Littattaffen da muke da su | Kwatanci

Murfi Taƙatchen bayani Yadda yake
Almasihu Cikin Islama Da Kristanci
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Almasihu cikin Islama``. Littafi ne wanda aka yi nazari game da koyaswar Christa da koyaswar Musulmai akan mutantakar Yesu Christi. Marubucin ya tattauna abubuwa game da Maryamu a cikin Ku´rani da Littafi mai Tsarki, da kuma matsayin Yesu Kristi. Ya kuma yi bincike akan haifuwar Yesu da sauran battutuwa game Yesu Dan Allah da sauransu.
HTML
GICCIYEN ALMASIHU GASKIYA NE, BA ALMARA BA
Na John Gilchrist
Da gaskiya ne wai an gicciye Yesu? Wannan muhimiyar tambaya ce, domin, an gina Kristanci akan gicciyewar Kristi da tashin sa daga Mattatu. Littafi mai Tsarki wanda ya zama tushen bangaskiyar Krista na tabbatar mana da cewa Yesu Kristi ya mutu akan Gicciye. Wannan littafi na kuma nuna cewa Yesu bai taba yin shiri domin ya hambarar dad a wata gwanati ba. Bai ma taba yin kokarin karekansa daga wani zargi ba.
HTML
KU AUNA ABU DUKA KU RIƘE MAI KYAU
Na Iskander Jadeed

Wannan dan littafi yana bayana wadansu koyaswar Krista a saukake game da:-

- Gicciye a cikin Sabon Alkawari da Ku´ani

- Masu neman yaki

- Zunubi

- Buddha da Kristi

- Halayen Kristi

HTML
Tarihin Matanin Kur’ani Da Na Littafi Mai Tsarki
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Littafi mai Tsarki Kalmar Allah ne?``. Ya kuma yi nazari akan wadansu shaidu daga cikin Kur`ani da Littafi mai Tsarki. Marubucin littafin ya kuma tattauna wadansu irin shaidu uku. Shaidu daga Littafe masu Tsarki, daga littafin Apokrifa da``Babbar nakasa``, kurakure dubu hamsin, da abubuwan da ke lalata Littafi mai Tsarki. Akwai kuma tarihin Yesu Kristi.
HTML
YA UBANGIJI KA KOYA MINI HANYARKA!
Na Iskander Jadeed

Mutane da yawa na son saninhanyar gaskiya ta sanin Allah. Kamar yadda akwai Allah daya kawai, hakannan kuma akwai hanya daya kadai zuwa wurinsa. Wani hanya ce?

Musulmai sun bada gaskiya cewar ``Islama ne addinin Allah``; Gaskiya cewa Islama ce hanya zuwa ga Allah. Yesu ya ce, ``Nine hanya``(Yohanna 14;6. Shine hanya? Kana iya samun amsar wannan tambayar a cikin wannan littafin.

HTML