KU AUNA ABU DUKA KU RIƘE MAI KYAU

KU AUNA ABU DUKA KU RIƘE MAI KYAU

ISKANDER JADEED


KU AUNA ABU DUKA KU RIƘE MAI KYAU

Ayan nan, mai kira a auna, ita ce ainihin batun “Hanya Mai Kyau”. Maganar Allah tana cewa, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga ’yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba” (Ishaya 8:20).

Zuwa ga Aboki,

A farkon saƙonka ka ce, “Wannan hanya tawa: “Na yi Kira ga Allah da tabbataccen sani, Ni da duk wanda ya bi ni” (Suratu Yusuf 12:108). Wannan ya sa na ɗauka cewa kai mutum ne wanda ya san abin da yake yi, wanda kuma yake aiki da abin da Kur’ani yake faɗa, “Kada ku yi jayayya da mazowa Littafi sai fa da magana wadda ta fi kyau” (Suratul Ankabut 29:46).

Amma bayan da na karanta waƙen da ka kwaso, sai na yi baƙin ciki. Ka kwaso cewa, “Abin mamaki Yesu yana cikin Kirista,” wannan ya yarda da abin da mafiya yawan Musulmin da muka yi cuɗanya da su suka sha faɗa, ya kuma yi daidai da ayar Kur’ani mai cewa, “Da faɗarsu, ‘Lalle ne mu, mun kashe Masihu Isa ɗan Maryama Manzon Allah’” (Suratun Nisa 4:157).

Cikin ruhun ƙauna, wanda shi ne haƙuri da fahimta, wanda kuma shi ne Kirista na gaske yake aiki da shi cikin biɗar gaskiya, bari in miƙa maka waɗannan batutuwa:

GICCIYE CIKIN LINJILA DA KUMA KUR’ANI

Bulus, ƙaƙƙarfan manzon Kristanci, cikin wasiƙarsa ta fari zuwa ga Korantiyawa ya ce: “Yahudawa kam, mu’ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suke nema su samu, mu kuwa muna wa’azin Almasihu gicciyayye, abin sa tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al’ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah” (1 Korantiyawa 1:22-24). Har yanzu wannan manzon yana cewa, “Sa’ad da na zo wurinku, ’yan’uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta iya magana ko gwada hikima ba. Don na ƙudura a raina, sa’ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyayye” (1 Korantiyawa 2:1, 2).

Cikin la’akari da shaidar manzon Almasihu, wanda ya yi tarayya da shi, ya kuma san shi a makaɗaicin Ɗan Uba cike da alheri da gaskiya, wanda kuma daga cikarsa suka karɓi alheri a kan alheri, mu gane cewa Bisharar da suka yi shelar ta a ɓullowar Kristanci, wadda mutane suka karɓa, wadda suka cetu ta wurin ta, ita ce Bisharar da Bulus ya taƙaita ta daidai cikin waɗannan kalamai: “Yanzu kuma, ’yan’uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi, wadda kuma ake ceton ku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku kankan, in ba sama-sama ne kuka gaskata ba. Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa, cewa an binne shi, an tada shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa... ” (1 Korantiyawa 15:1-4).

Wani manzo kuma, Yahaya ya ce, “Wannan rai kuwa an bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun da yake tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu to, shi wanda muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyan nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu” (1 Yahaya 1:2, 3). Wannan ya yi muwafaka da faɗar Bishara, “Kalman kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu” (Yahaya 1:14).

Wani manzo kuma, Bitrus, ya faɗa wa Yahudawa cewa, “Ya ku ’yan’uwa Isra’ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu’ujizai, da abubuwan al’ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani – shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ga ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi” (Ayyukan Manzanni 2:22, 23).

Shaidar Annabawa

Cikin littattafan annabci, annabce-annabce masu yawa sun faru a game da al’amuran da suka danganci mutuwar Almasihu a kan gicciye. Waɗannan annabci kuwa duka sun cika.

- An sayar da Yesu a bakin azurfa talatin, aka kuma sayi gonar mai tukwane da wannan kuɗin (Zakariya 11:13).

- Aka ƙusance ƙafafunsa da hannuwansa a kan gicciye (Zubura 22:16, 17).

- Aka jijji masa rauni (Ishaya 53:5).

- Aka yi masa bulala ƙwarai da gaske (Zabura 129:3).

- Ya sha wuya a shiru-shiru (Ishaya 53:7).

- Suka duke shi, suka tofa yau a fuskarsa (Ishaya 53:3, 4, 8).

- Aka yi masa ba’a (Zabura 22:6-8).

- Uban ya yashe shi (Zabura 22:1).

- Aka ba shi ruwan tsami don ya sha (Zabura 69:21).

- Sojoji suka jefa kuri’a a kan rigunansa (Zabura 22:18).

- Suka soki kwiɓinsa da māshi (Zakariya 12:10).

- Ya mutu a tsakanin ɓarayi biyu, aka kuma binne shi tare da masu arziki (Ishaya 53:9).

Sanarwar Yesu

Sau da dama, Almasihu ya yi ta sanar da almajiransa a game da saƙonsa na ceto yana bukatar sai an gicciye shi. An rubuta waɗannan faɗi cikin Matiyu 17:21; Marku 8:31; Luka 9:22; da kuma Yahaya 3:14, 15.

Tashin Almasihu Daga Cikin Matattu

Kwana uku bayan an gicciye shi, sai mafi girma daga cikin dukan mu’ujizai ya faru. Almasihu ya tashi daga cikin matattu. Littafi Mai Tsarki yana faɗa mana, “To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya, da ɗayar Maryamu, suka je ganin kabarin. Sai Kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala’ikan Ubangiji ne ya sauko daga sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai. Kamanninsa na haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kumar dusar ƙanƙara. Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu. Amma sai mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa” (Matiyu 28:1-6).

Shaidar Tarihi

Wasu takardun tarihi sun shaida cewa an gicciye Yesu. Daɗaɗɗun tarihi, na Al’ummai da na Yahudawa duka, sun shaida tarihin gicciye.

Takitus Ba’al’umme (A.D. 55) ya bayyana dalla-dalla yadda a ka gicciye Yesu, har da irin wahalar da Yesu ya sha.

Josefus Bayahude, an haife shi ’yan shekaru Kaɗan bayan an gicciye Almasihu, ya rubuta tarihin al’ummar ƙasarsa har kundi goma sha biyu. Cikin ɗaya daga cikin kundayen nan, ya rubuta cewa, an gicciye Yesu bisa ga umarnin Bilatus.

Lukiyas Bahellene (A.D.100) ya rubuta labarin Almasihu da Kirista. Ya ce, “Har yanzu Kirista suna bauta wa babban mutumin nan wanda aka gicciye cikin Falisɗinu saboda ya kawo sabon addini a duniya.”

Shaidar Alamar Gicciye

Wani littafi mai tsarki na Yahudawa da ake kira Talmud, shi ma yana shaidar gicciyen Almasihu. A littafinsa na 1943, a shafi na 42, ya ce, “An gicciye Yesu kwana ɗaya kafin Idin Ƙetarewa, domin shi mai sihiri ne, wanda ya fito don ya ruɗi Isra’ila ya kuma ɓadda su.”

Shaidar Abubuwan da Suka Biyo Baya

Kirista suna Cin Jibin Ubangiji don su riƙa tunawa da gicciyen Almasihu, shaida ce ta zahiri domin dukan zamanai cewa, Yesu ya mutu a kan gicciye.

Gicciye Cikin Islama

Idan mun yi nazarin Kur’ani, za mu ga cewa, littafin nan yana musun gicciyen Almasihu, amma ba MUTUWARSA ba kafin hawansa zuwa sama. Akwai nassoshi uku da suke magana a game da mutuwarsa, wasu biyu kuma suka nuna cewa an kashe shi ne.

A. “Kuma aminci ya tabbata a gare ni a ranar da aka haife ni da ranar da nake mutuwa da ranar da ake tayar da ni ina mai rai” (Suratu Maryam 19:33).

B. “A lokacin da Ubangiji ya ce: ‘Ya Isa! Lalle ni mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kafirta...’” (Suratu Al-Imrana 3:55).

C. “Kuma a lokacin da Allah ya ce: ‘Ya Isa ɗan Maryamu! Shin kai ne ka ce wa mutane, “Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautawa biyu, baicin Allah”?’... (Isa) Ya ce; ‘Ban faɗa musu ba, face abin da Ka umarce ni da shi, wato: “Ku bauta wa Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku... sa’an nan a lokacin da Ka Karɓi raina, Ka kasance Kai ne mai tsaro a kansu”’ (Suratul Maida 5:116, 117).

D. “Kuma lalle ne, hakika, Mun bai wa Musa Littafi, kuma Mun biyar daga bayansa da wasu manzanni, kuma Muka bai wa Isa ɗan Maryamu hujjoji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Ruhu Mai Tsarki. Shin fa, ko da yaushe wani manzo ya je muku tare da abin da rayukanku ba su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashewa” (Suratul Baƙara 2:87).

E. “Waɗanda suka ce: ‘Lalle ne Allah ya yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi imani saboda wani “manzo sai ya zo mana da Baiko wanda wuta za ta ci.” Ka ce: ‘Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabanina, da hujjoji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance masu gaskiya?’” (Suratu Al Imrana 3:183).

Ra’ayoyin Masharhantan Kur’ani

Al-Baidawi ya ce, “Wata ƙungiyar Yahudawa suka yi wa Yesu da uwarsa jafa’i, don haka ya la’anta su, Allah kuma ya maida su suka zama birai da aladu. Yahudawa sun yarda su kashe shi, amma Allah ya gaya masa cewa, zai ɗauke shi sama. Yesu ya ce wa abokansa: ‘Wanene cikinku zai yarda ya bayyana da kamannina, don su kashe su kuma gicciye?’ Sai ɗaya daga cikinsu ya yarda, to, sai aka kashe shi aka kuma gicciye.”

“Wasu suka ce lokacin da Yahudawa suka kama Yesu, sai suka sa a tsare shi, amma sai aka ɗauke shi sama ta hanyar mu’ujiza. A lokaci guda, Allah ya ba masu tsaron wani mai kama da Yesu. Suka ɗauke shi maimakon Yesu don su gicciye shi, yana ta ihu, ‘Ba ni ne Yesu ba.’”

“Wasu suka ce Yahuda, mabiyin Yesu, mai riya ne. Ya zo tare da Yahudawa don ya nuna musu inda Yesu yake. Duk da haka, Allah ya sa ya yi kama da Yesu, sai Yahudawa suka kashe shi a maimakon Yesu” (Baidawi II, 127, 128).

Cikin littafin Al-Tabari mai suna JAMI AL-BAIAN, ya ambaci labaru da dama. Cikin ɗayan labarun, Wahab Ibn Munabbeh ya faɗi cewa, “Yesu ya shiga wani gida tare da almajiransa goma sha bakwai. Yahudawa suka kewaye gidan, da suku shiga, sai Allah ya sa dukan waɗanda suke cikin gidan suka zama kamar Yesu. Yahudawa suka ce, ‘Ku masu sihiri, in baku faɗa mana a cikinku wanene Yesu ba, to, za mu kashe ku duka.’ Tun da fari Yesu ya tambayi almajiransa, “Wanene a cikinku zai sayi firdausi?” Sai ɗayansu ya ce, ‘Ni ne Yesu,’ sai aka kashe shi.”

An ba da labaru da dama masu kama da wannan cikin sharhohin su Sanawi, Ibn Kuthair, Galalan da Zamakhshari. Amma kafin mu rufe wannan batu, dole mu gama tattaunawar da ɗauko faɗar Fakhr al-Din Ar-Razi, wanda ya kuskure labarin “ɗaukar kamannin Yesu”. Cikin sura 3:55, wadda ta ce, “Ya Isa! Lalle Ni mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni,” Razi ya yi sharhi haka, “Mun fuskanci matsala. Kur’ani ya faɗi haka ne lokacin da Allah ya ɗauke Yesu sama, ya kuma sa wani ya yi kama da Yesu: ‘Ba su Kashe shi ba, ba su kuwa gicciye shi ba, amma su sun ɗauka haka ne.’ Muna da labaru masu rikitarwa a kan wannan. Wasu suka ce Allah ya sa maƙiyan da suka bi da Yahudawa zuwa wurin da Yesu yake suka yi kama da Yesu. Wasu labaran suka ce, ɗaya daga cikin almajiransa ne aka sa ya zama kamar Yesu, sai aka kashe shi maimakon Yesu. Sa wani ya zama kamar Yesu, wannan ya haddasa matsaloli kamar haka:

“1. In muka yarda da ra’ayin cewa wani ya ɗauki kamannin wani, to, mun yarda da an yi ruɗi ke nan. Sa’an nan, alal misali, idan na ga ɗana sai in yi shakka cewa ko shi ainihin ɗana ne; zai yiwu sojan gona aka yi. Ta haka hankali ba zai iya gaskata abin da rai yake ji ba. Wannan zai kai mu ga tunanin cewa, abokan annabi, waɗanda suka gan shi yana koyarwa, ba za su iya tabbatar da cewa da gaske shi annabi ne ba. Zai yiwu ya dai yi kama da annabi ne. Ka’idar hankali/tunani ta ruguje ke nan. Ya kamata mu tabbatar cewa tsarin sassalar masu ba da bayanan waɗanda suka isa a dogara da su ne. Zai yiwu mai ba da bayani na fari ya yi kuskure domin abin da ya gani kamanni ne kaɗai. A taƙaice, yarda da wannan ra’ayi zai sa mu fara da ruɗi mu kuma ƙarasa da soke/share annabce-annabce.

“2. Allah ya umarci Jibra’ilu ya kasance tare da Yesu a koyaushe. Abin da mafiya yawan masharhanta suka ce lokacin da suke tattaunawa a kan ayar, ‘Kuma Muka ƙarfafa shi da Ruhu Mai Tsarki’ (Suratul Ba ƙara 2:87). Suka ƙara da cewa, gefen ɗaya daga fukafakan Jibra’ilu ya isa ya lura da ɗan Adam. To, don me Jibra’ilu bai iya tsare Yesu daga Yahudawa ba? Yesu kuma ya iya tada matacce: To, me ya hana ya ceci kansa daga Yahudawa masu kisan sa, da masu nema su ji masa, ko ma ya buga su da shanyewa ko wasu naƙasa don ya sa su kāsa fuskantarsa.

“3. Da Allah zai iya ceton Yesu ta wurin ɗauke shi zuwa sama. To, in haka ne, ina baicin lanƙaya kamanninsa ga wani? Ashe, wannan ba zai yi sanadin mutuwar wani a banza ba ke nan?

“4. In Allah zai sa wani ya yi kama da Yesu, sa’an nan kuma ya ɗauke Yesu, har mutane su zaci cewa wannan mutumin Yesu ne, a gaskiya kuwa ba Yesu ba ne. Wato ke nan Allah ya ruɗi mutane ya ɓadda su, wannan kuwa bai dace da riƙe ayyukansa na hikima ba.”

“5. Ko da yake suna ƙaunar Yesu ƙwarai, Kirista a duk fāɗin duniya sun shaida cewa sun ga an kashe Yesu an gicciye shi. In mun yi musun wannan, muna musun jerin izni ke nan. Musun wannan ya zama sèkar annabci ke nan, har ma da tarihin Muhammadu ke nan, da na Yesu da kuma na sauran annabawa.”

“6. Wannan jerin sadarwa yana faɗa mana ke nan cewa, wanda aka gicciyen nan ya rayu lokaci mai tsawo. Idan ba Yesu ba ne, amma wani ne dabam, ai, da ya ce, ‘Ba ni ne Yesu ba. Ni wani ne dabam.’ Da ya faɗi haka a bainar jama’a, da kuma mutane da yawa sun sani. Amma haka bai faru ba; wannan ya nuna cewa, al’amuran sun bambanta daga abin da kuke iƙirari” (Al-Kabir 12:99).

MASU HARZUƘA YAƘI

Zuwa ga aboki, cikin wasiƙarka ka ce, “Duniya ba ta fuskaci hallaka ba sai da Kiristan Yammacin duniya suka ɗauki makaman yaƙi.”

Tarihi ya ɓalɓaltar da kai cikin wannan matsala; yaƙe-yaƙe da hallakawa sun kasance tun dubban shekaru kafin bayyanar Kristanci. Amma kafin mu ƙarasa wannan batu, muna bukatar mu gwama sanadodin yaƙi cikin Kristanci da kuma cikin Islama.

Cikin Kristanci

Bishara/Linjila tana gaya mana cewa, lokacin da Yesu ya ji an kashe Yahaya Maibaftisma, sai ya bar Nazarat ya zo ya zauna cikin Kafurnahum. Ya zaga dukan Galili yana warkar da kowane irin rashin lafiya, yana kuma wa’azin albishir mai daɗi na mulkin Allah. Suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, ko waɗanda aljannu sun shige su, ya kuwa warkar da dukansu.

Lokacin da Yesu ya ga taron mutane, sai ya hau dutse, ya koya musu yana cewa, “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin sama nasu ne. Albarka tā tabbata ga masu nadama, domin za a sanyaya musu rai. Albarka tā tabbata ga masu tawali’u, domin za su gāji duniya. Albarka tā tabbata ga masu Kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu. Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah. Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su ’ya’yan Allah. Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin sama nasu ne. Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta saboda ni. Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku” (Matiyu 5:3-12).

“Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su. Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome” (Matiyu 5:17, 18).

“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuma, za a hukunta shi. Amma ni ina gaya muku, kowa ke fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan’uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, “Kai wofi!” hakkinsa shiga Gidan Wata’” (Mat. 5:21, 22).

“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita” (Matiyu 5:27, 28).

An kuma ce, ‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.’ Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina” (Matiyu 5:31, 32).

“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse kan ƙarya, sai dai ka cika wa’adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’ Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah, ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce Birnin Babban Sarki. Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba. Abin da duk za ku faɗa, ya tsaya kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, daga Mugun ya fito” (Matiyu 5:33-37).

“Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’ Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. In kuma wani ya yi ƙarar ka da niyyar karɓe taguwarka, to, bar masa mayafinka ma. In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma” (Matiyu 5:38-41).

“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka.’ Amma ni iya gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci” (Matiyu 5:43-45; da kuma 6:1-7:29).

Cikin Islama

Tarihi yana faɗa mana cewa Omar Ibn el-Khattab, shi ne ya haddasa kafa ƙasar Musulmi. Ya bi waɗannan ka’idodi:

A. Addinin al’ummar ƙasa Islama ne. “Kafin Annabi ya mutu ya ce addini biyu ba za su kasance cikin yankin ƙasar Larabawa ba” (Littafin da ake kira a Turance ‘Life of the Prophet’ wato Rayuwar Annabi, wanda marubucinsa shi ne Ibn Hisham III, 813).

B. Larabawan da suke ba cikin yakin Ƙasar Larabawa ba dole su ci gaba da zama ’yan Jihadi, wato ƙungiyar mayaƙan addini.

C. Ayoyi da dama daga Kur’ani sun ba da iznin yaƙi, sun kuma ƙarfafa yin faɗa:

– “Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da muminai a kan yaƙi. Idan mutum ashirin masu haƙuri sun kasance daga gare ku, za su rinjayi metan (ɗari biyu), kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, za su rinjayi dubu daga waɗanda suka kafirta, domin su, mutane ne, ba su fahimta” (Suratul Anfal 8:65).

– “Ku yaƙi waɗanda ba su yin imani da Allah, kuma ba su imani da Ranar Lahira, kuma ba su haramta abin da Allah da Manzonsa Suka haramta ba, kuma ba su yin addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littafi, har sai sun bayar da jiziya da hannu, kuma suna ƙasƙantattu” (Suratul Tauba 9:29).

– “Kuma ku yaƙe su inda kuka same su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga Kisa” (Suratul Baƙara 2:191).

– “Kuma ku yaƙe su har ya zama wata fitina ba za ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah, Sa’an nan idan sun hanu, to, babu tsokana face a kan azzalumai” (Suratul Baƙara 2:193).

– “Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne su a wurin Ubangijinsu. Ana ciyar da su” (Suratu Al Imrana 3:169).

– “Saboda haka Ubangijinsu ya karɓa musu cewa, ‘Lalle ne Ni, ba zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashinku daga sashi. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu, kuma aka cutar da su daga cikin hanyata, kuma suka yi yaƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudana daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinsa akwai kyakkyawan sakamako” (Suratu Al-Imrana 3:195).

– “Suna tambayar ka game da Watan Alfarma. Ka ce: ‘Yin yaƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani ne daga hanyar Allah. Kuma kafirci da shi ne kuma da Masallaci Tsararre. Kuma fitar da mutanensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah.’ Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma ba su gushewa suna yaƙin ku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya” (Suratul Baƙara 2:217).

– “Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku yaƙi waɗanda suke kusantar ku daga kafirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cewa, Allah yana tare da masu taƙawa” (Suratut Tauba 9:123

– “Suna gurin ku kafirta kamar yadda suka kafirta, domin ku kasance daidai. Saboda haka kada ku riƙi wasu masoya daga cikinsu, sai sun yiwo hijira a cikin hanyar Allah. Sa’an nan idan sun juya, to, ku kama su, kuma ku kashe su inda duk kuka same su. Kuma kada ku riƙi wani masoyi daga gare su ko wani mataimaki” (Suratun Nisa 4:89).

Kristanci Da Yaƙi

Watakila Mr. Alawi ya karɓi Kristanci na ainihi, wanda Almasihu da hurarrun manzanninsa suka koyar, wanda kuma wasu ikilisiyoyi masu yawan gaske suke aikatawa a yau. Mun sani, ba kowane mai kiran kansa Kirista yake Kirista na ainihi ba. Yesu ma ya nuna wannan lokacin da ya ce, “Ba duk mai ce mini ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da ke cikin sama ke so”(Matiyu 7:21). Abin baƙin ciki, akwai Kirista masu yawan gaske da suke kara zube, wato ba na ainihi ba ne.

Don a iya gane Kirista na gaskiya, Yesu ya ce, “Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya cirar inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?” (Matiyu 7:16). Ya kamata mu auna kowace irin koyarwa ta wurin ka’idar da Yesu ya ba da. Ba za mu gane itacen kirki ta wurin ganyayensa ko furanninsa ba, amma sai ta wurin ’ya’yansa.

Cikin mafificiyar hikimarsa, Yesu ya ba da mafi girma da ɗan Adam zai sani domin zaman lafiya da fahimta: Ya ce, “Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, kuma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar Annabawa” (Matiyu 7:12). Wannan aya ce ake kira “Zinariyar Doka”, wato doka mafi daraja. Idan da mutane a ko’ina za su aikata wannan doka, da salama ta lulluɓe duniya, annabcin Ishaya kuma da ya cika, wanda ya ce, “Zai sulhunta jayayyar da ke tsakanin manyan al’ummai, za su mai da takubansu garemani, māsunsu kuma su mashe su wuƙaƙen aske itace” (Ishaya 2:4).

An ba da labarin wani da ya tambayi wani Bayahude malami da ake kira Rabbi Shamai don ya koya masa doka sa’ad da yake tsaye a kan ƙafa ɗaya. Shamai ya sallame shi hannu wofi. Sai mutumin nan ya je wurin wani malami, Rabbi Hillel ya tambaye shi kamar na farin. Hillel ya amsa masa, “Dokar ita ce: kada ka yi wa wasu abin da kai ba ka so a yi maka.” Yesu kuwa ya fasalta ta da maganar aikatawa”’ (wato ka yi yadda kake so a yi maka).

Na lura cewa ka husata a game da masu jihadi, ka ce duk Kristanci ne musabbabin wannan. Ban gane abin da kake nufi ba. ’Yan Jihadi ba a ɗaukar su a Kirista na ainihi, shaida mafi ƙarfi a kan wannan shi ne, sun kwashi ganima cikin Ikilisiyoyin da ake kira a Turance Eastern Orthodox Church. Babbar manufarsu kaɗai ita ce, su fāɗaɗa iyakokinsu.

Islama da Yaƙi

Masana tarihi suka ce, bayan ’yan watanni da saukar Musulmi a Madina, sai suka fara jin marmarin Makka. Muhammadu ne shugabansu, da shi suka shirya ɗaukar fansa a kan Kurashawa. Abin da ya ɗan dakatar da su daga ɗaukar fansa da sauri shi ne, suna fama da gina mahalli, da kuma neman kayan abincinsu.

Nan da nan suka fara kakkafa ƙungiyoyin mayaƙa. Ƙungiya ta fari Muhammadu ne ya shirya ta. Kawunsa, Hamza ben Abdul-Muttalib ne ya jagorance ta, tana da mahaya guda 30, dukansu daga Muhajereen (wato waɗanda suka tsere daga Makka zuwa Madina). Aka aike su bakin gāɓa zuwa wajen ‘Ais inda suka yi karo da Abu Jahl ban Hisham wanda ke jagorancin mahaya 300 daga Kurashawa. Nagdi ben Amro Al-Gahni ne ya raba su, ya hana su yaƙi.

Ibn Hisham ya gaya mana cewa Muhammadu ya jagoranci kai hare-hare fiye da sau ashirin da bakwai. Ga wasu nan:

Harin Wadan. Shi ne hari na fari

Harin Buwat, daga kusurwar Radwi

Harin Ashira, daga cikin Yanboa

Harin Badr, lokacin da suka kashe shugabannin Kurashawa

Harin Beni Salim, har suka isa Kadar

Harin Suwik, don su kashe Abu Sufian Ben Harb.

Harin Ghatfan

Harin Beni al Nadeir

Harin Paraa daga Bahran

Harin Uhud, lokacin da aka kashe wani gwarzon Musulmi

Harin Zatal-Rukaa, daga Nakhl

Harin Badr na ƙarshe.

Harin Domat al-Gandal

Harin Tsanya (ko hanyar ruwa)

Harin Beni-Kwaraiza

Harin Beni Lehian

Harin Zi-Kird

Harin Beni al-Mustalak

Harin Hudaibia

Harin Khaiber

Harin Amrat al-Kadaa

Harin Al-Fath

Harin Hunein

Harin Al-Taif

Harin Tabbuk.

Ibn Hisham ya gaya mana cewa Muhammadu ya yi yaƙi shi da kansa cikin hare-hare guda tara, daga cikin waɗannan: Badr, Uhud, Tsanya, Kwaraiza, Mustalak, Khaiber, Fath, Aunein da kuma Taif (Al-Sira daga Ibn Hisham, kundi na III da na IV, an buga a Alkahira, 1936).

Yaƙi Gāba da Ridda

Bayan mutuwar Muhammadu, sai wasu kabilu a kudu maso gabas na Kasashen Larabawa suka watsar da addinin Islama. Abokan annabi suka niyyatar da Abubakar don su aika da mayaƙa don su yaƙi masu ridda. Ana cikin haka, Halifa dai ya dāge a kan a aika da mayaƙan Usama ben Zaid don su ci Suriya. Ya ce, “Ba zan saukar da tutar da annabi ya ɗaga ba.” Abokan annabi suka kafa wata rundunar mayaƙa ƙarƙashin jagorancin Khalid Ibn Al-Waleed. Shi ya iya komo da kabilun gabashi da na kudanci, da na tsakiyar ƙasar Arabiya cikin Islama, da kuma wasu masu ridda daga Yemen, da Najd, da kuma Yamama. Ta haka ne Khalid ibn Al-Waheed ya sami muƙamin “Takobin Islama”.

Ruhun hargitsi yana nan cikin kabilun da suka tattaru cikin Islama, dole kuma su sami hanyar yin hargitsin. Dalilin ɓarkewar sababbin yaƙe-yaƙe ke nan. Shekara guda kafin mutuwar Abubakar, sai sojojin Musulmi suka fara yaƙinsu na fāɗaɗa daularsu.

Zan bar ku da tarihi don ku ga yadda yaƙe-yaƙe ne abokan tafiyar addinin Islama, da kuma hanyar yaɗuwarsa.

Tsananta wa Musulmi Marasa Rinjaye

Cikin wasiƙarka ka ambaci cewa, jama’ar Musulmi marasa rinjaye cikin ƙasashen Kirista an tsananta musu, alhali kuwa Kirista marasa rinjaye cikin kasashen Musulmi suna samun hakkinsu daidai.

Ban yarda da kai ba. A ƙasar Amerika Musulmi marasa rinjaye suna da cikakken ’yancin yin ayyukan addininsu. Muryar Amerika tana watsa shirye-shiryen addinin Musulunci da laccoci iri iri. Wani malamin tauhidin Islama, Maher Hathout, ya ambaci ayyuka domin farfagandar Islama cikin jama’ar Kirista. Aikin Islama wanda ba bisa doka ba a Amerika shi ne yin mata fiye da ɗaya, shi ke nan abin da aka hana bisa ga doka.

Bisa ga laccar da Sheikh Tah Ramouli ya bayar a Lebanon, ya ce Musulmi a Jamus ta Yamma ba su iya samun inda za su yi bikin idin Adha ba, sai Kirista suka ba su aron majami’arsu suka yi bikin. Musulmi ba za su taɓa yin wannan ga Kirista ba. Shaidar wannan ita ce, wata ƙasar Larabawa ta Musulmi sun hana Kirista gina majami’a a yankin ƙasarsu.

Ka ce ko da shike Musulmi sun fi Yahudawa yawa, duk da haka ba su da wakilai cikin majalisar Ingila. Dalilin wannan shi ne, Yahudawa sun haɗa kai da murya ɗaya, Larabawa Musulmi kuwa suna riƙe da bambance bambancensu nan cikin Birtaniya. Muni fiye da wannan, wasu ƙasashen Musulmi sun aika mutanensu don su yi wa abokan hamayyarsu kisan gilla maimakon ƙoƙarin yin sulhu.

A game da Musulmi cikin ƙasar Filiffin (Philippines) kuwa: ’Yan juyin juye halin addini sun fi mai da hankali ga siyasa fiye da addini.

Ka yi maganar wanke ƙwaƙwalwa. Babu wani abu haka cikin Kristanci. Muna da jinin Yesu kaɗai da yake wanke zunubanmu.

Ka yi maganar Mr. Alawi ya fito daga ƙasƙantaccen iyali. Bari in faɗo abin da manzo Bulus ya ce: “Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku ’yan’uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka masu asali ma ba yawa. Amma Allah ya zaɓi abin da ke wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima, Allah ya zaɓi abin da ke rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa. Allah ya zaɓi abin da ke ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin ya shafe abubuwan da ke akwai. Wannan kuwa duk don kada wani ɗan Adam ya yi fāriya ne gaban Allah” (1Korantiyawa 1:26-29).

Bari in ƙara wani abu a game da waɗancan da ka kira “malaman tauhidi” waɗanda kake fāriya da su saboda sun zama Musulmi: Kristanci bai yi hasarar su ba. Manzo Yahaya ya yi magana a game da su lokacin da ya ce: “Sun dai fita daga cikinmu, amma da ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu babu namu a ciki” (1 Yahaya 2:19).

ZUNUBI

Ka yi ƙoƙarin rikitar da batun zunubi da rashinsa cikin Islama, duk da haka Kur’ani ya ba shi babban muhimmanci.

Ga yadda Kur’ani ya fasalta manufar zunubi:

Laifi (zunubi) yadda yake cikin: “Lalle Mu, Mun yi maka rinjaye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne. Domin Allah Ya shafe abin da ya gabata na laifinka da abin da ya jinkirta, kuma ya cika ni’imarsa a kanka, kuma ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya” (Suratul Fath 48:1,2).

Nauyi (Zunubi), yadda yake cikin: “Kuma Muka saryar maka da nauyinka, wanda ya nauyayi bayanka?”(Suratush Sharha 94:2, 3).

Kuskure (ratsewa daga hanya ko daga gaskiya), kamar yadda yake cikin: “Ashe, bai same ka maraya ba, sa’an nan ya yi maka makoma? Kuma ya same ka ba ka da shari’a, sai Ya shiryar da kai? Kuma ya same ka matalauci, sai Ya wadata ka?” (Suratud Duha 93:6-8).

Masu Aikata Mugunta, kamar yadda yake cikin: “Kuma a lokacin da Ubangijinka Ya kirayi Musa, ‘Ka je wa mutanen nan azzalumai’” (Suratush Shu’ara 26:10).

Ɗanyen Aiki (Zunubi), kamar yadda yake cikin: “Kuma ku bar bayyanannen zunubi da ɓoyayyensa. Lalle ne waɗanda suke tsiwurwurin zunubi za a sāka musu da abin da suka kasance suna kamfata” (Suratul An’am 6:120).

Zunubi, kamar yadda yake cikin: “Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi, sa’an nan kuma ya jefi wani barrantacce da shi, to, lalle ne ya tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne” (Suratun Nisa 4:112).

To, ka bar ni in ɗauki batunka: “Abu na fari da zai zo ga tunani a kan batun zunubi da tabbacin gaskata wajabci domin fansa, shi ne ragoncin arna ga taɓuka wani abu domin cetonsu.”

In za a auna waɗannan kalamai cikin hasken hurarriyar Maganar Allah, zai zama tabbaci cewa sun fito daga wurin wani wanda ya watsa ƙasa a idanun mutane don ya hana su iya ganin gaskiya. Cikin Romawa muna karanta cewa, “To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi” (Rom. 5:12).

Wasu masana Ussan ilimi suka ce, an haifi mutum da tsarki. Idan yana zama cikin lalataccen halin zaman jama’a, shi ma zai shafu da lalacewar tun da cikin mutum akwai kashin ilhama wanda ko da yake yana nufin kirki, duk da haka yana ɗauke da mugun nufi.

Zunubi Gādo Ne

Mun koyi cewa babu halittar da za ta iya haihuwar wata halitta dabam. Saniya ba za ta haifi rago ba, kamar yadda Almasihu ya ce, “Mutane ba za su iya, tsinkar inabi daga cikin ƙaya ba”. Haka yake ga mutum, domin Adamu, uban talikai ya yi wa Allah tayarwa. Allah kuma ya kori Adamu daga cikin Firdausin Tsarki ya je ya zauna a ƙasar da ta la’anta saboda zunubi. A kan wannan Adamu ya haifi zuriya waɗanda bisa ga hali, su kuma korarru ne, don sun rasa gādonsu na Firdausi. Littafi Mai Tsarki ya kafa wannan gaskiyar lokacin da annabi Dawuda ya ce “Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni, mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni” (Zabura 51:5).

Muna kuma da mayaƙin bangaskiya, wanda ya ce, “Kamar yadda yake a rubuce cewa, ‘Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya, babu mai fahimta, babu wani mai neman Allah. Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya, babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya’” (Romawa 3:10-12).

Akwai wani Shehin Malamin Ingilishi, mai suna Huxley, ya rubuta cewa, “Ban taɓa sanin bincike mai wuyar wannan ba, wato kamar na binciken halittar ɗan Adam ta hanyar kasancewa daga mataki zuwa mataki kafin ɗan Adam ya zama yadda ake ganin sa yanzu, gama tun daga bayan duhun tarihi mun ga cewa, mutum yana ƙarƙashin wani irin iko dake daga cikinsa wanda yake mulki da shi da wasu irin ƙattan ikoki... Shi rarrauna ne, makaho abin da ikokin nan suke garawa zuwa hallaka, kuma yana ƙarƙashin ikon tsoro marar matuƙa, kasancewarsa ta haziƙanci ta zamar masa nauyin kaya, yana kuma lalatar da jikinsa da damuwa iri iri, da wahaloli. Bayan dubban shekaru yana nan yadda yake, yana ta yaƙi, yana ta tsanantawa, ya komo yana ta kukan mutuwarsa kaɗai yana kuma haƙa kaburburansu...”

Sai mutum ya saurari waɗannan shaidu na zaƙin baki daga tarihi kafin ya iya kama wannan gaskiyar? Ashe, bai isa ba mutum ya dubi zurfin halittar kansa don ya gano ya kuma koyi jin cewa ɗabi’un zunubi suna nan zaune a cikinsa?

Ba shakka, kasancewar zunubi cikin ran kowane mutum sanannen abu ne, saboda halin ɗan Adam na lalacewa a fili yake, domin ɗan Adam ya kāsa ga dokar halin kirki ta wurin ƙoƙarinsa. Ko ma ya tuba, akwai hatsarin komawa da baya in ba tare da taimakon Allah ba ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

A taƙaice, dubi tarihin zunubi cikin zamanun da suka shige. Za ka sami tabbas a fili cewa, akwai niyyar aikata mugunta kullum a cikin mutum. Bayyanar farko ta irin wannan niyya ita ce lokacin da Kayinu ya kashe ƙanensa Habila. Dukansu ’ya’yan Adamu ne.

Na yi baƙin ciki ƙwarai lokacin da na karanta Kalmominka cike da gatse (ba’a) a game da zunubi da fansa, fanni biyu da aka koyar cikin Linjila. Ka ce, “Ana iya taƙaice gaskatawar Kirista cikin almarar zunubi da fansa ta wurin gicciye.” Da zai fiye maka kyau in da ka tambayi Kirista su bayyana bisa ga umarnin da aka yi wa Muhammadu cikin Kur’ani, mai cewa, “Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, face waɗansu mazaje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai Ku tambayi mutanen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba” (Suratun Nahl 16:43). Fassarar ayan nan bisa ga Jalalaini “Mutanen Matuni sune da ikon Attaura da Linjila.” An ci gaba da cewa, “waɗannan ne waɗanda Muka bai wa Littafi da hukunci da annabci. To, idan waɗannan (Mutane) sun kafirta da ita, to, hakika, Mun wakkala wasu mutane gare ta, ba su zama game da ita kafirai ba. Waɗannan ne Allah Ya shiryar, saboda haka ka yi koyi da shiryarsu. Ka ce: ‘Ba ni tambayar ku wata ijara. Shi (Alƙur’ani) bai zama ba face tunatarwa ga talikai’” (Suratul an,am 6:89, 90).

Batun zunubi da gyara ta hanyar fansa kabari ne. Kafin a shiga wannan da zurfi, ba wani zaɓi cikin shirya tushen batun, amma a ambaci manyan al’amura cikin Littafi Mai Tsarki daga halittar mutum zuwa al’amuran da suka wukana cikin sa ƙaunar Allah domin ceton duniya.

Na Fari, Fāɗuwa

Littafi Mai Tsarki yana koya mana cewa, Allah ya halicci mutum cikin kamanninsa, cikin siffarsa, ya kuma ba shi alkawarin rai bisa ga sharaɗin cikakkiyar biyayya ga dokokinsa. Cikin Littafi Mai Tsarki muna karanta cewa: “Hakanan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da mace ya halicce su. Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, ‘Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da ke da rai da ke kai da kawowa cikin duniya’... Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta. Ubangiji Allah ya yi wa mutum umarni, ya ce, ‘Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace da ke gonar, amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle’” (Farawa 1:27, 28; 2:15-17).

Adamu ya zauna har tsawon wani lokaci cikin firdausin Aidan cikin zaman tsarki, ya ji daɗin zumuncin ruhaniya tare da Ubangiji Allah. Wannan zumunci kuwa ya cika zuciyar Adamu da murna. Adamu ba shi da laifi, rashin laifinsa ya jawo shi kurkusa da zuciyar Allah. Shi kuma cikakke ne, shafaffe kuma da ruhun Allah. shi mai bi ne na gaskiya, bangaskiya kuma ita ce hannun da aka miƙa a karɓi albarkun Allah. Shi adali ne, domin cikin adalci ne mutum yake nuna hasken Allah.

Amma duk da waɗannan dama na ruhaniya da Adamu ya ke jin daɗinsu, Allah ya yarda a jarraba uban talikai. Manufar wannan gwaji ita ce: Ko Adamu zai riƙe matsayinsa na biyayya ga Allah wanda ya ba shi dukan waɗannan albarku? Wato nufin Allah cikin wannan gwaji na uban talikai shi ne, domin a koya masa cewa, akwai kāriya tsakanin nagarta da mugunta, ƙetare wannan kāriya kuwa laifi ne. Ya yi wannan cikin hanyar kwatanci ta wurin sa itacen da ya hana a ci ’ya’yansa cikin lambun, yana nan kuwa kusa da Adamu.

Sauƙin wannan jarrabawa a fili yake lokacin da Shaiɗan ya zo da jarabarsa. Maruɗin ya nufo Hauwa’u kamar wani mashawarci, yana kishin nagarin iyaye na fari. Tambayarsa ta fari a gare ta ta ruɗi ce mai sauƙi kuma, ya ce, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itace da ke a gonar ba?’” (Farawa 3:1). A nan, tambayar tana bayyana mamaki, da rashin amincewa a lokaci guda. Kamar dai mugun yana cewa, “Na yi mamaki – mamaki ƙwarai da har Allah zai faɗi wannan!”

Lokacin da Hauwa’u ta saurari wannan daɗin baki da Shaiɗan ya shirya, sai shakka ta shere ta a game da nagarin dokar Allah. “Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta” (Farawa 3:5). Kalaman magabcin nagarta kamar suna daidai, kuma akwai rinjayarwa, yana nuna yadda Allah bai yi adalci ba da ya hana ita da mijinta su sami sani daidai da na Allah. Zuciyar macen ta cika da shakka, nan da nan ta miƙa wuya ga jarabar Shaiɗan. Karo na fari ke nan da Hauwa’u ta ga itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ga idanu, ga jan hankali. Sai ta tsinka ta ci, ta kuma bai wa mijinta shi ma ya ci tare da ita (Farawa 3:6-8). Ta haka ne iyayenmu na fari suka fāɗi. Macen ta fāɗi lokacin da ta yi shakkar amincin Allah da nagartar dokarsa. Ta kai kanta inda bai kamata ta kai ba. Ta so ta sami sani daidai da na Allah, ta kuma shigar da mijinta. Ta yin haka ne Adamu ya share alkawarinsa da Allah, ya wuce gona da iri. “Zunubi tawaye ne” (1 Yahaya 3:4).

Littafi Mai Tsarki yana cewa, “Sakamakon zunubi mutuwa ne” (Romawa 6:23). Don haka, Adamu da Hauwa’u sun fāɗa ƙarƙashin hukunci, daidai yadda Allah ya gargaɗe su tun da fari. “Gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle” (Farawa 2:17). Wannan mutuwa ba ta jiki ba ce wadda za a tura gawar cikin kabari, amma ana maganar rai ya zauna cikin azaba har abada.

Lokacin da Adamu ya fāɗi ya zama a ƙarƙashin hukunci iri iri na Allah ke nan, “Ga Adamu kuwa ya ce, ‘Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ’ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la’antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka. Ƙayayuwa za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma” (Farawa 3:17-19).

Bayan wannan hukuncin, sai Ubangiji ya kori Adamu da matarsa, Hauwa’u daga gonar Aidan. Sun yi ta ragaita a duniya, suna noma. Suna da ’ya’ya, amma, ’ya’yan ma, ba a bar su su shiga firdausin ba.

Romawa 5:12, “To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi.”

Wasu masana ussan ilimi suka ce, an haifi mutum da tsarki, amma da ya zauna cikin lalataccen wuri kewaye da shi, sai shi ma lalacewar ta shafe shi, zunubi ya shige shi. Gaskiya ne, lalacewar wuri takan taimaka wajen yaɗa zunubi, amma an haifi mutum da nufe-nufensa da dama, wasu kuwa na mugunta ne.

Mun gane daga koyarwa ta allahntaka cewa Allah ya yi alkawarin rai da Adamu ba don Adamu kansa ba, amma domin zuriyarsa ne, ta haka Adamu ya zama wakilin dukanin ’yan Adam, bisa ga Maganar Allah, “Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da kowa saboda Almasihu” (1Korantiyawa 15:22).

“To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zamar wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai. Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta biyayyar Mutum ɗaya za a maida masu ɗumbun yawa masu adalci” (Romawa 5:18,19).

Ka yi tambaya cewa, “Me ya faru da waɗanda suke tun kafin zuwan Almasihu, a cikinsu akwai manzanni da annabawa da suke ƙaunatattun Allah? Ba su karɓi, ko ba da gaskiya ga Ɗan Allah ba duk da shike ana bukatar yin haka ɗin, su ma ba su san gicciye ba?”

Amsa tambayan nan sai mun koma ga lokacin da Adamu ya fāɗi aka kuma kore shi. Cikin Farawa 3:7, 8 ana cewa, “Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa’an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura. Da suka ji Allah yana yawo a gonar da sanyin la’asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar.”

A nan mun ga sakamakon farko na zunubi shi ne kunya, na biya shi ne tsoro, na uku hukunci. Littafi Mai Tsarki yana gaya mana, “Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su” (Farawa 3:21). Wannan ya nuna cewa an yanka dabbobi ke nan cikin Firdausi. Ba mu da wata shaida mai nuna cewa mutum yana cin naman dabbobi a lokacin can, ko abinci mai nama cikin Firdausi, amma suna morar ganyaye da ’ya’yan itatawa da wasu kayan lambu don abinci. Maganar Allah ta nuna wannan sa’ad da ta ce, “Allah kuwa ya ce, ‘Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da ke bisa dukan fuskar duniya, da kowane itace da ke da ƙwaya cikin ’ya’yansa su zama abincinku” (Farawa 1:29). Ta haka, fatun da aka samu daga dabbobin hadayu ne waɗanda Adamu ya mora cikin hadayunsa. Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki yana faɗa mana cewa Allah ya kori Adamu da matarsa daga Lambun Aidan, ya je ya yi noma a ƙasa inda daga gare ta ne aka yi shi, Allah kuma ya sa Kerubim (Mala’ika) da takobi mai harshen wuta daga gabashin Aidan don ya yi gadin hanyar zuwa wurin da itacen rai yake.

A taƙaice, Littafi Mai Tsarki yana koyar da cewa tarayyar shugabancin Adamu ga zuriyar ’yan Adam ita ta kawo wahaloli a kan zuriyarsa kuma.

Adamu kuma wakili ne na zuriyarsa, haka kuma alkawaran da Allah ya yi masa sun shafi zuriyarsa. Lokacin da Allah ya fitar da Adamu daga Lambun Aidan, wannan hukuncin ma ya shafi zuriyarsa. An haife su cikin duniya wadda aka la’anta saboda shi, suka zama bayin mutuwa kamar yadda shi ya zama ƙarƙashin mutuwa. Haka kuma raɗaɗin naƙuda ya zama hukuncin da aka ɗora wa Hauwa’u, ya kuma shafi kowace mace ɗiyar Hauwa’u. Wani shahararren masani mai suna Abu El Alaa ya gane gaskiyar batutuwan nan, har ya ce, “Wannan aikin, da ubana ya yi mini, ni kuma dole in sha raɗaɗin, ko da shike ban yi wa kowa irin wannan ba.”

Wajen shekara dubu biyu da suka wuce manzo Bulus ya yi makamancin wannan kukan. “Mun dai san Shari’a aba ce ta rahu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi. Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi. To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari’a aba ce mai kyau. Ashe kuwa, ba ni nake yin sa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne. Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da ke daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwa ne babu. Nagarin abin da nake niyya kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa. To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yin sa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne. Sai na ga ashe, ya zamar mini ka’ida, in na so yin abin da ke daidai, sai in ga mugunta tare da ni. Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da Shari’ar Allah. Amma ina ganin wata ka’ida dabam a gaɓoɓina, wadda ke yaƙi da ka’idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ka’idan nan ta zunubi, wadda ke zaune a gaɓoɓina” (Romawa 7:14-23).

Sakamakon Zunubi

Littafi Mai Tsarki yana cewa, “Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu” (Romawa 6:23). Kuma, “ ...amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle” (Farawa 2:17). Hakika, Adamu da Hauwa’u sun mutu a ruhunce, sun kuma rasa zumuncin nan da Mahaliccin nan nasu mai ƙauna, ba su kuma jin marmarin kasancewa a gabansa. Ina misalin bala’in wannan sheɗara, “a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.” Lokacin da Adamu ya ji yanke hukuncin nan, sai shi da matarsa suka ɓuya daga fuskar Ubangiji saboda zunubinsu. Saboda haka, ta wurin annabi Ishaya Allah ya ce, “Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku” (Ishaya 59:2).

Littafi Mai Tsarki yana koya mana cewa, halin Allah cikakke ne, cikin jauharinsa kuma akwai gaskiya da adalci, gaskiya da adalcinsa kuma ba su da iyaka; ya yanke wa Adamu hukuncin mutuwa a kan tayarwar da ya yi. Amma kamar yadda gaskiya da adalcinsa ba su sākewa, haka kuma ƙaunarsa ba ta sākewa. Ƙauna ce mai banmamaki wadda ba ta da iyaka cikin yin gafara. Ya bayyana wannan cikin maganarsa. “Ya Isra’ila, budurwa! Na kusace ki da madawwamiyar ƙaunata, ba zan fāsa amintacciyar ƙaunata a gare ki ba” (Irmiya 31:3). Saboda haka wannan irin ƙauna marar iyaka ita ce ta tsakaita don gatancin mutum, domin Allah ya ce, “Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra’ila?” (Ezekiyel 33:11). Wani sanannen lauya mai suna Prentice, lokacin da yake gama kāriyar wanda ake ƙara a kotu, sai ya ce, “Na karanta a wani littafi cewa, Allah, cikin madawwamiyar shawararsa, ya tambayi adalci, da gaskiya, da ƙauna ya ce, ‘In yi mutum?’ Sai adalci ya ce, ‘Babu, domin zai tattake dukan dokokinka ya raina su.’ Sai gaskiya ta ce, ‘Babu, kada ka yi mutum, domin zai ƙazantar da kansa ya bi kayan duniya masu daraja ta banza, ya yi ta faɗar ƙarairayi.’ Ƙauna kuwa sai ta ce, ‘Na sani zai zama duk abubuwan da kuka faɗa a kan mutum in an yi shi, amma duk da laifofinsa, da muguntarsa, ni na yarda in lura da shi, in bishe shi cikin dukan hanyoyin nan masu duhu, har in komo da shi gare ka.’”

Na riga na faɗa, sadakokin hadaya suna nan tun adun adun, duka kuma suna nuno, “Ɗan Rago na Allah, mai ɗauke zunubin duniya” (Yahaya 1:29). Muna karantawa daga nassoshi masu tsarki cewa, hadayar jini da Habila ya miƙa wa Allah , inuwa ce kaɗai ta fansa da ke zuwa. Shiri ne daga Allah wanda ya hure ya kuma aikata.

Mun karanta cikin Littafi Mai Tsarki cewa, da ruwaye suka ƙafe, sai Nuhu da iyalinsa suka fito daga cikin jirgin; aikin da ya fara yi shi ne gina bagade ga Ubangiji, ya ƙona hadayu da dukan dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, “Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi” (Farawa 8:20, 21).

Haka kuma ragon da Allah ya ba Ibrahim ya yi hadaya da shi a madadin ɗansa (Farawa 22:13) ba shakka shi ma alama ce ta babbar fansar da Allah ya ƙaddara ta hadayar Almasihu.

Ɗan ragon ƙetarewa ma wanda Allah ya umarci Isra’ila su yi hadaya, su kuma shafa jinin a madogaran ƙofafinsu, wannan ma kwatanci ne na Ɗan Ragon Ƙetarewa na Sabon Alkawari. Hadayar da aka yanka Ɗan Ragon Allah kamar yadda manzo Bulus ya bayyana, “Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da ya ke an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato Almsihu. Saboda haka sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da gaskiya” (1 Korantiyawa 5:7, 8).

Abubuwan da Mutane Suka Samu

Mutanen Allah Cikin Tsohon Alkawari sun ji daɗin rashin ƙarfin mutum, da kāsawar da shari’a ta yi wajen wanke mai zunubi ta kuma kwantar da lamirin mutum. Muna karantawa cikin littafin Ibraniyawa cewa, “Bisa ga wannan ishara akan yi ta miƙa sadaka da hadaya, amma ba sa iya kammala lamirin mai ibadar” (Ibraniyawa 9:9). Wato ke nan, tsarin Lawiyawa dangane da hadayu ba su fi inuwa ba mai nuna albarkun Sabon Alkawari.

A zamanin dā, muryar annabi Dawuda ta hau gaban Allah cikin kalmomin nan, “Ba ka son sadakoki, ai da na ba ka, ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa” (Zabura 51:16).

Cikin Ishaya ma Allah ya faɗa, “Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki. Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa’ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina? Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku” (Ishaya 1:11-13).

Mun gani cikin maganar annabi Amos cewa, “Na ƙi bukukuwanku na addini. Ina ƙyamarsu! Sa’ad da kuka kawo mini hadayun ƙonawa da hadayunku na tsaba, ba zan karɓa ba. Ba kuma zan karɓi turkakkun dabbobinku waɗanda kuka miƙa mini hadayun godiya ba. Ku yi shiru da yawan hargowar waƙoƙinku. Ba na so in saurari kaɗe kaɗenku da bushe bushenku. Sai ku sa adalci da nagarta su gudano a yalwace kamar kogin da ba ya ƙafewa” (Amos 5:21-24).

Babban abu cikin kalamanmu shi ne, in mun duba tarihin mutanen Isra’ila da kyau, za mu lura cewa, sukan juyo ga Allah ta hannun Musa da Joshuwa ta wurin hadaya. Da aka kai zamanin sarakuna, nan ma mun ga cewa hadayu suka ɗauke mafi yawan zarafinsu, domin a can mun ga an yi ta miƙa hadayar ƙonawa ba fāsawa, har wutar ba ta taɓa ɓicewa ba, haka yake musamman a zamanin Sulemanu. A wancan lokaci, an miƙa dubban hadayu, har ma mutum na iya cewa, a tarihin Isra’ila sa’ad da suke da halin biyayya, sun dage ne a kan sadakoki da hadaya. Duk da wannan littafin Ibraniyawa yana maganar Mai Ceto da wannan ƙarfafawa. “Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, ‘Hadaya da sadaka kam ba ka so, amma kā tanadar mini jiki. Ba ka farin ciki da hadayar ƙonewa, da kuma hadayar kawar da zunubai. Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,” Kamar yadda yake a rubuce a game da ni a Littafi. Sa’ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da sadaka, da hadayar ƙonewa, da hadayar kawar da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu,” wato irin waɗanda ake miƙawa ta hanyar Shari’a, sai kuma ya ƙara da cewa, “Ga ni, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon ne, don ya kafa na biyun” (Ibraniyawa 10:5-9).

Ruhu Mai Tsarki musamman ya ƙarfafa mana wannan yadda ba zai yiwu Allah ya yi kafara don mai zunubi ba don kawai ya miƙa hadayar dabba ba, sai dai don ta kwatanta wata hadaya dabam.

“Sai kuma ya ƙara da cewa, ‘Ga ni, na zo in aikata nufinka’. Ya kawar da na farkon ne, don ya kafa na biyun. Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak ba ƙari” (Ibraniyawa 10:9,10).

Yanzu bari in yi sharhi a kan wasu maganganun iƙirarin cewa, mutum zai sami koyarwa da dama ta arananci cikin rukunan Kirista:

1. Addinin Farisawa mai suna Mitras. Bisa ga zarginka, wannan addini ya iso Roma cikin shekara ta B.C 70, kuma babban batun addinin nan shi ne, Mitras matsakanci ne tsakanin Allah da mutum. Ashe, ka kāsa gane cewa dukan addinan arna sun gaskata cewa abin bautawarsu shi yake kai su kusa da Allah? In haka ne, zan so ka karanta Kur’ani Sura 39:3, inda ya ce, “To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓanta, ba Shi ba, (Suna cewa) ‘Ba mu bauta musu ba face domin su kusatar da mu zuwa ga Allah, kusatar sujada.’ Lalle Allah na yin hukunci a tsakaninsu ga abin da suka zama suna sāɓawa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kafirci.”

2. Labarin Ba’al. Na duba littattafan ma’ana da dama, na samu cewa ba’al wani allah ne na Kan’aniyawa mijin Ba’ala ko Asherah ko Ashtaraf. Shi allahn gonaki ne da ubangijin haihuwar amfanin gona da na dabbobi. Mutanen gabas masu naciya ne ga bautar Ba’al, suna yi masa sunjada sosai, har da miƙa hadayar mutum a kan bagadansa. Sukan zaɓi tuddai ko ƙolin duwatsu don samun kyawawan wurare. A nan sukan yi gine ginensu masu ƙawa, su kuma kÊɓe ga wannan, gunkinsu mai girma.

Littafi Mai Tsarki yana gaya mana cewa, Ba’al ya zama sanadin tuntuɓe ga ’ya’yan Isra’ila, gama suka karya dokokin Allah lokacin da suka shigar da Ba’al ya zama abin bautawa ta wurin Yezebel, Sarauniyar Ahab (1 Sarakuna 18:17-40).

A taƙaice, zan ce, bautar Ba’al ta yaɗu ƙwarai cikin mutanen Gabas a wancan lokaci. Saboda haka ne za a ga an ambace shi da sunaye iri iri, domin kowace al’umma takan mori sunan da jama’ar wurin suka sani. Kowane sunan yakan fara da kalmar Ba’al, ta ƙarasa da sunan ƙasa ko birnin da yake zaune; ko kuma a kira shi da wasu jauhari nasa, ga misali:

– Ba’alzebub, shi ne allahn ƙudaje shi ne kuma allahn Aktron.

– Ba’alfghur

– Cikin Lebanon an san shi da allahn rana, yana kuma da haikali masu yawa cikin Ba’albeck, wanda aka fi sani shi ne ‘Haikalin Rana’ Girkawa suka gina shi, yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan banmamaki guda bakwai a duniya.

– Ba’altamar, wannan shi ne allahn itatuwan kwakwa ko na dabino. Zai yiwu shi ne gumakan da aka yi da itacen dabino wanda wata kabilar Larabawa mai suna Huthayfa suka bauta wa. Wata shekara sai dabino bai yi ’ya’ya ba. Su kuwa suna jin yunwa ƙwarai har suka cinye gumakan nasu, wannan ya sa wani mawaƙi ya rubuta wani waƙe kamar haka, “Huthayfa ta cinye ubangijinta a lokacin yunwa da karayar arzikin ƙasa. Ba su ji tsoron Ubangijinsu ba, ba su ko kula da horonsa ko tagomashinsa ba.”

– Ba-aljad-wannan zango ne na Ba’al.

– Ba-alhazur-wannan ne Ba’al na sa’a (awa).

– Ba’alharmon-Ba’al na Dutsen Hermon.

– Ba’alzabul-Sunan Kan’aniyawa ne mai ma’ana Ba’al na juji

– Ba’alshalisha-ma’ana Ba’al na uku

– Ba’alsafoon-ma’ana Ba’al na arewa.

– Ba’almaraheem-ma’ana Ba’al na fashewa.

– Ba’alfaghur-allahn Ammonawa

– Ba’almoon - ma’ana allahn yawan jama’a.

Yanzu bari mu tambaye ka, Imam Abu Zahra da Ahmed Shalabi don ka ba mu shawara, daga cikin waɗannan Ba’al, wanne ne za ka shawarci mabiyanka su kwatanta da koyarwar Kirista ko da rayuwar Almasihu?

A gare mu dai, muna riƙe da Yesu Almasihu na tarihi, Kur’ani ma ya ba da shaida a kansa.

BUDDHA DA ALMASIHU

Daga cikin zarge-zargenka akwai sharhin da ka yi cewa, “Akwai wasu abubuwa da ke kama da juna tsakanin Buddha da Almasihu a cikin fannoni ashirin da biyu... a game da haihuwarsu da aukuwar wasu abubuwa dabam dabam, amma don gudun ƙari na kanmu, za mu ambato su da dama.”

Ba zan bar wannan sharhi ya wuce ba ba tare da na haɗa ko gwama mutanen nan biyu ba a fannin farkon rayuwarsu.

Buddha da Jawabinsa

Labarin al’amarin abin da aka ba da cikin babban littafin Buddha ana iya sāke faɗar sa kamar haka:

“Sarauniya Mayana, tana rawar jiki ta faɗa wa mijinta Sarki Doshuadana irin mafarkin da ta yi. Cikin bazarar B.C 568 ta yi mafarki a wani dare. Tana kwance a gadonta sai mala’iku guda huɗu suka zo suka ɗauke ta duk da gadon, da kujeru, da dukan kayan gidan suka kai ta can ƙolin Dutsen Himalayas, suka ajiye ta a inuwar wani babban itace. Da ta duba haka, sai ga wasu sarauniya su huɗu suka matso kusa da ita; suka nuna mata yadda za ta tsarkake/tsabtace kanta, su ka sa mata riguna masu ƙawa, suka zuba mata turare mai ƙanshin gaske. Daga nan suka ɗauke ta zuwa wani wuri wanda aka yi shi da azurfa zalla, suka ajiye ta a wurin a kan wani gado mai tsarki. Ba labari sai ga wani farin toron giwa ya sauko daga dutsen zinariya, yana ɗauke da reshen itacen lotus a haurensa. Ya kewaye gadonta sau uku, sai ya taɓa kwiɓin dama na Sarauniyar daga nan sai ya shiga cikin mahaifarta.

“Sarauniya tana gama faɗar mafarkin ke nan, sai Sarkin a aika a kirawo masu hikima su 64. Suka zo fādar, suka saurari mafarkin Sarauniyar. Suka faɗa wa Sarki, ‘Kada ka damu, ya Sarki. Ka yi murna don Sarauniyarka tana da cikin ɗa namiji. Zai zama Sarkin dukanin ƙasar, in ya tsaya cikin fādarsa, amma in ya bar ta ya yi ragaita a ƙauyen gari, to, zai zama Buddha, wanda zai yaye jahilci daga fuskar duniya.’

“Bayan ’yan kwanaki, sai maganar masu hikima ta cika. Sarauniya ta ji lalle tana da junabiyu, akwai kuma abin mamaki: ana iya ganin tayin muraran tsugune cikin mahaifar uwarsa. Haka ya zauna har kusan lokacin haihuwarsa. Sarauniya Mayana ta roƙi Sarki ya bar ta ta je wajen mutanenta har ta haihu a can. Tana kan hanya ke nan sai ciwon naƙuda ya kama ta sa’ad da take gindin itacen sal, cikin lambun Tobini.

“Ta tsuguna a ƙarƙashin wani itace mai yawan ganye, baranta ya lulluɓe ta, wato ya yi mata makāri don kada a riƙa ganin ta a tsugune. Lokacin da ta so ta miƙe tsaye, sai ta miƙa hannu don ta kama wani reshe, sai reshen ya sunkuyo ya sami hannunta.

“Da miƙewarta, sai hannuwa huɗu na Brahmins suka karɓi jaririn cikin wata raga da aka saƙa da zaren zinariya. Nan da nan jaririn ya miƙe tsaye, ya yi tafiya taki bakwai, sa’an nan ya yi ihu cikin waƙa mai daɗi ya ce, ‘Ni ne ubangijin wannan duniya wannan rai kuma shi ne ƙarshena.’

“Labarin haihuwar ɗan sarki mai girma ya bazu ko’ina cikin fāɗin mulkin Sakyas, daga kuma ko’ina mutane suka yi ta zuwa taya Sarki murna.”

Zaman Jin Daɗi

Ɗan sarkin ya yi zaman daula a fādar ubansa. Shi da kansa ya bayyana zamansa kamar haka cikin ɗaya daga littattafansa, “Na yi zaman mubazzaranci. A fādar ubana akwai tafkuna da dama lulluɓe da lilin ruwa, ɗaya yana lulluɓe da shuɗin lili, na biyu yana lulluɓe da ja, na uku kuma da farin lili, dukansu an shirya su domin jin daɗi da farin ciki.

“Ina da fāda guda uku, ɗaya domin lokacin kaka da sanyi, ɗaya kuma domin bazara, sa’an nan guda domin lokacin damina. Nakan yi wata huɗu a fādar da aka keɓe domin lokacin ruwan sama. A nan ’yan mata masu raira waƙoƙi suna kewaye da ni, da bayi mata. Sai watannin bazara sun gabato sa’an nan in tashi daga nan.”

Ubansa Sarki ya shawarta sa ɗansa ya yi ta harkarsa ta wurin sa shi rayuwar aure mai daula ya kewaye shi da ɗaruruwan kyawawan ’yan mata. Wadda za ta zama amaryar ɗan sarkin sai zaɓe ya fāɗo a kan ’yar Sarki Yosodhar, ɗiyar kawunsa Sarki Koli. Tana da kyau ƙwarai da gaske, son kowa, ƙin wanda ya rasa.

Da farko ɗan sarkin ya ji daɗin aure na farin ciki da amaryarsa.

Almasihu da Jawabi/Saƙonsa

“A wata na shida Allah ya aiko mala’ika Jibra’ilu wani gari a ƙasar Galili, mai suna Nazarat, gun wata budurwa da aka ba da ta ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu. Sai mala’ikan ya je wurinta, ya ce, ‘Salama alaikun, ya ke zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!’ Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce. Mala’ikan kuma ya ce mata, ‘Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi wurin Allah. Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda, zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada, mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”

Sai Maryamu ta ce wa mala’ikan, ‘Kaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?’

Mala’ikan ya amsa mata ya ce, ‘Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Maɗukaki kuma zai lulluɓe ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. Ga shi kuma, ’yar’uwarki Alisabatu ma ta yi cikin ɗa namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shaida, ita da ake cewa bakararriya. Ba wata faɗar Allah da za ta kāsa cika.

Sai Maryamu ta ce, ‘To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, ya zamar mini yadda ka faɗa.’ Sai mala’ikan ya tashi daga gare ta” (Luka 1:26-38).

“Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa’ad da Yusufu ke tashin Maryamu uwar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki. Yusufu mijinta kuwa da yake mutumin kirki ne, ba ya kuwa so ya ba ta kunya a gaban jama’a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce.

Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala’ikan Allah ya bayyana gare shi a mafarki ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne. Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

An yi wannan ne duk don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, ‘Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, za a kuma sa masa suna Immanuwel’. Ma’anar Immanuwel kuwa, “Allah na tare da mu” (Mat.1:18-23).

“A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da ke ƙarƙashin mulkinsa. Wannan shi ne ƙirga ta fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya. Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi.

“Yusufu ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (Domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa), don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki. Sa’ad da suke can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi. Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komin dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.

“A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare. Sai ga wani mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya. Sai mala’ikan ya ce musu, ‘Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dwuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji. Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.’ Ba labari sai ga taron rundunar sama tare da mala’ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa, ‘Ɗaukaka ga Allah tā tabbata, can cikin sama mafi ɗaukaka. A duniya salama tā tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”

Da mala’iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, ‘Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu’”

“Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin. Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu a game da wannan ɗan yaro.

Duk waɗanda suka ji suka yi al’ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu. Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci. Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabon sa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

“Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala’ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.”

“Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari’ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji (kamar dai yadda yake a rubuce a Shari’ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce shi tsarkakakke ne na Ubangiji”), su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari’ar Ubangiji cewa, ‘Kurciyoyi biyu, ko kuwa ’yan shila biyu’” (Luka 2:1-24).

Abin La’akari

A fili yake gare mu daga sharhinka na nan bisa, inda ka yi ƙagen cewa akwai abubuwan da suka yi daidai da juna a game da iƙirarin mabiya Buddha da na Almasihu suke yi dangane da haihuwa (ta shugabansu). Wannan ra’ayi ba shi da tushe, hasali ma ambaton ‘Kirista’ da ka yi ta yi cikin al’amarin naka, ya ɓata tsarkin Almasihu, kuma ya yi gāba da furcin Kur’ani a kan ɗaukakar Almasihu cikin tada matattu, da warkar da kurame da kutare, da kuma mafificin girmansa da kuma kusatarsa da Allah.

a) Sanarwa. Uwar Buddha Sarauniya ce, mala’iku huɗu kuma suka kai ta can ƙolin Dutsen Himalayas inda farin toron giwa ya same ta har ta ɗauki cikin Buddha, Uwar Yesu kuwa budurwa ce matalauciya, wadda mala’ikan Ubangiji ya ziyarce ta da kansa, ya sanar da ita cewa za ta yi juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, za ta haifi ɗa ta kuma sa masa suna Yesu.

b) Sarauniya Uwar Buddha da za ta haihu akwai barori goma tare da ita, suka yi mata makāri kewaye da ita, da ta miƙe tsaye, sai ta haifi jaririn a hannuwan wasu firistoci huɗu da akan kira su “Brahmin”, suka karɓi jaririn cikin wata raga da aka yi da zaren zinariya.

Amma budurwa Uwar Yesu da ba ta sami wuri a masaukin ba a Baitalami, sai ta haifi jaririnta cikin wurin kwanan dabbobi, babu taimakon ungozoma, ta rufe jaririn da tsumma, ta kwantar da shi cikin komin dabbobi.

c) Da aka haifi Buddha manyan mutane da yawa suka zo murna, amma da aka haifi Yesu dukan duniya tana barci, sai wasu makiyaya, waɗanda suka ji mala’ikan Ubangiji yana sanar da haihuwarsa, makiyayan sun je sun gan shi cikin komi.

d) Uban Buddha, sarki ne ya umarta a ƙara yawan sadaka ga alloli. Amma Yesu, lokacin da aka kai shi haikali, uwarsa ta iya miƙa kurciya biyu kaɗai bisa ga Shari’ar Musa, sadakar hadayar matalauta ke nan.

e) Buddha ya yi rayuwarsa cikin fādodin alatu cikin ɗaruruwan bayi ’yan mata kyawawa. Amma Yesu ya yi rayuwa cikin talauci, yana aikin kafinta, wato masassaƙi. Lokacin da ya fara aikinsa, sai wani marubucin Attaura ya gaya masa, “Maigida, zan bi ka duk inda ka tafi”, Yesu kuma ya amsa, “Yanyawa suna da ramuka, tsuntsaye kuma suna da sheƙunansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai ɗora kansa.”

Yanzu bari in amsa zarginka mai cewa, “Batun Kirista da suke cewa Yesu Ɗan Allah ne sāɓo ne muraran ... ”

Ra’ayin Islama a kan Wannan Batu

Mun karanta cikin Kur’ani, “Mafarin halittar sammai da ƙasa. yaya ɗa zai zama a gare shi, alhali kuwa mata ba ta kasance ba a gare shi, kuma ya halitta dukan, kome, kuma shi, game da dukan kome, Masani ne?” (Suratul Anam 6:101).

Al-baidawi ya yi sharhi a kan wannan aya da ya ce, “A hankalance, ɗa shi ne wanda namiji da mace suka haɗu suka haifa, amma Allah ba ya yin aure.”

Wannan ra’ayin Islama ne, wato ba shi yiwuwa Allah ya haifi ’ya’ya tun da ba shi da mata, ba kuma zai taɓa yin ta ba. Dalili ke nan da ya sa Musulmi suke musun Yesu Ɗan Allah ne. Babu ɗiyanci bisa ga tunanin Kur’ani in ba tare da haɗuwar iyaye na jiki ba.

Wannan irin tunani ya sami goyon bayan littafin da ake kira “Jam’s El-Bayan” wanda Imam Tabari ya rubuta, inda ya ce, (bayan Ibn Wahab, bayan Abi Zaid) “Ɗa yana samuwa daga namiji da mace kaɗai, amma ko kusa, Allah ba zai taɓa yin aure don ya sami ɗa ba. domin kuwa shi ya halicci dukan abubuwa, idan kuwa babu abin da Allah bai halitta ba, to, ta yaya za mu ce yana da ɗa?”

Wasu manya suka ce, an rubuta wannan sura nan da nan bayan da wasu ƙungiyar ridda da suka shigar da kansu cikin ikilisiya.

Suka yi ƙoƙarin kawo bidi’a ko karkatacciyar koyarwa mai nuna budurwa Maryamu wata allahiya ce. Gurinsu shi ne su canza ta da Venu wadda suka bauta wa. Cikin littafin da ake kira “Al Kawl Al Ibrizi” na babban malamin nan mai suna Ahmed Al Makrizi aka ambaci wannan (a shafi na 26).

Ibn Hazm ma ya ambaci wannan bid’a cikin littafinsa mai suna “Al Malal Wal Ahwaa Wal Nahl” (shafi na 48). An iya ganewa cewa, ya kamata Kur’ani ya soki wannan irin bidi’a, domin tuni aka kawar da ita daga Kristanci.

Kome za a yi, mai karatun Kur’ani zai lura cewa Littafin Musulmi ya yi fayyatattun kalamai a game da girman Almasihu da fifikonsa a kan sauran annabawa. Duk da haka, ya kāsa yaye makārin nan don ya bayyana, ko ya fito da ɗaukakakkiyar kammalarsa a kan dukan kome. Ya zama kamar Kur’ani ya kawo mai tambaya a game da gaskiyar Almasihu cikin yadin gida amma ya tsaya ya kāsa buɗe ƙofa, “Su ne Marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da ke surar Allah, ya haskaka su” (2 Korantiyawa 4:4).

A gaskiya, madawwamiyar kasancewar Almasihu a matsayin Ɗan Allah, da ƙasƙancinsa na banmamaki, ya sauko har ƙasa ya zama Ɗan Mutum don fansarmu, wannan ne tushen ta’aziyyar da dukan mabiyansa suke sha.

Kur’ani yana musun madawwamiyar Ɗiyantakar Almasihu, ya ce shi da yake kamar Adamu, Allah ya yi shi da yumɓu (Sura 3:60). Mun lura cewa, ba abin da ya fi tada wa Musulmi hankali fiye da kalamin Kirista cewa, Almasihu Ɗan Allah ne.

Wasu Musulmi masu tsattsauran ra’ayi suna cewa, Kirista sun gaskata allah fiye da ɗaya, suna shayin mu da laifin bauta wa Allah fiye da ɗaya. Wannan irin rashin sani (jahilci) da maganar wauta, Shaiɗan ne yake kutta ta don ya hana Musulmi karatun Littattafai Masu Tsarki.

Ko ka tambayi Kirista marar zurfin ilimi cewa “Wanene Allah?” Nan take zai amsa, “Allah Ruhu ne, marar iyaka, madawwami, marar sākuwa cikin kasancewarsa, mai hikima, da iko, da tsarki, da adalci, da ƙauna, da gaskiya. Allah ba shi rabuwa, ba shi wāruwa ko riɓanyuwa. Ba a iya yi masa da’ira da halittunsa. Babu mahalukin da zai iya kama kasancewarsa ko jauharansa.”

Kamar yadda “waɗanda suke duban sa (Yesu) suna annuri, fuskokinsu ba za su taɓa rufuwa da kunya ba,” ina roƙon ka kada ka yi kuskuren fassara kalamaina ‘Uba’ da ‘Ɗa’ da cewa ina nufin ɗan da namiji da mace suka haɗu suka haifa ne, wannan ya nuna ke nan Uba ya riga Ɗan kasancewa. A ƙashin gaskiya, babu Kirista da zai yi wannan furci a kan Allah da yake Allah ɗaya ne kaɗai, wanda bai taɓa aure ko haifar ɗa ta wurin zaman miji da mata ba, sam. Amma Ɗa da yake Kalma madawwami, ya zama cikin jiki kamar cikakken mutum, da fari a mahaifar Maryamu ba tare da ya rabu da allahntakarsa ba. Don haka, Almasihiu a matsayin ɗan Maryamu yana da jiki na wucin gadi. Duk da haka a matsayinsa na Kalman Allah, shi tuntuni ne, madawwami ne, yana aikata mu’ujizai bisa ga halinsa na allahntaka.

Wani baƙon abu shi ne, ko da yake Kur’ani da hadisai sun shaida ɗaukakar Almasihu, da rashin kāsawarsa, da ikon aikata al’ajabai, Musulmi kansu sun kāsa bambance tsakanin Almasihu da sauran annabawa a game da halittarsu. A akasin wannan, mun ga suna ta musun madawwamiyar kasancewarsa, suna yi da ƙarfi ƙwarai da gaske. Hadisansu suna cike da maganganu a kan “hasken” Muhammadu da ya biyo bayan halitta (duba littafin Burhan En Din El Halaby mai suna “Insan Al Iyun”). Wani abin ruɗarwa shi ne, Islama ta ba Muhammadu jauharan da shi kansa bai yi iƙirari ba a game da zamanu marasa ƙarewa, amma sun musunce su dangane da Yesu Almasihu wanda dukan ikirarinsa suna da tabbatattun shaidu da ba su ƙidayuwa.

Dr. Zwemer cikin littafinsa Mai suna “Isa ko Yesu,” ya ce, “Idan ka karanta takardun Musulmi cikin Masar, da India, da sauran duniyar Musulmi, ba za ka sami abin da ake ta sèka ba fāsawa ba, kamar batun allahntakar Almasihu da aikinsa na fansar ’yan adam.” Alhali kuwa Kirista suna gaskata Yesu Allah ne Kuma mutum a lokaci guda, ƙari a kan kasancewarsa annabi, firist kuma sarki, Musulmi kuwa sun ce shi mutum ne zar, ko da shike annabi, amma baya ga haka ba ƙari. A game da batun sarauta da firistanci kuwa, waɗannan ra’ayoyi ne da Musulmi ba su fahimce su ko yarda da su ba, domin addinin Islama ba shi da firistanci, ba su kuma da cikikakkiyar gamsuwa domin kafara, Dalili ke nan wannan tushen ra’ayi a game da aikin Almasihu ya kuɓuce wa tunani/hankalin Musulmi.”

Dr. Sayus ya nuna cewa waɗannan ra’ayi ba su cikin tunanin Muhammadu lokacin da ya ce, “Tushen batun shi ne Muhammadu bai ji shi mai zunubi ba ne, don haka bai ga bukatar fansa ba. A sakamakon haka, dukan mabiyansa, a dukan zamanai sun yi ta birkitar da wannan tunani. Ya bayyana cewa, dalili ke nan da ya sa Musulmi kaɗan ne suka karɓi bangaskiyar Kirista in an kwatanta da sauran al’ummomin duniya. Yadda Kirista suka gane yadda zunubi yake ya zama ƙaƙƙarfar kāriya da ta kange Musulmi daga zama Kirista.”

Wani ma’aikaci cikin Musulmi, wanda ya karɓi Almasihu da kansa ya ce, “Babban dalilin rashin nasara a aiki cikin Musulmi shi ne, gaskatawarsu cikin halin Allah na jinƙai ga masu zunubi, ko yardarsa ya gafarta musu ba tare da fansa ba. Sun kāsa ganin bukatar ceto.”

A game da batun da ka yi na “dutsen da magina suka ƙi,” za mu ce halayyar Littafi Mai Tsarki ita ce, babu mai iya fassara shi ba tare da taimakon Ruhu Mai Tsarki ba, mai taimakon mai bi ya gane da abin da Littafin ya ƙunsa. Babban gwarzon bangaskiya ya ce, “Wanene a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda ke daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake. Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al’amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu” (1Korantiyawa 2:11-13).

Saboda haka “dutsen da aka ƙi” Yesu Almasihu ne, kamar yadda aka nuna cikin Bishara/Linjila, “Da yana duniya, duniyar ma ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama’arsa kuwa ba ta karɓe shi ba. Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama ’ya’yan Allah” (Yahaya 1:10-12).

Bulus ya shaida wannan gaskiyar, lokacin da ya ce, “Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan ’yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma, waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin” (Afisawa 2:19, 20).

Cikin Bishara ta hannun Luka 20:9-19 muna karantawa, “Sai ya shiga ba jama’a misalin nan, ya ce, ‘Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma sufurinta, ya kuma tafi wata ƙasa ya daɗe. Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dèka, suka kore shi hannu banza. Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dèka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu banza. Har wa yau dai ya aika da na uku, shi kuwa suka yi masa rauni suka kore shi.

“Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’

Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magājin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’ Sai suka jefa shi bayan shinge suka kashe shi.

“To, me ubangijin garkan nan zai yi da su? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.’

Da suka ji haka suka ce, ‘Allah ya sawwaƙe!’ Amma ya dube su, ya ce, ‘Wannan da ke rubuce fa cewa, “Dutsen da magina suka ƙi, shi ne ya zama mafificin dutsen gini”? Kowa ya fāɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya fāɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari’.

“Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nemi su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama’a.”

Yesu ya nuna a sarari cewa shi kansa ne “dutsen” ba Muhammadu ba, domin a sakamakon wannan, manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi su kama Yesu.

A game da maganarka mai cewa, “Za a ɗauke mulkin Allah daga cikinku,” Bishara ta hannun Matiyu tana faɗa mana cewa, Yesu ya je haikali don ya koyar kamar yadda ya saba yi, sai manyan firistoci da shugabanni suka tambaye shi, “Da wane izni kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izni?” (Matiyu 21:23). Sai ya ba su misalin mai garkar inabi kamar yadda muka gani cikin Luka 20, ya ƙarasa misalin da cewa, “ ...Ubangiji ya yi wannan, kuma abin mamaki ne a ganinku. Saboda haka ina gaya muku cewa, za a ɗauke mulkin Allah daga cikinku a bai wa mutane waɗanda za su ba da ’ya’ya” (Matiyu 21:33-43).

Kafin ka shiga ɓalle aya daga muhallinta cikin Littafi Mai Tsarki don biyan bukatar kanka, ya kamata ka san cewa akwai misalan da suke daidai da wannan a wani sashi na Littafi Mai Tsarki. Annabi Ishaya ya rubuta cewa; “Ku saurara in raira muku wannan waƙa, waƙar abokina da gonar inabinsa. Abokina yana da gonar inabi a wani tudu mai dausayi. Ya kauce ƙasar ya tsintsince dawatsu, ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau. Ya gina hasumiya don a yi tsaron ta, ya kuma haƙa rami inda za a matse ’ya’yan inabin. Ya yi ta jira don ’ya’yan inabin su nuna, amma kowannensu tsami ke gare shi. Saboda haka, abokin ya ce, ‘Ku jama’ar da ke zaune a Urushalima da Yahuza, ku shar’anta tsakanina da gonar inabina. Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi ’ya’yan inabi masu tsami, maimakon ’ya’yan inabi masu kyau da nake sa zuciya. Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da ke kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta. Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama,’ Isra’ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, jama’ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, amma a maimaikon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da ke daidai, amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci” (Ishaya 5:1-7). (Duba kuma Zabura 80:4-9). Cikin misalin nan Yesu ya so ya gabatar da tabbas daga littattafansu ga masu sauraron sa, musamman ma manyan firistoci da shugabanni, abin da Allah ya bayyana wa annabi Ishaya.

Almasihu ya yi sharhi a kan misalin nan da cewa, “Ubangiji ne ya yi haka, wannan kuwa abin banmamaki ne!” (Zabura 118:23). Wannan yana nufin cewa, batun ya rikitar da dukan ’yan kallo, domin ya juya ya zama akasi ga abin da dukanin al’ummar Yahudawa suke sa zuciya. Sai dai in fansa ta zama cikin shawarar Allah, in ba haka ba, ba za ta faru ba. Ba shakka, duk al’amuran da suka haɗa da fansa, to, baƙon abu ne. Ko akwai abin da ya fi wannan zama baƙon abu, yadda Allah zai aiko da makaɗaicin Ɗansa a matsayin mai fansa, kuma madawwamin Kalma ya zama jiki, kuma zaɓaɓɓiyar al’umma ta ƙi shi, ta kuma gicciye shi? Ko akwai abu mafi zama baƙo fiye da tashinsa daga matattu a kan rana ta uku, daga nan ya zama Dutse fā wanda aka kafa Ikilisiya a kansa? Daga nan Yesu ya ƙarasa misalin da yanke wannan hukuncin, “Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al’umma wadda za ta ba da amfani nagari.”

Almasihu ya mori wannan aya don ya bayyana abin da ya ke nufi da misalin, lokacin da ya fassara gonar inabin ta zama kamar ita ce mulkin Allah. Ya ce wa Yahudawa, hanyar alheri da albarka da suke domin Mutanen Allah, za a ɗauke ta daga gare su, a bai wa waɗanda suka karɓi Yesu ya zama Mai Cetonsu da Mai Fansarsu “Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama’a, da kowace al’umma” (Wahayin Yahaya 5:9).

Da fari dai, Yesu ya gargaɗi Yahudawa da cewa, “Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin sama, ’ya’yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cijon haƙora” (Matiyu 8:11, 12).

Wanene Mai Taimako?

Tun da daɗewa kalman nan – Mai Taimako – ta zama abin ka ce - na ce ƙwarai da gaske. Wannan kalma ta fito ne daga Hellenanci “Paracletos” (farakeletos) wadda ta yi daidai da ta Aramiyanci “Manhamana”, ma’ana Muhammadu. Ibn Hisham ya ambato Ibn Isaac yana ba da wannan fassara a kan. “Rayuwar Annabi” sai kuwa ta bazu cikin kusan dukan Musulmi. Ba na so in tsokano jayayyar addini a kan wannan batu, amma dagane da amsa ne ga Mr. Abdel Rahman Swad daga Masar, na ga ya wajaba in ambato bayanan da Ubangiji Yesu ya yi, Manzo Yahaya kuma ya rubuta su cikin maɗaukakin littafinsa.

Abu na fari, cikin Yahaya 14:16,17 Yesu ya ce, “Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa ba, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam kun san shi, domin yana zama a zuciyarku.”

Abu na biyu, Yahaya 14:26 tana cewa, “Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.”

Abu na uku, Yahaya 15:26 tana cewa, “Amma sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, wato Ruhu, shi ne zai shaida ni.”

Abu na huɗu, Yahaya 16:7 tana cewa, “Duk da haka ina gaya muku gaskiya, ya fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.”

Duk wanda ya yi lazumin waɗannan nassoshi, ya kuma gwama su da wasu ayoyi cikin Sabon Alkawari dangane da Ruhu Mai Tsarki da aikinsa, “Paracletos” (Farakeletos), ba shakka zai lura cewa ba su goyi bayan masu ra’ayin cewa kalman nan “Paracletos” (Farakeletos) tana nufin Muhammadu ba ne. Ga dalilan:

a) Domin Almasihu kansa ya fassara kalmar “Paracletos” ta jauhari fitattu da dama: Ruhu na gaskiya, Ruhu Mai Tsarki, Ruhu da aka aiko daga wurin Uban. Yanzu, waɗannan jauhari ba su shafi Muhammadu ba, domin Paracletos (Mai Taimako) ruhun allahntaka ne, alhali kuwa Muhammadu mutum ne ɗan adam kawai.

b) Yesu ya ce “Paracletos” (Mai Taimako) zai zauna tare da almajiransa har abada ya kuma zauna cikinsu. Muhammadu kuwa bai iya zama tare da su ba, balle ya zauna cikinsu, domin ya zo wannan duniya bayan shekara fiye da ƙarni shida bayan Almasihu.

c) Daga cikin jauharan Mai Taimako (wani suna na Farakeletos) akwai wanda duniya ba ta iya gani ko ta san shi ba. Amma annabi Muhammadu ’ya’yan mutane sun gan shi, ya zauna tare da su, sun kuma saurare shi, sun yi magana da shi.

d) Mai Taimako dai manzon Almasihu ne, Musulmi kuwa ba za su yarda a ce da Muhammadu haka ba, don sun ce Muhammadu ya fi Almasihu girma.

e) Mai Taimako yana ba da shaidar Almasihu cikin zukatan masu bi, yana kuma bayyana musu cewa Yesu Ɗan Allah ne (Matiyu 16:16, 17), Amma Muhammadu bai yarda da wannan gaskiyar ba, a maimakon haka, sai ya mai da ita sāɓo ne (Suratul Ma’ida 5:17).

f) Mai Taimako yana koya wa almajirai, yana bi da su cikin dukan gaskiya. Ba zai yiwu ba ga Muhammadu ya koyar ko ya sadar da su tun da yake sai bayansu ya zo ɗaruruwan shekaru da suka wuce.

g) Jauharai da ayyukan Mai Taimako ba su shafi wani nama da jini ba, wanda aka gani, hannuwa suka taɓa, ido kuma ya gani, don kuwa shi ruhu ne. A gaskiya, zuwan ruhu, Mai Taimako ya zo ne tun kafin zuwan zamanin Muhammadu, kusan wajen shekara ɗari shida.

h) Cikin Bishara/Linjila akwai muƙamai masu yawa na Mai Taimako masu tabbatar da cewa, shi ruhun allahntaka ne, ba ɗan mutum ba. An ambace shi Mai Taimako, Ruhun Iko daga sama, wanda yake kayaswa daga zunubi, Ruhun Allah Mai Tsarki, Ruhun da yake koya wa mai bi yin addu’a, shi ne kuma Ruhu Mai Tsarki.

i) Gab da Almasihu zai hau zuwa sama, ya umarci almajiransa kada su bar Urushalima, sai an yi musu baftisma da Ruhu Mai Tsarki, wannan Ruhu mai albarka kuwa ba shakka an zubo musu shi a ranar Fentikos (Ayyukan Manzanni 2:4, 5). Wannan zubo musu da ruhu kuwa cikar annabcin Yowel 2:28 ne, tana kuma tare da mu’ujizan yin magana da baƙin harsuna. Duk waɗannan suna tabbatar da cewa, ko kaɗan babu dangantaka da saƙon Muhammadu.

ƊIYANCIN ALMASIHU NA ALLAHNTAKA

A ƙarshe, zan amsa furcinka mai cewa: Almasihu ba Ɗan Allah ba ne, kuma ma bai yi iƙirarin allahntaka ba.

Masana suna tare gaba ɗaya cikin ra’ayinsu cewa, hanyar da Yesu ya sanar da allahntakarsa ga al’ummar Yahudawa tana shaidar hatimin ainihin wannan. Hasali ma, in mutum ya yi wuswasin abin da Linjila/Sabon Alkawari ta ƙunsa, zai kai ga sanin ainihin gaskiyar, wadda za ta taimake shi magance matsalar yadda bangaskiya ta ɓulla cikin halin zaman jama’ar Yahudawa, wadda take da matsanancin ra’ayi gāba da kasancewa da Allah fiye da ɗaya. Hanyar da ya mora ta warware wannan asiri mai zurfi sannu a hankali, kuma ta hanyar da ta dace da irin tunanin masu sauraro, tare da lura, haɗe kuma da hikima ta allahntaka.

Muna iya fahintar tunanin jama’ar Yahudawa, da matsanancin ra’ayinsu na dāgewa gāba da kasancewa da Allah fiye da ɗaya idan mun yi wuswasin al’amuran da ke tattare da kisan da aka yi wa Istifanas, kisan da aka ba da labarinsa cikin littafin Ayyukan Manzanni. A nan muka karanta yadda ’yan Majalisa suka yi haƙurin jin sa, har sai da Istifanas ya ce, “Cikin annabawa wanene kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa... Da suka ji haka suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa.” (Haka suke nuna haushinsu). Amma da ya ce, ‘Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah’..., suka aukar masa da nufi ɗaya, suka fitar da shi bayan gari, suka yi ta jifar sa da dutse” (Ayyukan Manzanni 7:52-58).

Sun yanke wa Istifanas hukuncin kisa domin sun ɗauka kalamansa a kan Yesu yana tsaye dama ga Allah, sāɓo ne, don a gare su ya sa Yesu ya zama daidai da Uba cikin ɗaukaka.

Idan da Yesu bai gabatar da allahntakarsa a hankali ba, da azanci kuma, da kuma ɓullowa farat ɗaya cikin maganarsa, tun da fari ya furta cewa shi makaɗaicin Ɗan Allah ne cikin jiki, daidai yake da Uban, yana kuma da jauhari daidai da na Allah, ai, da bai kai shekara uku cikin hidimarsa ba. Duk da haka, hanyar da ya bi daki-daki ta sa ya iya miƙa saƙonsa, ya kuma warware asirin kasancewarsa cikin jiki a matsyinsa na Masiha, Ɗan Allah, Mai Ceton duniya. A gaskiya, ya faɗa, ya kuma aikata ta hanyar da take nuna ainihin kowanene shi, ya kuma motsa tunanin masu sauraronsa, su gamsu da allahntakarsa. Ga wasu muhimman matani nan Cikin Bishara/Linjila a game da wannan batu:

1) Lokacin wuswasin Wa’azi a kan dutse, mun ga cewa Yesu ya koyar da iko yadda in banda Allahntakar Mai ba da Shari’a, Allah na Isra’ila, ba wanda yake da wannan ikon. Ji abin da ya ce, “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuma, za a hukunta shi’ Amma ni ina gaya muku, kowa ke fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan’uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ Hakkinsa shiga Gidan Wuta” (Matiyu 5:21, 22). “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita” (Matiyu 5:27, 28). “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse kan ƙarya, sai dai ka cika wa’adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’ Amma ni ina gaya muku, kada ku ma rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah” (Matiyu 5:33, 34). “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’ Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma” (Matiyu 5:38, 39). “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka,’ Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a” (Matiyu 5:43, 44).

Wanene yake da ikon cewa, “Amma Ni”, ya kuma ƙara a kan Shari’ar Allahntaka wadda Musa ya karɓa daga wurin Allah a kan Dutsen Sina’i?

Cikin Luka 6:22, Yesu ya ce, “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suke ƙin ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.” Ya haɗa wannan da faɗin da ke cikin Matiyu 5:10, “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata ‘adalci’, domin Mulkin sama nasu ne,” Kalman nan ‘adalci’ kamar yadda masu sauraronsa suka fahince ta, Shari’ar Ubangiji ce, ko Ubangiji Kansa. Ta faɗar haka, Yesu ya mai da kansa daidai da Ubangiji Allah ke nan.

Ba wannan kaɗai ba, amma Yesu ya bukaci a yi masa cikakkiyar ƙauna da miƙa kai ga shi kansa lokacin da ya ce, “Wanda duk ya fi son mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba, wanda kuma ya fi son ɗansa ko ’yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba”(Matiyu 10:37, 38). Wannan irin salon magana ya tuna wa Yahudawan da ke sauraro irin furcin ikon cikin Attaura cewa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da kuma dukan ƙarfinka.” Saboda haka, Yesu, cikin neman irin wannan cikakkiyar ƙauna ga kansa, ya mai da kansa daidai da Ubanguji, Allah na Isra’ila, wanda ga shi kaɗai za a yi wa wannan. Ya ƙarfafa wannan gaskiyar da ya ce, “Domin kowa ya girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan” (Yah. 5:23). Wato ke nan, allahntakarsa tana bukatar mutane su ba da girma ga Ɗan kamar yadda suke badawa ga Uban. A sakamakon haka, Ɗan ya zama daidai da Uban, wajibi ne mu yi wa Ɗan abin da muke yi wa Uban a game da ƙauna, da girmamawa, da biyayya, abin da mazauna cikin sama suke yi (Wah. Ya. 5:12).

Bugu da ƙari, Yesu ya koyar cewa, zai zama Mai Shari’ar masu rai da matattu a rana ta ƙarshe, yana cewa, “Zai kuwa aiko mala’ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato daga wannan bangon duniya zuwa wancan” (Matiyu 24:31). Wa zai iya yin irin wannan iƙirari, in ba Ubangiji Kansa ba?

2) Idan mutum ya duba mu’ujizan da Yesu ya aikata, zai ga cewa ya yi su da sunansa, da ikon kansa. Gaskiya ne, annabawan Allah sun yi irin mu’ujizan nan amma sun yi su da sunan Allah ne, Yesu kuwa ya yi da ikon kansa ne. Mun karanta yadda wani kuturu ya zo yana roƙon Yesu ya warkar da shi, yana cewa “Ya Ubanguji, in dai ka yarda kana da iko ka tsarkake ni” Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, ‘Na yarda ka tsarkaka’! Nan take kuturtarsa ta warke” (Matiyu 8:2, 3).

Haka kuma ya kwantar da hadirin teku. Bai ce, “Na umarce ka cikin sunan Ubangiji ba”, amma ya umarce shi cikin ikonsa, yana cewa, “Natsu! Ka yi shiru!” (Markus 4:39).

Kuma, lokacin da Yesu ya ta da ɗan gwauruwa daga matattu, a Nayin, “Sa’an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, ‘Samari, na ce maka ka tashi.’ Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga mahaifiyarsa” (Luka 7:14, 15).

Yesu bai tsaya kan warkar da kutare da ta da matattu ba, amma ya ci gaba da nuna cewa yana da ikon gafarta zunubi. Markus, mai bishara, yana faɗa mana cewa, “Bayan ’yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida. Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa’azin Maganar Allah. sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu na ɗauke da shi. Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗa rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayyen yake kwance a kai. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ‘Ɗana, an gafarta maka zunubanka.’ To, waɗansu malaman Attaura na nan zaune, suna ta wuswasi a zuciyarsu, suna cewa, ‘Don me mutumin nan ke faɗar haka? Ai, sāɓo yake! Wa ke da ikon gafarta zunubi in banda Allah kaɗai?’ Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, ‘Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku? Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayye, ‘An gafarta zunubanka, ko kuwa a ce, “Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya”? Amma don ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya,’ sai ya ce wa shanyayyen, ‘Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.’ Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa” (Markus 2:1-12.)

In muka yi wuswasin mace mai zunubi, wadda Yesu ya gafarta mata zunubanta a gidan Saminu Bafarisiye, mun ga nufin Yesu cikin nuna ikonsa na gafarta zunubai. Ya yi magana da mai masaukinsa cewa, “Saminu ina da magana da kai” Shi kuma ya ce, ‘Malam, sai ka faɗa.’ Yesu ya ce, “Wani na bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?” Saminu ya amsa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa, “Ka faɗa daidai.” Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu, “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta. Kai ba ka sumbace ni ba, ita kuwa, tun shigowarta nan ba ta daina sumbatar ƙafafuna ba. Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna. Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan ya ke yi.” Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.” Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wanene, wanda har yake gafarta zunubai?” Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya” (Luka 7:36-50).

A wannan karon mun lura cewa Yesu bai ce an gafarta wa macen nan mai zunubi don ta tuba ba, amma ya ce, “Ta yi ƙauna mai yawa,” wato ke nan ta nuna wa shi kansa ƙauna, wannan yana nuna cewa ƙaunar Yesu tana daidai da ƙaunar Allah kansa.

Sa’an nan kuma, mun karanta cewa Yesu, lokacin da ya aiki almajiransa karo na fari, ya aike su da sunansa, yana ba su iko su warkar da marasa lafiya, su fitar da aljannu. Karanta Matiyu 10:1-7; Markus 3:15-19 da kuma Luka 9:1-3.

3. Ya yi magana a kan Kansa ta hanyoyin da suka sha dabam da dangantakarsa da Uba na sama, yadda ya bayyana Allah a matsayin Uban jama’arsa, ya kuma nuna cewa Ubanci na Allah ya shafi ’yan adam. Saboda haka shi ba mai ƙagawa ba ne, don kuwa annabawan Tsohon Alkawari da suka gabace shi sun bayyana Ubancin Allah ga jama’arsa da masu bin sa. Mun karanta cikin Ishaya, ‘Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakon mu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe” (Ishaya 63:16). Akwai shaida da yawa daga faɗar su Musa, da Yusha’u, da Ishaya, da sauransu. Duk da haka Yesu Almasihu ya bayyana Ubancin Allah ga kansa kamar zama mabambanci, dabam daga Ubancin Allah ga ’yan adam. Sau da dama yakan kira Allah “Ubana,” ko da shike faɗar “Ubanmu” ta wakana sau ɗaya cikin addu’ar Ubangiji.

Daɗin daɗawa, shaida mafi fayyacewa a kan dangantakar Yesu da Uba ta zo mana cikin wani furci mai ƙarfi da ya yi wanda cikin sa ya yi murna, yana cewa, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri... Ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa. Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku” (Matiyu 11:25-28).

Cikin waɗannan kalamai masu daraja muna jin amsakuwar muryar madawwama, da kuma gane girman wannan asirin banmamaki lokacin da muka ga yadda Yesu ya ƙayyade sanin Uban sai gare shi kaɗai, ya kuma ƙayyade sanin Ɗan ga Allah kaɗai, kuma wannan cuɗanyar dangantaka yana nuna daidaitaka.

Har yanzu akwai wani abin da ya faru, inda Yesu ya so ya kawo mabambanciyar dangantakarsa da Uba ga hankalin Yahudawa. Ya tambayi Farisiyawa, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wanene?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.” Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce, ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a damana, sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’ Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?’” (Matiyu 22:41-45).

A ƙarshe mun gan shi a tsaye gaban Kayafa, babban firist, kafin a yanke masa hukunci. “Sai babban firist ya ce masa, ‘Na gama ka da Allah Rayayye, faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.’ Sai Yesu ya ce masa, ‘Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune dama da Mai Iko, yana kuma zuwa kan gajimarai’” (Matiyu 26:63, 64).

Cikin wannan amsa mun gan shi yana nuna annabcin Daniyel, a kan Masiha inda annabin yake cewa, “A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, aka kai shi gabansa. Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, domin dukan jama’a, da al’ummai, da harsuna su bauta masa” (Daniyel 7:13, 14).

TAƘAICI

Idan muka yi wuswasin waɗannan gaskiya, za mu sami kanmu muna fuskantar wani mutum, wanda ba a taɓa samun kamarsa ya bayyana cikin tarihin ɗan adam ba. Hotonsa da muke da shi yana kama zukata ya iza mutane su yi masa sujada. Domin mun ga allahntakarsa ta haɗu da kowane sashi na rayuwarsa, haɗe kuma da kalamansa, da ayyukansa, da mu’ujizansa, da rayuwarsa, da mutuwarsa a kan gicciye, da tashinsa daga matattu da kuma hawansa zuwa sama. Waɗannan ne gaskiyar da suka tilasta wa mutanen Sabon Alkawari, mutanen da suka tsotsi madarar gaskata Allah ɗaya tak tun daga ƙuruciyarsu su gaskata allahntakarsa. Idan mun yarda da waɗannan gaskiyar za mu iya mu warware ra’ayin nan da ke akasin gaskiyan nan. Za mu kuma sami mun tilasta kanmu mu ɗauka lalle cewa ikilisiyar farko ce ta ƙirƙira wannan tarihi, waɗannan al’amura da suka faru kuma sun zo ne daga shayin wata ’yar ƙungiyar Galilawa kawai. Amma wane mai tunani ne zai iya gaskata cewa wasu jahilai kawai za su iya ƙaga wannan mutumin allahntakar banmamaki daga shayinsu kawai. Sun yi nasara cikin shiyin rashin zunubinsa, sa’ad da su suke raunana, ɗaure kuma cikin zunubi. Sun amince da allahntakarsa duk da kasancewarsu da jinin gaskata Allah ɗaya tak da ke gudu ko’ina cikin jikinsu; su ƙaga hanyoyi dabam dabam, da dabaru da al’amura iri iri, da lokatan da ya bayyana allahntakarsa; yarda da rashin ƙarfi haɗe kuma da ƙarfi da ɗaukaka haɗe da tawali’u; mutane marasa zurfin sani sun yi tunanin dukan wannan ya fi gaban yiwuwa.

Wannan ne matsalar Kristanci mai wuyar karɓuwa, wannan ne kuma maganin matsalar kamar yadda muka samu a rubuce cikin Sabon Alkawari. Mun yarda da maganin matsalan nan, domin kuwa babu wani maganin da zai maye gurbin wannan. Saboda haka, mu ma, mun gaskata, “Saboda haka muke magana.”

Cikin littafin C. G. Pfander, mai suna a turance, “Balance of Truth,” (wato Balas ɗin Gaskiya) ya faɗa daidai da ya ce, “ ‘Kalma’ yana nuna furci cikin tunanin mai magana, a cikin wannan Allah ne kansa. Ta bi da cewa, in Almasihu ne Kalma daga Allah, menene shi in banda faɗar cikakken nufin Allah, ko kuma a ce buɗi daga Allah. Daga baya ya yi magana da su ta wurin Ruhunsa Mai Tsarki. Maganar Allah tana nuna cewa Almasihu ne kaɗai ya nuna Allah ga mutum, domin kuwa ya san Allah, yana kuma nuna nufinsa cikakke. Yesu ma ya faɗi wannan gaskiyar lokacin da ya ce, ‘Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa. Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku’” (Matiyu 11:27, 28).

(Matuni = Musammancin “Kalman Allah” da ta shafi Almasihu kaɗai, ya nuna cewa Muhammadu ya ɗauki wannan muƙami daga bakin wasu Kirista da ya yi cuɗanya da su. Wannan kalami dai Kristanci ne dukaninsa).

A ƙarshen wannan tattaunawa ina jawo hankalinka ga aya ta 91 ta Suratul Anbiya (21:91) wadda ke cewa, “Kuma da wadda ta tsare farjinta daga alfasha. Sai Muka hura a cikinta daga ruhunmu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ‘aya’ ga duniya.” Morar kalman nan “aya” (wato alama) abu ɗaya ne, amma mai yin batun fiye da ɗaya ne, yana tuna mana abin da aka ce da Mai Cetonmu cikin annabcin Ishaya, “Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al’ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama” (Ishaya 9:6).

Baidawi ya yi ƙoƙari ya ƙasƙantad da Muhimmancin kalmomin nan bisa ga dabarar sharhinsa inda ya ce, “Aya (wato alama) ga duniya, domin duk wanda ya riya a kansu, ya yarda ke nan da ikon mahalicci!”

Rayuwar Almasihu, Mutuwarsa da Tashinsa

Mun fuskanci wahaloli cikin tattaunawar nassoshin Kur’ani dangane da rayuwar Almasihu. Na fari, yadda Kur’ani yake a gutsuttsure, (wato guntu-guntu, ko kashi-kashi aka tattara). Babu mahaɗi tsakanin abubuwan da suka faru da jerinsu. Don haka mutum ba zai sami jerin yadda abubuwa suke bisa ga faruwarsu ba, domin ayoyin Kur’ani sun sauko daga sama ne(bisa ga cewar Musulmi) a lokatai dabam dabam, kuma a wurare dabam dabam. Wannan, haɗe da sauran ruɗami ya ƙara rikitar da mai karatun da yake ƙoƙarin karatun kan magana, ya bi daga farko har ƙarshe. Ta haka, sai ka ga daƙiƙai sun gauraye da labaru da aukuwar al’amura, da alkawarai tare da wasu barazana.

Abu na biyu, abu mafi rikitarwa, shi ne, nassoshi cikin Kur’ani dangane da Ubangiji Yesu Almasihu ba su kuɓuta daga wannan rikitarwa ba. Alhali wasu ayoyi suna magana a kansa a shi mutum ne kawai, annabi kuma, wasu sun kira shi da muƙaman da ba za a iya kiran wani taliki da su ba sai shi. Rikitarwa mai muni ita ce wadda ta danganci mutuwarsa, domin ba shi yiwuwa a sasanta ayoyin nan ba tare da an dama tunanin hankali ba.

Abu na uku, shi ne, matsalar jerin surori. Idan mun bi ainihin tunanin Muhammadu da ci gaban tunanin nasa a game da Almasihu, sai mu fara da ambato na fari, sa’an nan a ci gaba a hankali, ana jerawa bi da bi har a kai ga sura ta ƙarshe. Amma abin baƙin ciki shi ne, babu yarjajjeniya tsakanin manyan masanan Islama su kansu a kan tarihin jerin Surorin Kur’ani. Su ma sun san da cewa jerin surori da ake da su yanzu ba bisa ga aukuwar abubuwa ba ne.

Me Bulus Ya Faɗa?

A game kalamanka a kan zunubi wanda ya zamanto cikin Kristanci, “cewa bai fi ansakuwar arnanci ba wadda ta yi wa Kristanci launi, Bulus ya nuna, don kowa ya iya koyon wani abu daga gare shi, zama Bayahude ga Yahudawa, arne kuma ga arna... da dai sauransu.”

Kafin ya tuba, Bulus Bayahude ne mai matsanancin kishin addini, sunansa kuma Shawulu. Ya yi suna saboda himmarsa domin Shari’ar Musa. Bulus ya bayyana kansa da waɗannan kalamai, “In kuma akwai wanda ke tsammani yana iya dogara da al’amuran ganin ido, to, ni na fi shi. An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Biliyaminu, Ba’ibrane ne ɗan Ibraniyawa, bisa ga Shari’a kuwa ni Bafarisiye ne, wajen himma kuwa mai tsananta wa ikilisiya ne ni wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari’a, marar abin zargi nake. Amma dai kowace irin riba na taɓa ci, na ɗauka hasara ce saboda Almasihu. Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tosari domin Almasihu ya zama nawa” (Filibiyawa 3:4-8).

Masana tarihi sun faɗa mana cewa, ubansa Bafarisiyi ne, kuma an yi renon sa bisa ga tsananin shari’a/doka. Ya kammala dukan iliminsa a Tarsus, yana matashi, aka aike shi zuwa Urushalima don ya koyi shari’ar Yahudawa da addini. A nan ne sanannen malamin tauhidin nan yake, Gamaliyel, wanda Bulus ya yi zaman almajirci a hannunsa. Kafin Yesu Almasihu ya bayyana kansa gare shi, ya tsananta wa Kirista ƙwarai da gaske. Abin da ya ƙara fushinsa shi ne kalaman Istifanas da aka kashe, waɗanda ya furta kafin su jajjefe shi, “Wannan Yesu Banazare zai hallaka wannan wuri, ya kuma sāke al’adum Musa waɗanda aka danƙa mana.” Saboda himmarsa, aka ba shi izini daga shugabannin Yahudawa don ya hallakar da Kirista cikin Dimashƙu. Amma da yana tafiya zuwa birnin, sai Yesu Almasihu ya bayyana gare shi, ya kuma yi magana da shi, ya kuwa ba da gaskiya ga Almasihu. Daga baya ya ba da labarin tubarsa a gaban Sarki Agaribas cikin waɗannan kalmomi, “Cikin haka ne, ina tafiya Dimashƙu da izinin manyan firistoci da kuma saƙonsu, da rana tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata. Da duk muka fāɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da Yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Da wuya a gare ka ka yi ta shuri bisa kan tsini.’ Ni kuwa na ce, ‘Wanene kai, ya Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a kaina, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka nan gaba. Zan tsirar da kai daga jama’an nan da kuma al’ummai, waɗanda zan aike ka gare su, domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni’” (Ayyukan Manzanni 26:12-18).

Kalamin manzo mai cewa, “Ga Yahudawa na zama Bayahude... ” da sauransu, wannan ya nuna sai ka ce ba ka karanta da kyau ba, don haka ba ka fahimci ma’anar ba, ko zai yiwu ka ƙudura ruɗar da tunani ne ta wurin cire matani daga mahallinsa.

Mun riga mun ce an goyi manzo Bulus cikin addini a ƙarƙashin Rabbi Gamaliyel; cikin wannan shahararriyar makaranta an koyar da shi shari’un Yahudawa cikin ka’idodinsu, da kowane abin da bai sāɓa da tsarin lamiri ba. Ta haka ne bai yarda ya juye su ba don ya sami zarafin nuna musu Yesu ne Masihan da ake sauraron zuwansa. Gaba da dukan la’akari, ya wajaba a nuna cewa Kristanci bai zo don ya lalatar da Shari’a ba amma don ya cika ta.

Shi Ba’ibrane ne, kamar yadda muka gani, kuma in ba tare da wannan sanin gargajiyar ba, da ba zai iya samun rinjayar Yahudawa ba, ko ma a yardar masa ya shiga masujadansu ya yi wa’azin Bishara.

Ga Al’ummai kuma, muna karantawa a Ayyukan Manzanni cewa, ikilisiyoyin Kirista na farko, musamma na cikin Yahudiya, sun riƙa gudanar da sujadarsu ne bisa ga dokoki da suke asalin na Musa ne, amma an ƙara wasu ta hannun malamai da su rabbi bisa ga yadda zamanu da tsararraki suke tafiya, cikin samfurin ayyuka masu yawa, a kan wanda kaciya ce wadda a kullum ita ce kāriya mai hanawa. Bisa ga wani rabbi, “Amma domin wannan farilla (kaciya) da ba a halicci ƙasa da sararin sama ba.” Wani kuma ya ce tana daidai da dukan dokokin Shari’a. Duk da haka, ikilisiya cikin Antakiya, inda Bulus da Barnaba suka yi aiki har shekara biyu, suka buɗe ƙofar bangaskiyar Kirista don karɓar Al’ummai waɗanda suka karɓi saƙon Bishara. Amma ’yan’uwa na asalin Yahudawa Cikin Ikilisiyar Urushalima ba su so su ji daɗin jin labarin nan ba, wannan ya kai su ga yin muhawara mai zafi.

Ikilisiya cikin Urushalima ta yi taron majalisa don su yi muhawara a kan wannan batu. Bulus da Barnaba suka ba da labarin aikin al’ajaban da Allah ya yi lokacin da suka fara tafiyarsu ta aikin mishan cikin Kubrus har zuwa cikin Asiya Ƙarama. Bayan sun saurari wannan labari mai daɗi, na yadda dubban Al’ummai suka karɓi Kristanci, sai Bitrus ya miƙe, ya tuna wa waɗanda suke a nan cewa, Allah ya zaɓe shi don ya yi Bishara ga Al’ummai don su ma su ba da gaskiya.

A ƙarshe, Yakubu shugaban majalisa, ya miƙe ya taƙaice shawarwarin cikin batu huɗu kamar haka: Kirista ’yan asalin Al’ummai su guji cin abincin da aka miƙa wa gumaka; su guji ci/shan jini; naman da aka maƙare; da kuma zina.

Masana tarihin ikilisiya sun faɗa mana cewa, Bulus ya yi da Al’ummai cikin tawali’u, akasin girmankai irin na Yahudawa, ya kuma nuna ƙaunar Almasihu ga masu bi cikinsu. ya kuma gayyato wasu daga cikinsu don su shiga aikin mishan, ya kafa wasunsu a matsayin fastocin ikilisiya. Yadda muka fahinci kalamansa ke nan da ya ce, “Ga marasa Shari’a kuwa, sai na zama kamar marar Shari’a - ba wai cewa ba wata Shari’ar Allah da ke iko da ni ba, a’a, shari’ar Almasihu na iko da ni - domin in rinjayi marasa Shari’a ne. Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna, domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu. Wato bai kiyaye ka’idodin shari’ar Yahudawa ba cikin Al’ummai, amma yana ƙarƙashin Shari’ar Almasihu” (1Korantiyawa 9:21, 22).

Abu Na Ƙarshe

A shafi na biyu na wasiƙarka ka ce, “Wannan wasiƙa zuwa ga masu marmarin hanya madaidaiciya ne,” amma ka far wa wasu shafuna da zagi kamar na la’ana maimakon “Kira ga fahimta”. Da za mu iya amsa maka ta zafi kai ma, ko ma da muni fiye da taka, don kuwa Islama tana da kāsawa da yawa iri iri, amma ba mu yi ba, tun da Ruhun Almasihu ya tsarkake tunaninmu haka kuma alƙalumanmu. Ya ba mu wannan doka, “Ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a” (Matiyu 5:44). A ƙashin gaskiya muna addu’a domin ka, yadda Allah, wanda muke yi wa sujada cikin ruhu da cikin gaskiya kuma, ya ba ka ganewa ka san gaskiya, yadda za ta ’yantar da kai daga ruhun riƙau.

KACINCI-KACINCI:

KU AUNA ABU DUKA KU RIƘE MAI KYAU

Zuwa ga mai karatu,

Saƙon marubucin, sunan littafin nan ya nuna shi, kira ne domin aunawa da gwadawa. Yi ƙoƙari ka gwada saninka bayan ka karanta shi a hankali, ta wurin amsa tambayoyin da ke nan ƙasa. Idan ka amsa su, sai ka aiko mana, mu kuma za mu aika maka da wani ɗan littafin.

Tambayoyi:

 1. Ina kayan aiki da ya dace domin bahasi da gwadawa?

 2. Menene babban batu na I Korantiyawa 1:22-24?

 3. Don wace manufa Almasihu ya mutu, kuma domin su wanene?

 4. Menene ainihin shaidar annabawa a kan Almasihu kafin zuwansa?

 5. Ko Almasihu ya shaida cewa za a gicciye shi ya mutu? Ba da misali guda.

 6. Ka ambaci wasu al’amuran da suka faru da suke haɗe da tashin Almasihu.

 7. Me ya zama taken Kristanci tun daga bayyanarsa?

 8. Ka faɗi wata ayar Kur’ani da take magana a kan mutuwa ko kisan Almasihu.

 9. Ka taƙaita fassarar Al-Razi ta aya ta 55 a Suratu Al-Imrana (3:55) “Ya Isa! Lalle Ni Mai Karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni” da sauransu.

 10. A ganinka, wace aya ce ta fi muhimmanci cikin Wa’azin Yesu A kan Dutse?

 11. Daga cikin addinai, wane ne yake ƙarfafa yaƙe-yaƙe, wane ne kuma yake kiran mutane ga salama da ƙauna?

 12. Ko ya kyautu a auna/shar’anta addini bisa ga halin mabiyansa ko ta wurin dokokinsa/da hukunce-hukuncensa?

 13. A ra’ayinka, ko hare-haren Islama na farko sun zama hanya ko sun ƙare a kan kansu?

 14. Yaya za ka ba da ma’anar “zunubi”?

 15. Ka fassara ayoyin Romawa 5:18, 19 da 20

 16. Menene sakamakon zunubi?

 17. Ta yaya za mu tsere wa mutuwar da zunubi ya saukar a kanmu?

 18. Ko Kristanci ya hori mutane da su yi adalci, da kirki, da gaskiya, da tsarki, ko kuwa da su yi arnanci da bautar gumaka?

 19. Ka taƙaita rayuwar Almasihu cikin jumla biyu masu ma’ana.

 20. Ta yaya za mu kāre Kristanci daga zargi a kan rashin gaskatawa da kasancewar Allah fiye da ɗaya?

 21. Ka nuna bambanci tsakanin koyarwar Kur’ani da koyarwar Bishara/Linjila a kan Ruhu Mai Tsarki.

 22. Ka ba da misalai na Ɗiyancin Yesu na allahntaka cikin dangantaka da Allah

 23. Me ka koya a game da rayuwar Bulus, da tubarsa, da kuma wa’azinsa?

Ka rubuta amsoshinka a wata takarda dabam, da cikakken suna da adireshinka, sa’an nan ka aiko zuwa ga:


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland