba. Rayuwa, Sajan Sama da halin wariya da tozartawa sun kai inda ban iya jurewa ba. Ina so in bata daga aikin.

Iyalina kuma su ka fara matsa mini. Sa’ad da ina cikin Sojan Sama ina hulɗa da su, ko akwai marar lafiya cikin iyalin, nakan je gida koyaushe. Amma yanzu su na so in komo gida. Yanzu da mahaifina ya mutu, sai na ga zai fi kyau in bi shawararsu, sai na ba da sunana don a sallame ni.

Da farko, akwai alamar ba za a bar ni nan da nan ba. Ka’idodin sun nuna cewa, mutumin da ke cikin sashin haziƙanci, zai ci gaba da aiki shekara guda da rabi daga lokacin da ya nemi a sallame shi. Dalilin wannan, don a sa mutum ya manta da duk asiran sarrafa, don kada ya mori bayane-bayanen nan lokacin da ya koma farar hula. Amma kyaftin Dr. Abdullah ya zo don ya kuɓutar da ni, ya ce saboda matsayin lafiyata ina bukatar kulawar likita nan da nan. Sai aka sallame ni, na kama hanya zuwa gida da takarduna na sallama ɗauke da sharfin kyaftin Dr. Abdullah a game da raunin da na ji a idona na dama. Amma mahaifiyata ta girgiza lokacin da na komo. Ɗanta bai sami lamba ba!

IV - MAYAƘIN ‘YANCI

Jin yadda babu kome a raina na komo Janmu, Kashmir, cikin watan Maris 1947. Amma yanayin ƙiyayya, da rabuwa suka tilasta ni in damu da zamn lafiyar iyalina, in taimake su cikin lokatan wahala da mu ke zama ciki. Wanna zarafi ne da zan iya ɗinke ɓarakar da ta faru cikin dangantakarmu.

Mawuyancin lokaci ne, Dole mu lura da abin da mu ke faɗi ko muke yi. ‘Yan Hindu ne su ka fi yawa a Jammu, Musulmi kuma sun fi yawa a arwacin Kashmir. Mu na sane da cewa a kewaye muke da mutane masu ƙiyayya. Matsayin Kasmir babu tabbas.

Mulkin Birtaniya ya ƙara a tsakiyar watan Agusta 1947, amma an raba ƙasar biyu maimakon ɗaya. Pakistan ƙasar Musulmi, da reshe guda a gabas, ɗaya kuma a yamma, an yanke su daga sauran India.

Sauyi ya shigo cikin al’ummar ƙasa, dubban mutane suna ta ƙaura zuwa wuraren da su ka zaɓa da iyalinsu. Musulmi dole su yi tafiya mai isa zuwa Pakistan a yamma. Shan wahala baba misali. Tarzoma ta jawo kisan-gilla. ‘Yantattun jihohi kamar su. Kashmir ta na ɗaya daga cikin muhimman jihohi kima da ba su sa hannu ba daga kayan aikin hawan mulki da aka kira dukan ‘yantattun jihohi su sa hannu. Maharajah ta Kasmir ta na ta gaba da baya, ko wanne ne za ta zaɓa. Hari Singh, da Maharaj mai gargajiyan Hindu ne da tsanani, akwai kuma ƙiyaya ƙwarai tsakanin su da Pandit Nuhru, Firanyin minista na ‘yantacciyar India. Hari Singh ya na jin tsoro kada India ta tilasta demokuraɗiya a jiharsa, sai ya dakatarda da kowace irin ƙungiyar Haɗin kai har na lokaci mai tsawo.

Ko da shike shugabannin siyasu sun yi ta nanata roƙonsu don ƙuduta yardar jama’a, duk da haka bai nuna wata niyya ta yin haka ba. Mafiya yawa na mutanensa Musulmi ne, amma ko da mafarki, ba wanda zai sa zuciyar ɗan Hindu mai mulki ya ba da kai ga Musulmi. Ya yi ta ɗagewa, wato fāsawa tare da nuna jin daɗi.

Kashe-kashe, da halin babbanci da aka fara ya rarrabaƙasar, sun ci gaba. A ko ina babu zaman lafiya. Al’amura suna ta aukuwa da sauri, mulkin mugunta ya na ta yaɗuwa a kowane mataki na zaman jama’a. Amma har a cikin wannan duhun, akwai ɗan haske da ya ke haskawa. Ba kowa da kowa ya juya ya zama mayaƙi ba, don kawai al’amuran siyasa sun sassāke. Ƙaunataccen maƙwabcinmu, Igbah Singh, ɗan Sikh, ya shawarce mu da mu bar garin saboda al’amuran su na ƙara tsamari.

Ya ce mini, “Idan wani zai yi barazana ga rayukanku, mu da muke maƙwabtanku dole me kāre ku – ko da za mu rasa ranmu ne.” Wannan irin karancin ruhu a tsakiyar tekun ƙiyayya haka, ai alama ce ta haska a cikin katantanwar ruwa mai barazanar durmiyar da mu. Mun sani a ƙarshe Maharajah za ta haɗe da India, ko da yake mafiya yawan mutanen a cikin Kasmir Musulmi ne. Rayukanmu su na cikin hatsari har kullum, dole mu yi wani abu. Na rinjayi ‘yan’uwana su aika da matansu da yara zuwa garinmu. Sun yi haka ba da son su ba, amma ba su da zaɓi. Al’amarin ya ƙara muni. Kowace hari a kan niyyar kansan kai na mutane ya ƙaru. Hukumomi ba su iya hana kome. Ya zama dole na tilasta yayyena biyu maza su bi matansu zuwa garinmu. Wannan ya zamar musu kamar duka mai ƙarfi, don kuwa suna da gonaki da kaddarori da yawa a nan Jammu. In sun tafi, ya zama sun yi hasarar dukan abin da suka yi aiki matuƙa a duk rayuwarsu. Amma da shika yi aiki matuƙa a duk rayuwarsu. Amma da shike rayukansu su na cikin hatsari, dole su zaɓi abin da ya fi musu, sun kuwa gane ba za su iya musanya ransu da mallakarsu ba. Duk da wahala da jin ɓacin rai, sun tafi. Ya alkawarta zan tsaya don in lura da mallakar iyalinmu.

Barazana ta saɗaɗo kusa da ma’aikatrmu, ta mamaye. Mu na da wani lebaru ɗan shekara gomasha huɗu, mai suna Illiyas. Da bai iya zuwa gida cin abinci ba wata rana, sai ƙanwarsa ta zo don ta ga kome ya far. Sai na faɗa mata cewa, ai, bai ko zo aiki ba a ranar, amma ta matsa cewa ya bar gida zuwa wurin aiki kamar kullum. Sai na fara zato. Zai yiwu ya fāda hannun mugaye. Na ji tsoro ko abin da ake gudu ya faru. Na kama hannun yarinyar, na tafi tare da ita titititi mu na neman ɗan’uwanta. Nan da nan sai mu ka ga gawarsa a lambatu. Na ji kamar na kamu da ciwo, ‘yar yarinyar kuma ta kama kuka ba dama. Na yi ƙoƙarin rarrashin ta amma a banza. Daga baya, na baza labarin ga iyalinsu, na kuma taimaka ga shirin jana’iza. Aka binne Illyas a ranar. Dukanmu an sa mu gaba. Wani ma'wabcinmu ɗan Sikh ya roƙe ni cewa, ya kamata in bar garin. Yana da wuya ma’aikata su yarda su bar aiki domin inda kaɗai su ke samun abin zaman gari ke nan. Idan sun bari, to, ba abinci, sai yunwa ta tagayyara su da iyalansu. Ga su kuma da halin ba. Amma na matsa dole su bari su tafi, na biya su. Birnin Sialkot da ke a kan iyaka a Punjab, Pakistan, su ka ba da mafaka, sai su ka tafi can. Na rufe ma’aikatar. Wannan abin baƙin ciki ne a gare ni. Begenmu na ƙarshe na ceton mallakarmu duk ya tafi. Muna da gidaje uku a cikin jammu, da kanti, da ma’aikata, da kadada ɗari huɗu ta gonaki maiƙo. Dole mu bar duk waɗannan.

Biya don samun sabuwar jiharmu ya na da tsada ainun, amma manufar da ke ƙunshe cikin wannan raba ƙasar don Musulmi – Pakistan – ta yi nasara.

Kusa da ƙarshen Septemba 1947, sai na sa kayan sarki, na rataya bindigata, na kama tafiya ina ƙetare titi-titi. Na yi kamar wani hafsa ne don kada wani ya musguna mini. Duhu ya yi sa’ad da na isa kogi tui, wanna ya ba ni kyakkyawan zarafi, na yi iyo na haye. A wannan hayi, sai na ji mai gadi ya daka mini tsawa, “Dakata!” na kuwa ji tsoro, amma sai ya ce, “Ba kome wuce dama ina dubawa ne.” Na ci gaba da tafiyata, na yi gudu wajen mil ashirin zuwa gidanmu a ciki Zaffarawal. Mahaifiyata ta marabce ni da hawaye. Rayuwar muka gina tare, yanzu ta rushe. Babu wani begen kirki. Amma bisa ga ‘yan siyasa, wannan abin sha’awa ne, sabon mafari kuma. Mun dai yi sa’a. Al’amuranmu ba su lalace kamar yadda muka zata ba. Har yanzu mu na da gida mai kyau, da isasshen abinci, mun tsira daga kwashewa zuwa sansanin ‘yan gudun hijira.

A gare ni rayuwa ta rasa ma’ana. Kome ma ya zama fanko, ba amfani. Na fidda rai, ina fama da baƙin ciki. Amma ban manta da manufar da rayuwa take da ita a dā ba. Ni ne dai na rasa ta, aikina ne kuma in nemo ta. Na komo wajen addini don in sami sauƙin baƙin ciki da sabuwar manufar – abin da mutum zai rayu a kai, har ya mutu a kai. Ina marmarin yin aiki mai amfani. Na hakikkance cewa,, dukan yadda nake a dā, da abin da na gogu da shi, na horu da shi, suna bukatar sabuwar hanyar aiki da su.

Na fara ɗaukar Musulinci da tsanani. Addinin da aka goye ni a ciki ke nan. Na ƙudurta zama Musulmi nagari, ina ta yin salla a kan kari, amma ban taƙaice kaina a kan wannan ba, ban kuwa maishe shi wani babban abu ba. Na nemi malaman addini waɗanda za su bi da ni a kan hanya sosai.

Daga kowane masallaci ana ta kira a yi “Yaƙin Jihadi.” Kamr yadda mu ka ji tsoro, haka ya zama, an haɗe Maharajah ta Kasmir India. Yawancin Musulmi sun husata, idan Kasmir ba ta kasance cikin Pakistan ba, to, gwamma ta yi zaman kanta. Wanna babban aiki ne. Ka’idar Jihadi tana kiran dukan amintattun Muslmi su yi yaƙi da arna. Tun kafuwar Musulunci, siyasa da addini a haɗe suke. Babban aikina shi ne in gamshi Allah don ya bishe ni in zama mayaƙin ‘yanci. Ta haka abin ya fara a cikin raina lokacin da dukan darajar renon da aka yi mini ana yi masa barazana. Himmata ta rufe dukan lamirina, na cika da neman ramuwa da mutuwa. Na fara shirin shiga wannan ƙungiya wadda bisa ga alama za ta biya mini dukan bukata a wannan lokaci. Yanzu akwai abin da zai cike gurbin da ke cikin zuciyata.

Na sadu da sardar Muhammed Ibrahim, shugaban farko na ’yantacciyar Kasmir ya ba ni Katinsa in kai zuwa hedkwatar sojan maya'kan ’yanci. Na shiga a matsayin soja kurum marar wani mu'ami. Ban nemi in sa a san ni a irin goguwata ta dā ba, ban faɗi kome a game da irin horarwar da na samu a Sojan Sama ba. Yawancin mayaƙan ‘yanci tsofaffin sojoji ne, na ƙasa da na sama. Amma wannan ƙungiya ba ta shiryu da kyau ba, kuma ba a biyan albashi. Masu goyon bayanmu su ke ciyar da mu. Ba mu da wata hanyar samun kuɗi ta kanmu. In ba mu da kome, sai mu kashe dabba don mu sami abin ci. Sau da yawa hankali yana a tashe, saboda Sojan ƙasar Pakistan, waɗanda sun fi so su gan mu a shirye, kuma horarru don yaƙin ’yanci. Amma wannan bai yiwu ba ko kaɗan.

A cikin watan Oktoba, mutane masu yawan gaske daga Arewa Maso Yamma su ka kwararo zuwa Kasmir. Ni da wasu abokan aikina muka haɗa kai da su cikin kai hari na farko daga Muzaffarabada a Bada Mavla. An ci gaba da kai samame har wajen wata biyu. Lokacin kuwa sanyi ya fara, a ka aika da ni zuwa fagen dāga na ɓarin kudu. Yaƙin ya na da tsanani ƙwarai a nan. Sashin da aka tura ni an ba su aikin datse hanyar da ta hade da ta Pathankat (wato sauran India) da Jammu, in ya yiwu kuma, mu kame ta, mu zauna ciki. Bayana da Maharajah ya haɗa kansa da India, sojojin India kuwa an aika da su don su taimake shi kwantar da tarzoma, da kabilu masu tasar masa. Mun nace da niyyarmu ta mamaye hanya, amma an yi ta ba mu kashi, an kashe mana mutane da dama. Duk da haka mun ƙoƙarta mun karkasje wasu na sashin abokan gāba, duk da kashin da muke sha.

Lokacin da na shiga ƙungiyar yaƙin ’yancin sosai da sosai ne mu ka sāke saduwa da Salima. Ta yi farin ciki, ta zaƙu mu sabunta abutakarmu, har ma mu kai ga aure. Iyalina sun rasa arzikinsu, har ma mu kai ga aure. Iyalina sun rasa arzikinsu, don haka babu batun ƙin yarda da aurenmu. Ni ma ina son haka, amma ba na take ba. Na kamu kwarai, cikin niyyar zama ɗan gaban goshin ’yan ƙasanci, da zaƙuwata cikin addini ta neman farin cikinta. Muka rabu, amma ban sani ba, ashe ƙarshen saduwarmu ke nan.

Wani lokaci daga baya, na je ƙauyen su Salima, na tarat ba ta da lafiya. Ba a yarda in ganta ta ba. Ban san tsananin ciwon ba, sai na yi tafiyata na kama abin da na sa gaba, na bar ƙauyen ba tare da matsawa in gan ta ba. Bayan wata guda na koma ƙauyen don in ga Salima, abin da na gani ya karya zuciyata ƙwarai da gaske. Zuciyata ta na bugawa da sauri kamar kirjina zai ɓarke. Na ga ƙanen Salima, da iyalinta, da dangi su na komowa gida da doguwar fuska cike da baƙin ciki. Na razana, tsoro ya kama ni. Na yi tambaya. Ko wani abu ya faru da Salima? Sai ƙanenta ya ce mini: “Salima ta rasu da safen nan.Mu na komowa daga binne ta ke nan.” Sai na rafke.

Na dubi sama, na ga rana tana fāɗuwa. Ga haske mai kyan gani a sararin sama. Yini ya kusa ƙarewa, ran Salima kuma ya ƙare. Ta mutu saboda karayar zuciya ne, in ne da alhakin mutuwarta? Na cika da nadama da baƙin ciki. Ƙofar murna da farin ciki kamar ta rufe. Na komo wurin abokan yaƙina cike da karyayyiyar zuciya. Abin da kaɗai zan yi don ya kawar da baƙin cikina shi ne, in tsunduma kaina da zurfi cikin ƙungiyar neman ’yanci. Ya zama kamar wannan kaɗai ne abin da zan rayu a kai. Nan da nan kwamandojina su ka lura da irin goguwar horuwar da nake da ita, wadda za ta amfani ƙungiyar ƙwarai da gaske. A ka yanke shawarar naɗa ni kwamanda a wani dare. Akan yi kome a asirce a cikin wannan yaƙin sunƙuru. Na zama kwamandan wani ɓangare da nawayar horar da sauran ’yan yanƙin ‘yanci. A hankali na shiga aikin zurfin basiri.

Na tuno wani lokaci sama-sama. Muna kan wani aiki, saura kamar kwana biyu mu gama. Mu uku ne mu ke yi wannan aiki na basira a cikin tsaunuka. Sai itace ya ƙare mana. Abincinmu masara ne kaɗai irin mai zaƙin nan wadda muke dafawa mu shafa mai. Mu na jin yunwa ƙwarai da gaske. Nan kusa da wasu ‘yan Hindu su ka ƙone gawar wani ɗan’uwansu. Wannan wuri ya kamata mu yi ta zaga shi, don ba a son ganin wani ɗan Hindu ya na ragaita a wurin. Amma kamar yadda ban taɓa jin tsoron kome ba, ina kuma tunani ko yaya za mu sami maganin yunwa, sai na sami wata dabara mai kyau -–isa ga tunanina. Sai na ɗauki masarata, na nufi wajen masu jana’izar. Mu na cikin yankin magabta, ba za mu kunna wuta ta kanmu ba' don kada ta jawa hakali. Na gasa masarata da gawarshin wutar jana’izar. Abokan aikin sun ji daɗin ina komowa da gasassihiyar masara, su na ta tambaya yaya na yi har abin ya zama haka. Bayan sun ci sai na ɗan faɗamusu a lalace. Ba mamaki sai su ka fara nuna jin kyama, su na gunagunin ciwon ciki. Sai na ɗauka su na tsarguwar tunani ne!

Ayyukanmu sun haɗa da kowane irin ruɗi. Wani lokaci sai na ɓadda kama na zama kamar ɗan Hindu Brahmin mai neman mafaka daga Pakistan. Saboda ana sāke tsugunnar da mutane don yanke ƙasar daga Indiya, ‘yan gudu hijira bai zama abin mamaki ba. Ban zama abin kama hankali ba domin dubban ‘yan Hindu suna barin mallakarsu duka a Pakistan suna tafiya India. Aikina shi ne, in gane ƙarfin sojan India, da inda su ke samun kayansu a wannan yanki. Da na isl kan iyaka, sai na fara kuka ina bada labarin yadda a ka karkashe iyalina, a ka kashe mallakarmu duka. Suka damu ƙwarai su ka ta’azantar da ni, su ka tabbatar za su taimake ni. Su ka gaya mini za su ba ni gida da kayan gida, don in fara rayuwa tun daga farko. Na sami sauƙi, abu ya yi kyau. Amma ga wata masifar, sai su ka ce in hadace wani sashi na nassin Hindu. Na kuwa san wasu da dama, na koye su sa’ad da nake karatu a makaratar Hindu a Jammu. Amma ainihin wanda su ke so in haddace ban san su ba. Wuri ya yi wuri, na tsoranta, dole in yi tunani da sauri. Sai na fara kukadon in sa su ji tausayi na. Na ce na ruɗe, na kuma gaji 'kwarai da zan iya yin wani haddace yanzu. Amma wannan bai dame su ba, sai su ka fara shayi na. Na dugunzume. Idan fa suka gane ko wane iri ne ni, za su zaci sauran mutanena ma suna kusa.

Ba zai yi musu wuyar gane ko wanene ni na ainihi ba, don ina ɗauke da saida a jikina. Kowane ɗan Musulmi dole yana da kaciya. Tuɓe ni za su yi zindir don su gani ko wanenen ni. Abin da ya ƙara munana abin shi ne, ina ɗauke da su gurnet cikin tufafin jikina. Da su ka kai ni gafe guda don su yi caji na, sai na ƙwaci kaina, na yi tsalle ta katanga. Sai na jafe gurnet guda, bayan kamar daƙiƙa sha biyar sai na ƙara je fa wani. Wuri duk ya harƙume da wuta.

Irin wanna hallakar da ’yan adam da dukiya ba sabon abu ba ne. Aikinmu ne mu shiga ƙauye, mu iza ƙeyar kowa da kowa da bakin bindiga zuwa cikin gidajensu, mu kukkulle ƙofofi daga baya sa’an nan mu ɗirka wa ƙauyan wuta.Wannan rashin imani da halin dabbanci bai taɓa lamirina ba sam. Ni kawai ina aikina ne dole in yi shi da kyau. Muddin Allah ya yarda da aikin don me zan dami raina?

An yi ta gwabza yaƙin neman ’yanci har shekara biyu. Wajen ƙarshen wannan lokaci, abubuwa sun yi ta faruwa da suka tuna mini da abubuwa masu daraja da na koya cikin ƙuruciyata' zaman tsarki da kulawa da wasu. Waɗannan abubuwan suka zo mini, sai kuma su bata, sai in bi abin da ya fiye mini a rai.

A matsayina na kwamandan sashi, na zama mai shishirya kai hare-hare. San da dama muka riƙa samun taimako daga Pathans na Arewa maso yamma, da yarda su suka ba da kai don taimakon mu ƙara yawa. Ba wasu ƙwararru ba ne, sun fi maida hankali ga neman mata da sauran jin daɗi fiye da yaƙi don ’yantar da Kashmir. Amma muka shirya taro a sashina don mu tattauna shiye-shi-ryenmu tare da su. Da lokacin ya gaboto, na yi tafiya a kan titi, abin mamaki, sai na ji wani ya kira sunana. Wata ‘yar murya ce ta mace, ban gane ta ba. Sunan da ta kira, iyalina kaɗai da kuma shaƙiƙan abokai suke kira na haka. Ta kirani, “Gama,” wani sunan barkwanci da aka ba ni. Na duba wajen da muryar ta ɓullo, sai na ga wata yarinya, ƙanwar wasu ‘yan Hindu abokina, tana tsaye a bayan wata taga. Da kyar na gane ta, amma na tuna tana cikin iyalin da mahaifiyata ta ba su mafaka a cikin gidanmu har wata biyu, kafin su sami ƙetare kan iyaka zuwa cikin India. Na ce “Ko ke ƙanwar sudesh ce?” Ta ji kunyar yin magana da ni, sai ta kaɗa ka. Na ce, “Me ya kawo ki nan?” Na roƙe ta ta faɗa mini, don na ga tana cikin tsananin wahala. Aƙarshe dai ta ba ni labarin irin wahalar da ta gamu da ita. Pathans goma sha biyu su ka ƙetara, su ka kai hari a ƙauyensu, su ka kawo ta wannan wurinn inda kowannensu ya yi mata fyaɗe. Na kāsa magana. Me nake gani haka? Sakamakon zaƙuwar addinin ke nan? Musuluncin ne ya kawo irin wannan hali? Karo na farko da na sa alamar tambaya gaba da irin ayyukana, shakka ta fara rufe ni. Wannan ɗan abu ya zamar mini da wuya ya ɓace mini. Dole in yi wani abu yanzu a cikin wannan al’amari. Na mori muƙamina aka sake ta. Na kaita wurin mahaifiyata, aka lura da ita har ta warke sarai, sa’an nan aka sāda ta da iyalinta a ƙetaren iyakar ƙasa.

Wannan rashin adalci ya sa na tuna da wani abin da na taɓa gani. Ina cikin garin Gujarat a hanyata ta zuwa Kashmir. Da ina tafiya ta inda a ke bazaar, na ga inda ake sayar da ’yan adam. An sayar da mata uku bisa ga darajarsu. Mace ɗaya-budurwa-aka sayar da ita a kan kimanin naira ɗari uku na kudin ƙasar can, wata kuma da ta yi aure har da ɗan yaro, a kan kimanin naira ɗari biyu na ƙasarsu can' wata tsohuwa kuma naira ɗari biyu na ƙasarsu can' Na tuna yadda abin ya girgizani. Ta yaya ake iya kimanta kamanin mutum, na yi wa kaina wannan tambaya?

V - MAƘIYIN DA BA A ZATO

Natsuwar hankalina ta na a tashe. Yanzu ban ni ta tabbas a kankaina. Duk da haka zan ci gaba. Ba zan tsinke a tsakiya ba. Ina ta lilo a tsakanin Pandit Nehru, Firayin Ministan India,da Liaguat Ali Khan, Firayim Ministan Pakistan. Sojan India sun amfana daga wannan shirin, sun ƙarfafa matsayinsu a Kasmir. Amma mayaƙan ‘yanci cikin Sojan ‘Yantacciyar Kashimir su na ta ƙara taɓarɓarewa. Akan watsa mayaƙan ‘yancin barkatai ba tare da shiri mai kyau ba, babu tunani. Sun ɓalɓace saboda rashin hanyar samun guzuri, sai da dare kaɗai su ke iya yin yaƙi.

Wani dare, ni da abokaina muka shiga wani ƙauye. Ƙauyen yana gab da kan iyaka daga cikin India. Na ji cewa akwai wasu da ba Musulmi ba a cikin ƙauyen sai na aika a zo da Numberdar, wato sarkin ƙauyen, na tambaye shi ko gaskiya ne akwai waɗanda ba Musulmi ba su na zama a ƙauyensa.

Ya amsa ya ce: “Ranka ya daɗe babu ‘yan Hindu, amma akwai wani iyali Kirista.”

Kirista? Ka na nnufin mabiya Isa?”

“I, mutum uku ne kurum.“

Wannan matakin a gare ni ba sabo ba ne bisa ga fahimtata da Kristanci a wannan matakin. Na tuna wata rana ina tambayar Mulana (Shahararren malamin Islama) don ya ƙara bayyana kalmar kafiri, “arne ko marar bi.” Ya amsa cewa, duk wanda bai yarda ya faɗi kalmar shahada ba, wato Dokar Musulunci' arna ne. Kalmar shahada ta ƙunshi manyan ka’idodi biyu:

Babu wani Allah sai Allah kaɗai.

Muhammadu kuma Manzonsa.

Kowanen musulmi na gaskiya dole ya gaskata ya kuma furta wannan tushen dokar. Duk wanda bai faɗi wannan ba za ɗauke shi arne ne. Saboda haka akwai abin yi yiwuwa guda biyu kawai domin kowane mutum: kofar salama ko ta yaƙi. In ba mutum ya karɓi dokar ba, ya kuma miƙa wuya ga koyarwar Muhammadu ba, ba zai sami salama da kyayyewar Allah ba, ya zaɓi yaƙi ke nan da sakamon yaƙin.

waɗannan a fanyace suke. Amma na yi wata tambaya ta musamman. Me Malalm ya ke tunani a game da Kirista? Sai ya ce, su kuma “Mutanen Littafi” ne. Kirista da Musulmi su na iƙirarin su na bauta wa Allah guda ne, sun kuma gaskata ya ba da wahayai cikin littafin. Na Kirista ya ƙunshi Tsohon da sabon Alkawari, Musulmi kuwa Kur’ani. Musulmi sun gaskata cewa wahayoyin da aka yi wa Muhammadu a cikin ƙarni na bakwai a Makka da Madina, Mal’ika Jibra’ilu ne ya kawo masa akwai kuma makamantansu a sama. Sun taƙaita saƙon Allah ga dukkan annabawa marigaya, na Muhammadukuwa su ne wahayoyi na ƙarshe na Allah zuwa ga Mutum. A cikin Allah ne ba, amma an amince shi annabi ne kamar sauran dukan annabawa. Musulmi sun gaskata cewa an shashare wasu nassoshin Yahudanci da na Kristanci, aka maye gurbinsu da wahayin da aka yi wa Muhammadu a cikin Kur’ani. Duk da haka, a ganina, in Kirista su ma “Mutanen Littafi” ne, ba za a haɗa su daidai da arna ko wanda bai yarda ya faɗin kalmar Shahada ba ne kurum, to, su ma kafirai ne ka nan, sun kuma cancanci a yaƙe su ke nan. Malamin bai ci gaba ya kawo ni ga ƙarshe ba, bai kuma tabbatar da duka abin da zai yi mini jagora har in kai ga yin wani abu ba. Wannan hira ta fari kawo rudarwa maimakon ba da haske. Amma a gare ni, al’amarin a yanke yake, ko su kafirai ne ko babu. Tun da shike ba su faɗin kalmar Shahada, su kafirai ne, dole a shirya a yaƙe su.

Da shirin waɗannan tunanin ne na nufin gidan Akwai wani ɗan ɗaki a cikin katangaggen gidan, amma an kulle ƙofar daga ciki. Mu ka ƙwanƙwasa aka buɗe ko'far.

“Ku Kirista ne?”

“Har a wannan lokaci ku Kirista ne. Yanzu ba za ku juya ku zama Musulmi ba?”

Mutum biyu su na tsaye a gabana, su na rawar jiki. Su na tunanin irin amsar da za su ba ni,sai wata yarinyata jawo jiki daga ƙarƙashin gado, ‘yar wajen shekara goma da haihuwa, ta tsaya a gabana ta amsa mini cewa:

Ba za mu zama Musulmi ba,”

Na fashe da dariya, na ce mata don me?

Ta amsa, “Ba za mu canja addininmu don kowane irin dalili ba.”

Na ce, “Wawa kurum, ai, dole ku yi tunani a game da ranku, hanyar kaɗai da za ku ceci ranku ke nan.” Duk da haka ba ta ba da kai ba.

Ta ce, “Mun ba da gaskiya ga wannan dā ya ce, ‘Ina tare da ku har matuƙar zamani, mun kuma gaskata ya na tare da mu ko a yau ma.”

Ban yi haƙuri da irin wannan ba. Taurin kanta ya ci mini rai, na yanke shawara nan da nan, na ce “Da kyau, za mu gama da sau biyun nan, ke kuma za mu tafi da ke zuwa sansani, mu yi canji da ke da wata ‘yar Musulmi daga India.” Amma wannan ‘yar yarinya, ‘yar shekara goma kurum ba ta yarda ko kusa ta ba da kai ga bantsoron da nake yi mata ba.

Sai ta ce, “Ka yi duk abin da ka ga dama, amma muna da roƙo guda za mu yi gare ka.”

Na ce “Mene ne?”

“Ba muna roƙon ka don ka bar mu da rai ba ne, amma ka ba mu ’yan mintoci kaɗan mu yi addu’a, domin mu roƙi wannan da ya yi mana alkawari zai zo ya taimake mu,” ta faɗi haka cike da amincewa. Babu ko alamar tsoro a idonta.

“Wawar yarinya kawai! Ai, yau baubu allahn da zai ceci kowa a nan. Babu mai ceton Musulmi ai, a kan iyakar ƙasa daga sashin India, a wannan gefen kuma babu allahn da zai ceci ‘yan Hindu. Ba ku ga yadda aka yi kaca-kaca da haikali ba a Fort Haptal, a can an rushe shi har ƙasa cikin ‘yan so’o’i kaɗan?” Na faɗi haka don dai in tsorotar da ita.

Ta nace da cewa, “mu dai ka ba mu ‘yan mintoci kaɗan kawai.”

“Na yarda ku yi addu’arku,” na amsa da gatse na ƙara da cewa, “Ku yi, kila ku samar da bam ta wurin addu’ar.”

Yarinyar da da sauran su biyun, su ka durƙusa. Ban ji abin da su ke cewa ba, amma na lura hawaye suna gangarowa daga kumatun yarinyar, leɓunanta su na motsi. Sa’an nan sai na ji shiru dukansu uku su ka amsa tare: “Cikin sunan Yesu Almasihu. Amin.”

Da dai su ka ce Amin, sai wani haske mai ƙarfin gaske, kamar bango ya taso daga ƙasa, ya kange su daga gare mu. Ko da shike na taɓa riƙe da mugun gurnet da kayan wuta mai barna amma ban taɓa ganin haske mai ƙarfi da bantsoro kamar wannan ba tun da nake. Wanna dabam yake, hasken ba na duniya ba ne, ban iya bayyana shi.

A hankali, sai hasken nan ya matso ni, sai na fara tsoro. Na ga kamar zai zo ya ƙone ni ƙurmus. Zufa ta ɓarko mini, hankalin tunana ya tashi. Karo na farko ke nan, ban da wanda na taɓa gani tun ina ɗan shekara tara rabon da in ji tsoro irin wannan – ainihin jin tsoro. Ban san abin da zan yi ba. Nan da nan, na yi tunani cewa, dole in ba zan yi ba. Nan da nan, na yi tunani cewa, dole in ba su haƙuri, in roƙi gafara ga waɗanan matsiyata, cikin tsoro da rawar jiki na ce musu, “In kun yarda ku gafarace ni.” Abin da ya sa na roƙe su ya fi gaban ganewata, amma ba shakka su na da halƙa da wani iko mafi girma da ban taɓa gani ba. Duk da haka dai, sai na ji “Mun gafarceka cikin sunan Yesu Almasihu.”

Da dai su ka faɗi haka, sai bangon hasken nan ya ɓata. Su na nan tsaye a gabanmu, a natse, cike da salama, su na a shirye su yi abin da zan umarce su. Ba mu ci gaba da tsayawa a wurin ba. Muna da wasu kayan ado na duwatsu masu daraja da muka sace a wasu gidaje da aka gudu aka bari na ‘yan Hindu. Sai muka watse musu kayan nan mu ka tafi, munajin mu mabartansu ne saboda wahalar da mu ka ba su.

Bayan mun komo wurin zamanmu, ban iya yin barci ba Sai sunan Yesu Almasihu ya ke ƙara a kunnena, yana ta kai mini hari akai-a kai. Na fara tunawa da abin da ya faru a baya lokacin da aka kawo sunan Yesu Almasihu da ƙarfi a cikin tunanina. “Ubangiji Yesu” na Baxter ne – dukanmu kuma mun san haka cewa wannan ne kaɗai baynai a game da kuɓutar da rayukanmu – sa’an nan ni mabarcin raina ne a gare shi. Duk da haka ban san shi da kaina ba, ban ma san abu sosai a game da shi ba. Ta yaya zan iya nuna godiya ga wanda ban sani ba? Amma dole in gode masa, domin ya ceci raina.

Sa’an nan ga batun “Yesu Almasihu” na su Amber da Maryamu wanda suka dogara gare Shi, wanda saboda shi ne su ka ceci ran saurayi matashi, suka yi jinyar raunukansa. Ba ceton raina kaɗai wannan Yesun ya yi ba, amma ya tabbatar almajiransa sun lura da ni lokacin da na yi rauni babu taimako. Don me zai yi wannan domin na? Ban ba shi girma ba. Ban san hanyar rayuwar da ya biɗa daga mabiyansa ba, ba na ma bin hanyar. Kasancewata Musulmi na gaskiya, na kiyaye dokokin Musulunci. Na ba na Yesu Almasihu ba ne.

“Yesu Almasihu” na Philip, ya ba Philip ƙarfin da zai yi sadakarwa mai girma. Ni ma na yi hadayu, na rasa zarafi da dama don farin ciki na kaina tare da Salima, na rasa ta har abada saboda muradina na in gamshi Allah cikin Yaƙin Jihadi. Amma ban ji wata dangantaka ta kaina tsakanina da Allah ba, ko in gaskata cewa ya ba ni ƙarfin hali da zan yi kowane abu. Na dogara a kan abin da nake da shi ko salihancin kaina.

Abin da ya burgawa duka cikin goguwata shi ne karona da “Yesu Alamasihu” na ƙaramar yarinyan nan wanda ya zo ya cece ta nan take. Shi ne wanda ya cika alkawarinsa. Idan ina da wata shakka a kansa da ya ceci ƙungiyarmu da bom ɗin Japanawa, to babu daliln shakkarsa da idona. Ba abin da zai kawar da wannan gaskiyar. Da alam “Ubangiji Yesu” ya na ta, yadda na roƙi iyalin na ga fara, ban taɓa yin wani abu kamar haka ba. Ko ya zamar mini na yi ba daidai ba na yi tunanin kashe su? Ko dukan rayuwata cike da zunubi da ƙin yin biyayya ga abin da lalle na sami daidai ne? Ga shi sun gafarta mini cikin sunan “Yesu Almasihu.”

Nan da nan na fara gane abin koyi daga cikin goguwata. Sun zama warwatsaattsun abin duwatsun wuya, waɗanda sai an tattara su, a haɗa a sami cikakken dutsen wuya. A kuɓutar da ni daga wata irin mutuwa, an lura da ni, an kuma nuna mini fa’idar hadayar Yesu Almasihu a cikin rayukan wadanda a ka gafarta musu cikin sunansa.

Ko an ware somin wani abu? In haka ne, to, menen?

Irin waɗannan tunani da ke azatad dani, su na ta zuwa a kai-a kai, sun hana hutuwa. Su na tilasta kansu a kan tunanina. Duk dahaka ikonsu bai isa ya jawo sauran tunani da kuma miƙa kai ba. Har yanzu ina cikin ƙungiyar ’yan yaƙin yanci da zurfi ƙwarai da gaske. Yana da wuya in ajiye makamai kawai in yi tafiyata. Ba ni da wani abin da zan ba kaina. Ko da shike zaƙuwata ta sassauta, har yanzu ina ci gaba da ayyukansa.

Wani dare ke nan, sai mutanena su ka kai hari cikin nasara, su ka sa wa wani kauye wuta, yana can cikin gundumar Jammu. Ina tsaye ni kaɗai a gefen wata gona a kan hanyar datanufi cikin lardin. Ina ji mutanen da ake kashewa su na ta kuka da kururuwa a ƙauyen. Ina jiran duk wanda ya ke ƙoƙarin tserewa in harbe shi.

Na hangi wata gyatuma a hasken wuta ta na zuwa, tana kore hayaki da wuta daga abin da take ɗauke da shi. Tana maƙale da wani jariri a kafaɗa. Sai na ga ba amfani in ɓata harsashina a kanta, zuguri da gindin bindiga kaɗai ya isa ya gama da ita duk da jaririn. Da na matsa kusa da ita, sai ta saukar da yaron a gabana ta ce, “Ci gaba ka kashe, kashe shi! Wannan ɗan Hindu ne, allahnka yana jin daɗin kashe mutane, don haka ci gaba ka kashe-yaron!” Hannuna ya ɗage cikin iska, na tsaya shiru, duk na gigice. Kashe su ba tare da wuta musaya ba tsakaninmu, ba kuma tare da wata musaya ba tsakaninmu, ba kuma tare da tunanin abin da nake yi ya zamar mini wani abu. Amma ina ganin suna fuskanta ta a hanyan nan, har in ci gaba da cika aikina, abin ya fi ƙarfina. Da ban yi kome ba., sai gyatuman nan ta taho wuri na, ta dubi tsabar idona, ta tambaye ni gagabaɗi “Ɗana, ko kana da ‘ya’ya?” “Mama ba ni da su, amma ’yan’uwana maza suna da su.” (Ban rabu da halin girmana tsofaffi ba, don haka sosai lokacin da su ke wasa cikin laka su na gina dakuna a lokacin damina?”

“I mama, ni kaina na taɓa yin dawaki da laka, da shanu, da gidaje sau da dama.” A hankali, sai hirar ta kwance ɗamarata. Ai, tana da hakima, ta sa muka shiga hira. Ta ci gaba: “Yaya kakan ji idan wani ya zoya rurrushe gidajen nan na laka na wasa?” “Mama nakan ji haushi ƙwarai na amsa cikin kunya.

“To, ɗana. Ka duba ka gani Allah ne ya yi jikin yaron nan da hannunsa don ya bayyana nagarinsa. Idan ka ji haushin wanda ya rushe abin da ka yi da laka cikin wasa, yaya ka ke tsammani Allah zai so dukan waɗannan abubuwa da kuke yi? Allah ba shi da ƙarfi ne da zai bukaci taimakonku ku karkashe arna? Idan Allah ba ya son wani mutum ko abu, ai yana iya kawo ƙarshen sa da kansa.”

Waɗannan kalmomi sun buga tunani da raina kamar da ƙatuwar guduma, sai na yi ihu: “Mama ya isa haka! Daga yau ba zan ƙara ɗaga hannuwan nan gāba da kowa ba cikin sunan addini. Kin sa na gane da irin lalcewata. Zan kawo ƙarshen wannan. Ya mamata, ki yi mini addu’a. Na sani ni ɓatacce ne.”

A can cikin zuciyata na tabbata tana da gaskiya. Ta sa shakka ta kai matuƙa a game da ayyukan da na shigar da kaina. Ci gaba da wannan yaƙi ya yi rauni a cikina. Yanzu kam ba zan iya ci gaba ba. Na karaigaba ɗaya. Na sa sashi na su ja da baya. Mutanena sun ɗauka na haukace ne, su ka fara gunaguni. Su na cewa sai ka ce ba ni bane. Duk da haka dai su ka yi biyayya.

A daren nan na yi ta tuna hanyoyina na aikin ƙarfi da yaji. Na ga gidan wuta kawai ya rage wa mutum kamar ni, domin ni da hannuwana, na kashe abin da yake na Allah. Allah mai Dukka ya halicci dukkan duniya, na hallaka halittarsa mafi daraja. Amma ba ni kaɗai ke da alhakin dukan ayyukana ba. Ba shakka na ba da kai ga malamina na addini. Amma in ba ni ne da alhakin dukan aikin nan na zub da jini ba, to, wanene? Allah ne?

Na sha azabar tunani, na ƙarasa da cewa ba zan ci gaba da irin wannan rayuwa ba. Na daina jin cewa ina gamsar Allah ta wurin kashe arna. Dole in fita. Yin murabus kaɗai zai fi mini amfani. Duk da haka na sani sakamakon ba mai daɗi ba ne. Amma na sani dole in yi haka. Na je wurin kwamanda, na tambaye shi idan zai yiwu in yi murabus daga ƙungiyar yaƙin ‘yancin. Ya cika da mamaki da shakka. “Don me ka ke so ka yi murabus?” haka ya tambaye ni. Ban iya faɗa masa dukan labarin ba. Abin ya zama babban al’amari a gare shi. Ta ko yaya dai, a wanna hali ba zan iya bayyana wa kowa ainihin abin da nake tunani ba. Ba ni kawai na faɗa masa cewa ba ɗaure nake da ƙungiyar ba. Ba na karɓar albashi, ba su kuma bi na bashin kome. Da yardar raina na shiga, yanzu kuma ina so in yi murabus da yardar kaina. Ya dai gane cewa ba amfani ya ci gaba da ƙoƙarin rinjiyata don in tsaya. Ya ce in ba shi a rubuce. Wannan ya ba ni zarafi in tattara tunanina wuri gudda. Na rubuta shafi huɗu don dai in bayyana dalilaina na son yin murabus. Ya karanta wannan a hankali, kuma cikin haƙuri. Ya gaya mini abin da ya yi tunani a kaina ba tare da wata shakka ba. Ya ce hankalina ya gushe mini. Na gode masa saboda nasa ra’ayin a kaina, na ce na yi murna da na zama motsattse. Ta wurin wannan lahanin cikin kwanyata, haske na gaskiya ya iya shiga. A ƙarshe ina komowa cikin hankalina. Kwamanda dai abin ya gagare shi, amma ya ba ni awani aikin, na kuwa karɓa – tattara dukan kayan da ‘yan Hindu suka gudu su ka bari zuwa India. Akwai wasu ‘yan aikin sa kai tae da ni na Askarawan Musulmi matsara, da jagoran addini. Wannan aikin ya komo da ni ga iyalina. Wata rana da na zo gida cin abinci, sai ‘ya’yana Haji Khuda Bakhsh ya ga ina da wani kyakkyawan abin wuya, ya tambaye ni ko ina na same shi. Na bayyana masa na ɗauka daga cikin kayan da aka ƙwace daga gidajen wasu ‘yan Hindu. Sai yayana ya karɓe ya jefa cikin wuta. “Ka ƙasƙantar da kanka duk da mu da ka ɗauki wannan abin wuya,” ya yi mamaki cikin fushi. “Yanzu za ka zuna gida, ba za ka ci gaba da wannan aiki ba, wanda yake haɗe da kwasar ganima! Ka ji Ko?’

Na yi mamaki. Ba wani abu na dabam nake yi ba. Ko malamanmu na addini ba su ɗauki wannan ya zama laifi ba, ko abin kawo ƙasƙanci don mun mori kayan da aka tsere aka bari. Na tuna, Malami ya ɗauki murhu daga gidan wani ɗan Hindu ya ajiye a gidansa. Wannan mutum kuwa sananne ne ga iyalinmu. Lokacin da yana cikin koleji a Deoband da Bulandshahr don samun horarwa a kan shugabancin addinin Musulunci a arewacin India, mahaifina ya ɗauki nauyinsa ta fuskar kuɗi. Har ya yi ƙoƙarin samar masa ƙaton gida inda ‘yan Hindu su ka gudu su ka bari a wani ƙauye kusa da mu. Wata rana na gan shi yana neman a biya shi diyya. Wata rana na gan shi yana neman a biya shi diyya. Ya nuna shi ɗan gudun hijira ne, ya bar takardar neman biyan diyya. Ina gaskiyar wannan faɗin: Na sami wasu ‘yan fashi sun sha ado kamar shugabanni, ya kamata in ceci kaina ko kuwa girmana? Ga yayana nan, ya cika da fushi don kawai na ɗauki ƙyallen ɗaure wuya. Misalin wa zan bi? A nan ma na ruɗe, na rasa na yi ga aiki. Me zan yi da raina?

VI - AN SA NI A KWANA, AN YI NASARA DA NI

Karona da gyatuman nan a daren ƙaddaran nan ya sa na yi wa’adi nan take cewa, ba zan ƙara kashe kowa ba. Ƙudurin cika wannan alkawari ne ya sa na yi murabus daga ƙungiyar yaƙin ‘yancin Kashmir. A lokacin rayuwa a gare ni ta na da ma’ana da kuma manufa. Yanzu kuwa, zaƙuwata ta addini, da kuzarin siyasa duk sun wargaje. A maimakon haka, duk na tsorata da irin rashin imani Na ƙara zama a wani matsayi inda ban san na yi ba, ban san inda zan juya ba.

Maimakon zama fanko, sai na cika da shakku da tsoro. Wani tsoro musamman ya kāsa bari na – shi ne na mutuwada shiga gidan wata. Ban san makomata ba. Mutuwa dai tabbas ce a gare ni. Ina damuwa ko me zai faru in na mutu a lokacin can. Ni, da ban san menene jin tsoro ba tun ina ɗan shekara tara, tun daga nan ban taɓa jin tsoron zuwa wurin aiki mai hatsari ba. Ni wanda na sha zuwa kusa da mutuwa, yanzu an garkameni cikin ƙangin ƙarfe na tsorace-tsorace abin da na san an cancance shi. Na ga kawai na dace da gidan wuta. Shakka ta auko mini, ta jefa ni cikin babbar ruɗewa. Me zai fari in babu Allah? Ba za a hukunta ni ba ke nan a kan yadda nake, da abin da na yi. Daga nan babu dalilin jin tsoron gidan wuta. Na ga mutuwa da hallakar ‘yan adam kewaye da ni. Ba shi yiwuwa a ce akwai' hannun Allah cikin wannan duka. Amma muryar lamirina ta ƙi ta yi shiru. Tana kuka da iko da rinjayarwa, tana cewa, “Ba shakka akwai Allah.” Kasancewar dukan duniya ya tabbatar mini cewa akwai wanda yake tushenta. In kuwa ba haka ba, to, Allah ba zai yi kurkusa da halittarsa ba, da kuma duniya ta zama ba kowa, ba mai sha’awar ta. Amma na sani ba haka abin yake ba' kuma abubuwan halitta babu shakka shaidu ne na ƙwarai.

Ko da na yardacewa akwai Allah, wanda ya halicci duniyan nan da dukan kyawawan abubuwanta, ina mamaki don me ya yarda ake lalatar da abin da shi kansa ya halitta. Na gaskata, na kuma ƙarfafu da malaman addinin nan waɗanda su ke tunanin cewa Allah ya yarda da kisan arna da marasa bangaskiya. Amma ta yaya wannan zai zama haka in shi ne ya halicci duka? Na tabbata da zai fi kyau in ya rinjayi biyayyarsu, maimakon a yi ta kashe su kawai!

Zai yiwu ba ruwan Allah, mutum ne kawai ya ke morar ‘yancin nufin kansa ta hanyar da ba daidai ba. Zai yiwu bai ji daɗin kisan ‘yan adam ba. Duk da haka na yi tunani cewa, Allah ne da hakkin wannan, tun da shi ne ya ba mutum ‘yancin nufin kai tun da fari. Lokacin da na kashe arna, ina ji ai, ina biyayya da umarnin Allah ne. Idan Allah bai ji daɗin haka ba, da ya gwada ikonsa a kan nufina don kada in cika wannan aikin.

A matsayina na Musulmi mai ibada, na gaskata cewa na yi aikina daidai, don na maida na maida martani bisa ga kiran da aka yi a masallaci na a fito a yi Yaƙin Jihadi. Na ba da kai, da ma ma’anar Musulunci shi me “Miƙa wuya.” Don haka ba ni da hakkin dukkan abin da na aikata ba. In kuwa haka ne, to, babu dalilin da zai sa in yi ta damuwa a kan na yi laifi, ko na cancanci shiga gidan wuta. In ban yi laifi ba, to, babu dalilin da zai sa in tuba. Zai yiwu kuma duka na yi kuskure ne. Zai yiwu da na yi aiki da '‘ancin nufina ta yadda da ban aikata abubuwannan da lamarina ya ke kāshe ni ba. Idan lamirina yana kāshe ni, idan kuma akwai Allah, na tabbata ya fi lamiri girma.

Bisa ga yawan tunanina a kan al’amuranan, bisa ga ƙara ruɗewata da fidda zuciya. Hankalina ya na ta kai da komowa da azabar tunani. Ina ji na zama kamar wanda aka yaudara. Babu sauran wani ɗan haske a cikin raina. Amma tunanina yana a shirye a munane don ya iya amsa irin tambayoyin nan. Tunanina yana hana ni barci. Zan kwanta in kāsa barci, a ƙarshe barci yakan zo da shike kwanyata ta gaji, zai yiwu mutum ne ya ƙaga, addini, su da su ke so su sa talakawa su riƙa jin rashin cancantar kansu.

Wahalallen hankalina ya yi tsere da tunaninsa amma ban sami kwanciyar rai ba. Dole akwai amsa. Dole kuwa in sameta. Ban iya samun amsoshin ba. Ban damu da barci ko abinci ba. Na yi kwana goma sha bakwai dare da rana ban ci abinci ba. Halayyata ta ƙara harzuƙa wahalar da ke cikina, da kuma waɗanda ke kewaye da ni duk sun ƙara mini wahala. Na zama mai fitina, da wuya a yi abu tare da ni. Abokina ba su biɗi kamfanina ba. Na soki dukan addini, na kuma raina darajarsa. Gaba ɗaya na ƙi kowace shawara daga shugabannin addinin Musulunci. Mutane sun fara cewa na haukace. Sun ɗauka watakila kashe-kashen mutanen da na yi ne yake damu na. Ban sani ba, ni ne nake ƙin mutanen ko mutane ne su ke ƙi na. Zai yiwu duka biyu ne.

Ya zamana na ware kaina daga iyalina. Na sani na zama baƙo a gidana, ba mai son yin magana da ni cikin iyalina. Ba su san abin da ya ke faruwa ba, ba su iya taimako na. Fidda zuciya haka yakan sa jin haushi. Mahaifiyata ta damu ƙwarai. Ta ce mini, “Ɗana, ka faɗa mini abin da ke damun ka,zan taimake ka.” Amma ba wanda zai iya taimako na. Na damu ƙwarai saboda baƙin ciki da haddasa, kuma ban iya yi kome a kai ba. Na zama kamar ina kulle a wurin da yake ta wurga damuwar tunanina ba ƙarewa, yana kuma ta neman tambayoyi.

Lokaci-lokaci, sai ɗan haske ya ratsa duhun tunanina, har in ga ashe, ba dukan rayuwa take fanko, da kuma rashin ma'’na ba. Akwai Allah. Yadda duniya take biye da ka’idarta ta halitta wannan ma yana magana a kan akwai iko mai mallakar kome. Ga wannan iko ne dukan duniya, da ‘yanadam, da sauran halitta za su ba da lissafi. Mutum ba shi da ‘yancin yin duk abin da ya ga dama ba tare da tunanin sakamakon ba, ko a tura shi cikin makoma waɗannan abubuwa za su jefa shi. Na ƙara ɗaura aniyar neman ikon nan, ko Allah ne don in nemi salama da shi. Ni kaina na fara jin tsoron natsuwar tunanina. Na gane cewa ba zan iya samun natsuwar tunanina ba a inda nake. Ina a ware daga masu ƙauna ta, daga kuma waɗanda nake ƙauna.

A farkon watan Mayu, 1949, sai na zare jiki na bar gida. Ban san inda za ni ba. Muradi ɗaya kaɗai ya ke ci mini rai-in sami samala. Ban ko yi bank-wana da iyalina ba. Ina biɗar salama da gaske, amma ban nufi wajen Kristanci ba. Na sadu da mutane waɗanda na iya ganin salamar da nake nema, duk da haka ba ni duban wajen da suke. Har yanzu ni Musulmi ne, na ƙudurta auna Islama a hankali kafin in yi watsi da shi. Mutum yana iya rabuwa da abubuwa da yawa a rayuwarsa, amma rabuwa da addininsa ba tare da dalilai masu ƙarfi ba ya zamu wauta a gare ni, idan addinin Islama ne, yakan zama da wuya, gama Islama ta ƙunshi kowane abu na rayuwar mutum duka tare da sa mutum ya miƙa wuya ga Allah. Ba ni da wata shakka, ko ƙeƙƙega a game da yarda da tushen bangaskiya mai cewa: “Babu wani allah sai Allah kaɗai.” A gare ni, akwai Allah ɗaya kaɗai, kamar yadda Islama ta ke iƙirari a ɗaukake. Kamar yadda gaskatawan nan take ta ƙwarai, za a ga ba mamaki in mutum ya dubi asalin da addinin ya ɓullo. Larabawa a dā suna da alloli da yawa, su na da gumaka wajen 360 a cikin Ka’aba. Larabawa a Makka su na girmama wani ɗakin ibada saboda wani baƙin ibadar. Wannan tsafi na wasu alloli ne mata da a ke kira Lat, da Manat, da kuma Uzza' tsafi ya kahu da ƙarfi cikin sashin addinin. Waɗannan alloli mata an ɗauke su a su ‘ya’yan Allah ne Allah ne mafi iko duka. Muhammadu ya keɓe Allah a shi ne Allah shi kaɗai, ya watsar da sauran allolin. Rungumar wannan bangaskiya, rungumar gaskiya ta ƙwarai, duk da haka darajar Islama ta ragu a idanuna. Ko zai iya samar mini abin da nake so.

Bisa ga shugabanninmu na addini, Allah ya umarci mabiyansa su shiga Yaƙin Jihadi, wato Yaƙi Mai Tsarki gāba da kafiri. Shiga cikin wannan Jihadin ne ya kawo ni cikin wannan halin ƙaƙanaka-yi. Na bincika da zurfi, na ga cewa Islama ta na koyar da cewa, ina iya yin fatar samun gafara bayan mutuwa idan na yi nagarin ayyuka sa’ad da nake a nan duniya. Amma ni ina son samun gafara yanzu, da salama, da sulhu a cikin rayuwata yanzu. In sai bayan mutuwane, an malara. In gama sauran rayuwata babu tabbas sai fata kurum ta samun gafara bayan na mutu bai isa ga gamsar da ni ba, ko ya kuɓutar da ni daga haƙubar da nake ciki. Bugu da ƙari, ya yi mini wuya in girmama in kuma saurara ga Malamai. Na tuna da kalmomin mahaifina, ya ce: “Ka ji, ɗana, mafiya yawa daga cikin Malamai ba mutanen kirki ba ne. Ka ji faɗarsu, amma kada ka bi gurbinsu. Sun tura salihai ga mutuwa kamar yadda suka kashe Mansur. Lalle ka ba su girma, amma kada ka amince da su. In zai yiwu kuma, ka sa su yi nesa da gidanka.”

Zai yiwu mahifina ya faɗi wannan a lokacin da wata mace, wadda ake shakkar al’amuranta, aka ɗauke ta daga gidan wani mutum wanda ya iya haddace kur’ani cikin Larabci. Saboda gurin addini na Musulmi ya sa ‘ya’yansu, daga shekara goma sha biyu da haihuwa su ke sa su haddace Kur’ani cikin Larabci har su zama abin da ake kira Hafiz Al-Kur’an, wato masu tsoron Kur’ani. Amma a gaskiya wannan Malami zamansa Hafiz Al-Kur’an bai hana shi aikata mugayen abubuwa ba. Sakamakon rayuwar rashin tsarki ke nan ta shugabannin addini da su ka sa mahaifina ya daina zuwa masallaci don yin jam’in sallar da Musulimi su ke yi ranar Juma’a da azabar.

Mansur mai asiri, wanda mahaifina yakan ambata, ya na kuma ganin darajarsa ƙwarai, ya yi rayuwarsa a cikin ƙarni na goma. Su ka yi masa kisan gilla a Bagadaza. Sauran Musulmi masu ra’ayin riƙau, sun ɗauka ya yi sabon ridda. Ya faɗi wasu kalmomi kamar haka, “An Hakk”, wato “Ni gaskiya ne.” Wata irin koyarwa ce ta mutum ya maida kansa abin yi wa sujada. Ya shahara ƙwarai cikin wannan asirancin addini – cikakkiyar haɗewa da Allah. Amma duk mutumin da dangantakarsa da Allah ba ta zama a fanyace ba, Musulmi ‘yan ra’ayin riƙau ba za su yarda da shi ba. Mahaifina, da ya ke ganin kansa na kusa da Allah a asirce, zai yiwu ba zai ga wuyar wannan ba. A gare shi, kalmomin ayar Farisa a gaskiya tana bayyana fahintarsa a game da dangantakar da ke a tsakanin Allah da mutum:

Mutanen Allah ba za su taɓa

Zama Allah kansa ba,

Amma kuma ba za a taɓa

Raba su daga Allah ba.

In na tuna kalmomi da ra’ayoyin mahaifina, sai in ji kamar ni ma in zama asirtacce na kusa da Allah. Zai yiwu ta wannan hanya zan iya samun salamar da nake nema. Kamar yadda na ambata tun da fari, a cikin duniyar Musulmi ta ƙarni na takwas ko na tara, mutane masu ibada masu biɗar salamar rayuwa mai cike da niyya ana kiran su sufi. Sun kwantata sufi irin na Kirista waɗanda sun kutsa zuwa cikin Gabas ta tsakiya. Ga ‘yan Sufi, irin biyayyar da Musulunci ya ke bukata ga dokoki na waje na hallayyar ɗan adam ba su ne abu na fari ba. Abu na farko shi ne girmama Allah ne kauna tun daga cikin zuciyar mutum. Sun gaskata goguwa cikin ma’amalar kai tsaye da Allah. Ba shakka, ina tsammani abin da nake muradi ke nan fiye da kowane abu.

Ya zamar mini tabbatacce ina bukatar taimako. Kadaitaccen bincikena bai kai ni ko ina ba. A sakamakon haka, na yi kwanaki babu barci a masujadai iri iri, na yi ta bin “tsarkakan mutane” masu yawa. Bisa ga bin “Tsarkaka” ko “adalai”, bisa ga samun karaya da nake yi. Zai yiwu wannan ya haɗu da irin horarwar da na samu ne ta aikin soja wadda ta sa na zama mai shakkar gaskiya addinina. Duk lokacin da na lura da rayukan mutanen nan a hankali, sai in ga cea, ko da shike sun yi iƙirarin su masu binciken gaskiyar uluhiya ne, a kullum sukan nuna da baƙin cikin yadda aka bauɗar da su. Na same su sun shiga sosai cikin mugayen ayyukan da ni da kaina ina jin kunyar ba da labarinsu. Idan na lura da irin salon rayuwarsu ta sufi, wato masu jagorancin al’amuran ruhaniya, sai na ƙara jin zafi. Ga talakawa leburorinsu su na fama da yunwa, sun shiga irin ayyukan ɓata lokaci kawai na masha’a, kamar sayo karnuka daga Russia don jan iri kawai. Waɗannan da su ke ciki a gonakin shugabannin nan ba su ko iya ciyar da ‘ya’yansu, amma su na darajanta karnukansu ta wurinn ciyar da su da tsokokin nama sau biyu a rana. Wannan sukukucewar ta sa tunanina ya zube. Duk da haka, ban karai ba. Na tafi na haɗa kai da wata ƙungiyar daliɓai Musulmi waɗanda su ka shigar da ƙungiyar daliɓai Musulmi waɗanda su ka shigar da kansu cikin holewa da ƙwaya, da muziƙa da rawa domin hanƙalinsu birkice, tunaninsu da lamirinsu duk ya zama a kan Allah ne, duk da haka, wannan ya zama aikin banza, ban sami kome ba, sai ma na ƙara ruɗewa. Bincikena na neman salama ya gama cikin cikakkiyar rashin nasara. Cikin halin fidda zuciyata, sai na tuno da kalmomin farko na Kur’ani:

Ka bi da mu a kan hanya madaidaiciya

Hanyar waɗannan da ka yi musu rahama

Ba a kan waɗannan da fushinka ya sauko

A kansu ba

Ko waɗanda su ka ɓata.

Galibi an fahimta cewa “madaidaiciyar hanya” ana nufin bangaskiyar Musulmi. Wannan kuma sunan wata matsattsiyar gaba ce, wadda Musulmi sun gaskata cewa tana nan daga saman gidan wuta. Musulmin kirki zai iya ƙetarewa lafiya, amma sauran za su fāda cikin harshen wuta.

Da shike na fidda rai ga amince wa dokokin da mutum ya yi, sai ina ji dole dai ko ta yaya akwai hanyar kuɓuta daga nawa gidan wutar, sai na roƙi Allah ya nuna mini hanyar wannan rai. Na ci gaba da tashi tun da sassafe, ina roƙon Allah da gaske domin ya yi mini jagora. Na yi wannan daga zurfin zuciyata, kukana ya kai sama na neman taimakon ruhaniya.

“Ya Ubangiji Mai Iko Dukka! Ba shi yiwuwa a musunci kasancewarka. Kowace hanyar jinin jikina da harhaɗuwarsa su na bayyana ɗaukakarka. Dukan halitta ta maida hankali ne ga kasancewaka. Na san da kasancewarka. Raina ya tabbatar da kasancewarka. Na sani kuma kai ka halice ni tare da sauran mutanen duka. Ta wurin kwaiƙwayon banzayen shugabannin addini, da bin mugayen shawarwarinsu, na matsanta wa waɗanda ka halitta. Mugayen ayyukana sun tabbatar mini cewa gidan wuta ne rabona gama kai ya Ubangijina, za ka hukuta masu zunubi. Ban gaskata addinai da ka’idodi a cikin wannan duniya ba kuma. Ya Ubangijina, ka nuna mini madaidaiciyar hanya. Ba na so in shiga gidan wuta. Ka nuna mini madaidaiciyar hanya, yadda zan iya ganin ka, Ina shan wuya, Ya Ubangijidana. Ina marmarin salamar zuciya amma ban iya samun ta ba. Ka taimake ni, ya Ubangiji. La’akari da zunubina ya keta ni kamar da mashi. Ka yi mini jinƙai ya Allah, ka yi mini jinƙai. Amin “

Ban iya tunawa da ranar ba, amma wajen ƙarfe uku ne ko huɗu na asuba, lokacin da nake salla kamar yadda na saba yi. Ina kuka mai zafi, cike da baƙin ciki. Ina a tashar jirgin ƙasa, cikin ɗakin jira sa’ad da na yi wannan addu’a ta sama. Ba labari, sai na ji an dafa ni a kafaɗa, dafawa da hannun ƙauna a ke ce,

“Alherina ya ishe ka!”

Aka maimaita wannan magana har sau uku, sai na ji kamar wutar lantarki ta ratsa jikina. Nan da nan nauyin zuciyar da nake fama da shi ya tafi, ya rabu da ni. Sai na ji wani sabon ƙarfi, cike da murna, kuma da labari, hankalin tunanina ya gushe, zan dai ce na sami saduwa da Allah. Babu abin da zai iya raba mu. Ina jin gafara da salhu sun tabbata. Na fara maimaita kalmomin nan daga Allah kai tsaye. Ban taɓa samun irin wannan murna da farin ciki mai yawa haka ba. Babu shakka “basamiya” ce.

Wani tsoho ma’aikaci a tashar yana shara kusa da benccin da nake kwance a kai, lokacin da ya lura da irin murnar da nake yi, sai ya tsaya ya tambaye ni, ko ni Kirista ne. Sai na kaɗa kai cewa babu, sai ya yi mamaki ya ce, “To, don me ka ke ta cewa, “Alherina ya ishe ka?” Sai na amsa cewa: “Ban san abin da ya sa nake ta faɗar waɗannan kalmomin ba. Na dai san cewa, wani ya faɗa mini su, ya kuma nuna mini wani allo inda aka rubuta dukkan mugayen ayyukan da na taɓa aikatawa. Amma gaba ɗaya wani ya share su da hannunsa, ya share allonan sarai. Tun daga lokacin nan, sai na ji na zama kamar sabon mutum. Dukan nauyin da ke kan ruhuna an ɗauke mini duka. Zuciyata tana so ta raira waƙa da ƙarfi.”

Sai tsohon nan ya ce mini, “Ɗana, dole ka gode wa Allah. Ubangiji Yesu Almasihu ne ya zo wurinka. Shi ne ya faɗa wa manzo Bulus Kalmomin nan. Ban iyatuna ainihin wurin ba a cikin Linjila Mai Tsarki. Yanzu Ubangiji Yesu ya na so ka zama bawansa.”

“Ta yaya? Ta yaya zan iya zama bawansa?”

“Bari a yi maka batisma cikin suna Ubangiji Yesu Almasihu, ka fara binsa nan take.”

“Ka faɗa mini zahiri abin da zan yi. Na kai wurin da dole in juyo a cikin rayuwata.”

“Ɗana, ban san kome ba. Na dai san cewa idan daganan ka tafi Tandlianwala, sa’an nan zuwa Isanagri, akwai wani fasto a can da ake kira Rev. Inayat Rumal Shah. Zai taimake ka.”

Sai tsohon nan ya ajiye tsintsiyarsa, ya zo kurkusa da ni, idanunsa cike da hawaye. Na rungume shi da ƙarfi, dukanmu mu ka yi ta kuka da ƙarfi, hankali duka ya tashi. Bayan ɗan lokaci, ina tunani, ko shi ne uban yarinyar da ni da abokan aikina mu ka so mu kashe. Tunanin nan ya yi mini nauyi ƙwarai. Abin ya motsa ni ƙwarai, yadda mutumin nan da yake cikin rainannu, da su ke can kasa ga dukan sahun mutane, mai shara kurum, shi ne ya ke nu na mini matakin da zan ɗauka nan gaba Ba wuya a iya ganin dalilin da ya sa da yawa daga cikin irin wannan sahun sahun suka karɓi Bisharar Yesu Almasihu. A cikin Almasihu su ke samun asalinsu na gaskiya. Gane cewa an yi su cikin kamanin Allah, su ‘ya’yansa ne, sun sami sabon asali mai daraja. Na yi murnar kasancewa ɗaya daga cikin cu.

Sai kalmomin nan “Alherina ya ishe ka” suka ƙara amo a cikin kunnuwana, zuciyata ta cika da murna, sai na shiga jirgi zuwa Isanagri. A ƙarshe dai baƙin ciki ya ƙara. Yanzu salama ce ta ke mulki. Ina misalin jin daɗin danake ya! Abin ya kusa ya shere ni. Abin ya yi wa tunanina yawa. Ubangiji Yesu Almasihu wanda ya ceci ni daga mutuwa ta jiki, ya kula da ni cikin ciwon da na yi, ya nuna mini hadayarsa, ya bayyana dukan isasshen alherinsa yanzu ya yi nasara da zuciyata. Shi ya ke nasara. Na daina ragaita cikiin duniya babu manufa, ina neman manufa dama’ana wadda ta jefa ni cikin bauɗewa. Yanzu na sami ma’ana da manufa na gaskiya domin rayuwata. Na sami shi wanda ya ke ba mu salamarsa, ya ke kuma sulhunta mu da kansa. Shi nawane, ni kuma nasa ne.

VII - AKIN HAJJI

Ta hanyar banmamki an ‘yantad da raina da halin fidda zuciya da taɓewa da suka duhuntar da raina. Zuciyata cike fal da murna sa’ad da na sauka daga jirgi a Isanagri wani ƙauyen gundumar Faisalabada, na kuwa sadu da Rev. Inayal Ruma! Shah.Ya gaishe ni 'warai, ya kuma nu na mini karamci. Bayan mun ci abinci, sai ya yi murmushi, ya tambaye ni cewa, “Me ya sa kake so ka zama Kiristi?” Ga shi dai bai san tushen ba, ko zurfin biɗar salama da na yi wadda na sami biyan bukata ta hanyar mu’ujiza, kai kamar ba zai yarda ba. Amma ba ni ne nake zaɓen Almasihu ko Kristanci ba. Ba maganar ko ina so in zama Kirista ba ce. Yesu Almasihu ya zaɓe ni. Ba na so in ɓata wa Revered rai, sai na amsa a sawwaƙe “Wani ne ya gaya mini, wajen ƙarfe uku ko huɗu na safe a yau, Yesu Almasihu da kansa ya sadu da ni ya ce mini, “Alherina ya isha ka.” Akwai hoton Yesu Almasihu gicciyayye a bango. Sai Rev. Shah ya kama hannuna, ya kuma nuna hoton da hannu guda. Wannan Yesu ne ya yi magana da ni? Na ji Rev. Shah ya ce: “Mutane sun yi wa Almasihu fashi har da tufafinsa. Su ka tuɓe shi, suka bulale shi, su ka kuma ƙusance shi a kan gicciye! Me zai iya ba ka? Abin da tambayan nan ta ƙunsa zai tada hankalina idan da a ce ina cikin halin tunani ne. Ba na son kome sai salamarsa kaɗai. Ceto nake nema, na kuwa samu. Idan da ni mai fahariya ne, da na husata. Da na yi tunani cewa, da ya kamata an yi mini gaggarumar maraba. Amma al’amarin duka sabo ne mai sherewa kuma a gare ni. Don haka waɗannan abubuwan tada hankali tunani ba su sami wuri a cikin zuciyata ba, wadda take da farin cik.

A lokacin ban sani ba, amma ba da daɗaewa ba sai na gane cewa waɗanda su ke nema su san abu game da Kristanci galibin lokaci akan ɗauke su da shāyi. Ana gani da yawa sukan so su zama Kirista saboda wasu amfani da za su samu waɗanda Mishaneri sukan ba da. Kaya, ko tufafi, abinci, ko illimi, da gida ko mahalli. Ba abin mamaki ba ne ashe, shi ya sa Kirista mafiya yawa daga ‘yan Hindu sun fito ne daga sahu na ƙasa, wato ƙasƙantattu, masu shara, matalautan matsiyata. Amma kada mutum ya ɗauka cewa dukan waɗannan da su ka tuba sun zo neman kayan duniya ne. Kamar ni, haka kuma da yawa sun sami Kristanci ya biya bukatarsu mai zurfi. A gare su, kalmomin nan gaskiya na ce:

Ban kawo kome ba a hannuna,

Sai ga Gicciyenka nake jingina,

Ka wanke ni, ya Mai Ceto,

Ko kuwa in mut.

Abin da na amsa kaɗai ke nan: “Kada a ce Almasihu ba mai taimako ba ne, kuma ba shi iya da ni kome. Ya riga ya bani kowane abu. Ya maida ne sabon mutum, ya kuma ba ni kwanciyar rai.”

Sai ya ce, “Ya yi kyau, abin da kaɗai zan iya yi maka shi ne, in aike ka zuwa wurin wani abokina Mishaneri a Gojra. Zai iya taimakon ka.”

Ba za a iya karɓa ta nan da nan ba, n ma ban sa zuciya ba. Akwai doguwar hanya a gaba na. Bayan ‘yan mintoci, sai Rev. Shah ya ba ni wasiƙa, da wasu kuɗi don in iya shiga saa zuwa Gojra. Wannan abin karya zuciya ne a farkon aikin hajjina cikin wannan sha’ani, duk da haka ban karai ba. Sabuwar bangaskiyata ita ce mafi girma, ba kuwa wanda ya isa ya ƙwace mini ita.

Na isa Gojra da marace, na kuma sadu da Rev. R.W.F. Wootton. Daga yanzu da na riga na san cewa hanyar fa ba mai sauƙi ba ce. Rev. Wootton ya gaya mini cewa, za su jarraba ni don su gani ko lalle da gaske nake marmarin in zama Kirista, daga nan su yi shawarar yi mini baftisma. Na yarda da farin ciki.

Baftisma muhimmin mataki ne. Ba abu ne da yakan auko wa mutum kamar mungāda ba ne. Ta na nufin miƙa kai da sani ga Almasihu, da kuma Bisharar mulkin Allah. Dukan sabon tuba. A cikin ƙasar da babu tarihin Kirista, tuba babu tantama ta ƙunshi tumɓukewa, da karya wasu al’adu a kuma ɗauka wasu sababbin al’adu. Ga wasu kuwa za su sha azaba ne. Bai kamata a ɗauki baftisma da sauƙi ba. Zama Kirista, ya rasa “Zarafin zama cikin jihar Musulmi ke nan a matsayin Musulmi.” A wasu ƙasashen Musulmi, tubabbu zuwa Kristanci ba su samun kāriyar doka. Ba su da ikon ɗaukaka ƙara zuwa kotun shari’a don a yi musu shari’ar adalci, in an yi musu ɓarnar kadrorinsu, ko an zalunci wani cikin iyalinsu. Abu mai sauƙi ne su rasa rayukansu Amma na yi murna da za a jarraba ni. Cikin yin haka, ni da su duka za mu tabbatar da biyayyata.

Rev. Wootton ya sa aka sa ni a ɗakin baƙi. Daƙin dai dai wata tsohuwar kujerar rangaji, da wani tsohon gado da zane biyu. Idan na ja zannuwan sama, sai zafi ya dame ni, idan na ture su gefe, sai sauro su yi ta shagali a kaina! Babu wani cikakken shiri a game da abinci. Idan an ba ni, in ci, in ba a tuna da ni ba, sai in yi ta zama da yunwa. Akwai lokacin ba wanda ya tuna dani a game da abinci har kwana uku! Kwana biyu na fari, na jure, na kashe lokaci mai yawa ina addu’a. Amma kwana na uku, ba ni da ƙarfin da zan hau gadona. Rev. Wootton ya yi tafiya, da ya dawo, sai ya zo ɗakina mai duhu. Ya tambaya: “Ɗan’uwa, ba ka da lafiya?”

Na amsa da kyar, “Babu, ba na ciwo.”

Amma me ya sa ba ka da ƙarfi haka? Ka sami abinci kuwa?”

Sai na ka:da kai, “Tun yaushe?” Babu sauran ƙarfi a jikina, na dai yi ƙoƙari in hana hawaye gangarowa daga idanuna amma na kāsa. Sai na yi muni da yatsotsina cewa, kwana uku ban ci kome ba. Ya damu ƙwarai da jin wannan, ya ta’azantad da ni.

Ya ce, “Mu waɗanne irin mutane ne? Wace irin mugunta ce wannan! Babu ko mutum ɗaya da ya tuna da kai, ko ya yi tambaya a game da kai da abincika da ba ni nan?”

“Kada ka damu, ni na ɗauka wannan duk cikin jarrabawar ne, don haka ban fada wa kowa ba. Ban ma ko fita daga ɗakin nan ba, domin mutane su na raɗeraɗin abubuwa marasa kyau a game da ni. Wani ya ce ina so in zama Kirista don kawai in sami yarinya da zan aura. Wani kuma ya ce ina neman aikin lebura ne wurin mishan. Wani kuwa cewa ya yi ina nema kuɗi ne kawai. Na ji waɗannan duka, amma ban ce kome ba.”

Mutane a gidan mishan ba su nuna mini kirki ba tun da farkon zuwana. A ganinsu ni mai kutsa kai ne kurum. A wurinsu kyakkyawan zarafi ne su riƙa aiki a gidan mishaneri. Ba su da zarafi domi na.

Sai na fara jin tausayin su a maimakon jin haushin waɗannan Kirista. Zai yiwu sun fi kowa baƙin ciki. Zama a gidan mishan, ya yanke hulɗarsu daga sauran mutanensu. Su na kishain juna don su sami karɓuwa da tagonashi ga mishaneri, wannan ya yi ta zuga riya maimakon gaskiya.Maimakon su marabci masu zuwa yin tambayoyi, su da ke neman maƙasudi mafi kyau da ma’anar rayuwa mai zurfi, sai waɗannan su riƙa raina su, sun mai da su kamar kishiyoyinsu. Ba su damu da sadakar da ran masu tambayan nan ba, amma sai neman su gamshi mishaneri fiye da gamsar Ubangiji wanda suka ce sun miƙa rayukansu a gare shi. Na faɗa hannun mazalunta.

Rev. Wootton dai ya nuna mini kirki ƙwarai da gaske. Ya kawo ni gidansa, ya umarci kukunsa ya riƙa shirya abinci domina ko yana nan, ko ba ya nan. Ban ƙara zama babu abinci ba kuma, amma yanayin mazauna gidan mishan ɗin bai sāke ba. Halayensu ba abin da za a jure da su ba ne. Saboda haka, sai na rinjayi Rev. Wootton a shirya yadda zan zauna a masaukin baƙi na mishan.

A wannan lokaci, ban faɗa wa Rev. Wootton labarin kaina ba tukuna. Abin da ya faru a bya ba shi ne muhimmi ba. Ba na son wani ya sani a game da tushena na masu arziki, ko kuma dā ni wani jami’i ne na Sojan Sama in sa ya daratta ni da kyau, a’a. Lokacin da ya ba ni shawara in zama mai yi musu gadi da dare, na yarda da murna, don ba na so in zamar wa kowa nawaya. Akan rufe makaranta da gidan kwanan ‘yan makaranta a Gojira a watan Yuni. A sakamakon haka, aka danƙa shiri na a hannun wani Kirista a nan gidan mishan wanda yake kamar wani salihin mutum. Sunansa Sewak Boota Masih. Na yi sa’a ƙwarai da aiki ya haɗa ni irin wannan mutum. Shi masinja ne a makarantar ‘yan mata da kuma gidan kwanan ‘yan makaranta. Albashinasa ƙalilan ne, duk da haka yana taimakon mutane kama ta.

Boota Masih ya iya karatun Gurmukhi, irin yaren Sikhs. Halinabukarsa ya afa tushen girmana na ruhaniya. Daga gare shi ne na koyi ainihin halin bangaskiyar Kirista, da kuma abin da ainihin aikatawar rayuwar Kirista ta ƙunsa. Addu’a ta yi babban aiki a ɓangaren rayuwarsa. Ana iya cewa, dukan rayuwarsa ta addu’a ce. Mun riƙa game dare farai muna addu’a. muna assu’a. Na tuna kasancewa tare da shi a wani dare kafin in tafi aiki. Mun nutsa da zurfi cikin addu’a har lokaci ya wuce ba mu lura ba. Amma abin mamaki, kashegari sai mutane su ka ce sun gan ni da dare har sau huɗu. Su na mamakin irin ƙoƙarina cikin aikinna. Daga nan na gane abin mamakin da ya faru. Lokacin da muke addu’a, Yesu da kansa ya yi aikina! Zuciyata ta cika da murna cikin Mai Ceton wanda yake nuna kansa Zahiri a gare ni.

A ƙarshen Satumba, 1949, sai aka gaya mini, za a yi mini baftisma ran 2 ga Oktoba, lokacin babban taro na fari na Gojra. Aka yi mini wasu tambayoyi don a san irin zurfin ganewata a game da matakin da nake ɗauka. Waninsu ya damu saboda yawan takardun kirista da na karanta. Naji daɗin faɗa musu cewa, na karanta kusan dukan littattafan Urdu na Rev. Wootton da kuma wasu nasa da dama da suke na turanci. A daren 30 ga Satumba, sa’ad da nake addu’a, sai Ubangiji ya tada lamirina, ya nuna mini cewa, ban yi wa Rev. Wootton cikakken aminci ba. Da shike ban ba shi labarin abubuwan da su ka faru da ni a baya ba, wannan ya zama kamar akwai abin da nake ɓoyewa, wannan rashin ƙarfin hali ne, kuma ruɗi ne, wannan kuma zai hana girma na ruhaniya da ci gaba. Ya yi mini wuya in sake bayan wannan bayanin. Sai na tashi da tsakar dare na tafi gidan Rev. Wootton. Dole in sauke wannan kayan in faɗa masa dukan labarina na baya. Ya ji daɗin yadda na faɗa masa gaskiya da amincina muka sami zarafin yin addu’a tare.

Aka yi mini baftisma ran 2 ga Oktoba. Na yi murna ƙwarai da gaske da na sami baftisma. Ina bin sawun Ubangijinmu. Yanzu na zamaɗaya daga cikin ‘yan’uwa Kirista da ake gani. Almamar na zama mabarcin kamalin abokina, don in nuna gamsuwata a game da abin da abutakan nan take a gare ni, Sai na sa wa kaina sunan Ghulam, wato “bawa” ya zama sunan na baftisma, na ƙara da Masih wato “Masiha” ko “Almasihu,” don ya bayyana sabon aikina – bawan Yesu Almasihu.

A mako biyu na gaba, na zama cikin farin cikin ƙwarai. Jin na zama na Yesu Almasihu, da kuma zama cikin zumuncin Kirista ya ɗaga sosai zuwa wani mataki. Ubangijina ya zama zahiri a gare ni. Ƙudurina na in bauta masa muddin raina sai ƙaruwa ya ke yi da ƙarfi kullayaumi. Da gaske ina jin tagomashin Allaha kaina, na kuma san yadda yake, ina jin Mahalicci yana ƙaunata, na kuma ji ƙaunan nan tana motsawa a ciki na, duk da rashin cancantata. Duk da haka, nan da nan na koyi abin da ake nufi da bi ta cikin tsarkakewar wuta. Nan da nan al’amurana da ake gani daga waje suka sāke gaba ɗaya. Haka ya faru a ranar da gidan Mishan ya zama kamar ba kowa ciki. Babu Rev. Wootton ko Mr. Charan Dass, shugaban gidan kwanan ɗalbai maza. Rev. B.M. Augustine wanda ya yi mini baftisma shi ma ba ya nan. Daga baya na ji ashe duka sun je wurin wani taro ne a Lahore. Ni kaɗai na fuskanci wani kawuna da yayana da suka zo wurina a husace a ran nan.

A yawandin ƙasashen Gabas, kalman nan iyali ta ƙunshi ba mama da baba, ko ƙanne da yayye maza da mata kaɗai ba, amma ta haɗa da dukan ‘yan’uwa na wajen uwa da na wajen uba. Dukansu hakkinsu yana a kan mutum. Dangantaka mai kyau da su muhimmin abu ne don daidaita makomar mutum. Ba zan ki kula da su ba tare da samun hukunci ba. Kusan ba zai yiwu in nuna ‘yancina daga gare su ba. Su na da arziki, da iko, da rinjayarwa. Kawuna ya bani zaɓi biyu.

Na fari, in tafi tare da su nan take, ba tare da wani ya sani ba. Na biyu, barazana, idan na ƙi tafiya tare da su, za su shiga gari su yi shelar tubata zuwa Kristanci kowa ya ji. Wannan zai tunzura mutane yadda ni da dukan Kirista a Gojra za a yi mana dukan tsiya. Zaman lafiyar sababbin iyalina na Kirista ya na cikin hatsari idan ban yi yadda su kawuna su ka ce ba. Ba na so a yi wa ‘yan’uwana Kirista ɓarna. Ko da shike na damu ƙwari, babu kuma tabas a kan yadda ya kamata in yi da wannan matsala a cikin farkon aikin hajjina na Kirista, tuna da wanda na ba da raina gare shi. Wa’adi ne ga Ubangijina cewa zan yi masa biyayya shi kaɗai. Nufinsa ne jagoran rayuwata. Saboda haka, sai na ce wa kawuna, “Zan tambayi Maigidana.”

Sai na kulle daƙi, na roƙi Ubangiji ko me ya kamata in yi. Ba a bar ni da shakka ba. Ya gaya mini “Har yanzu akwai sauran shingaye masu ƙaya da yawa da za ka yi ta fama da su sa’ad da kake bi na. Ka tafi tare da su, gama a gida ne za ka fara aikin Urushalima, sa’an nan Yahudiya, sai Samariya, daga nan har iyakar duniya.” Abin mamaki, an ba ni umarni daidai da na almajiran Almasihu a cikin Ayyukan Manzanni.

Na komo wurin dangina na ce na shirya zan tafi tare da su. Ban ji tsoron miƙa kaina gare su ba, gama na sani ko da ikon wa nake yi, na san ko hannuwan wa su ke tallafe da ni su na riƙe da ni. Don haka, sai na bi su zuwa Lyallpur wadda ake kira Faisalabad yanzu.

VIII - TSIRA TA MU’UJIZA

Tubata ta ba ni kwaciyar da ma’ana da kuma manufar rayuwata. Ai, canjin rayuwata ba shi kwatantuwa da matsayin da nake ciki a dā sa’ada da nake tare da iyalina! Abin baƙin ciki, duk sākewata ba ta da ma’ana a gare su. Abin da su ka fi so shi ne, in watsar da Kristaci in komo cikin Musulunci, in zama “Musulmin kirki.” Tubata ya jawo musu raini bisa ga ganinsu. Mutane masu hali kamar su, ba su jurewa da Kirista a cikin iyalinsu: Sai matalauta, matsiyata su ke tuba su zama Kirista, sun kuma sani, in zan yi ta cuɗanya da irin matalautan na. Wannan wulakanci ne da ba za a iya jurewa da shi ba. Ya zama na kuyatar da iyali ke nan. Na tuna watadaga cikin ‘yan’yan ɗan’uwana mata ta taɓa ce mini samarin da suke neman ta da aure duk sun ƙi ta saboda ni na zama Kirista. Abin da na zama ya kawo wa iyalina wahalar komabaya. Abin da ke gabansu shi ne, in gane cewa na yi kuskure.

A gare su, Musulunci shi ne ɗaukakakke addini duka. Ta yaya zanmusaya shi da Kristanci? Akwai Allah na gaskiya guda ɗaya kaɗai da Muhammadu Manzonsa, abin da ya ke ta kaɗewa cikin kunnuwan kowane ɗan Musulmi ke nan tun yana ɗan yaro. Amma ga ni ina hakikanta cewa Yesu Almasihu ba annabi kawai bane, amma Shi Ɗan Allah ne. Ai wannan sābo ne ga iyalina, don sun dāge cewa, Allah bai haifa ba, ba a kuwa haife Shi ba. Da shike Musulmi sun ɗauka maganar haihuwa ta jiki ake magana, wannan furci ya ƙunshi matuƙar ɓatanci, duk da haka, magana a zaurance, ko aron ma’ana ba baƙon abu ba ne cikin hadishin Islama. Ɗaya daga cikin abokan Muhammadu mai suna Abu Harera, “Uban Kuanwoyi,” an yi masa wannan laƙabi domin shi mai son waɗannan dabbobi ne. Wani kawun Muhammadu, ana kiran sa Abu Djihal, “Uban Jahilci,” saboda bai yarda Muhammadu Annabi ne ba. Ta haka, “Ubanci” an more shi ne domin a iya bayyana manufa wadda gaba ɗayanta ta kawu daga dangantaka ta jiki. Haka yake kuma a game da “Diyanci” an Almasihu.

Wani lokaci, in mutane ba su fahimci abu ba, sai su watsar da shi gaba ɗaya babu amfani a gare su, domin ya zama babar ƙalubalan da ta fi ƙarfinsu, Idan da Musulmi za su Yesu Shi Ɗan Allah ne, da muhimmancin Muhammadu a matsayin annabin Allah da bayanin Allah a cikin Kur’ani, za su ɗauki matsayi na biyu ga. Na Ɗaya wanda yake Ɗan Allah – Shi wanda ya bada cikakken baynain Allah ga ɗan Adam.

Musulmi sun gaskata cewa, ayyuka masu kyau za su ba su gafararar zunubai, murna a rai bayan mutuwa. Amma na ga bukatar gafara domin zunubaina yanzu, domin in iya ba da raina ga Allah nan take, in kuma bar shi ya zaɓar mini abin da zan yi nan gaba.

A wurin iyalina, ni arne ne a yanzu, a haka kuma su ke riƙe ni. Da na komo gida, sun tilasta mini cin abinci a titi. Wannan abin da iyalina su ka yi mini, ya ba ni zarafin shaida wa jama’a a sarari a game da Ubangijina.

Babu abin da ba su yi ba domin su maido ni cikin Musulunci. Kawuna ya kai ni kauyansa a cikin Gundumar Sheikhupura. Sun nemi malaman addini, aka kawo su gidan domin su yi nazari tare da ni. Ba da jimawa ba, sai wani sabon malami ya saki, ya yanke hukuncinsa na kafirta ni, ya tafi rai abace.

Mako shida muna ta taruwa da malamai iri-iri, duk a banza. Daga nan sai na nemi sāduwa da Sayyed Ata Ullah Shah Bakhari (wai shi daga zuriyar Annabi Muhammadu ne) ya kawo ziyara a Sheikupura a wannan lokacin. Da lokaci ya yi aka yi mini iso, na shiga wurinsa.

Maimakon mutumin nan ya tattauna da ni don ya sa in musunci Kristanci, a’a, sai ya riƙa yi mini dariyar rainako, ya na cewa, “Wato sai ka zama Kirista, ko?”

Na amsa masa cewa, “I haka ne.” Sai kome ya yi tsit. Muryata ta nuna raina ya ɓaci, amma cikin bangirma na ce masa, “Ci gaba da magana.”

Shah ba shi da ta cewa, sai ya ce, “Me kuma zan faɗa?” Na amsa masa cewa, “Kana iya bada ‘yar shawara da bishewa in ya yiwu, na amsa ina marmarin in ji abin da zai faɗa ga mutumin da yake shirin fasar da tubarsa idan har an ba shi ƙwararan hujjojin da su ka isa.

Na san abin da ya ke tunani. Yana danganta tubata da sha’awar auren yarinya Kirista. Ban iya ci gaba da jurewa ba, na nemi iznin yin magana: “Ya Maigirma Shah, na zo in saurare ka domin iyalina sun sa zuciya ƙwarai gare ka don bi da ni zuwa ‘Hanyar Gaskiya’, amma ban sa zuciyar jin irin wannan gaggautsar magana daga gare ka ba. Me ya fi, zan so in ce jima’i da addini abu biyu ne mabambanta, duk wanda kuwa ya karɓi ko ya ƙi addini saboda ya sami jima’i, to, ya zama wawa. Ina so in nuna cewa, kasancewa Musulmi, ina da ‘yancin auren mata huɗu – har fi in ina da hali! A lahira ma ina begen samun mata saba’in da biyu a aljanna. Amma addini da bangaskiya duk sun wuce abubuwan duniya da ake damuwa da su. Ba za a daidaita su da duniya da ake damuwa da su. Ba za a daidaita su da jima’i ba. Ka zarge ni da cewa na yarda batun jima’i da aure su zama tushen bangaskiyata duk abubuwa nan zan fi samun su idan na koma zama Musulmi. Batunka ba shi da tushe.”

Maganta ta sa Shah ya husata, ya ce, “Ka yi shiru, marar ɗa’a mai halkin dabba!”

Cikin tawali’u, na ce, “Ya maigirma Shah, ai abin ba na fushi ba ne, bari mu duba tare.”

Sai ya yi tsawa ya ce, “Ku jefar da shi can ƙasa!” Sai hankalin yayana ya tashi, ya ce, “Ban yarda ku sa masa ko tsaya ba. Idan batun ne, ai, da iyali sun gama da shi tuni.”

Bayan wannan ƙoƙarin da bai yi nasara ba, sai kawuna da yayana su ka fara gane cewa, ba abu mai sauƙi zai sa in watsar da sabuwar bangaskiyata ba. Sai su ka aika da ni zuwa Lahore. Zai yiwu akwai hannun wani dangin kawuna mai suna Hussain Ali. Sai ya lura yadda na riƙa ziyartar wani fasto da dare lokacin da nake tare da kawuna mukan yi addu’a, sunan faston Kyaftin Isaac na ƙungiyar da ake kira Salvation Army (Wato Rundunar Ceto). Ba za su yarda wannan ya ci gaba ba.

Lokacin da nake a Lahore iyalina ba su tone ni don sauran dangi su san na bar Musulunci ba. A wannan lokaci, na haɗa sadarwa da Rev. Wootton ta wurin wasiƙu, wata rana wani mishaneri mai suna Douglas ya gane inda nake. Ya yi ta nema na da sunana na Kirista, Ghulam Masih, to, ba wanda ya san ni da wannan sunan. Dana gan shi a wurin ba za’ar, sai na matso kusa da shi na ce, “Nine Ghulam Masih”. Ya tambayi ko yaya nake, sai ya tafi. Labarin sāduwar nan ta mu ta kai kunnen yayana. Da shi da abokinsa su ka ga lokaci ya yi da za su ɗauki tsauran matakai. Dole su ga bayan wannan abin kunya. Lahore ta fi zama daidai saboda Kogin Ravi yana malalowa daga wannan yanki. Wannan kogi ya yi suna wajen “kwashe mutane ya halakar.” Ya sha tafiya haka shekara da shekaru, amma barnamafi duka ta faru cikin 1947 lokacin da ɗaruruwan gawawwakin Musulmi su ka yi ta lilo a kan ruwan kogin tun dagaa Gundumomin Gurdaspur da Pathankot a cikin India. Yayyena su ka ƙuduta a daren nan za su ƙunshe ni a cikin buhu a jefe cikin ruwa kogin don ya cika aikinsa.

An yi tsananin sanyi da daren ran 6 ga Disamba. A Lahore sanyi yakan zama jaura. Bayan abincin dare, sai suka tuɓe ni sindir sai kanfai a jikina. Aka kulle ni cikin wani ɗaki mai sanyi babu kome ciki. Sun yi haka don sanyi ya daskare ni yadda ba zan iya hasafa kome ba, wato sai yadda su ka yi da ni.

Da suka kulle ni, na san abin dake tafe, abin da zan yi duka shi ne addu’a. Daga ran da na zama Kirista, sai na tsiri halin yin addu’a da haddacen ayoyi. Sai na fara haddace da zuci. Nassoshi kamar su “Ubangiji Makiyayina ne,” sun ta’azantar da ni ƙwarai. Wani lokaci in yi kuka, wani lokaci in yi hadaccewa, amma yawancin lokaci na yi ta magana da Ubangiji ne. Na sani yana nan tare da ni, bayan na mutu kuma zai rungume ni. Ina nan a tsakanin murnar kasancewa a gabansa, da kuma azabar raɗaɗin mutuwar da zan sha. Wani lokaci kuma sai in yi dariya, domin na san ikon Ubangiji, yadda iyalina suke so su ƙarasa ni abin dariya ne. Ban taɓa jin shakkar nagarin Allah ba. Ban taɓa jin na yi kuskure da hanyar da na zaɓa ba. Na sani, Kristanci ne kaɗai hanya domi na. Ina da tabbas cewa zan kasance tare da Ubangiji bayan mutuwata. Ba abin da zai girgiza ni game da wannan, sani na zaɓi hanyar da ke daidai, ko da shike za a ƙarasa raina cikin wulakanci a cikin wannan duniya.

Lokacin da nake ta maimaici da smun ta’aziyya cikin Nassoshi, sai wani sashi ya fādo mini daga cikin wasiƙar Bulus zuwa ga Filibiyawa, ya buga ni da ƙarfi, shi ne: “Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai.

Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu domin wannan shi ne ya fi kyau nesa. Amma in wanzu cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku.” (Filibiyawa 1:23,24). Ko da shike batun mutuwa ya ɗauki hankalina saboda rai maɗaukaki na sami zai faru nan gaba, yanzu kuma hankalina ya juwa ga gefe guda – rayuwa saboda ‘yan’uwana. Sai ya karaiko mini cewa, dole in so in rayu domin waɗannan da har yanzu suke cikin duhu. Ina so in iya kai hasken Bishara ga mutanen ƙasata da suke da bukata- albishri mai daɗi na abin da Allah ya yi domin ‘yan adam ta wurin mutuwar Yesu Almasihu tashinsa daga cikin matattu. Wannan sabon hakikancewa ta ƙarfafa a ciki na sa’ad da na tuno da kalmomin Sadhu Sundar Singh, (wani tubabbe daga Sikh) ya ce: “Ya fi sauƙi a mutu domin Almasihu, amma rayuwa mutuwa ce kullayaumin.” A hankali take amma tabbacciya ce, wannan ra’ayi ya cika tunanina da sabon jin ɗaukak. Ina misalin kyan wannan wahayi da ya zo mini – ba dai in mutu haka farat ɗaya domin Ubangijina ba, amma in yi ta mutuwa kullayaumin. Ruhuna ya yi murna ƙwarai saboda wahayinnan a cikina duka. Ribar kaɗai da take akwai a cikin mutuwata za ta zama domin iyalina ne, za su daina jin kunyar da na ba su ta dalilin bangaskiyata cikin Ubangiji Yesu Almasihu. Zai yiwu ma su shafe ni daga tunaninsu, tun da tunawa da ni zai kawo musu jin haushi kawai.

Ga ni nan a tsakanin son in mutu nan take domin Almasihu ko kuwa mutuwa kullayaumin dominsa cikin rayuwata ta cikakkiyar miƙa wuya da sadakarwa. Na gane cewa hadayar miƙa wuya da sadakarwa. Na gane cewa hadayar da ya yi domi na cikin mutuwarsa a kan Gicciye tana da daraja, da zurfi, ko da na yi ta mutuwa sau dubu a rana ɗaya, ba za ta kwatantu da darajar guda na jininsa domi na ba. Na hakikance cewa, ina bukatar yin addu’a da naciya domin samun kuɓuta, ba domin ina jin tsoron mutuwa ta jiki ba, ko wani abu dabam, amma kawaidomin in rayu in yi ta mutuwa kullayaumin cikin yin shaidarsa, wanda ya ƙaunace ni, ya ba da kansa domi na. Ga yadda addu’ar tawa take.

“Ubangijina da Mai Cetona, ruhuna yana da salama, domin na san cewa bayan wannan rai zan taho gare ka. Babu abin da zai kange tsakanina da kai. Amma mutanen nan, masu mugun shirin kisa za su ɗauka kamar sun kawo ƙarshen raina ke nan. Mutuwa ƙofar: rai ce a gare ni. Ɓangarena ya na neman shiga, amma mutuwata ta zama ƙarshen shaidata ta sunanka a wannan ƙasa. Saboda haka, in ya yiwu ka fidda ni daga wannan wurin da daren nan, ka kuma ba ni zarafin shelar babban abin da ka yi cikin mutane. Daga nan zan iya faɗa musu yadda ka ke iya wartasakar da rayukan mutane, ka kuma ba masu zunubi tabbzcin rai na har abada. Ya Ubangijina, ina marmari daga daren nan harshena ya furta kalmominka masu bada rai kamar yadda na more shi wajen ba da umarni a kashe wasu' Idanuna sun ga ikonka, Yanzu idan ya gamshe ka, ka kuɓutar da ni daga nan, yadda da safe ya zama sabuwar safiya a cikin raina. Kuɓutar da ni daga kason nan tabbatarwa ce cewa, zan zama mashaidinka. Ya Ubangiji, da daren nan ka tsarkake ni daga sonkai, da damuwa don raina kawai. In ka bar ni rai, da damuwa don raina kawa. In kabar ni da rai, na yi alkawari in yi rayuwa ta bauta maka da nufin kawo ɗaukaka ga sunanka. Ya Ubangiji, ba ka bukatar in taimake ka, ko hidimata, amma ina mai farin ciki da mai samun dama in bauta maka. Kamar yadda nake ɗokin in shafe mutane da ka halitta daga duniya a dā, haka nake ɗoki yanzu kawo su zuwa gare ka. In wannan zai zama nufinka mai daraja, to, ka cece ni, ka fitar da ni daga wurin nan yau da dare nan. Aminin.”

Bayan furta kalmomin nan, maimakon daskarewa saboda sanyi, sai na ji zufa ta faso mini a goshina! Ba labari, sai na ji wani ya buɗe ƙofa daga waje. Na jira ko zan ji wani yana shigowa. Da na ga babu kowa, sai na matsa a hankali na duba waje na ga babu kowa a titi. Daganan sai na ji Ubangiji ya na yi mini raɗa a kunne cewa, “ka gudu, na buɗe ƙofa domin ka!” Na fara gudu, amma ban san ko wace kusurwa zan dosa ba. Ina da abokai biyu kawai a Lahore, su kuwa musulmi ne. Ba ko Kirista ɗaya a can. Na ci gaba da gudu biye da hanyar jirgin ƙasa wadda daga Lahore ta nufi Raiwind. Na wuce wata tasha ke nan, sai na fāda cikin lambatu. Na gaji ƙwarai da gaske, nan na ƙasa daren. Na yi ta barci, ban farka ba har wajen ƙarfe goma sha ɗaya na kashegari, da hasken rana a kaina. Na tashi na kama hanya zuwa Model Town (Wata gundumai mai arziki cikin ƙasar Lahore). Ina duban kyawawan gine-gine, ba labari, sai na lura da kayan da ke jikina, ya zama akasin yanayin wurin nan ƙwarai da gaske. Bayan Model Town, sai na ga wani ƙauye sai na nufi can.

Da na shiga ƙauyen, sai ga wasu yara su na wasa a fili. Sai na tambaye su, “Ɗana, ko akwai wani Kirista a nan? Sai wani yaro ya amsa, “I, akwai, babana ma fasto ne a nan. Me ke so mu yi maka?” Sai na ce, “Ka kai ni wurin babanka in ka yarda.” Yaron ya kai ni gidansu, na sadu da babansa, Kyaftin Samuel na Samuel na Salvation Army (wato Rudunar Ceto). Na sami sawaba.. Kyaftin Samuel ya nuna mini alheri lokacin da na ba shi labarin abin da ya faru da ni duka. Ya tabbatar mini cewa ba abin da zai faru da ni a nan yanzu, in ma akwai wata wahala, zai kāre ni a bakin ransa. Muka ɗauki ɗan lokaci mu ka yi addu’a, sa’an nan ya nuna mini wurin kwanciya. Ya aika likitan ƙauyen ya zo ya auna lafiyata, ya yi mini allura, ya kuma ba ni wasu magunguna. Na zauna nan har Mutumin kirkin nan ya ba ni taguwa da kaklmi, da wani irin gyale maganin sanyi, da kuma kuɗi da ɗan dama.

Na isa Gojra ran 15 ga Disamba. Dukan abokaina sun yi murnar gani na, musamman Rev. Wootton, da Rev. B. M. Augustin, Boota Masih da Mr. Charan Dass. Labarin kuɓutata ta mu’ujiza ta zama dalilin murna ƙwarai. Ranar Kirismati, na yi sujada tare da abokina. Bawa Masih a ƙauyukan kewaye. Baban Bawa Masih da ƙwarai. Muhimmin abu a gare ni yanzu shi ina ɗaya daga cikin jama’ar Kirista. Na ɗauki matalautan mutanen nan suka zama ƙaunatatuna mafiya kusa da ni. Ƙaunar juna ta zama abin yi na ƙwarai a gare su. Zununtar Kirista cikin jiyayya da gaskata juna ita ce tushen ƙarfafawa da taimako cikin girma zuwa balaga cikin Almasihu. Ina zaune lafiya cikin abokaina waɗanda suka karɓe ni. Na sami biyan bukata ƙwarai da gaske na yi godiya ga Allah ƙwarai da gaske.

IX - AIKIN BISHARA DOMIN ALMASIHU

Cikin tsaron lafiya da salamar zumuncin Kirista, sai na fara ɗaura niyyar hidima. Har zuwa lokacin da na tuba, dama abin da nake biɗa don muradin kaina ne kawai, amma yanzu tunanina ya juya. Na tuno da kalmomin wani wāƙe na Ghalib:

Nasara ba za ta zo ba

Ga aikin ƙauna na addu’a

Sai an wanke tsananin sonkai

Da zuciya sarai.

Masu nufi na da alheri su na ta ba ni shawarwari iri iri. Wasu su na cewa in kama kasuwanci, wasu kuwa su na cewa in shiga aikin Ubangiji. Amma na san abin da nake so in yi. Ban manta da ƙudurin da na yi ba a daren da na sami kuɓuta daga mutuwa. Da nake yabon Ubangiji domin dukan abin da ya yi domin na, sai na yi masa wannan roƙon.

“Ya Ubangiji, ka ba ni ikon yin shelar ayyukanka na banmamaki a duniya. Ka ba ni halin yin ibada a gare ka, yadda zan riƙe kaina da tsarki a cikin wannan duniya mai zunubi. Ka ba ni irin ƙaunar da zan iya samu daga cikarta, yadda halin duniya ba zai taɓa samu ba. Ka bishe ni a hanyar da nake bi don kada in yi tuntuɓe, kawo kunya ga ɗaukakar sunanka.”

Na hakikance cewa, aikina domin Ubangiji shi ne aikin bishara, na kuma yanke shawara in fara a inda nake. Da ni da wasu matasa muka fara fita kewayen Gojra mu na shaida Bishara. Wani lokaci Rev. Wootton yakan fita tare da mu, amma ban cika son haka ba, domin wannan yakan hana mutane su yi da kamar yadda su ke so ba. Bagu da ƙari, ina so in auna karɓuwata yadda cin aikina ya ke a cikin dukan ƙauyukan Punjuba. Na fara da tafiya da ƙafa. Daga nan sai abokaina su ka sayo mini keken hawa. Mutane su ka riƙa kira na Sadhu, wato mutum mai tsarki. Ko’ina na je nakan zauna cikin matalauta. Ta haka nake sajewa da ‘yan’uwana Kirista. Ina so in yi rayuwa irin ta su a ko’ina na je. In ba su da abinci, ni ma haka zan zama. Tushen na gatanci bai zamar mini hani ba.

Duk lokacin da na shiga sabon wuri, sai na fara zuwa in gabatar da kaina ga faston wannan yanki, sai na sami amincewarsa kafin in fara aiki cikin yankinsa. Wannan ma hanya ce da nakan bi in yi wa Kirista wa’azi don ƙarfafa bangaskiyarsu. Lokacin tafe-tafena na aiki, wata rana sai gani a wani gidan mishan na Anglican, kusa da Lahore. Na zauna tare da Canon Stanley Huck, har na riƙa shiga cikin wasu tarurrukan da yakan shirya. Lokacin da nake jiran sa a Ofishinsa, sai Ubangiji ya yi magana da ni a sarari. Ya ce, “Ka je ka ba da shaidar kanka ga ‘yan’uwanka a Lahore. A can ne za ka fara.” Wajen ƙarfe tara ne da dare. Abin da na fi begen yi shi ne biyaya da Ubangijina, ba na jinkirin yin biyayya da umarninsa. Na ji tilas in tafi da daren nan. Na barkekena a nan, na kama jirgi zuwa Lahore. Na ƙwanƙwasa wa yayana ƙofa, ya buɗe mini. Cike da mamki, da ‘yar alamar bege a idonsa, ya tambaye ni “Ka dawo?” Ba dawowa gida kaɗai yake zato ba, amma har da komowa cikin bangaskiyata ta dā. Na ce, “I, na komo, amma ba domin in zauna tare da ku ba kuma. Na zo kawai don in faɗa muku cewa, Ubangiji Yesu Almasihu shi ne Mai Ceto. Ya cece ni, na kuma sani zai cece ku ku ma.” Nan da nan ya sāke fuska. Ya na ƙoƙarin danne fushinsa, ya amsa dakyar, “Na gode da yawa. Amma ba mu son ka, ba mu kuma son Ubangijinka Yesu. Ba mu son Ceton nasa. Sai wata rana.” Da haka ya rufe ƙofa. Na yi ɓācin rai, amma ban yi mamaki ba. Na ji sanyi a raina domin na cika aikina, ko da shike kama babu amfani.

A daren nan kalmomin Ubangiji sun ratsa ni ƙwarai, na hakikance cewa dole in yi wa abokaina Musulmi shaida, musamman su da suke a ƙauyen nan mai tasowa ƙwarai, Zaffarawal. Na tuna zuyarar da na kai wa wani mishaneri. Ba-Amerke da matarsa a gidansu a ƙauyenmu. Da ina yaro, mu yara mukan je gidan, matarsa ta riƙa koya mana waƙa. Bayan na tuba, sai na yi sauƙi da zuwa wannan yanƙi, amma yanzu na rubuta masa cewa ina so in ziyarce su domin. Ubangiji ya nuna mini cewa, ya kamata in fara aikina a ƙauyena. Ya yi marmarin gani na ƙwarai. A sakamakon haka, sai na tafi zaffarawal a cikin watan Maris, 1950. Da na isa, sai na sami labarin baƙin ciki, mamata ta rasu ‘yan kwanaki da su ka wuce saboda baƙin cikin rabuwa da ni. Na yi baƙin ciki rashin ganin ta kafin ta mutu. Ba ta san an shirya maƙarƙashiyar kashi ni ba' ta dai san ina da damuwa, da tana iya taimako na da ta yi. Amma ban yarda duk waɗannan su sa in fāsa shirina na bauta wa Ubangiji ba, wanda ya sāke komo da ni a ƙauyena.

Bayan mutuwar mahaifiyata, sai ƙiyayyar ‘yan’uwana ta ƙaru. Sun sha shirya maƙarƙarshiyar kashe ni. Lokacin da nake zama tare da mishaneri, sun sha kira na in zo gidansu. Da fari na ƙi, amma daga baya na nemi shawarar abokina. Ya ce in je amma tare da wasu, ya kamata in tafi da abokai biyu tare da wasu, ya kamata in tafi da abokai biyu tare da ni. Haka na yi, na ziyarci ‘yan‘uwana. Muna zaune muna magana, sai na ga wani takobi a kan tebur kusa da ni. An wasa shi sosai. In zato saboda ni ne. Na ɗaga takobi, sai mai kisan ya kashe kansa tukuna. Sai lamirinsa ya mutu kafin ya iya ɗaga hannu a kan wani. Alamar mugunta ke nan.” Na maida takobin cikin kubensa.

Mun tattauna lokaci mai tsawo. ‘Yan’uwana suka gayyato Malami don ya yi magana da ni. Duk dai a banza. Ba shi da wani abin dake daidai da zai faɗi a ƙarshe aka ba mu shayi. Na ɗan kurɓa. Ya na da ɗaci ƙwarai, sai nan da nan na gane an sa dafi a ciki. Ban ji tsoro ba, na tuna da kalmomin da Yesu ya faɗa wa almajiransa bayan tashinsa cewa, waɗanda suka ba da gaskiya, aka kuma yi musu baftisma za su yi alamu masu yawa. Ɗaya daga cikin su shi ne, “kowace irin guba kuma sukasha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan” (Markus 16:18). Na tabbata, wannan zarafin ne da zan san wannan ɗaya daga cikin alamun. Na shanye shayin, na yi addu’a “Ya Ubangiji, ka riƙe ni.” Nan da nan abin ya fara damu na, ina ganin jiri ƙwarai. Na ce yadda na ke ji ba. A bayan gari babu nisa da gidan mishan, sai na ce wa abokaina su yi gaba su bar ni nan. Wajen ƙarfe goma ne na dare. Na yi addu’a: “Ya Ubangiji, in na mutu da daren nan mutane za su ce Kristanci ƙarya ne. Ba sunana ba, amma sunanka ne zai ƙasƙanta.” Da dai na gama addu’ar, sai na yi amai sau biyu, dafin duk ya fita daga cikina. Sai na yi barci lafiya. Da safe na tafi gidan misahn. ‘Yan’uwna su na sauraron ko me zai faru da ni, da na ga wani ya zo daga ƙauyen, na sani an aiko shi ne. Na gane shi ɗaya daga cikin barorin ‘yan’uwana ne, na ce m,asa faɗa wa iyalina cewa har yanzu ina nan da rai.

Ba bangaskiyata kaɗai take damun ‘yan’uwana ba. Suna tsoro kuma ko zan nemi rabo cikin kayan gādo. Sun ƙara wani shirin kashe ni. Lokacin da na ziyarci Narowal, sai wani abokina Musulmi ya zo gidan Rev. Isaac Dass don ya gaya mini cewa wasu matasan Kasmir su na jira na a bakin gada. Sai na ƙudurta zan yi watsi da dukan abubuwan nan da za su sanar a rubuce cewa, ba ruwana da dukan mallakar mahaifina, Chaudhry Lal Khan, na bar wa ‘yan’uwana duka. Ta haka ne warware dukan abin da ke ɗaure da ni da iyalina. Yanzu ba su da sauran jin tsoro. Zai yiwu su ƙyale ni in ci gaba da rayuwata ta yin shaida. Amma na gane a hankali raina ya na cikin hatsari a Punjab. Na fara aikina a can kamar yadda a ka gaya mini, amma babu dalilin ci gaba da zama a can. A lokacin wannan tunani ne na sādu da wani aboki mai ƙauna, mai kirki, Rev.Chandu Ray, wanda daga bisani ya zama Bishop Mun yi magana da dama a game da aikina. Ya shawarce ni in tafi Sukkaur a Sind. Na yarda da shawararsa ina tunawa da kalmomin Bulhe Shah, wāƙen Punjabi:

Zo a kan Bulhe

Bari mu je wuri

Inda babu wanda ya san ƙasƙancinmu

Ko a maida hankali a kan mu.

Mishanerin da ke a Sukkar a wannan lokaci shi ne Padre Carson, wanda a ke girmamawa. ‘Yan watani kaɗan na yi aiki da Bible Society, wannan aiki ya ƙunshi gudanarwa da rubutun rahotanni. Na damu sosai. Zuciyata ba ta cikin wannan aiki. Bugu da ƙari, na fara jin cewa shi da sauƙi ba. Sai ragaita nake yi daga wahayina na asali, don haka na yanke shawara in ajiye aikin nan.

Na ga kaina mai aikin Bishara ne, don haka dole in shirya kaina domin aikin nan, Na fara koyon Sindhi' Padre Carson ya riƙa taimako na. Nan da nan na iya yaren Sindhi har na fara magana cikin yaren da rubutawa sarai. Babu sauran matsalar yare, na iya tafiya tare da Mr. Carson cikin aikinsa na bishara. Aikina ya ja da baya a Sukkur. Bazara ta iso, yanayi ya fara yi mini zafi ƙwarai. Ko da shike na ƙudurta a raina cewa Sind ne zai zama wurin aikina, dole in bar wurin don ɗan lokaci.

Na komo Punjab. Sa’ad da ina can, na sādu da Leroy Selby, wani fasto ba amirke a Lyallpur (yanzu ana ce da wurin Faisalabad). Ya gayyace ni mu yi aiki cikin matasa. An fara babban taron lyallpur ke nan. Shekara biyu shi domin matasa. Ba ni da wurin zama, don kuwa ba na son zama tare da mishaneri, na shirya yadda zan zauna tare da wani Kirista mai suna Chaudhry Jalal Masih. Mai alheri ne shi, ya zama kamar uba a gare ni. Na sami karɓuwa cikin iyali, ɗansa da ‘yarsa sun yi da ni kamar ɗan’uwansu nake. Wannan dangantaka ta buɗe ƙofofin jama’ar garin a gare ni, har na zama hankalina duka ya shiga cikin aikina domin Ubangi. Daga nan cikin Lyallpur, na riƙa zuwa ko’ina cikin ƙasar a kan keke. Na yi tafiyar wajen mil, 12,000 tafiya lokatai da dama tsakanin Kemir a kudu (cikin Karachi) da landin Kotal a arewa (kusa da Peshawar a kan iyakar ƙasar Afghan).

Da fari sai wani mishenari Ba amirke na Reformed Presbyterian ya kai ni wani ƙaramin gari. Ya sa na yi wa’azi a wata sujada. Da lokacin karɓar baiko ya yi, ina ta fama da tunani. Abin da ke aljihu na ƙalilan ne. Me zan yi? Ina bukatar wannan ɗankuɗi, duk da haka ba za a wuce da tasar baiko ban saka kome ba. Ba ni da zaɓi da a ka zo kaina. Na saka ɗan kuɗin nan baiko. A gama sujada amma ina ta tunani ko yaya zan yi, don babu ko kwabo a aljihu yanzu. Ashe, ba da jimawa ba Allah zai yi aikin nasa, sai tanada mini.

Na komo gidan abokina ɗan Pakistan. Sai matarsa ta tarye ni da saƙo ta ce, “Ɗan’uwa, wani yana son ganin ka.” Na yi mamaki, don ba ni jiran zuwan kowa. Sai ta bayyana cewa wasu malamman jinya ne su biyu daga asibiti su ka zo don su gan ni saboda zan tashi gobe. Ba su sādu da ni ba a wajen sujada sai su ka bar ambulon domi na. Da na je ɗakina na buɗe ambulon nan, sai ga kuɗi mai yawa, sun rubuta cewa “Ubangiji ya nuna mana kana bukatar kuɗi domin tafiyarka. Ka karbi wannan da godiya.” Na rasa abin da zan ce. Ba shakka, Allah nagari ne!

Akwai abin da ya ƙi mini a rai. Na ziyarci wani mutum da ya nuna marmari ga bangaskiyar Kirista. Na isa garinsa amma ban same shi ba. Na shigo mota safa da rai a ɓāce, na kuma gaji. Kusa da ni cikin motar, akwai wani tsoho musulmi, sai muka shiga hira da shi. Ya tambaye ni labarina, da na faɗa masa cewa ni mai wa’azin bishara ne, sai ya ji daɗi ƙwarai. Kamar dama Allah ya amsa addu’arsa ke nan. Ya kamata musulmi ya je Makka sau ɗaya amma shi ya je har sau baƙwai, amma bai sami abin da ya ke nema ba. Ya ce mini wani ya ba shi ɗan littafin Bishara cikin yarensa, ya na ta karantawa. Kamar dai Bahabashin nan na cikin Ayyukan Manzanni, ya bukaci wanda zai yi masa bayani. Ga shi nan cikin wannan mota, yana addu’a yadda Allah zai aiko wani, sai duk gajiyar ta sake ni, da murna na mori zarafi don in bayyana masa Bishara. Da muka iso inda ya sauka, sai ya gayyace ni zuwa gidansa. Yana da gidaje da filaye, yana da gona wajen kadada 7,000. Bayan doguwar hira, sai ya roke ni in yi addu’a domin sa. Na ce ya yi addu’a domin kansa. Ya yi tambaya da mamki, ya ce, “Zan iya kuwa?” Na ce masa, “I, muddin ka iya yin magana da ni, ai za ka iya magana da Allah kuma”. Daga nan sai ya ce “Ubangiji Yesu na gode da ka aiko bawanka, domin ya bi da ni a kan hanyar da ke daidai. In ka yarda ka karɓe ni, na karɓe ka ka zama mai ceto na daga yau.” Na sani Allah ya yarda da shi. Nagari, da alherin Allah ba su da iyaka. Dukan masu kira da gaskiya da Ubangiji sun sami Ceto.

X - DUKA DOMIN YESU

Allah ya zaɓar mini hanyar da zan bi, na kuwa miƙa wuya. Ta wannan hanyar ne kaɗai zan yi rayuwar da za ta ɗaukaka Shi. Na zama mabarcin sa, Shi da ya fara ƙauna ta, ya sa ƙaunarsa a kaina. Da ƙarfin kaina ba zan iya yin kome ba. Dukan abin da na zama, da dukan abin da na iya yi, sun kammlu ne ta wurin aikinsa a cikina.

Hanyata zuwa “Calvary” ta na ƙayayuwa. Tana da wuya fiye da yadda nake zato. Amma na sani tabbatacce ne cewa, Yesu Banazare ya bi wannan hanyar kafin ni. Wannan tunanin ya ƙarfafa ni, har ma ko a lokacin da “gicciyen” yaken yi mini nauyi ainun. Kalmominsa sukan yi mini tuni a kai a kai, cewa: “Duk mai son bi na, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa ya bi ni” (Markus 8:34). Wannan ce kaɗai hanyar da zan bi, hanyar kaɗai da zan bauta masa, in kawo wasu ga Gicciyensa. Maida martanina ke nan saboda ƙaunarsa domin na.

Akwai kaɗaici cikin hidima. Wani lokaci akan kāsa fahimtar wannan kaɗaici, inda makonni da dama, ko ma watanni ba na samun jin daɗi cikin tattaunawar, da kuma cuɗanya da mutane. Amma ta wurin haka ne nakan iya sajewa kurkusa da Ubangijina. Mutuwa domin Almasihu cikin wannan rai tana sa in gone da ikon tashinsa daga cikin matattu. A cikinsa nake sanin nasarar rayuwa a kan mutuwa, tun kafin in mutu. A cikin babban waƙen Pakistan Sir Muhammed Igbal, ya bayyana rai da mutuwa kamar haka: “Rai suna Odar da ake iya gani ce ta abubuwa, mutuwa kuwa ita ce, lokacin da odan nan ta kakkarye, ta kuma warwatse.”

Bayan na bar dangina na kusa, su arba’in da biyu, ya yi mini wuya in daidaita cikin sababbin al’amura. Matar yayana ta nuna mini ƙauna ƙwarai da gaske, mahaifiyata ba ta taɓa tsauta mini cikin fushi ba, ba ta yin faɗa da kowa, mahaifina mai alheri, mai kwarjini, kyakkyawan gurbi, wanda ya tanada hikima domi na, bishewa mai kyau, ‘yan’uwana maza su huɗu waɗanda su ke kula da zaman jin daɗina' abin baƙin cikin yanzu su ne maƙiyana ƙwarai da gaske. In ba tare da su ba rayuwa za ta yi mini wuya ainun. Har abokina Musulmi waɗanda su ka ci gajiyar abokaina Musulmi waɗanda su ka ci gajiyar abokatar mu da aminci sun zama baƙi a gare ni yanzu, ko da shike waɗannan dangantaka an ƙirƙiro ta cikin mawuyatan al’amura. Na tuna wani al’amari lokacin da nake mayaƙin ‘yanci, lokacin da nake kula da kan iyakar ƙasa na Kashmir. Muna cikin tsananin faɗa, Muna musayar wuta da bindigogi. Sai bindigar abokina Akbar Kazmi ta haɗe ya firgita, domin ya zama kamar wanda aka ƙwace wa makami Na ga ya zama marar bege cikin halin ƙaƙa naka yi. Sai na jefa masa bindigata don ya kare kansa. Ina ji ya fi ni bukatar ta, don ina ji da ƙarfin ƙuruciya, ina iya kāre kaina ko da ƙaƙa ƙarfin abotakarmu. Amma da iyalina suka faratsananta mini, bar abokina mafi kusa kamar Kazmi, dole in nemi hanyar rayuwa ta kaina ya zama kamar “mutuwar zaman tare” a gare ni. Mutuwa kullayaumin domin Ubangijinmu, ba abin da za a ɗauka da sauƙi ba ne. Ba na kaicon yin ta. Idan na ga sākewar rayuka da samun albarku , nakan yi matƙar murna. Amma akwai lokatan karaya, idan na ga kamar aikina ya zama banza. Idan na ga mata matasa, waɗanda na taimake su suka yi ilimi, sun taso cikin bangaskiyar Kirista, amma sun watsar da duka, sun zama cikin damuwa da baƙin ciki, sai kuma na tuna cew, Ubangijinmu ya mutu domin dukka, duk da haka kaɗan ne suka karɓi ƙaunarsa. Daga nan na tambayi kaina. “Da me za a kwantanta ƙaunata da aikina da nasa?” Hadayar kansa a kan Gicciye an gani kamar kāsawa ce. In aka zage ni ban rama ba, sai a zarge ni cewa na kāsa. Ba na begen a yi da ni dabam da Ubangijina.

Ina a shirye yanzu in ya kira ni don in sāke tsofaffin tufafina in sa sababbi.” Na sani mutuwar Kirista ba ƙarshen rayuwa bane, amma mafarin sabuwar rayuwa ce mafi kyau. Bayan na bar duniyan nan, ba ni da zarafin mutuwa kullayaumin domin sa. Ina ƙarfafa mutane da dama su yi tafiya cikin duniyan nan da amincewa, don su ɗaukaka suna Ubangijina, su yabe Shi. Ubangijina da Allahna ya bi da ni da aminci dukan shekaruna. Yabo ya tabbata ga sunansa! ‘Yan shekarun da su ka wuce, na je taron yanki a Karaci, na ga Manzaur da Dadu su na hidima a Babbar Majamai. Na sunkunyar da kai na gode wa Allah. Da na karɓi albarka daga gare su, sai na ji wani irin daɗi ya ratsa ni kamar zuciya za ta fashe don murna! Ni Ubangiji ya mora don kawo su gare Shi. Me kuma bawan yake biɗa. Na gode wa Allah da ya same ni. Addu’ata ita ce, waɗanda su ka karanta labarin Ubangiji a littafin nan su zama an lasafta su a cikin tsarkaka masu yabon Ubangiji cikin haske madawwami.

Ƙarshen Battu

Ghulam Masih Na’aman ya bauta wa Ubangiji Yesu Almasihu shekara bakwai ya na matsayin mai wa’azi. Daga baya ya je makarantar tauhidi a Gujranawala, aka haɗa shi ya zama fasto cikin ikilisiyar Anglican. Ya auri wata ma’aikaciyar jinya mai suna Daisy, ta zama amintacciyar mataimakiyarsa a cikin dukan famansa na rayuwa. Su na da ‘ya’ya uku, maza biyu da mace ɗaya. Dukan iyalin suna bauta wa Rayayyen Almasihu.

IX - KACINCI-KACINCI

Alherina ya Ishe ka

Zuwa ga Mai Karatu, idan ka karanta labarin nan na Rev. Ghulam Masih Na’aman, za ka iya amsa tambayoyin nan. Idan ka ansa su, ka aiko mana, mu kuma za mu aiko maka da wani littafin.

 1. Yaya marubucin nan ya ke ji da iyalinsa?

 2. Don me babansa ya zama mai zurfin Musulunci a asirce?

 3. Menene manufar Sufis?

 4. Ɗon me marubucin ya bar neman ilimi ya shiga Sojan Sama?

 5. Ta yaya addu’ar Baxter ta shafi na ƙasa da shi?

 6. Waɗanne ka’idodin Kirista ne su ka bi da masu jinya su biyu Amber da Mary har su ka lura da Na’aman?

 7. Me ya zuga Philip har ya auri yarinyar da take cikin halin lallacewa?

 8. Don me marubucin ya bar aikin Sojan Sama?

 9. Ta yaya ya zama mayaƙin ‘yanci?

 10. Ta yaya musulunci ya halatta yaƙin Jihadi?

 11. Wane Zahirin matsi ya girgiza mayaƙin ‘yancin nan cikin aikinsa?

 12. Ta yaya Yesu ya amsa shaida da addu’ar yarinya ‘yar shekara goma da haihuwa tare da iyayenta a wani ƙauye kusa da kan iyakar ƙasa?

 13. Wane roƙon damuwa ne na mayaƙin ‘yancin ya yi ga Iyalin da Almasihu ya kiyaye? Yaya su ka maida martani?

 14. Me tsohuwa ‘yar Hindu ta bayyana wa shugaban masu kisa don ta ceci ran jariri daga kisa?

 15. Menene tunanin marubucin nan a game da Yaƙin Jihadi lokacin da ya sabuntata nazarinsa cikin Islama?

 16. Ina manmanyan kalmomin addu’ar Ghulam zuwa ga Allah Mai Iko Dukka?

 17. Waɗanne kalmomi Yesu ya faɗa domin ya ceci karyayyen Mai biɗar Allah a ɗakin jira na tashar jirgin ƙasa?

 18. Me Yesu ya ba Ghulam lokacin da ya yi magana da tsoho Kirista mai shara daga ƙasƙantattun sahun mutane?

 19. Waɗanne ne kalmomi na ainihi na Rev.Rumal Shah a Isanagri?

 20. Wace wahala marubucin ya jure, sa’ad da yake zama tare da Kirista Leburori a gidan mishan?

 21. Ta yaya Ghulam ya koyi zumunci cikin addu’a tare da Sewa Boota Masih, me kuma abin ya zamar masa?

 22. Me baftisma ta zama ga marubucin da shike sabon tuba?

 23. Me ya sa Ghulam ya bi kawunsa da yayansa zuwa gida, ko da shike ya sami ransa ya na cikin hatsari?

 24. Ta yaya iyalin Ghulam su ka yi ƙoƙarin komar da shi cikin Musaulunci?

 25. Don me ‘yan’uwan marubucin su ka so su kashe shi, wace dabara su ka bi?

 26. Menen manufar addu’ar marubucin, lokacin da yake kulle cikin ɗaki mai sanyin jaura yana a tuɓe?

 27. Me Yesu ya faɗa wa bawansa, yaya kuma ya bi ya kuɓuta?

 28. A ina ne Ghulam ya fara hidimarsa ta Bishara? Ina sakamakon, kuma ina ya tafi daga nan?

 29. A ina ne Ghulam ya fara hidimarsa ta Bishara? Ina sakamakon, kuma ina ya tafi daga nan?

 30. Me ka koya daga shaidan nan, wato labarin nan?

Ka aiko da amsoshinka, da cikakken adireshinka zuwa ga namu adireshin. In kana da wani sharfi sai ka rubuta a wata takarda dabam, ba a cikin wadda ka rubuta amsoshinka ba. Mu na jiran amsarka da sauri.


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland