HASKEN DUNIYA

HASKEN DUNIYA

GEORGE FORD


Table of Contents

HASKEN DUNIYA

HASKEN DUNIYA

Duk mutum mai hankali zai fahinci cewa, amfanin jama’a da abubuwan da ake bukata don ci gaba, da tushen wayewa, duk suna bukatar kulawar abin da yake haɗa kan bangaskiya iri iri da kuma abin da ke rarraba su.

Gaskata ɗayantuwar Allah ce a kan gaba da kome da ke sa ƙungiyan nan uku su ɗayantu, waɗanda aka sani da, “Mutanen Littafi”. Domin Yahudawa da Kirista suna shelar wannan da ƙarfi kuma a sarari, haka ma Musulmi. Yahudu da Kirista ba su amince cewa Musulmi sun fi riƙe wannan muhimmin abu da ƙarfi ba kamar su, wato batun ɗayantuwar Allah, wadda dole a ƙarshe za ta yi rinjaye a kan dukan ra’ayoyin nan masu kuskuren nuna cewa ɗayantuwan nan ai, gaskata Allah fiye da ɗaya ne ko kuma bautar gumaka.

Kirista na gaskiya, lokacin da yake tarayya da Musulmi cikin kashi na biyu na wannan shaida, in banda faɗar Musulmi mai cewa, “Muhammadu Manzon Allah ne, to, zai zama kamar Musulmi a kan dalilin nan gudu, ba shakka suna da ra’ayi guda cikin kashin farko na wannan batu, wato “Babu wani allah sai Allah ɗaya kaɗai,” zai kuma gamsu da wannan da dukan ƙarfinsa. Zai yi fāriya cikin tabbatar da kowace ƙungiya mai ƙudurin kawar da kowace gaskatawa a kan Allah fiye da ɗaya, irin wanda ke akwai lokacin da Islama ta kuhu.

Babban abu na biyu na ɗayantuwa tsakanin ƙungiyoyin da aka sani “Mutanen Littafi” suna da shi har yanzu, ba a ba shi muhimmancin da ya dace ba, ba a kuma ba shi isasshiyar kulawa ba. Wannan shi ne Yesu Almasihu, ko Isa ɗan Maryamu, da gurbinsa da kuma koyarwarsa. Saboda haka nufinmu shi ne mu tattauna tsakani da Allah sassa daban daban na wannan ɗayantuwa maɗaukakiya tare da Musulmi na gaskiya wanda yake ɗoki domin addinisa .

An yarda cewa abubuwan gaskiya ana iya fayyace su kaɗai ta wurin gwaje gwaje da bincike. Muddin an gano su, an kuma yarda da su, da jituwa – maƙasudin da ake muradi a wannan zamani – ya kahu a tsakanin masu tattaunawa a kan batutuwan nan.

Mun gaskata sakamakon wannan bincike ba agazawa kaɗai zai yi ba ga rage ƙiyayyar da Musulmi yake ji a ransa dangane da wasu al’amura na Kirista, amma ta wurin bayyana masa, sai wannan irin tunani ya rabu da shi gaba ɗaya daga zuciyarsa. Muna batu musamman a kan batutuwan da suka danganci Yesu Almasihu kansa, wanda cikin muhawara da shugabannin Yahudawa, ya yi iƙirari, “NI NE HASKEN DUNIYA”.

Magana a kan mutumin nan, Yesu, wani abu na biyu ne a game da batun ɗayantuwa da ke tsakanin “Mutanen Littafi” ta kahu a kan gaskiyar cewa sun yarda cikin girmama shi, wata yarjajjeniyar da ba a cim ma wa ba cikin tarihin ɗan adam duka, dangane da wani annabi. Waɗannan ƙungiyoyi sun ƙunshi a ƙalla rabin dukanin mutanen duniya, rabi guda kuwa masu ci gaba ne cikin dukan fannoni na ci gaba.

Sanin kowa ne cewa, Yahudawa sun ɗauki Masihi (wanda suke ɗokin zuwansa) shi ya mamaye manyan wurare fiye da annabi mafi girma. Wannan kuwa jazaman ne a cikin ayoyi masu yawa cikin Attaurarsu wadda daga ciki muka zaɓo waɗannan: “Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu, za a kira shi, Mashawarci Mai Al’ajabi, Allah Maɗaukaki, Uba Madawwami, Sarkin Salama. Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin... tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani” (Ishaya 9:6,7).

Girmamawar da Kirista suke yi wa Yesu Almasihu, ba girma kaɗai gare ta ba, amma mabambanciya ce, ɗaukakakkiya kuma fiye da girmamawar da suke wa manzanni da annabawa mafiya girma. Kirista suna ɗaukar Almasihu shi ne Masihin da aka alkawarta wa Yuhudawa cikin Attaura, gaba da kome kuma, ya zama makaɗaicin ɗan Allah. Wannan a fili yake cikin matani da dama cikin Bishara (Linjila), wadda saboda iko da baƙuncin wannan al’amari, ya zama abu mafi wuya ga wanda ba Kirista ba. Mun zaɓi waɗannan ayoyin:

“Tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. Shi ne tun fil azal yake tare da Allah. Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane” (Yahaya 1: 1-4).

“Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da ke haskaka kowane mutum” (Yahaya 1:9).

“Kalman nan kuwa ya zama mutun, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa ɗaukaka ce ta makaɗaicin ɗa daga wurin Ubansa” (Yahaya 1:14).

“Wanda ya zartar ga Almasihu sa’ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya, Allah kuma ya sarayar da kome ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikilisiya ya zama kai mai mallakar abu duka” (Afisawa 1:20, 22).

“Domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa, kowane harshe kuma ya shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba” (Filibiyawa 2:10,11).

Lokacin da kuma muka buɗe nassoshin Musulmi, za mu ga dukan ayoyin da suka yi batun Yesu, ɗan Maryama, suna ɗaukaka shi zuwa matsayi mafi girma fiye da dukan annabawa, har fiye da Muhammadu annabinsu. Ga wasu daga cikin irin ayoyin nan:

“Masihi, Yesu ɗan Maryama, shi Manzon Allah ne kaɗai, Kalmansa da aka danƙa wa Maryama, Ruhu ne kuma daga gare Shi” (Suratun Nisa 4:171).

“A lokacin da mala’iku suka ce, ‘Ya Maryama! Lalle ne Allah yana ba ki bushara da wata kalma daga gare shi; sunansa Masihu Isa ɗan Maryama, yana mai dajara a duniya da Lahira kuma daga makusanta” (Suratu Al Imrana 3:45).

“Wancan ne Isa ɗan Maryama, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta” (Suratu Maryam 19:34).

“Muka biyar da Isa ɗan Maryama, kuma muka ba shi Linjila, kuma muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan waɗanda suka bi shi... ” (Suratul Hadid 57:27).

“ Kuma muka ba Isa ɗan Maryama, alamu fayyatattu, muka kuma tabbatar da shi da Ruhu Mai Tsarki” (Suratul Baƙara 2:87).

“A lokacin da Allah ya ce, ‘Ya Isa ɗan Maryama! Ka tuna ni’imata a kanka... a lokacin da Na ƙarfafa ka da Ruhul ƙudusi” (Suratul Maida 5:110).

Ƙari a kan ayoyin nan na sama, akwai wasu tabbaci kuma masu goyan bayan matsayin Almasihu cikin Musulmi. Daga waɗannan mun kwaso daga hadisin annabci cikin “Mishkal al- Masabih”, wani littafi ne da ake girmamawa ƙwarai, musamman cikin Musulmin India. Wannan labarin bayani ne na mabiya da yin gyara a Ranar Tashin Kiyama ga annabawa farawa daga Adamu, suna biɗar annabawan su yi roƙo domin su. Bisa ga wannan labari, kowane annabi ya bayyana baƙin cikinsa saboda rashin cancantarsa, saboda zunuban da ya aikata waɗanda aka ambata cikin tarihin Isra’ila, suka nuna su ga juna. Da suka zo wurin Musa, shi ma sai ya furta kāsawarsa ya ce, “Ku tafi wurin Yesu, wanda shike shi ne Bawan Allah, Manzon Allah, Ruhun Allah, kuma Kalman Allah”. Yesu kuwa bai yi banhaƙuri ba, duk da rashin zunubi a gare shi, shi ma sai ya gaya musu, “Ku je wurin Muhammadu ɗan Abdullahi, wanda Allah ya gafarta masa farko da ƙarshe” (Mishkat al-Masabih 23:12).

Addinin Islama ya yarda cewa, Yesu ɗan Maryama shi kaɗai ne jikinsa bai raɓa cikin kabari ba.

Wata yarjajjeniya ta banmamaki ta dukan sassan, wato “Mutanen Littafi,” da na Islama sun girmama Yesu ƙwarai da gaske, wannan ya zama muhimmin mahaɗi, sun yarda da juna, sai dai cikin gaskata ɗayantuwar Allah kaɗai. Ya kamata su kasance tare cikin ƙauna da jiyayyar girmama juna.

Ga abin da ya rage, shi ne, Yahudawa su yarda cewa wannan shi ne ainihin Masihinsu, Musulmi kuma su yarda cewa Bishara (Linjila) wadda ke ɗauke da albishir mai daɗi na Yesu ɗan Maryama da kuma koyarwarsa, Bisharar ke nan ta ainihi wadda Kur’ani ya girmama. Daga nan ne hanya za ta buɗe ta samun dangantaka mai fa’ida, mai dacewa tsakanin jinsunan nan guda uku masu riƙe da ragamar ikon duniya.

Da farko dai dangantakar tana bukatar fahimta. A gefe guda, bisa ga irin matsayin da Almasihu yake da shi cikin shirin abubuwansu, Musulmi suna iya zuwa kusa da fahinta da Kirista. A gefe guda kuma, Yahudawa za su iya zuwa kurkusa su kuma, domin Kirista, sun rungumi Attaura a rubuce cikin littattfansu Masu Tsarki tare da Bishara (Linjila). Fahinta tana bukatar a kawar da shayi daga tunanin ƙungiya guda a game da gaskatawar wasu. Wannan ya sa ya zama wajibi ga kowace ƙungiya ta wadata ’yar’uwarta da nata irin Nassoshin, don su iya samu. Idan ɓoye kayan rayuwa, wato na masarufi laifi ne, kuma cikin wayayyun ƙasashe ma an ɗauki wannan mugun laifi ne, to, ai, kuwa, ɓoye muhimman al’amuran addini masu dogara ga tagomashin allahntaka da madawwamin ceto ko hallaka ya fi zama babban mugum laifi. Musulmi da ke ƙaunar mutanensa ba zai gamsu da irin wannan al’amari ba, amma zai yi ƙoƙarin yaɗa amfanin addini da ya samu. Zai kuma yi marmarin samun nasa rabo na kowace sabuwar albarka da za ta zo masa da jama’ar wata bangaskiya.

Idan wanda ya ce, “Ni ne Hasken duniya,” mai gaskiya ne, dole mu auna maganarsa da gaskiya, kuma a hankali, domin mu fahimci abin da take nufi. Ashe ƙarshen batun ba zai zama cewa, Wanda da gaske Shi ne, “Hasken duniya” na mutanen Islama waɗanda suka ƙunshi kashi ɗaya daga cikin bakwai na jimlar mutanen duniya?

Haziƙin Kirista zai karɓi girmamawar da Kur’ani ya ke yi wa Almasihu, Yesu ɗan Maryama, da litattafan Kirista (Attaura da Bishara, wato Linjila). Zai kuma gamsu da yadda Kur’ani ya ke girmama Shi, domin Shi ɗaya ne daga cikin “Mutanen Littafi.” Cikin girmamawan nan zai sami buɗaɗɗiyar hanyar yin yarjajjeniya tsakanin shi da Musulmi.

Tun da fari an ambaci wasu ayoyin Kur’ani dangane da Almasihu kansa. Ga wasu da suke dangane da Almasihu:

“Kuma lalle ne kana samun mafiya kusantarsu a soyayya ga waɗanda suka yi imani su ne waɗanda suka ce: ‘Lalle mu ne Nasara’ Wancan kuwa saboda akwai ƙissisuna da ruhubanawa daga cikinsu. Kuma lalle ne su, ba su yin girman kai” (Suratul Maida 5:82)

“Lokacin da Ubangiji Ya ce; ‘Ya Isa, ni... sanya waɗanda suka bi ka a bisa waɗanda suka kafirta, har Ranar ƙiyama’” (Suratul Al Imrana 3:55).

“Lalle ne, waɗanda suka yi imani... da Nasara wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba” (Suratul Maida 5:69).

“Kuma ba mu aika ba a gabaninka face mazaje, muna yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma’abuta ambato idan kun kasance ba ku sani ba” (Suratul Anbiya 21:7).

“Muka biyar da Isa ɗan Maryama, kuma muka ba shi Linjila, kuma muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan waɗanda suka bi shi” (Suratul Hadid 57:27).

Gaba da wannan duka, duk mutum mai wayewa ya sani, kuma ya yarda cewa amince wa gaskiya shi ne abu mafi muhimmanci, ba zai sadakar da gaskiya ba don ya kāre ƙungiyarsa cikin aikinsa na kuskure.

Saboda haka, kyautata wa gaskiya ya bukaci Kirista kada su mai da hankali ga ayoyin nan kaɗai na yabo da aka ambata a nan sama, amma har ga waɗancan kuma da suke masu ƙasƙantarwa. Ga wasu kamar haka:

“Kuma Yahudawa suka ce, ‘Nasara ba su zamana a kan kome ba’, kuma Nasara suka ce: ‘Yahudawa ba su zamana a kan kome ba’; ...” (Suratul Baƙara 2:113).

“Ya Mutanen Littafi, ... kada ku ce ‘Uku’. Ku hanu daga faɗin haka. Allah Ubangiji ne guda” (Suratun Nisa 4:171).

“Lalle ne haƙiƙa, waɗanda suka ce, Allah na ukun uku ne, sun kafirta, kuma babu, wani abin bautawa face Ubangiji guda” (Suratul Maida 5:73).

“Kuma lokacin da Allah ya ce, ‘Ya Isa ɗan Maryama! shin kai ne ka ce wa mutane, “Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautawa, baicin Allah”’” (Suratul Maida 5:116).

“Sun riƙe malamansu (Yahudu) da ruhubanawansu (Nasara) ubangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Maryama (haka)” (Suratul Tauba 9:31).

Sukar da aka bayyana cikin ayoyin nan ba shakka saboda taɓarɓarewar addini ne na Kirista a wancan lokaci, abin da ya sa sukar ta sami tushe ke nan. Lokacin da mutane suka ratse daga ka’idodin addininsu, da dokokin allahntaka da ke ciki, dole a kāsa girmama su. Ta wurin bin takalidan ’yan adam a maimakon na wahayin allahntaka da kuma bin camfe-camfe marasa kan gado a maimakon bin tabbatattun abubuwan gaskiya maɗaukaka bayyananmu daga sama. Irin mutanen nan sun cancanci tsautawa. Mashawartan gyaran addini, da waɗanda gurinsu ne su rushe duk wata hanyar sujada wadda ba ta Allah Mai Rai kaɗai ba ce, ta madawwamin Ruhu, ba za su yi shiru ba suna kallo ana ta tafka kuskure. Zai yiwu kawo canji shi ne manufar wannan ci gaba da ƙasƙanci da soke-soken nan.

Musulmi masu ɗari-ɗari da al’amuran Kirista, ko suna jin ƙiyayya gāba da Kirista, da yi musu ba’a, zai yiwu su ce ai, yaƙe-yaƙen da aka sani da “Jihadi” su suka shuka wannan iri na mugun nufi, da na ƙiyayya. Ya kamata Kirista ya zama a shirye ya yarda da kuskuren da mutanensa Kirista na baya suka yi cikin yaƙe-yaƙen nan da aka yi, ya kuma san cewa duk waɗannan akasin koyarwar Kirista ne da Ruhun Almasihu. Kiristan da suke cewa ai, abubuwannan sun faru saboda zaƙuwar Kirista ne, ba don ƙiyayya ga Masulmi ba ne, amma don su kuɓutar da wurare masu tsarki, waɗannan Kirista ba su kuɓuta daga hukuncin da manzo Bulus ya yanke a kan wasu mutanensa Yahudawa ba. Ya ce, “Na dai shaide su kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba. Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tasu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar” (Romawa 10:2,3).

Himma ba tare da sani ba makamtacciya ce, mai ɓadda waɗanda suka sami gaskiya, da kuma ruɗar da waɗanda suka riga suka ɓata.

Kuskuren Kirista cikin wancan al’amari da bai auku ba, amma saboda rashin kular Kirista, har ma da shugabaninsu na Littafi Mai Tsarki, wanda shi ne tushen addininsu. Idan takalidan ’yan adam sun maye gurbin tsarinsu na allahntaka, dole waɗannan yaƙe-yaƙe na ban kunya su auku, akasin bayyana dokokin Ubangijinsu da Maigidansu, Almasihu. Dokokin nan sun nuna cewa addini yana kasancewa cikin zuciya kamin ya bayyana cikin ayyuka. Tushensa shi ne dangantaka ta gaskiya da zuciya ɗaya da mahalicci da kuma sauran talikai. Da fari doka ce cikin Attaura, daga baya aka fayyace ta cikin Bishara cikin faɗar Almasihu cewa, dukan shari’a da dokoki an tarke su cikin manyan dokoki guda biyu, su ne ka ƙaunaci Allah da dukan zuciya, da kuma mutum ya ƙaunaci maƙwabcinsa kamar kansa (Matiyu 22:37-40).

Bisa ga tsarin dokokin Kirista, duk abin da yake akasin ƙaunar Allah da ɗan adam to, bai tafi tare da addini ba. Addinin gaskiya ba da takobi ake kafa shi ba, amma ta wurin tabbaci da nagartar da ke fitowa daga gare shi. Wanda kuwa aka kafa da takobi, zai dogara ga takobi don ci gabansa. Kirista sun gane cewa nasarar da suka samu cikin jihadi da takobi ba ta ɗore ba, domin ko da shike, sun yi cikin sunan Yesu, sun ƙaryata Ruhunsa da dokokinsa, sun manta cewa ɗaya daga cikin muƙamansa masu daraja, wanda annabi Ishaya ya mora shekara ɗari bakwai kafin haifuwar Almasihu, shi ne, “Sarkin Salama.” Ɗaya daga cikin dokokinsa mafi muhimmanci ita ce: “Kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. In kuma wani ya yi ƙarar ka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma... Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci” (Matiyu 5:39,40,44,45).

Wanda dai ya ba mabiyansa irin waɗannan dokoki, ya aikata bisa ga dokokin nan lokacin da yake zama tare da mutanen, a gab da ƙarshen zamansa na duniya, ya kuma yi wannan addu’a domin waɗanda suka gicciye shi: “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba” (Luka 23:34). Kirista na ƙwarai ya yarda cewa ya kamata ya bukaci mutanensa su fi mai da hankali ga koyarwar addininsu, ya kuma kiyaye dokokin addinin, idan za su cancanci ƙauna da girmamawa daga Musulmi ga kansu ko ga Nassoshinsu da kuma bangaskiyarsu, idan kuma har suna so su rinjayi Musulmi ga gaskiyar da Ubangijinsu yake faɗi, “Ni ne Hasken duniya.”

Kiristan da ya ƙware cikin addininsa zai lura da wani dalili kuma da ke sa Musulmi ya yi sukar da ke ƙara ba shi baƙin ciki. Kirista zai gane cewa maganin wannan daɗaɗɗen ciwo ba zai magantu ta wurin mai da takobi cikin kube kurum ba, da kuma dogara ga ƙauna da adalci ba. Amma yana bukatar Kirista ya gane ainihin ma’anar kiransa, da yadda zai gabatar da shi ga Musulmi.

Duk wanda ta wurin nazari a natse, ya ƙware cikin abin da Bishara ta ƙunsa, zai san cewa babban saƙon Kirista ba shi ne kiran mutane su sāke bangaskiyarsu ba ne, don kuwa Bishara ba ta damu da batun ɗariku da ra’ayoyi ba. Ko tana kira ga sāke suna saboda kuwa sunan nan “Kirista” ya bayyana sau uku ne kawai cikin Sabon Alkawari, wato sunan muƙami ne wanda a ka san masu bi da shi. Bugu da ƙari kuma ba ana kira ba ne don yin wasu ayyuka farillai kamar su yin baftisma, ko ma ayyukan waje mafiya muhimmanci suna bi daga baya ne.

Babbar manufar saƙon Kirista kira ne ga mutum ya yi rayuwar bangaskiya, wadda take zurfin zuciya, cikin rayayen Mutum wanda yake kasancewa a ruhunce, wanda Allah ya tasa daga cikin matattu, makaɗaicin Mai Ceto ga dukan ’yan adam. A game da Kirista kuwa, waɗansunsu ba dole a aikata su ba, aikata waɗansu kuwa suna da amfani a aikata kawai lokacin da aka ji yin haka bayan an ji yin haka a zuciya ga wannan kira na ruhaniya. Karɓar bangaskiyar Kirista a fili, da karɓar sunan Kirista ba wani abu ba ne muddin an yi da riya, don son a sani kawai. Lokacin da aka yi wannan da gaskiya, yadda ya kamata kuma, ba wani amfani gare su ba illa shiri ne kawai don muhimmin abu na fari kawai. Lokacin da Musulmi ya gane wannan gaskiyar, yawancin sukar da yake yi wa saƙon Kirista zai ƙare.

Duk wanda yake bincike da zurfi zai lura cewa Yesu Almasihu bai ce, “Ni ne ɗaya daga haskokin duniya ba.” ya yi magana a Shi ne Hasken dukanin duniya, don haka idan wani dabam ya haskaka, ko zai haskaka cikin duniya, to, yana samun haskensa daga wurin Almasihu, kamar yadda wata da taurari suke samun haskensu daga rana wadda ita ce mafi girma duka, ba su ma kwatantuwa.

Musulmi na gaske, mai biyayya ga bangakiyarsa tana hana shi yarda nan take da gaskiyar faɗin Yesu cewa, “Ni ne Hasken duniya,” ba shakka zai yarda cewa gano gaskiya ba zai kammalu ba sai da dogon binciki, da nazari, da kuma tunani, a kuma yi dukan wannan da ainihin gaskiya. A sakamakon wannan ba zai ƙi tattaunawa ba tare da mabiya wasu addinai. Ba kuma zai raina karɓar tabbacin kowace matsala ba don kawai ra’ayi bai zo ɗaya da abin da ya gāda ba. Zai kasa kunne ga darasi daga sananniyar ayan nan ta Kur’ani wadda take tsawatar wa waɗannan da ke nace wa gargajiyarsu, ayar tana cewa, “Ko mun ba su wani littafi ne a gabanninsa (Alƙur’ani) saboda haka da shi suke riƙe? A’a, sun ce dai, ‘Lalle mu, mun sami ubanninmu a kan wani addini (na al’ada) kuma lalle ne mu, a kan gurabunsu muke masu neman shiryuwa; kuma kamar haka, ba mu aika wani mai gargaɗi ba a gabaninka, a cikin wata alƙarya, face mani’imtanta sun ce, ‘Lalle mu, mun sami ubannimu a kan wani addini, kuma lalle mu, masu koyi ne a kan gurabunsu”(Suratuz Zukhruf 43:21-23).

Ya gane cewa idan da Yesu, ɗan Maryamu, ya dāge kansa ga bangaskiyar da ya tarar, ya manne wa abin da ya gāda, ya kuma koya a matsayinsa na Bayahude, da babu zancen Kristanci, da kuma Bisharar Almasihu ba ta kasance ba. Haka kuma in da a ce Muhammadu ɗan Abdullahi na Koroshiwa, wanda cikin ƙoƙarinsa na neman gaskiya, bai tsaya a kan abin da ya gāda kawai ba, da abin da ya saba kaɗai yake kuma son su ba, ai, da ba haka abin yake ba, amma ya buɗe sababbin hanyoyi, ya kuma sadar da su da waɗanda ya gāda ya kuma aikata daga abubuwan da ke cikin Attaura da Bishara (Linjila). Wannan haziƙanci mai ’yanci yana da muhimmanci wajen hana ratsewa.

Ba shakka cewa, kowane baligi zai yarda da bukatar girmama kafaffiyar gaskiya, ya kuma biɗe ta da naciya, daidai, da himma, ba cikin littafinsa kaɗai ba, amma cikin na waɗansu kuma, da sanin cewa gaskiyan nan ba ta kāduwa. Yana tunawa da muhimmancin kalman nan “Gaskiya” wadda ita ce ɗaya daga cikin sunayen da aka fi misalta mutumin Allahntakan nan. Irin wannan mutum yana tabbatar da batutuwan annabi Dawuda, wanda ya ce, “Na yi niyya in yi biyayya, na mai da hankali ga ka’idodinka” (Zabura 119:30), da kuma abin da Sulemanu ya faɗa, ɗan Dawuda mai Hikima, ya ce, “Gaskiya, da hikima, da ilimi, da hankali, sun cancanta a saye su, kome tamaninsu” (Karin Magana 23:23).

Ba shakka kuma irin wannan mai binciken zai mori basirarsa, ya yi nazarin al’amura dangane da addini da yake hurarre don ya gane da abin da yake gaskiya, ya kuma ƙi abin da yake ƙarya. Zai ji ƙyamar karɓar abin da yake na yarantaka da na maganganun banza, waɗanada suka mallake tunanin mutane ma su yawa na mabiyan dukan addinai. Haka kuma, zai ƙi kowane matani da kuma mu’ujizai waɗanda ba hurarru ba. Cikin wannan ne ya yaba wa maganar Zamakhshari’s cewa “Duk hanyar da ba ta sami goyon bayan nassi ba, to ba ta da wani tasiri.”

Mai tunanin kirki zai gane cewa ko nagartar ruwa ba za a shar’anta ta ta wurin ɗanɗana ruwan laka daga kogi ba, amma sai ta wurin shan tsabtataccen ruwa daga maɓuɓɓugarsa, haka yake ga shar’anta Kiristanci, ko na dā ko na zamanin yanzu, ba za a shar’anta ko auna shi bisa ga abin da ake gani cikin Kirista ba, masu kāsawa a kai a kai. Irin wannan shar’antawa dole a dasa ta daga hurarrun nassoshi da kuma cikin Shugabansu mai girma, Jogora kuma, Sassalar koyarwasu da kuma cikakken gurbinsu.

Mutum mai tunani, mai mutunci zai guje wa ’yan gani-kashenin addini, wanda ke ɗaure ikokin tunani, domin ya lalluɓe haske, ko da shike hasken na haskakawa kewaye da shi. Wanda ya kauce wa son zuciyar addini cikin biɗar gaskiya da yake yi, zai gane cewa, ka’idodin addini, ko da yake suna da kyau kuma sun wajaba, ba za a dogara a kansa ba don auna balanshin gaskiya. Amma, kamar tufafin da mutum yake sanyawa ne. Ko da shike suna da kyau kuma sun wajaba, duk da haka ba su isa zama ma’aunin gaskiya na mutumin da ke sanye da su haka ba. Kamar yadda tamanin mutum ya danganta ne a kan ingancin mutumin, ba a kan tufafinsa ba, haka yake ga matsayin addini, bai danganka a kan suna ba, amma a kan ka’idodin da aka kafa shi, da kuma abu mai ba da rai da addinin ya ƙunsa wanda shi ne ka’ida ta gaskiya cikin addini.

Ana iya kamanta addini da lambu mai itatuwa da kuma rukunai iri iri da itatuwan da kansu. Gaskatawar addini wadda ke daidai kawai yana kama da itace marar ’ya’ya bangaskiya ta gaske shi ne adalci, babu kuma itatuwan da za a daddasa idan babu begen samun ’ya’ya daga gare su. Idan itace ya ci gaba da rashin ’ya’ya, sai a sare shi a ƙone. Duniya ba ta gamsu da daidaitar rukunai kawai ba waɗanda ba su kawo gamsuwa ko murna daga ’ya’yansu, a gani cikin hali nagari da ayyukan adalci. Hukuncin rashin kula da wannan ya na da tsanani, fiye da na rashin kula da juyowa ta gaskiya, haka yake ga hukuncin masu bauta wa alloli fiye da ɗaya, zai yiwu ya fi hukuncin masu bi waɗanda halin rayuwarsu yana musuntar bangaskiyarsu.

Gāsar addini tsakanin balagaggun mutane, wayayyu kuma, suna sa ido ga nagarin hali a maimakon fifikon rukunai. Nagarin hali ya fi samun girmamawa domin gāsa tsakanin ƙungiyoyi kamar yadda yake a tsakanin mutane, shi ne kuma tabbaci mafi riba da ba da sakamako mafi kyau. Wannan kuwa saboda jayayya a kan rinjayen ra’ayi sau da dama takan haddasa ƙiyayya da bambance-banbamce lokacin muhawara a game da adalci take ƙaruwa cikin sassan duka biyu, ya kuma kawo su kurkusa da juna.

Manyan ka’idodin waɗanda akwai yarjajjeniya a kansu suna da iko fiye da ka’idodin musamman waɗanda bambance-bambance suka kasance a kansu. Manufar wannan tattaunawa ita ce don a kauce wa kowace irin jayayyar da za ta jawo niyyar rushe juna. Tattaunawar a matsayin aboki na gaskiya, cikin nazarin muƙamin Almasihu da kuma Littafi Mai Tsarki, wannan ce doka domin mutanensa.

Ana ba da shawara cewa, da fari sai a duba cikin goyan bayan da ke cikin Kur’ani wanda ke nuna hurarren Littafi Mai Tsarki, wanda cikin dukan sassansa biyu, wato Attaura da Bishara (Linjila), sun rigayi Kur’ani. Ana iya samun wannan goyan baya cikin ayoyi da dama na Kur’ani. Amma za mu gamsu da wasu waɗanda suke taɓo Attaura da Linjila a wasu fannoni.

“Ya ku waɗanda aka bai wa Littafi! Ku yi imani da abin da muka saukar, yana mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku” (Suratu Nisa 4:47).

“Sa’an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku” (Suratu Al Imrana 3:81).

“Kuma mun saukar da Littafi zuwa gare ka da gaskiya, yana mai gaskatawa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littafi (Taurata da Injila)” (Suratul Maida 5:48).

“Amma tabbatattu a cikin ilimi daga gare su, da muminai suna imani da abin da aka saukar daga gabaninka” (Suratun Nisa 4:162).

“Kuma wannan Alƙur’ani bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabaninsa... babu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake” (Suratu Yunus 10:37).

Akwai kuma ayoyin da suka taɓo Attaura da Linjila da sunansu musamman, kamar waɗannan:

“Ya sassaukar da Littafi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatawa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah ya saukar da Attaura da Linjila” (Suratu Al Imrana 3:3).

“Waɗanda suke suna bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjila; yana umarnin su da alheri, kuma yana hana su daga barin abin da ba a so” (Suratul A’araf 7:157).

“Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waɗannan dake tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai ... wannan shi ne siffarsu a cikin Attaura, kuma siffarsu a cikin Linjila” (Suratul Fath 48:29).

“Kuma da dai lalle mutanen Littafi sun yi imani, kuma sun yi taƙawa ... Kuma da dai lalle su, sun tayar da Attaura da Linjila da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, hakika, da sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafafunsu” (Suratul Maida 5:65,66).

“Ka ce: ‘Ya ku mutanen Littafi! Ba ku zama a kan kome ba, sai kun tsayar da Attaura da Linjila da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku’” (Suratul Maida 5:68).

“Kuma a lokacin da na sanar da kai rubutu da hikima, da Attaura da Linjila” (Suratul Maida 5:110).

“Ya ku mutanen Littafi! Don me kuke hujja cewa a cikin sha’anin Ibrahim, alhali kuwa ba a saukar da Attaura da Linjila ba face daga bayansa? Shin ba ku hankalta? (Suratu Al Imrana 3:65).

“Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujada wannan shi ne siffarsu, a cikin Attaura” (Suratul Fath 48:29).

“Kuma muka biyar a gurabansu Isa ɗan Maryama, yana mai gaskatawa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma muka ba shi Linjila, a cikinsa akwai shiriya da haske, yana mai gaskatawa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa’azi ga masu taƙawa” (Suratul Maida 5:46).

Waɗancan ayoyi masu goyon bayan Linjila kaɗai suna daga cikin waɗannan:

“Kuma sai mutanen Linjila su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a ciknta kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fasiƙai” (Suratul Maida 5:47).

“Muka biyar da Isa ɗan Maryama, kuma muka ba shi Linjila!” (Suratul Hadid 57:27).

Waɗancan ayoyin masu goyan bayan Attaura kaɗai suna daga cikin waɗannan:

“Kuma yaya suke gabatar da kai ga hukunci, alhali a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah” (Suratul Maida 5:43).

“Lalle ne mu, mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske, annabawa waɗanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ... da aka neme su da su tsare daga Littafin Allah, kuma sun kasance, a kansa masu ba da shaida ... Wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to waɗannan su ne kafirai” (Suratul Maida 5:44).

“Misalin waɗanda aka ɗora wa ɗaukar Attaura sa’an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misalin jaki ne, yana ɗaukar littattafai. Tir da misalin mutanen nan da suka ƙaryata a game da ayoyin Allah! Kuma Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai” (Suratul Jumu’a 62:5).

“Sai su ce, ‘muna imani da abin da aka saukar a gare mu,’ kuma suna kafircewa da abin da ke bayansa, alhali kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tare da su (na Attaura)” (Suratul Baƙara 2:91).

“Kuma a lokacin da Isa ɗan Maryama ya ce ‘ya Bani Israi’ila! Lalle ni, manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura’” (Suratus Saff61:6).

“Kuma ina mai gaskatawa ga abin da yake a gabana daga Attaura” (Suratu Al Imrana 3:50).

“Ya Bani Isra’ila... ku yi imani da abin da na saukar, yana mai tabbatar da abin da yake tare da ku” (Suratul Baƙara 2:40,41).

“To, ku zo da Attaura, sa’an nan ku karanta ta, idan kun kasance masu gaskiya ne” (Suratu Al Imrana 3:93).

Akwai wani ra’ayi da ake zagawa da shi a tsakanin Musulmi, yana iƙirarin cewa Kur’ani ya maye gurbin Attaura da kuma Linjila, hujja cewa ya ƙunsa kuma ya taƙaita cikin mataninta dukan abin da yake muhimmi da amfani kuma cikinsu duka. Bugu da ƙari kuma, shi ne, littafin da yake na ainihi kaɗai bayan zuwan Islama shi ne Kur’ani.

Bari ma a ce ra’ayin nan daidai ne, muhimmanci da fa’idarsa ga Musulmi ba za ta fi yadda take ga Kirista ba. Tabbacin ingancisa da ya gamshi Musulmi haka kuma da zai gamshi Kirista. Amma duk da haka, ayoyin Kur’ani su ne suka fi sukar wannan ra’ayi, domin sun ambaci Attaura da Linjila sai ka ce shi ne littafi na uku mai ’yancin kansa. Kur’ani ya ce:

“Suna yaƙi cikin hanyar Allah, saboda haka suna kashewa ana kashe su. (Allah ya yi) wa’adi a kansa, tabbatace, a cikin Attaura da Linjila da Alƙur’ani” (Suratul Tauba 9:111).

“Kuma waɗanda suka kafirta suka ce, ‘Ba za mu yi imani da wannan Alƙur’ani ba, kuma ba za mu yi imani da abin da yake a gabansa ba (na waɗansu littattafan sama’” (Suratus Saba 34:31).

“To, wanda ya kafirta da Allah... da Littattafansa... to, lalle ne ya ɓace, ɓata mai nisa” (Suratun Nisa 4:136).

“ ...waɗanda suke riyawar cewa suna imani da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabaninka... Shaiɗan yana neman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nisa” (Suratun Nisa 4:60).

Kalman nan, “maganar Allah da kuma littattafansa,” da suke cikin ayoyin nan ya fito da abin a fili cewa, gaskatawa da rashin gaskatawa ba a kan Kur’ani kaɗai ba ne, amma har da Littattafai uku da aka ambata cikin aya ta fari a nan sama, su ne, Attaura, da Linjila da kuma Kur’ani. Ta yaya gaskatawa ko rashin gaskatawa zai shafi wani abin da aka share ko aka maye gurbinsa da wani?

Lokacin da Muhammadu yake amsa wa masu tufkawa da shi, bai wadatu ta wurin nuna bangaskiyarsa ga abin da aka saukar masa kaɗai ba, amma ya ƙara da wanda aka saukar gabaninsa. Lokacin da ya nuna Shaiɗan yana ɓatar da’yan adam da nisa, ya haɗa wannan ba ga shaidar Kur’ani kaɗai ba amma har da wanda aka saukar kafin Kur’ani, su ne, Attaura da Linjila.

Saboda haka, ra’ayin nan mai cewa Kur’ani ya maye gurbin Attaura da Linjila, ba shi da tushe. Wannan ra’ayi bai sami goyan baya na kowane iri ba cikin ko da aya ɗaya ta Kur’ani, inda Musulmi zai tsaya a kai kome bincikensa a kan wannan al’amari.

An kuma ce, idan an saukar da Kur’ani don ya maye wahayan da suka gabace shi, ai, da cikin bangirma ga wahayin Allahntaka, da ya ƙunshi ayoyi kalmomi bi da bi na wasu ayoyi na hurarrun da suka gabata. Cikin Linjila haka yake, ta faɗo ayoyi da dama da wurare da take da cikakkiyar dogara cikin littattafan da suka gabata, wato Attaura.

Babu shakka, su da ke kāre ra’ayoyin nan da muke tattaunawa a kai suka yi hujjar cewa Allah ya saukar da Attaura ga Musa, daga baya kuma ya saukar da Linjila ga Yesu don ta maye gurbin Attaura, sa’an nan kuma Muhammadu ya sami Kur’ani, Littafi na uku ya zama magājin littattafai biyu da suka gabace shi, wato ya maye gurbinsu ke nan. Idan kashi na farko na wannan muhawara gaskiya ne, to, zai zama ke nan kashi na biyu shi ma gaskiya ne. Amma iƙirarin nan cewa Linjila ta maye gurbin Attaura ta kuma gāje ta, ko kaɗan ba gaskiya ba ne, kuma ya musunci matanan Kur’ani. Kur’ani bai shafe waɗannan littattafai da suka gabace shi ba, amma ya martaba su ta wurin ambaton su a kai a kai tare.

Linjila muhimmin sakamako ne, kuma babu kokanto ita cikar Attaura ce. Babu wata daraja cikin kowane sakamako ko cika sai dai in an tabbatar, an kuma adana na ainihin.Yesu Almasihu, da farkon aikinsa a duniya sai da ya tabbatar da wannan gaskiyar a lokacin da ya ce, “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su” (Matiyu 5:17).

Bugu da ƙari, idan Kur’ani ya maye gurbin Attaura da Linjila, da ta yi shelar wannan a sarari ga mabiyansa don su sani. Kur’ani bai faɗi ainihin haka ba cikin abubuwan da ya faɗi yadda aka ambata tun da fari, ko wani batun da ya cike gurbin Littattafan da suka gabata. A gaskiya ma, sai ya musunci wannan a kai a kai cikin ayar da ta soki waɗancan, “Suna so su musanya maganar Allah” (Suratul Fath 48:15). Da wadda ta ce, “To, shin, suna jiran (wani abu ne) face dai hanyar (kafiran) farko. To, ba za ka sami musanya ba ga hanyar Allah. Kuma ba za ka sami juyarwa ba ga hanyar Allah” (Suratu Fadir 35:43).

Mun sani cewa, ’yan adam suna iya fāɗawa cikin kuskure, suna yin farillai da dokoki. Lokacin da aka gano kura-kurai cikin dokokin nan sai aka yi gyara, aka ƙara inganta dokokin. Amma ba haka yake ga Allah ba. Dukan dokokin addini an saukar da su a lokatai daban daban don a bambanta mutane, da umarnan kiyayewa, waɗanda sai dai a yarda da su bisa ga ka’ida duk da kowace irin rashin jituwa da taka taso. Dangantakar da ta ɗaure su tare ta dole ce, a fili take, kuma da ƙarfi. Wahayin da aka yi wa Bayahude ba zai iya bambamta da wanda aka yi wa Kirista ba, ko wanda aka yi wa Kirista ya zama akasin wanda aka yi wa Musulmi, babu bambamci sai dai abin da ba a rasa ba, ko irin na gamo da katar a wasu wurare. Duk mai cikakken hankali ba zai yarda cewa akwai fili domin rikitarwa ba cikin wahayin Allahntaka.

Saboda haka, ana iya gani cikin doka/shari’ar Kirista wadda Allah ya saukar an tattabatar da ita, an kuma ƙarfafata, an kuma gina ta a kan dokan Yahudawa wadda aka fara saukarwa. Kirista sun yarda da babbar daraja ba ta Linjila kaɗai ba amma har da ta Attaura. Sun tabbatar da littafi na farko, sun sa ya zama sashi na Littafinsu Mai Tsarki, sun girmama shi kamar yadda suke girmama Linjila domin shi ne ginshiƙin da aka gina Linjila a kai. Attaura da Linjila sun haɗu sun zama littafi guda, ba biyu ba. In ba suna tare da juna ba, ba su zama cikakku ba; na biyu in ba shi tare da na fari, to, ba shi da tushe. Ana iya ganin dawwama da muhimmancin mahaɗi a tsakanin Attaura da Linjila cikin alkawarai, da ayoyi, da alamomi, da kuma annabce-annabce, waɗanda suka bukaci cika a cikin Linjila. Ta haka muka tabbatar cewa kowannensu ba ya zama cikakke idan ba tare da ɗayan ba.

Attaura ba domin Yahudawa kaɗai ba ne, Linjila ma ba domin Kirista kaɗai ba ne. Duk littattafan biyu domin dukanin duniya ne, wanda Allah Makɗaici ya aiko, domin dukan halittunsa a kowane wuri domin yana ƙaunar su, yana kuma nufin su da kowane abu mafi kyau ba tare da bambanci ba. Aiki a kan waɗannan tabbacin da aka ambata, sai mu bar su ga Musulmi mai sanin ya kamata ya auna ya hukunta kuma a game da ra’ayin nan mai cewa Kur’ani ya “maye gurbin” Attaura da Linjila ba shi da tushe, kuma babu wata hujja da ta goyi bayan wannan. Wannan shaci faɗi ne kawai, ba gaskiya ba, kuma an ƙaga ne kawai don a haɗa muhawara mai zafi ta Yahudawa da Kirista. Saboda haka, Musulmi ba zai yi mamaki ba in ya ji cewa, yana da wuya a rinjayi saura su yarda da wannan ra’ayi. Me ake bukatar a ce a game da guda ra’ayin wanda Musulmi da dama suke da shi? Ra’ayin da ke cewa, Attaura da Linjila na yanzu ba abin karɓa ba ne, wai an dagula su, ba na ainihi ba ne wanda Kur’ani ya tabbatar. Suna iƙirarin cewa an ɓadda na ainihin. Gaskiya da rashin gaskiyar wannan ra’ayi ya shafi Kirista da Musulmi duka. Cikin binciken wannan, suna da manufa mai jiyayya, wato gudanar da bincike da gaskiya don a gano zurfin wannan gaskiyar.

Abu na fari da za a daidaita cikin wannan batu wanda mutum zai yi furcin cewa littattafan nan biyu ba na ainihi ba ne, dole sai ya nuna hujjojinsa tabbattu na zahiri dake goyon bayan iƙirarinsa, musamman a kan hurarrun littattafan guda biya. Dole ya kawo kofe na ainihi don ya nuna shi a matsayin shaida, don ya nuna inda aka yi kuskure cikin kofen da ake ƙi. Idan ya yi iƙirarin an daddagula, ko an yi jabu ne na abin da ke ciki, dole ya nuna shaida ta hakika mai goyon bayan iƙirarinsa, idan kuwa ba haka ba, iƙirarin ya zama marar tushe, na banza wanda ba a aiki da shi. Ana iya kamanta shi da mutumin da ya kai ƙara yana zargin wani da mugun laifi, sai shari’a ta nemi cikakkiyar shaida, in kuwa babu sai kotu ta kori wannan ƙara saboda rashin cikakkiyar shaida.

A game da Attaura kuwa, Yahudawa sun yi furci tare da tabbatarwa iri iri, cewa daga ranar da aka rubuta littafinsu sun lura da shi, sun dubi kowace kalma da wasalinta, fiye da yadda Musulmi suka tsare lafiyar Kur’ani. Gaskiya ita ce, wannan littafi yana nan cif, duk da irin lalatarwar da aka yi wa birninsu mai tsarki, da mashahurin haikalinsu, da kuma warwatsar da su da aka yi ko’ina a duniya kusan shekara dubu biyu, wannan abin mamaki ne cikin tarihi.

Wani abin la’akari shi ne, yadda Kirista suka rungumi Attaura ta Yahudawa ka’in da na’in, sun amince da ita. Sananne ne cewa, ana ta ci gaba da jayayya tsakanin sassan nan biyu wadda da za ta sa Kirista su ƙi Littafin Yahudawa, idan da haka ɗin zai yiwu.

Tsananin da Yahudawa suka yi wa Kirista a lokacin da Yahudawa suke cikin ganiyarsu ta daraja da iko, kowa ya san wannan. Har abin ya kai lokacin da Yahudawa suka gicciye Almasihu, suka bi bayan wannan da tsanantawa, da azabtarwa da kisan ɗubin mabiya da manzanni.

Yahudawa da kansu ba su yin musun wannan, sai ma fāriya suke yi cikin sa. Lokacin da tsamiya ta juye da mujiya, sai Kirista suka ɗauki fansa, suka yi ta tsananta wa Yahudawa a kai a kai. Shaida bisa ga misali, Kirista sun yi musu mummunan kisan kiyashi a Turai ta tsakiya da gabas inda aka hallakar da dubban Yahudawa, wannan ya haddasa muguwar ƙiyayya a tsakanin su biyu. Wannan ya ɗauki kusan tsawon shekara biyu.

Idan littafin Yahudawa yana da dalilin da za a soke shi a kan lalatarwa ko jabu, ashe, da Kirista za su yarda su amince da shi, su duƙufa a kansa kamar yadda Yahudawa suke yi? Ashe, da za su ɗauke shi a yadda yake mai tsarki kamar Linjilarsu, su ɗauke shi ya zama tushen duk wallafarsu, su ba shi girma su kuma ci gaba da karanta shi, da nazari, da fassara shi kullayaumin su kuma yi biyayya da abin dake cikinsa? Kirista sun ci gaba da morar sa cikin mafakarsu, da makarantunsu da gidajensu, suna kashe ɗumbin kuɗi kowace shekara don buga shi, da rarrabar da shi a duk fāɗin duniya, ko da shike littafin abokan hamayyarsu ne. Ashe, a nan ba a ganin darasi na muhimmanci, da banmamakin tarihi, da kuma zama ɗaya daga cikin muhimman tabbaci na ingancin Attaura da kuma rashin lalacewar da ake zargin ta?

Manyan masana na zamanin nan suna shaida cewa kofe da dama da ake da su yanzu na Attaura da Linjila an rubuta su tun ɗaruwan shekaru kafin isowar Islama, suna kuma tabbatar da cewa waɗannan kofe suna muwafaka da waɗanda ake aiki da su a yau. Babu ta yadda za a iya lalatar da Attaura da Lijila, wato daddagular da su bayan isowar Islama, ga kuma tabbatarwar da Kur’ani ya ke yi musu.

Babu shakka idan da an yi karambanin yin wani gyara ko sokewa cikin Linjila bayan bayyanar Almasihu, da kuma kafin Islama ta ci da yaƙi, da Kur’ani ya tayar, ya ƙi su a maimakon ya tabbatar da su. Idan kuwa an yi wani karambanin gyara bayan nasarar yaƙin Islama da ya nuna ta wurin gwamawa da tsofaffin kofe na tun farko.

Inda a ce wani zai zaburo ya ce Kur’ani da ake da shi yanzu ba na ainihi ba ne. Ashe, amsar ba za ta zama ba cewa ƙungiyoyin Musulmi da suka yi hilafa kamar su ’yan Sunna, da Shiat da dai sauransu shaida ce ta tabbas cewa Kur’ani da ake da shi yanzu na ainihi ne? In ba haka ba ashe wani daga cikin ƙungiyoyin nan ba zai kawo wani Kur’ani dabam ba, ya yi iƙirari cewa, ai, wannan ne na ainihi, kuma wanda sauran suke da shi lalatacce ne?

Abin a yi la’akari ne ganin cewa, ikon Allahntaka ya bi da masana su gano rubutattun littattafai cikin Ibrananci, da Helenanci, waɗanda bisa ga yadda rubutunsu yake, sun nuna an rubutasu, tun kafin zamanin Islama ya zo, waɗansu suna fiye da shekara 250 tun da aka rubuta su. Da aka gwada su da na yanzu, babu bambanci ko kaɗan da abin da Attaura da Linjila na yanzu suka ƙunsa. Sauran rubutattun takardu da wasu littattafan fassara (sharhi) sun ƙunshi matani daga Attaura da Linjila wanɗanda suka bi da masana su nuna cewa, idan da waɗannan littattafai biyu sun ɓata, da zai yiwu a iya sāke rubuta wata Attaura da Linjila na ainihi daga waɗannan ɗumbin rubuttun takardu cike da matanai daga Attaura da Linjila na ainihi. Abin shaida irin wannan ya isa zama isasshen tabbaci na mutuncin littattafai (Linjila) wadda Kirista suke da ita a yanzu. Duk da zub da jini sau da dama, da kuma muguwar ƙiyayyar da ke a tsakanin wasu daga cikin ɗarikunsu, sun haɗu babu wata shakka a kan wannan batu. Bari a san abin da ke akwai, shi ne bambance-bambancen da suka shafi juya Linjila cikin harsuna ne da kuma fassarar ta. Waɗannan ma sun tarke a kan wasu kalmomi ne ’yan ƙalilan, da wasu taron kalmomi kima waɗanda ma ba muhimmai ba ne ainun ko kaɗan, kuma ba su yi wani lahani ba ga ɗayantakar Linjila wadda dukan Kirista suke riƙe da ita a kowane mataki na tarihi.

Bari mu komo ga batun da muka nuna a can baya a game da shisshiƙen ɗayantakar da ke a tsakanin Attaura da Linjila, wanda ke tabbatar da ainihinsu. Lokacin da Musulmi ya karanta Attaura zai yi la’akari, ba shakka, a kan bambance-bambance da dama ga sabuwar tsara da ke jira. Wannan hange na sabuwar tsara, Yahudawa da Kirista dukansu sun yarda da haka yake. Linjila wadda ya kamanta da bukatan littafin da aka saukar a gabaninta, wanda ta tabbatar, ba yadda za a yi jabunsa ko a dagula shi Sunansa “Sabon Alkawari”, wannan yana nuna dangantakarsa da “Tsohon Alkawari”, wato Attaura. Kirista masana ba za su damu da kāre Linjila ba sai dai in abin ya zama jazaman. Sun fi damuwa ko kula da tabbatar da ainihinta. Mutum mai basira, yana da sanin cewa lokaci zai fallasa ƙarya da maƙaryacin, ba kuwa zai taɓa yarda ya zama mai bin abin da yake ƙarya ne ba. Zai bayyana duk wanda ya manne wa ƙarya ya zama abin raini.

Sai mutane masu sani kaɗai za su gane irin zurfin ƙoƙarin da masana suka yi cikin bincike a kimiyyance na Linjila da wasu batutuwa da suka dangance ta. Wasu daga cikin masu binciken, masu ƙin koyarwar Linjila, sun so, in da ya yiwu, su ƙaryata Linjila a kimiyyance. Sauransu da suke gaskata Linjila, suna da himma ƙwarai cikin bincikensu don su kawar da wani son zuciya nasu da zai ɓata hukuncinsu. Duka biyun sassan suna da manufa guda: ita ce su gane gaskiya ko da shike suna da bambance-bambance cikin maƙasudansu. Sakamakon bincikensu cikakkiyar yarda ce cewa almajiran Almasihu ne Suka rubuta Bishara (Linjila) da tsararsa waɗanda littattafansu suna ɗauke da sunayensu. An gabatar da cikakkiyar shaida mai tabbatar da cewa Attaura da Linjila da suke a yanzu na ainihi ne, Kur’ani kansa ma ya yarda da haka, don haka ba su da aibun kome, ko zama ’yan jabu.

Duka an yarda cewa muhawara ta kai tsaye kuma ta gaskiya zai sa kowane sashi a ɗan lokaci ya zaci cewa iƙirarin abokin hamayyarsa daidai ne, sa’ad da ake jiran kafa gaskiya yadda muhawara za ta ci gaba. Saboda haka, a mafarin wannan nazari, mun ɗauka hakanan cewa iƙirarin Musulmi na cewa Kur’ani yana da hurewar allahntaka. Muna da ’yanci ke nan mu ce wa Musulmi da Kirista kowannensu ya tsayar da kansa cikin al’amuran addini na littattafansu waɗanda suka gaskata cewa hurarru ne. Idan kowa ya tsaya kan nasa, to, yawancin matsaloli mawuta masu kawo rashin jituwa za a kau da su daga tsakaninsu cikin al’amuran addini. Waɗannan abubuwan sa tuntuɓe sun taso ne daga ƙare-ƙaren da aka yi ga abin da aka rubuta ta wurin hurewa.

Za mu gamsu da ambatar wani ƙari guda na Kirista, da kuma ƙari guda na Musulmi. Zai yiwu mafi wuya duka shi ne, Musulmi ya ji Kirista ya furta, ko ya karanta cikin littattafan Kirista, yana ambatar Maryama, mahaifiyar Yesu, a matsayin “Maryama uwar Allah”. Idan akwai irin waɗannan muƙamai cikin hurarrun littattafan Kirista, to, babu wani zaɓi sai a more su.

Amma saboda ba shi da wani iko na kowane iri, ba a yarda da a yi aiki da shi ba. Gama, Almasihu, wanda yake ɗan Maryama ne bisa ga jiki kaɗai. Ba shi yiwuwa Maryama ta sami wani matsayi cikin Allahntakarsa. A gefe guda kuma, zai yiwu abu mafi wuya da Kirista zai ji daga bakin Musulmi, ko ya karanta cikin littattafansa shi ne, rashin kāsawa ko rashin isa na annabawa cikin hanyar rayuwarsu. Idan wannan batu gaskiya ne, to, bai yi muwafaka da Attaura da Linjila ba, sun soke wannan. Saboda haka, ba shakka cewa, hanya mafi kyau ta kaiwa ga fahimta, da yarjajjeniya ita ce, a yi watsi da ƙare-ƙaren da ’yan adam suka yi, a wadatu da ainihi na Allahntaka. Bayan duba abin da Musulmi na gaskiya yakan faɗa bisa ga Kur’aninsa, tambayar ita ce, “Me Kirista na gaskiya yakan faɗa bisa ga Linjilarsa wadda aka tabbatar cikin Kur’ani?” Tun da fari an lura da abin da Musulmi na gaskiya, mai bin bangaskiyarsa da kyau, zai ambato daga lambunsa na Kur’ani a game da matsayin ɗaukaka na Almasihu, kuma daga Linjila wadda take ɗauke da labarin rayuwarsa da koyarwarsa. Yanzu ana bukatar Kirista ya bayyana wa Musulmi wasu abunbuwa masu daraja na lambunsa na yin bishara, ta haka zai taimake shi ya kai ga daidaitaccen hukunci a kan al’amuran Kirista.

Sharhohin da ake kan yi, gabatarwa ne ga babban maƙasudin rubutunmu don mu auna muhimmancin maganar Almasihu da ya ce, “Ni ne Hasken duniya”.

Linjilar da muka mallaka wadda Kur’ani ya tabbatar da ita, Kur’ani kuma ya nuna cewa babban Annabin ya furta haka, duk da haka, da wannan furci ya zama maɗauri ga Musulmi kuma. Kamar yadda hasken rana yake ga kowa da kowa, ba a tarke ga wani sashin ’yan adam ba, haka ga Hasken Allahntakar gaskiya domin kowa da kowa ne.

Furcin nan na Almasihu, “Ni ne Hasken duniya,” ya zo ne daga cikin jawabin da ya yi wa mutanen Yahudawa da shugabanninsu a cikin babban Haikali a Urushalima. Wannan magana ba mai sauƙi ba ce, kuma da wuya a yarda da ita, sai masu sauraronsa suka ƙi wannan magana gaba ɗaya. Amma ƙi, ko yarda da wannan furci ya danganta ne ga abin da aka gaskata a kan mutumin da ya yi furcin.

Idan wani baƙo mai ziyara ya yi iƙirarin cewa, “Ni ne mai mulkin jiha mafi girma a duniya,” yaya masu sauraronsa za su ɗauke shi? A gaskiya za su yi tunanin cewa: a) yana wasa ne, ba za su ma kula da batunsa ba; b) yana da taɓin hankali shi ya sa yake magana marar ma’ana, sai su ji tausayin sa, su nesanta kansu da shi; c) shi babban maƙaryarci ne, sai su yi masa ba’a, su kauce masa; ko d) batunsa gaskiya ne, yadda har masu sauraron sa za su girmama shi saboda babban muƙaminsa.

Tabbatacce ne, babu Musulmin kirki da zai zargi Isa ɗan Maryamu a kan yana maganar wasa, ko maganar rashin tunani ko ta ruɗi. Saboda haka duk maganarsa gaskiya yake faɗi duk da wadda ya ce, “Ni ne Hasken duniya”. Idan da irin wannan kalmomin ne kaɗai ya yi iƙirari, da sai a yi zaton cewa an shigar da ita cikin Linjila da kuskure ko kuma da yaudara. Amma duk da haka, wannan iƙirari ya yi muwafaka da sauran iƙirarai da wannan mashahurin Annabi ya yi suke cikin Linjila. Ya kuma yi daidai da muƙamin da ya riƙe cikin dukan lokacin da ya bayyana cikin mutane, saboda haka dole shi ne ya zama “Hasken” Musulmi kuma. Wannan batu muhimmi ne domin ya haɗu da cetonsu madawwami, Mutum mai hankali ya san cewa batun ceto da madawwamiyar tāɓewa muhimmi ne kuma mai kyau fiya da bambance-bambancen ɗariku/addinai, batun nan kuma ba shi sākuwa daga mutane zuwa mutane, ko daga doka zuwa doka. Waɗannan batutuwa kwatanci ne ga hasken ruhaniya wanda haske yake alamtawa, wanda bambancinsa bai shafi ainihin tushen batun ba, domin shi marar sākuwa ne har abada.

Ba shakka lokacin da Allah ya ta da Mai Ceto domin ’yan adam, ceto daga madawwamiyar tāɓewa/halaka. Wannan kuwa yana da amfani ga Yahudawa, dole kuma yana da amfani ga Musulmi, da Kirista da arna ma. Tambayar cewa wanene Mai Ceto wanda Allah ya sa ya ceci ’yan adam daga zunubi da hallaka ita ce muhimmin batu ga dukan addinai, amsar kuma iri ɗaya ce duka.

An yarda cewa bambance-bambance a kan aukuwar abubuwa zai yiwu su zama da amfani, ko ma wajibi, kamar yadda yatsotsin hannu suka bambanta, da bambancin sassa na sojoji. Amma bambance-bambance masu ma’ana da kuma amfani ba fa za su iya zarce shika-shikan addini ba.

Kamar yadda dukan “Mutanen Littafi” sun yarda cikin gaskata cewa akwai Allah ɗaya kaɗai mai mafificin jauhari, don haka aikinsu ne su yarda a kan wanda aka sa wa wakilcin Allahntaka, Allah ya sa shi domin ceton dukan ’yan adam. Wannan yarjajjeniya tana da zuzzurfan muhimmanci. A kan wannan tabbataccen wakili kaɗai, bayanin tunanin Mahalcci ya dangana da bayanin cikakken nufinsa, da kuma bayanin shirinsa na Allahntaka domin ceton ’yan adam daga zunubi, tare da sharuɗa domin tsira daga madawwamin hukunci. Wannan kaɗai da aka aiko daga sama yake iya zama misali da kansa a idon ’yan adam, duk abin da zai yiwu, yardajje kuma don ya bayyana ko ya nuna jauharin Allah Mai Iko Dukka, ya sa a gabansu ta wurin rayuwarsa cikakken misalin ɗan adam domin su bi a kowane mataki. Daga nan, wanene wannan makaɗaicin wakili da aka aiko domin ceton ’yan adam?

Linjila tana ɗauke da ayoyi masu nuna cewa, cikin Isa ɗan Maryamu, dukan cancanta da sharuɗa da muka ambata suka cika. Asirin ke nan, na murna marar matuƙa take ga masu karanta Linjila da gaskiya, da hankali, da kuma muradi mai aminci don sanin yadda mutu ya cetu daga zunubi da hakkin zunubin.

Kimiyya tana sanar da mu cewa, lokacin da tsirkiyoyin rana suka fāɗa a kan wani abu mai ƙarfi da ya tare su, yakan rarrabu cikin bakwai da hasken ya ƙunsa. Lokacin da tsirkiyoyin kuwa suka fāɗa a kan su ɗigon ruwan sama, sai su sa bakangizo; zamanin da can, an ba da wannan a matsayin tabbaci ga adali Nuhu, jinƙan Allahntaka ga ’yan adam. Almasihu ne jinƙan Allahntaka ga ɗan adam zunubabbe, halakakke, Shi ne Hasken duniya ya zo daga sama. Idan duniya ta sami ribar kayan duniya daga hanyar ’yan kimiyya sun raba haskensa cikin launi iri iri domin a mori kowanne don dalili na musamman, ina misalin girman amfanin ruhaniya da za a samu daga nazarin kowane jauharin mutumin nan da yake “Hasken duniya”?

Mai karatu zai sami muhimmin nassi dangane da irin wannan batu dalla-dalla cikin maganar da manzo Yahaya ya yi a cikin Sabon Alkawari, mai cewa:

“A ranar Ubangiji ya zamana Ruhu ya iza ni, sai na ji wata murya mai ƙara a bayana ta ƙoho, tana cewa: (Ni ne Alfa da Omega, farko da ƙarshe)... sai na juya in ga wanda ke mini magana, da juyawata kuwa, sai na ga fitila bakwai na zinariya. A tsakiyar fitilun nan kuwa, na ga wani kamar ɗan Mutum, saye da riga har idon sawu. ƙirjinsa kuma da ɗamarar zinariya. Kansa da gashinsa farare fat ne kamar farin ulu, farare fat kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kamar harshen wuta, ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar wadda aka tace a maƙera, muryarsa kuma kamar ƙugin ruwaye masu gudu. Yana riƙe da tauraro bakwai a hannunsa na dama... ” (Wahayin Yahaya 1:10,11,12-16).

Muna iya ɗaukar kowane tauraro daga taurarin nan bakwai dake cikin hannuwan mutumin nan maɗaukaki wanda ke “kama da Ɗan Mutum” a shi wakili ne na ɗayan na mabambantan halaye, wanda ya haɗe ya zama mutum guda, ya samar da haske mai haskakawa, wanda ya cancanci zama Hasken dukanin duniya.

Cikin tattaunawarmu ta yanzu, muna mai da hankalinmu ga waɗannan jauharai na Almasihu, wanda zamansa na dabam, shi kaɗai yake da su ba wani ba. Ba muna duban waɗannan halaye waɗanda cikinsu ne ya fifita gaba da sauran manzanni da annabawa ba, halaye kamar su hikima, kamewa, tawali’u, himma, tausayi, da adalci, biyayya ga nufin Allahntaka.

An gane cewa, ba a iya sanin halayen Almasihu, sai dai an karanta tarihinsa cikin Linjila. Labaru domin wannan tattaunawa su ne kalmomin Sabon Alkawari waɗanda a saninmu su ne na ainihi a rubuce, mun gaskata kuma su ne zahiri, rahoton gaskiya kuma a game da Yesu Almasihu kansa, kalamansa, da kuma ayyukansa. Muna da ’yancin kafa bege cewa Musulmin da ba ya ɓoye gaskiya zai yarda da halaye mabambanta na wannan mutum mai martaba, wanda aka alamta cikin taurari bakwai da yake riƙe a hannunsa na dama.

Haske na wannan duniya da aka saba gani ba daga duniya kanta ba ne amma na wasu halittu ne basamaniyai sama da duniya. Hasken ruhaniya na duniya ba yadda za a yi ya zo daga mutanen duniya, amma zai zo daga bisa, daga sama, tushen hasken ruhaniya. Saboda haka, ba mamaki cewa, wanda ya ce “Ni ne Hasken duniya”, Sau da dama yakan hurta cewa ya zo daga sama. Linjila tana sanarwa cewa: “Tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin ɗa daga wurin Ubansa” (Yahaya 1:1,14).

Yesu ya faɗa wa Yahudawa masu sauraronsa: “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyan nan ba ne” (Yahaya 8:23). “Domin haka musamman kuma na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya” (Yahaya 18:37). “Ni ne gurasan nan da ya sauko daga Sama” (Yahaya 6:41). “Tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne” (Yahaya 8:58). Cikin dukan al’ummomi da ɗariku, sanannen abu ne a sa wa yaro sunan wasu manyan mutane, musamman sunayen annabawa. Mun lura cewa, mutane da yawan gaske sun ɗauki irin sunayen nan kamar su, Ibrahim, Saratu, Yakubu, Yusufu, Rebeka, Rahila, Musa, Haruna, Sama’ila, Hannatu, Dawuda, Sulemanu, Iliya, da kuma su Muhammadu, Ali, Hadiza, Fatima, Hassan, Husaini, da Su Ahmadu. (Yesu kuwa da shike sunan Linjila ne, wanda Musulmi suke kira Isa). Sunan nan Yesu ba a taɓa ba da shi ba ga ’ya’yan mutane kusan sama da shekara dubu biyu saboda sassalarsa basamaniya ce alhali sunan mahaifiyarsa, Maryama, yana ɗaya daga cikin sunayen da aka fi mora ko’ina a duniya.

Lokacin da Yahudawa suka ƙi maganarsa mai cewa shi ne hasken duniya, ga amsar da ya ba su, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbataciya ce, domin na san inda fito, da kuma inda za ni” (Yahaya 8:14).

Daga baya, lokacin da ya yi addu’a ya ce, “Yanzu kuma ya Uba ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakan nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance” (Yahaya 17:5).

Ba shi yiwuwa idon ɗan adam ya fahimci hasken Allahntaka. Muna da shi cikin Linjila, “Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Amma Makaɗaicin ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi” Yahaya 1:18).

Wannan aya tana nuna cewa Shi da yake “Hasken duniya” ya sauko daga sama zuwa ga ’yan adam ta wurin ɗaukar ainihin surar ɗan adam, lokacin da budurwa Maryamu ta haife shi. Ya zama dabam da sauran manzanni ko annabawa ta wurin saukowarsa daga sama, da kuma zama mutum. Tun da shi kaɗai ne mutum basamaniye da ya taɓa zama a fuskar duniya, to, yana da ’yancin zama Hasken dukanin duniya.

A can baya mun ambaci cewa, halayensa mabambanta shi da yake “Hasken duniya” an nuna su kwatanci ta wurin taurari bakwai da ya riƙe a hannunsa na dama (Wahayin Yahaya 1:16) na fari daga cikin abubuwan da ke nunawa . . .

Basamaniyen asalin Yesu Almasihu

Daga wannan tauraro ake haskaka hasken cikakken tsarkin halinsa, domin babu shakka ba wanda ya isa ya zama Hasken duniya sai wanda yake tsantsan tsattsarka.

Daga cikin mutanen duniya babu tsantsan tsattsarka, ba kuma inda irin mutumin nan zai fito sai dai daga sama, inda tushen tsarki yake. Saboda haka, saukowa daga sama muhimmin sharaɗi ne ga mutumin da Allah zai ɗaga ya zama Mai Ceto da mai roƙo domin ɗan adam. Zukatan mutanen da ke biɗar ceto da adalci galibi sukan buɗe zukatansu ga Mai Ceto da ke zuwa gare su daga sama, domin shi kaɗai ne ya ke bayyana al’amuran samaniya a gare su a sarari, kuma cikin gaskiya. Wanda yake bin Mai Ceto wanda asalinsa basamaniye ne, wanda tsarkinsa tsantsa ne, wanda yake biɗar ya shaƙu da shi, yana kuma karɓar tsarki ta wurin duban sa kullayaumin. Hasken tsarkin mai ceto yana haskake duhun hanyarsa, ya kuma bayyana masa sabon zahirin samaniya, domin Mai Ceton nan da fari ya fi son tsarkin zuciya, na biyu kuma ana ganin tsarkin a aikace. Yesu ya fayyace wa mabiyansa wannan cikin maganarsa. “Amma ni ina gaya muku, kowa ya ke fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi... saboda haka, in kana cikin miƙa hadaya a kan bagaden hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan’uwanka yana da wata magana game da kai, sai ka dakatar da hadayarka a gaban bagaden hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan’uwanka, sa’an nan ka zo ka miƙa hadayarka... Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita. In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar... Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah... ko da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki. Kada kuwa ka rantse da kanka... Abin da duk za ka faɗa, ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A’ a’ kawai, In dai ya zarce haka, to, daga mugun ya fito” (Matiyu 5:22-24, 28-30, 34-37).

“Saboda haka, sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke” (Matiyu 5:48).

Shi kaɗai ne mutumin da ya aikata dukan abin da ya faɗi. Ya aikata fiye da abin da ya sa wasu su aikata. Dubansa da gaskata shi babban taimako ne ga duk wanda yake muradin tsarki domin kansa; gama Nassi yana cewa: “Ku zama a tsarkake, in banda shi kuwa ba wanda, zai ga Ubangiji” (Ibraniyawa 12:14).

Sananne ne cewa, cikin wahayi, muhimmin abu shi ne mutumin da ba ya ganin abin da ake gani; cikin ji kuwa, mai jin ne ba abin da ake ji ba, cikin jawabi kuma, mai yin jawabin ne ba jawabin ba. Cikin addini kuma, muhimmin abu shi ne mai bi kansa, ba irin gaskatawar ba. Wannan ba ana nufin ƙasƙantar da muhimmancin abubuwa, da sauci da magana ko irin gaskatawa ba ne, amma an yi niyyar misalta koyarwar Kirista ne, wadda take shelar muhimmancin dangantakar mutum, mai ɓuɓɓugowa daga zuciya, da ɗayantuwar ruhaniya a tsakanin kowane mai bi, da Mai Ceton duniya da Allah ya sa.

Daga wannan ɗayantuwa ne rinjayen ruhaniya yakan samu, wanda a hankali ya ke sāke halayen mai bi na ƙwarai zuwa kamannin Mai Ceto, cikin halin kirki da kammalar addini. Duk mai kiran kansa Kirista amma rayuwarsa ba ta da irin rinjayen nan, ba shi da tabbaci, Kristancinsa kuma na bisa - bisa ne, ba na ƙwarai ba ne.

Saukowan nan daga sama da Almasihu ya yi, ba fifita shi ya zama mafi girma da zama adali kaɗai ta yi ba a kan dukkan ’yan adam, amma bambantakarsa cikin dukkansu ne. Babu wanda zai iya riƙe wannan muhimmiyar tauraruwa a hannunsa, sai Yesu Almasihu Shi kaɗai.

Raɓe da tauraruwan nan akwai na biyu shi ne:

Annabce-annabce a Game da Almasihu

Ko da shike an yi annabce-annadce a game da ɓullowar wasu mutanen tarihi, Yesu Almasihu ya sha bamban cikin irin sanarwa da aka yi kamin zuwansa. Sun bambanta daga annabce- annabcen da a ka yi a kan kowane mutum ta wurin daɗewa da riɓanya da ci gaba har dubban shekaru. Gaskiyar annabce-annabce kuma an nuna ta ta wurin bayanai marasa kuskure, da mutane da dama wurare dabam dabam cikin rayuwar wanda ya nuna su. Waɗannan wahayi an yi wa mutane da yawa waɗanda aka gusar can nesa cikin lokaci da wuri, suka kuma zauna a ƙarƙashin al’amura dabam dabam. Masihin da aka yi faɗinsa, zai zo cikin wata hanyar da ba wanda zai iya bi, ba wanda zai iya shiga tarihinsa.

Daga cikin mafiya muhimmanci na waɗannan wahiyi su ne, alamun da aka ba da ta wurin umarnin Allahntaka, kuma Isra’ila suka aikata su ka’in da na’in cikin dukan tarihinsu. Cikin zamanin dā can, tushen haske domin zaɓaɓɓun mutanen Allah shi ne, Masihi da aka alkawarta. Lokacin da “cikar lokaci” ta zo, wannan mutum ya bayyana, ya tabbatar gaskiya ne cewa Shi ne Hasken duniya tun kafin ya zo – Shi ne daga lokacin halittar Adamu har zuwa lokacin bayyanarsa, ba sai tun lokacin da ya bayyana kaɗai ba.

Daga tauraruwar waɗannan wahayin annabci, da aka yi ta maimaita su cikin dubban shekaru, tana haskaka hasken mutuncin Yesu Almasihu da gaskiyarsa, domin mutumin da wahayan suka cika a cikinsa, ba wani ba ne in banda mabambancin nan. Ceton ’yan adam ya dogara ga gaskiyar maganarsa da alkawarinsa, gama gaskiya cikin ceton ’yan adam muhimmin inganci ne. Gaskiya kaɗai ke haskakawa. Sauran abu duka duhu ne. Hasken duniya ba kome ba ne illa gaskiya. Shi wanda ɗaukaka ta tabbata a gare shi ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yahaya 14:6).

Shi mai aminci ne cikin kowane alkawari nasa, saboda haka waɗannan alkawarai wuri ne mai lafiya, kuma ƙaƙƙarfan ginshiƙi cikin dukan al’amura na rayuwa. Ga mai bi na ƙwarai alkawaran suna tabbatar da wadatuwa tagari, da kuma cikakkiyar wadatuwa a nan gaba (lokaci mai zuwa). Yaya gaskiyar maganan nan take a game da murnar da mai karanta Linjila zai samu, wadda take ƙunshe da waɗannan alkawarai, murnar da ke watsar da dukan shakka da jin tsoro da kuma baƙin ciki.

Saboda haka, ba mamaki yadda kowane Kirista wanda ya gane da ma’anar gaske ta jawabin Kirista, zai yi marmarin faɗa wa wasu, musamman ga ɗan’uwa Musulmi. Wannan saƙo albishir ne na farin ciki, wanda yake kore baƙin ciki, ya cika zuciyar mai bi da cikakkiyar salama, da wadatarwa da murna. Wannan tauraro mai hasken annabtaccen wahayi ba a riƙe shi da hannun wani ba sai hannun daman Yesu Almasihu.

Ƙari a kan taurarin nan biyu mun ga na uku. Shi ne:

Ikon Yesu Almasihu Cikin Magana da Aiki

Sauran annabawa da manzanni sun yi iƙirari cewa, kalmomin da suka faɗa ba nasu ba ne. Sun fara da cewa: “Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce” ko “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa...” Amma Yesu ya yi magana ta hanyar da ta hura marubutan Linjila su faɗi, “Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba” (Matiyu 7:28,29).

Almasihu Yesu wata rana ya ce, “An mallaka mini dukkan iko a sama da ƙasa” (Matiyu 28:18).

“Uba ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukkan hukunci ga ɗan, domin kowa ya girmama ɗan, kamar yadda ake girmama Uban da ya aiko shi” (Yahaya 5:22,23).

Ya yi alkawari zai komo duniya cikin ɗaukakarsa, cikin iko tare da tsarkakan mala’ikunsa, da zaɓaɓɓunsa (Matiyu 25:31). Saboda haka, ɗaukaka, da mala’iku, da zaɓaɓɓu duka nasa ne, domin kuwa Shi da Uba ɗaya suke kamar yadda ya faɗi.

Ya kuma ce rana ta ƙarshe zai ta da waɗanda suka gaskata Shi (Yahaya 6:39,40), zai kuma ta da, ya ba da rai ga wanda ya nufa (Yahaya 5:21).

An nuna ikonsa cikin ayyukansa da kalamansa, domin ya aikata kai tsaye yana ba da cikakkiyar gafarar Allahntaka mai ɗorewa ga waɗanda suka yi tuba. Yin haka ya harzuƙa fushin shugabannin Yahudawa masu zargin sa da yin sāɓo, suka yi tambaya “Wa yake da ikon gafarta zunubai, sai Allah kaɗai” (Markus 2:7).

Lokacin da ya tada matacce, shi ne ya ba da umarni, kamar lokacin da ya tada Li’azaru, ya ce, “Li’azaru, ka fito!” (Yahaya 11:43).

Haka kuma ya umarci aljannu, da raƙuman ruwa, kamar wanda yake da iko a kansu, sun kuwa yi masa biyayya. Cikin nuna ikonsa cikin magana da aiki, ba shi kwatantuwa da kowane annabi ko manzo.

Daga wannan tauraruwa mai haske, tauraruwar ikonsa, ta haskake hasken dukan ikon da yake da shi. Ya ce, “Amma don ku sakankance ɗan mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya” (Markus 2:10).

Ko akwai wani wanda ba shi da irin ikon nan amma ya iya ba da haske ga dukanin duniya ya kuma iya ceton ’yan adam? Ko kaɗan ba zai iya ba, domin kuwa ba wanda zai dogara ga mai ceto wanda iyawarsa ta ɗan adam ce kawai.

Ta haka ne tauraruwar iko na Yesu Almasihu take haskaka hanyar duk wanda ya gane da kāsawarsa, yana neman Mai Ceto wanda yake da iko don ya nemi mafaka a cikin sa. Zai sami wannan cikin Yesu Almasihu, wanda ya fitar da aljannu, Mai Ceto wanda ya fitar da Shaiɗan sarkin alljannu daga zuciyar mutum. Cikin Almasihu, wanda ta wurin magana ya kwantar da haukan hadirin teku, mutum zai sami wanda zai kawar masa da makārin da ke sa fāɗuwa. Cikin wanda ya ta da matacce, mutum zai sami Mai Ceto wanda daga cikin Ruhunsa mutum zai sami rabon rai da iko. A cikinsa ne Shi wanda ya buɗe hannuwansa da zuciyarsa ga matalauta, da rainannu da tubabbun masu zunubi, mutum zai sami wanda zai yi roƙo domin sa da ma’ana a gaban kursiyin ɗaukaka cikin Sama. Cikin Almasihu, Shi wanda ya tashi daga cikin matattu a rana ta uku, mutum zai sami Mai Ceto wanda zai tumɓuke tsoron mutuwa daga zuciyarsa, ya sāke gādon mutuwa zuwa dakalin rai. Cikin Almasihu mutum zai ga nasarar gidan wuta ta fāɗi, an yi nasara da ita, kuma ƙofar zuwa cikin duhun kabari ta juye zuwa ƙofar da take jagora zuwa murna marar matuƙa cikin maɗaukaka na sama.

Iko, ya zama muhimmin abu domin Mai Ceto wanda Allah ya tasa, ya kuma mai da shi Hasken duniya. Wannan ne tauraruwar da ba mai riƙe ta a hannun damansa, sai Yesu Almasihu kaɗai.

Tauraruwa ta huɗu ita ce:

’Yancin Samun Mubaya’a

Duk mutumin da ke ƙin a yi masa sujada, yana tabbatar da cewa bai cancanci a yi masa wannan irin mubaya’ar ba. Duk da haka lokacin da mutumin da aka sani mafifici ne cikin adalci ya bayyana, ya kuma nuna shi ne Makaɗaicin ɗan Allah, ya zo daga sama, ya karɓi mubaya’a sujadar da aka yi masa, wannan karɓa da ya yi tabbatarwa ce ta iƙirarin da ya yi mai nuna shi mafifici ne a kan kowane ɗan adam, kuma shi mabambanci ne. Ba shakka, wannan ne ma’anar karɓar sujada da Almasihu ya ke yi.

Mun san cewa babu wani manzo, ko annabi, ko mala’ika da ya isa a yi masa sujada, ko a ba shi wasu muƙamai waɗanda Allah kaɗai yake da su. Amma Yesu Almasihu, da saninsa wanda ya fi na kowa, da tawali’unsa mai gairma da zumuntarsa ta kurkusa da Allah wanda ya girmama, duk da yardarsa da cewa ga Allah kaɗai za a yi sujada, bai ƙi yarda a yi masa sujada ba, yana karɓar sujada har daga wurin almajirinsa, waɗanda koyarwarsa ta girmad da su. Lokacin da ɗaya daga cikin almajirinsa ya ce “Ya Ubangijina da Allahna” (Yahaya 20:28), Almasihu bai tsauta masa ba, ko ma a lokacin da guda almajirin ya ce, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka” (Yahaya 21:17).

Mutane sun san shi kafinta ne matalauci daga ƙauyen Nazaret, ba shi kusa da wani mulki na yanzu ko nan gaba. Amma lokacin da ya shiga Urushalima haye da jiki, jama’a sun gaishe shi da sowar murna: “Albarka ta tabbata ga sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji” (Luka 19:38).

Maƙiyansa sun mori wannan al’amari ya zama hujjar neman su gicciye shi, suka yi ƙararsa a gaban gwamnan Romawa cewa yana tayarwa gāba da kursiyin Kaisar. Da gwamna ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” (Yahaya 18:33), Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne” (Yahaya18:36). Gwamna da kansa ya rubuta muƙamin ya manna shi a gicciyen.

Rubutun cikin harsuna uku ya yi shi, yana nuna cewa, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa” (Yahaya 19:19).

Ba a taɓa yin irin wannan abu ba ga wani annabi ko manzo. Ko wani ya tarke aikin ceto ga kansa kaɗai kamar yadda Yesu Almasihu ya yi, shi da ya yi ta kiran mutane su zo su ba da gaskiya gare shi. A fayyace yake cikin wasu hurcinsa da dama kamar haka: “Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku” (Matiyu 11:28).

Lokacin da ya ke magana, bai yi da jam’i don haɗa kai da wasu cikin al’amuran addini ba, kamar yadda akan yi, amma ya ce “Ni” ba “Mu” ba, yana nuna bambantakarsa cikin mutane cikin ikon addini. An kuma nuna bambantakarsa ta wurin yadda bai taɓa neman gafarar Allah ba, ko ya nuna tuba ko furta wani zunubi.

Daga wannan tauraruwa ne, aka haskaka ’yancin Yesu Almasihu na karɓar sujada, da kuma ’yancin zama shugaban ’yan adam. Bukatar ’yan adam ita ce ta shugaban da ya dace ya bi da dukan mutanuwan duniya a kowane wuri da kowane zamani, daga kowace kabila, da kowane harshe, da al’amura, da al’adu, ko bukatu. Don ya fisshe su daga lalacewar zunubi da duhu zuwa firdausin tsarki da salama, ɗan adam yana bukatar shugaba wanda yake da ’yancin faɗin yadda Yesu ya faɗi, “Wanda ke bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai” (Yahaya 8:12).

Wannan shugaba wanda ya zo daga Sama, aka kuma ba shi iko, da ’yancin karɓar sujada, Shi ne wanda ya dace domin dukan duniya, da kuma zama zaunannen shugabanci a kan dukan ’yan adam. Tauraruwar mubaya’a wadda aka danƙa wa wannan Mai Ceto don ya haskaka, ya ƙarfafa dukan mutane su bi gurbin waɗanda suka ba shi girma. Irin waɗannan jama’a sun amince da ’yancinsa na karɓar sujadar bisa ga zamansa na zama kwatanci na halin mutunci, da tawali’u, da musun kai. Mutanen nan sun sami murna irin ta daban ta wurin yin addu’a gare Shi, domin ya ɗauki siffar ’yan adam, duk da jarabobi, da shan wahalai, da kasancewa kusa da su, ya tausaya wa kumamancinsu. Wannan tauraruwa ta mubaya’a tana cikin hannun daman Yesu Almasihu kaɗai, ba wani sai Shi.

Tauraruwa ta biyar ita ce:

Kasancewarsa A nan

Sau da dama Almasihu ya nuna cewa zai kasance cikin ruhu da a zahiri tare da waɗanda suka ba da gaskiya gare shi, a ko’ina, a dukan lokaci kuma, kuma zai haskaka duhun zukata, zai zauna cikin su ta wurin Ruhunsa. Kamar yadda yake gaskiya gaba ɗaya, wannan alkawari na kasancewa ya sa ya cancantar da shi ya zama haske domin dukanin duniya, kai mai rai na dukan waɗannan da suka gaskata da shi.

Daga tauraruwar ci gaba da kasancewarsa tare da masu binsa a duk inda suke, tana haskaka hasken mafificin saninsa. Wannan sani muhimmin inganci ne a cikin sa shi wanda a cikin cikar annabce-annabce, ya zo daga Sama, ya karɓi iko, an kuma ba shi girma cikin mubaya’ar sujada. Bugu da ƙari, kasancewar mutum da irin wannan muhimmiyar fifita ta kawar da dukan shakka a game da mafificin saninsa. Linjila ta faɗa a game da Almasihu, “Domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin Shi kansa ya san abin da ke zuciyar ɗan adam” (Yahaya 2:24,25). Linjila kuma ta ce, “Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, ya ce, ‘Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?’” (Matiyu 9:4).

Almajirinsa ma suka ce masa, “Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito” (Yahaya 16:29,30).

Wannan irin inganci na “kasancewarsa tare” ba a taɓa samun sa ga wani annabi ko manzo ba, ko waninsu ya yi iƙirarin haka a kan kansa. Daga nan wannan ya zama tauraruwa mai haske wadda babu mai riƙe ta a hannun damansa, sai Yesu Almasihu kaɗai.

Tauraruwa ta shida tana haskaka gaskiyar:

Mutuwarsa da Tashinsa daga ciki Matattu

Babbar manufar zuwan Yesu Almasihu cikin duniya shi ne, don ya mutu domin ’yan adam ta wurin miƙa kansa hadayar kafara domin zunubansu, ya kuma buɗe ƙofar ceto da aljanna ga waɗanda suka tuba. Ya ce, “Ɗan Mutum ma ya zo domin ya ba da ransa fansa saboda mutane da yawa” (Matiyu 20:28), a game da gicciyensa marar makawa kuwa ya ce, “Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, domin duk wanda ya gaskata da shi ya sami rai madawwami” (Yahaya 3:14,15).

Yesu ya yi magana sau da dama kamin a gicciye shi a game da ƙudurinsa na ba da kansa ya mutu a kan gicciye, yana nuna cewa, ta wurin gicciye shi wasu annabce-annabce za su cika. Ɗaya daga cikin waɗannan irin faɗi sun ce, “Aka ƙware shi ba tausayi, amma ya karɓa da tawali’u bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya bai ko ce uffan ba” (Ishaya 53:7). Wata ayar kuma ta ce, “Nufina ne ya sha wahala, mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kowa gafara” (Ishaya 53:10).

Ba za a rarrabe mutuwarsa da darajar tashinsa mabambanci ba a kan rana ta uku, bayan mutuwa ta hanyar da ta bambanta da ta sauran mutane. An tabbatar da manufar mutuwarsa ta wurin tashinsa, kamar yadda ya bayyana a sarari lokacin da yana da rai tukuna. Kamar yadda yake a bambance cikin yin annabcin mutuwarsa ta gicciyewa, da shike kasancewar manufar zuwansa daga sama ke nan, domin haka ya zama mabambanci cikin tashi daga matattu, tun da cikin al’amuran nan biyu, babu manzo ko annabi da ya kwatance shi.

Daga wannan tauraruwa ta mutuwarsa ta kafara, da tashinsa ta bugo hasken ƙaunarsa marar iyaka. Gama dukan sauran taurarin ba su da amfani ga ɗan adam mai zunubi idan ba tare da tauraruwa ta shida ba. Zuwan Yesu Almasihu daga sama, da cikakken ikonsa, da cikar annabci, da karɓar mubaya’ar sujada da zamansa tare da mabiyansa za su nuna kamar zama abin tsoro, da hukunta ɗan adam zunubabbe da halakarsa, sai dai in ya haɗu da ƙaunan nan. Ƙauna irin ta mutum da aka sani ba ta da haske ga duniya mai duhu, domin tana kwatanta lagwani mai hayaƙi kawai. Amma lokacin da aka haɗa al’amuran nan da ƙauna marar iyaka domin zunubabben ɗan adam cikin mutumin nan wanda ya cika dukan sharuɗɗan da suka wajaba domin ceton mutane daga zunubi da madawwamiyar ɓata, to, wannan mutum shi ne ya cancanci zama Hasken duniya.

Girman Almasihu ba shi ne shisshiƙe mafi girma ba na bangaskiyar Kirista, domin jauhari kansa ba ya haskawa. Alal misali, wata, lokacin da ya wuce kwana goma sha biyar, yana nan da cikakken girmansa amma ba ya iya haskake dukan duniya. Haka kuma rana takan rasa girmanta lokacin da dare ya lullaɓe haskenta. Yesu Almasihu ne Hasken duniya cikin muƙamansa, da koyarwarsa, da dukan abubuwan da ke tattare da ƙaunar Allah da ƙauna zuwa ga maƙwabta, har ta kai ga ƙaunar maƙiya.

Hasken ƙauna, wadda ta kai har ga mutuwa domin masu halaka, ta tsiro daga tararuwar mutuwar kafara da tashin Yesu Almasihu. Shi kaɗai ne yake riƙe wannan tauraruwa.

Ƙarin Bayani: Muhimmancin hadaya da zub da jini cikin gaskatawar Kirista ta sa hadaya a kan Dutsen Arafat da tunawa a “sallar layya” (Id-ul-Adh-ha) ta zama mahaɗi mai ƙarfi tsakanin bangaskiyan nan guda biyu.

Tauraruwa ta bakwai ita ce:

Halinsa Na Allahntaka.

Tauraruwa ta shida da aka riga aka ambata, ita ta shirya hanya domin ta bakwai, tana haɗe da ita ba maraba. Mun san cewa gaskatawar Kirista da ta Musulmi, cewa Yesu Almasihu, budurwa ta haife shi, ba batun halinsa na Allahntaka ba ne, amma aukuwa ce ta halitta. Wannan ba ana nufin cewa, shi ɗan adam ne daga baya ya zama na Allahtaka ba, haka ba zai yiwu ba. Haihuwarsa ta wurin budurwa bai sa a yi gardamar Allahntakarsa ba, ko kuma ya tabbatar da Allahntakarsa. Wannan da budurwa ta haifa, ya ɗauki ainihin siffar ɗan adam, tun fil azal kuma yana da ainihin Allahntaka, wannan kuwa bai hana ɗayantakar Allah ba.

Rukunan Allahntakar Yesu Almasihu da kasancewarsa ɗan Allah shaida ce mai iko, gaskata wannan kuma ba zai yiwu ba in ba tare da kyakkyawar muhawara ba da kuma wasu tabbas masu rinjayarwa. Saboda maɗaukakin matsayin Yesu Almasihu, da cikakkun ingancinsa, da iƙirarin da yake yi a game da kansa, dukan waɗannan ƙarfafan tabbaci ne masu yiwuwa. Ya nuna cewa shi ba ɗan Allah ne kaɗai ba, amma kuma shi kaɗai ne ɗan Allah. Kamar yadda Allah Ruhu ne tsantsa, ɗiyancin Almasihu dangantakarsa da Allah ɗiyancin ruhaniya ne tsantsa, babu ko sofanen batun jiki cikin ɗiyancinsa, yin haka ya ɓata ruhunci da ɗayantuwar Allah ke nan.

Kalmomin nan “makaɗaicin ɗan Allah” a harshen Larabci an juya shi cikin harshen (Girkawa) Hellenanci, wanda a ciki ne aka rubuta ainihin Linjila kamar haka, “Makaɗaicin ɗan Allah haifaffensa”. Daga wannan ya zama shaida cewa Yesu Almasihu mabambanci ne daga cikin waɗanda ake kira ’yan’yan Allah, domin ɗiyancinsu ta wurin tallafi ne, ba ta wurin haihuwa ba, amma duka biyu ɗiyancin ruhaniya ne.

Bisa nassin Linjila, Yesu Almasihu ɗan Allah ne cikin cikakkiyar ma’anar kalmar, kamar yadda yake Ɗan Mutum cikin cikakkiyar ma’anar kalmar. Damuwarsa da a san shi a Ɗan Mutum muhimmin manuni ne cewa shi ba ɗan Mutum ba ne kamar yadda sauran mutane suke. Idan ba haka ba, da babu bukatar ya yi ta maimaita yadda shi ɗan Allah ne. Idan wani ya tarar cewa, kalmomin Linjila na almajiran Almasihu ne kawai, to, wannan zai ba da ƙaƙƙarfan goyon baya ga wannan tabbaci: Yadda almajiransa suka fi damuwa da iƙirarinsa na zama Ɗan Mutum bai fi na iƙirarinsa na kasancewa ɗan Allah ba. Dalilin da ya sa Almasihu ya damu da mutane su san shi a Ɗan Mutum, don muradinsa ne ya yi kurkusa da su domin su jingina zukatansu gare shi, ya kuma sami amincewarsu, yadda za su neme shi domin zama Mai Cetonsu.

Dole mu maimaita batun cewa Yesu Almasihu Shi ɗan Allah ne cikin tsantsan ruhanniya, ma’ana marar aibu. Wajabtaccen sharaɗi ga wannan shi ne cikakkiyar kiyaye ɗayantuwar Allahntaka. Ba abin da ya fi wannan wautar jahilci a kan wannan sharaɗi cikin gaskatawa. Musulmi bai fi Kirista na ainihi sanin maganan nan ba mai cewa “Babu wani Allah sai Allah ɗaya kaɗai wanda ba shi da abokin tarayya” kuma “Shi Allah ne, Allah ɗaya, Madawwamiyar Mafaka, bai haifa ba, ba a haife shi ba, babu kininsa” (Suratul Ikhlas 112:-1-4).

Wanda ya kāsa daidaita waɗannan batutuwa da rukunan Kirista mai cewa, “Uban, Allah ne, Ɗan kuma Allah ne, Ruhu Mai Tsarki kuma Allah ne” dole ya mai da hankali ga abin da aka sani a game da ɗayantuwa da kuma akasinta cikin mutuntakar ɗan adam, don kuwa mutum yana da halitta biyu, ɗaya ta jiki, ɗaya kuma ta ruhaniya. Kowane yana zaman kansa, babu shakka. Mutum yana iya faɗar abin da ke daidai ko wanda ba daidai ba a lokaci guda. Alal misali, a ce wane mai mutuwa ne don ya zo daga turɓayar ƙasa, zai kuma koma turɓayar ƙasa. Aka kuma ce, yana da rai marar mutuwa zai rayu har abada. Duk batun nan biyu gaskiya ne. ko wannan rikicewa mai sauƙi haka tsakanin maganan nan biyu za ta iya ƙaryata ɗayantakar mutumin nan?

A cikin Zabura, annabi Dawuda ya ce, “Ka yabi Ubangiji ya raina, kada ka manta da yawan alherinsa” (Zabura 103:2). A nan muna da biyu a haɗe cikin muhimmin ɗayantaka inda mutumin da yake mai yin maganar, kuma shi yake karɓa maganar; kamar yadda yake mai ba da umarini, shi ne kuma mai karɓar umarnin. Bisa ga dokar harshe, wannan wuri mutum biyu ne suke harka, amma a tabbatacce, kuma ga tunani da kyau, mu sani biyun nan abu ɗaya wato mutum guda ne.

Wannan ƙiyasi bai zama kamar ana tabbatar mana cewa, a cikin Allah ɗaya akwai mutum uku ba, wato Uba, da Ɗa da kuma Ruhu Mai Tsarki, ko a cikin Almasihu guda akwai halittar Allahntaka da ta mutuntaka. Amma wannan yana zaman matuni ne cewa, mun yarda da gaskiyar biyuntakar mutum cikin halittarsa, kuma biyuntakar mutum ba ta rikita ɗayantakar halitta ba. Idan haka ne, don me ba za a yarda a faɗi haka ba a kan biyuntakar cikin Almasihu ba, da kuma ɗayantaka da Mahalicci, bisa ga Attaura, ya halicci mutum cikin surarsa.

Kuskuren da wasu Musulmi sukan yi a game da Kirista, shi ne, wai Kirista suna sa wa Allah wasu abokan tarayya, to, wannan rashin ganewa ne. Ɗayantakar Allah shi ne tushen addini, koyarwa Tirniti (Murhunniya) kuwa, kamar ɗiyancin Almasihu, sai a ɗauke shi kawai, yadda ba zai karya ɗayantakar Allah ba, tun da shike doka ta fari daga su goman nan, wadda ta ɗaure Yahudawa tare da Kirista ita ce, “Ni ne Ubangiji Allahnka... kada ka kasance da wasu alloli sai ni” (Fitowa 2:2,3).

Da shike Allah na dukanin ’yan adam ne, babu wata ƙungiya musamman, ko ɗarika, ko al’umma, da za ta iya iƙirarin iya raba shi da sauran, dole kuma haka yake ga wanda yake makaɗaicin ɗan Allah. Shi ba Masihin Kirista kaɗai ba ne, bai ware Musulmi ba. Yadda Kirista suka ɗauka kamar Almasihu ya fi dacewa da su kaɗai, babban kuskure ne wanda ya samu ta wurin rashin kularsu cikin nazarin Linjila, da kuma kāsawarta cikin aikata koyarwarta. Isa, ɗan Maryama, shi ne Masihi domin kowa da kowa, daga dukan ’yan adam, a kowane wuri, a kowane lokaci, in dai mutum ya karɓe Shi. Wanann kira domin dukan duniya ne, babu tārar kabila ko doka. Dukan wannan yana nan a bayyane cikin Linjila, ta kuma amince da haka.

Kowane haske da mutum ya yi iyakantacce ne wuri guda da aka sani, ba kamar hasken da Allah ya yi ba, wanda yake hasken dukan duniya. Haka kuma akwai bambanci a tsakanin addinin da mutum ya fara, ya kuma takura shugabansa da littafinsa ga ɓangare guda kurum na mutanen duniya, akasin addini guda wanda Allah ya hure ya kuma saukar. Wannan ya shafi dukan duniya da kuma ’yan adam, babu takurawa ko kenkenewa. Haka Yesu Almasihu yake Mai Ceto domin dukan mutane, Littafi Mai Tsarki kuma da ya ƙunshi Attaura, da Linjila saƙo ne zuwa ga dukanin ’yan adam, babu bambanci. Ko da sau nawa za a yi ta maimaita gaskiyan nan, ai, muhimmancin wannan ba sai an faɗa ba.

Cikin ƙasashen da suka ci gaba, mutumin da ake zargi a kotu, salihi ne, sai lokacin da aka tabbatar da laifinsa tukuna sa’an nan ya zama mai laifi, musamman ma idan ba a taɓa samun sa da wani lafiya ba a baya, an kuma san shi da hali mai kyau. Haka yake da maganar da aka faɗa a can baya cewa Linjila gaskiya ce, faɗarta kuma daidai ne, daidai take babu kuskure har sai in an tabbatar da akasin haka tukuna, musamman albarkacin fa’idar Linjila cikin duniya daga ranar da aka rubuta ta har zuwa yanzu ba ta musuntuwa. Za ta kuma ci gaba cikin ɗaukakarta, mafiya yawan mutanen duniya kuma suna ta girmama ta.

Yarda cewa Littafi Mai Tsarki na ainihi ne, Yesu Almasihu kuma gaskiya ne, to, duk wanda ya musunci Allahntakarsa ya gamu da babbar wahala, domin kuwa ta wurin musun nan, ya fitar da Almasihu daga layin annabawa, ba ma wannan kaɗai ba, amma har daga layin mutanen ƙwarai, na kirki, ya saka shi cikin maƙaryata, masu sāɓo, mayaudara kamar yadda Yahudawan zamaninsa suka yi. A kan wannan zato da zai cancanci mutuwa bisa ga dokar da aka saukar wa mutanensa. Duk mutum mai cikakken hankali, ko da menene dokarsa, zai ƙyamaci wannan zato da aka ambata nan sama. Tauraruwar Allahntakar Yesu Almasihu ta haskaka ƙaƙƙarfan haskenta a kan dukan taurarin da aka ambata da fari, waɗanda suka sami haskensu daga wannan tauraruwar. Daga wannan tauraruwa ne hasken cikarsa ya kwararo.

Duk da haka inganci da ci gaban mutum cikin adalci, ba zai iya zama cikakke ba, domin babu cikakke sai Allah kaɗai. Amma zaman Yesu cikakke na Allahntaka ya zama bisa tushen halinsa na Allahntaka ne, wannan ya sa ya zama cikakke, ba tare da ruɗar da tarke cika ga Allah kaɗai ba. Kamar yadda manzo Bulus ya ce: “Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, an bayyana shi da jiki... an yi wa al’ummai wa’azinsa, an gaskata da shi a duniya, an ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka” (1Timoti 3:16).

Akwai yarjajjeniya mai banmamaki a tsakanin halin Allahntakarsa da sauran taurari guda shida: Saukowarsa daga sama, wahayan annabci na zuwansa, mafificin ikonsa, ’yancinsa na karɓar mubaya’ar sujada, kasancewarsa tare da mabiyansa, da mutuwarsa ta fansa da kuma tashinsa daga cikin matattu, dukan waɗannan suna nuna wannan marar kwatantuwa, da mafificin bambancinsa a kan kowane matsayi na ɗan adam. Tauraruwar halin Allahntaka da yake riƙe da ita a hannunsa na dama, babu mai iya riƙewa, sai Yesu Almasihu, kuma Shi kaɗai.

Abin da ya zama a fayyace gare mu daga taurarin nan bakwai shi ne, Yesu Almasihu tun fil azal ne, kamin a halicci duniya. Annabce-annabce gabanin zuwansa suna da yawan gaske, kuma a sarari suke, masu ci gaba, ya kuma sami iko cikin magana da aiki, shi abin girmamawa ne, da yi wa mubaya’ar sujada, waɗannan kuwa bisa ga doka ba daidai ba ne a yi wa wani mutum kawai, Shi kuwa da yake cikakken adali bai ƙi a yi masa ba. Ya bayyana kasancewarsa kullayaumi tare da mutanensa a kowane wuri, kuma a dukan lokatai, iƙirarin da babu wani talikin da zai iya yi; ya kuma ba da kansa ga mutuwa don kafarar zunuban ’yan adam, ya kuma tashi daga cikin matattu zuwa ɗaukaka domin cika manufar mutuwarsa. Ta wurin dukan alamun nan da sauran waɗanda ya bayyana halin Allahntakarsa, wanda ya zama mutum lokacin da ya ɗauki siffar mutum ta yadda budurwa Maryamu ta haife Shi.

Hasken wata ya samu daga hasken rana ne. Lokacin da wata ya faso da dare, yana sanar da isowar rana ne wadda ta fi shi daraja, hasken da wata ya yiwo aro kafin rana ta bayyana. Hasken Yahudawa wanda ya samu daga hasken Masihi, ya haskaka da wuri, ya kasance har sai da babban haske, wanda aka yi faɗinsa, ya taso. Ashe, ba za mu sa zuciyar ganin hasken Masihin nan ba mai girma, wanda yake daga cikin Almasihu kansa, zai yi ta ci gaba da haskakawa da ƙaruwa cikin duniya, ya kasance har iyakar tarihin ɗan adam?

Yanzu dai mun san cewa, mai riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama Shi ne Shugaba na gaskiya na addinin da aka saukar wa Yahudawa da Kirista. Girmansa da ɗaukakarsa suna nan daga zamanin Adamu har ya zuwa wannan rana.

Ba shakka, duk mutum mai tunani zai yi wa kansa waɗannan tambayoyi:

1). Menene muhimmancin kasancewar Almasihu shi kaɗai ne mutum a cikin tarihin duniya, wanda ya haɗa waɗannan taurari bakwai a cikinsa sun zama tushen abubuwan da ake bukata?

2). Ashe, wannan ba alama ba ce mai nuna cewa Almasihu zai kasance mabambanci a cikin tarihin ɗan adam nan gaba?

3). Ashe, ba Shi ne wanda Allah ya tasa ba tun fil azal ya zama Shi kaɗai ne Mai Ceto domin zunubabben ɗan adam, Shi ne kuma cikakken wakili a gaban mutane daga wurin Allah Ruhu, wanda yake gani amma ba a ganin sa, bisa ga nassoshin Linjila?

Allah ya sawwaƙa, a ce muma mu yi fāriya cikin wannan tattaunawa a kan dokokinmu. Ko kusa ba haka ba! Amma da so samu ne, tun daga zurfin zuciyarmu, mu ga Musulmi su ma su sami albarkun da suke kwararowa daga wurin Yesu Almasihu, wanda ta wurin ɗaya daga cikin manyan annabawansa ya ce: “Duk mai jin ƙishi ya zo, ga ruwa a nan” (Ishaya 55:1). Shi kansa ma ya yi alkawari, “Duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami” (Yahaya 4:14).

“Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda ke duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da Shi ya sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe” (Yahaya 6:40).

Tabbatacce ne daga cikin Linjila cewa, Yesu Almasihu, ba nufinsa ne ya tara babban taron jama’a don ya mai da su mutane na musamman ba, waɗanda za su yi ta bin sa, a riƙa kiransa da sunansa kawai. A akasin wannan, bai so mutane su yi ta zuwa don su zauna tare da shi ba. Babban muradinsa shi ne, hasken samaniyan nan da Allah ya saukar ya yaɗu ya mamaye duniya zuwa ga dukan ’yan adam.

Ana iya faɗin haka ga Kirista, waɗanda suke bin gurbin Ubangijinsu, wato babbar manufan nan ta yaɗa basamaniyen hasken nan, kamar yadda Almasihu ya bayyana shi, ba don kawai a ƙara yawan mutanen wata ɗarika musamman ba. A fili yake cewa, wannan manufa tana iya haifar da ƙiyayya da hamayya; manufa ta fari kuwa ta shafi mutane masu tunani da dukan dokoki cikin biɗar da suke yi da gaske a game da gaskiya.

Kirista ya gaskata cewa ɗaya daga cikin mafiya muhimmancin batutuwan Yesu Almasihu “Ni ne Hasken duniya” Shi ne koyarwarsa masu watsar da zaton kuskure, ya kuma bayyana gaskiya a kan fannin addini.

Wasu daga waɗannan gaskiya su ne:

1) Duk wani addini mai nuna son ibada kawai, mai nuna yana da tabbacin ceto da murna, ba tare da ya damu da canjin zuciya da halayya ba, to, ba addinin gaskiya ba ne, amma na kuskure da zato kawai. Wannan kuwa domin irin son ibadan nan marar ma’ana ne, mai nuna nagarta ta waje tana gamsar mutane kuma ta isa, alhali kuwa tana kama da ruɓaɓɓiyar igiya wadda ba za ta iya ceton wanda ruwa ya ci ba; ko kuma butar da take fanko babu ruwa ciki, ba za ta kashe ƙishirwa ko yunwa ba. Wannan ya zama wurin zaman ƙwari masu dafin mutuwa. Irin waɗannan butoci ko tukwane, gara ma babu su. Son yin ibada tushensa riya ne, shi ne zunubi mafi muni.

2). Duk addinin da ke nuna wa mutane cewa Allah ya yarda da su muddin suna biyayya da dokokin shugabanninsu da na majalisunsu amma ba su damu ko kula da dokokin Allahntaka ba, sai dai bin ka’idodin addini, da wanke-wankensa da aka tsara, to, wannan addini fanko ne kawai, ba shi da wani iko. Wannan ya zama mai ƙasƙantar da addini, bai ma cancanci a ce da shi addini ba, domin shugabanni da majalisun addini ba su da ikon kafa ko shigad da al’adun addini su mai da su doka da sunan addini ba. Don mu gamshi Allah, dole ne mu kiyaye farillan Allah. Babu abin da za a iya girmamawa da sunan “addini” domin bai wuce jahilci da ruɗi kawai ba.

3). Addini na gaskiya, mai amfani kuma shi ne, wanda zai sa mabiyansa su yi ayyukan addini banda jin tsoro, cikin ƙauna da biyayya ga Allah, ba jin tsoron mutum ba. Ibadar irin wannan mutum takan samu daga zurfin ganewa da jin ƙan Allah da alherinsa. Yana jin daɗin bimbinin jauharin Allah da jin muradin ɗaukaka shi. Yana furta zunubansa da kāsawarsa a gaban Allah, yana neman gafara ta hanyar da Allah ya bayyana. Ya nace ga zaman adalci, tare da la’akari da ayyukan addini, ba don neman yabon mutum ba, ko samun rinjaye cikin mutanensa, ko samun nasara cikin aikinsa, ko daga tsoron gidan wuta, ko marmarin shiga sama kawai. Dukan ƙoƙarin nan sakamako ne daga fāriyar kai, wadda ta ke sa mutum ya yi sujada ga kansa a maimakon ga Allah. Irin wannan mutum ba mai ibada da gaske ba ne.

4). Tushen gaskiya na addini shi ne abin da Allah ya ba mutum cikin alheri, ba abin da mutum ya ke yi ba. Abu mafi muhimmanci cikin addini shi ne, abin da Allah yake badawa ga mutum daga ƙaunarsa zuwa ga mutum. Abin da mutum ya ke miƙawa kuwa domin ya gamshi Allah shi ne abu na biye, yana ɓuɓɓugowa daga zurfin godiyar abin da Allah ya yi.

Ana iya misalta gaskiyan nan ta wurin la’akari da cewa, alherin babban Sarki ga ’ya’yansa ko barorinsa, abin da ya cancanci a ƙara mai da hankali gare shi ne, yabo da baza labarinsa fiye da ibadarsu ko hidimarsu gare shi, gama alheri shi ne mafifici, ya kuma fi hidima nauyi nesa ba kusa ba. Amintacce kuma wanda ake girmamawa, bara ko ɗa ga Allah ba safai zai riƙa maganar hidimarsa ga Allah ko mutum ba, amma zai yi shelar tagomashin wannan mai Taimakon Alheri wanda jiye-jiyenƙansa na ruhaniya sun fi gaban na jiki, kamar yadda madawwamin rai ya wuce jiki mai mutuwa nesa ba kusa ba.

Daga nan Linjila ta sha ambatar baye-bayen ruhaniya na Allah a kai – a kai kamar yadda yake cikin sananniyar ayan nan:

“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami” (Yahaya 3:16).

Jinƙai, da gafara, da alheri da kuma salama tare da ƙarfin ruhaniya don bijire wa jarabobi, da wasu baye-baye makamantan waɗannan, su ne duwatsun gaskiya na kan kusurwar addini. Tunawa da waɗannan kyautai masu fifiko a kai – a kai, suna kawo ƙaunar ɗa ga Allah wadda ke sa shan wuya tare da tagomashin Allah ya fi kyau da karɓuwa fiye da jin daɗi tare da fushin Allah.

Bangaskiya ce ta zama tushe da sharaɗin ceto, gama bangaskiya yardar mutum ce ga dukan kyautai na Allahntaka na waɗannan abubuwa masu fiko, tare da cikakkiyar amincewa haɗe da su. Babu tantama cewa, irin bangaskiyan nan tana kama da itace mai rai, mai ba da ’ya’ya kuma. ’Ya’yan bangakiya ana ganin su cikin rayuwar adalci wadda take gudanowa daga gare ta. Bangaskiyar da ba ta kawo waɗannan ’ya’ya muhimmai to, ba ta da rai, kuma ba ta gaske ba ce. Kyawawan ayyuka a zahiri ba kyawawa ba ne sai dai idan ’ya’yan bangaskiya ne. Wannan yana bayyana dalilin da ya sa batun nan, ko ceto ya dangana a kan bangaskiya ne ko ayyuka ya zama da muhimmanci ƙwarai. Kewaye da wannan batu akwai doguwar jayayya, da kura-kurai, da umarnai daga tsara zuwa tsara.

Kyawawan ayyauka sun cancanci a kira su kyawawa a lokacin da aka auna su ta wurin amfanin da suka kawo kaɗai ga mutum baya ga mai aikatawar. Ba mutumin da za a ɗauka mai tsarki ne idan ya yi watsi da bukatun addini waɗanda suka amfani wani mutum, kamar kasancewa mai gaskiya, mai kirki, mai sauƙin kai, mai haƙuri, mai yin gafara, mai ba da haɗin kai, kuma mai hannu sake. Duk mai yin watsi da waɗannan inganci, ba zai sami biyan bukatarsa ba domin ceton rai, ko da shike yana da fiko cikin aikata ayyukan addini.

Idan ƙungiyoyi iri iri cikin “Mutanen Littafi” sun iya yarda cikin bi da waɗannan rukunai na Linjila a su gaskiya ne, sun kuma dace da duka, ana kuma iya ɗaukar su a su tushe ne, to, tsofaffin rarrabe-rarraben za su shuɗe, son zuciya da ƙiyayya kuma za a maye su da jiyyaya, da ƙauna, da kuma salama.

Cikin Allah kaɗai muke da isa har da za mu iya cim ma maɗaukakin sakamako mai albarka, a KANSA muka dogara. Ɗaukaka ga sunansa har abada abadin. Amin!


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland