BISHARA TA HANNUN BARNABA

BISHARA TA HANNUN BARNABA

SHAIDAR ƘARYA

ISKANDER JADEED

All Rights Reserved

1999


An tabbatar da cewa littafin da aka sani da suna Bishara ta hannun Barnaba, ko kaɗan ba shi da wata dangantaka da Kristanci. Wannan shaidar jabu ce a kan bishara mai tsarki, an yi ta da nufin karkatar da fassarar addinin Kirista. Cikin wannan hali ta yi daidai da wani kundin Kur’anin da Museilma Maƙaryaci ya rubuta, ko kuwa wanda Al-Fadhl bin Rabi’ ya ƙaga. Littafin da aka lanƙaya wa Barnaba. Dr. Khalil Sa’adah ne ya juya shi daga Turancin Ingilishi zuwa harshen Larabci cikin shekara ta 1907 bisa ga roƙon Sayyid Muhammadu Rashid Ridha, wanda ya kafa Mujallar Al-Manar. Kirista sun ƙi wannan gaba ɗaya domin na jabu ne.

Wata ɗarikar Musulmi ce ta yarda da wannan. Sun yarda da haka kuwa domin dalili guda kawai, wato littafin ya goyi bayan cewa ba a gicciye Almasihu ba, amma kamanninsa ne aka lanƙaya wa Yahuda Iskariyoti, sai aka gicciye shi a maimakon Almasihu.

RA’AYOYIN MASANA

Masanan da suka yi binciken al’amarin a hankali, sun yarda gaba ɗaya cewa wannan littafin, wanda a ƙaryace aka ce na Barnaba ne, bai kasance ba kafin ƙarni na goma sha biyar. Wannan kusan shekara 1500 ne bayan mutuwar Barnaba. Idan da yana nan kafin wancan lokaci, Manyan malaman Musulmi kamar su Al-Tabari, da Al-Baidhawi, da Ibn Kathir da ra’ayinsu bai rarrabu ba a game da ƙarshen rayuwar Almasihu a duniya, ko a game da rarrabe mutumin da aka gicciye a maimakon Almasihu.

dan mun dubi sanannun rubuce-rubucen Musulmi kamar su “Makiyaya ta Zinariya” na Al-Mas’udi, da “Farko da Karshe” na Imam’ Imadud-Din, da “Kundin Ibrizi” na Ahmad Al-Magrizi, za mu lura cewa, waɗannan shahararrun masana sun nuna cikin rubuce-rubucensu cewa, bisharar Kirista idan wannan ce da marubuta huɗu suka rubuta, wato Matiyu, Markus, Luka da kuma Yahaya; Al-Mas’udi ya rubuta cewa, “Mun ambaci sunayen almajirai goma sha biyu da guda saba’in na Almasihu, da watsuwarsu cikin ƙasa, da wasu labaru na abubuwan da suka yi, da wuraren da aka binne su. Marubutan bishara sun haɗa da Yahaya da Matiyu cikin su goma sha biyun, Luka da Markus, kuwa suna cikin su saba’in” (Al-Tanabih wal Ishraf” shafi na 136).

Idan mun duba tsofaffin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki da aka yi can baya tun kafin zuwan Islama, waɗanda kuma Kur’ani ya yi magana a kai, yana kuma ba da shaidar gaskiyarsu, amma ba mu ga wata Bishara da aka liƙa wa Barnaba ba. Babu ma ko ambaton ta cikin jerin sunayen littattafan da iyayen Ikilisiya suka shirya na halattaccen Littafi Mai Tsarki. Binciken tarihi ya nuna cewa rubutun asali na wannan jabun Bishara ta bayyana ne a karo na farko cikin 1709, a hannun Craemer, Mashawarcin Sarkin Prussia. Aka karɓa daga gare shi aka ajiye cikin Åakin Karatu na Vienna Cikin 1738. Dukan masanan da suka bincika wannan bishara sun lura cewa, salon rubutun ƙasashen gabashin duniya ne, a gefen shafi kuma akwai matuni da aka rubuta da Larabci. Daga auna takarda da tawada da aka mora kuwa, sai aka ga cewa an rubuta ta cikin ƙarni na 15 ko na 16.

Wani masanin Ingilishi, R. Sale, ya ce ya sami kofen littafin nan cikin harshen Spanish wanda wani mutumin Ukraniya mai Suna Mastafa Al-Arandi ya rubuta, wanda ya ke iƙirari cewa shi ya juya shi daga harshen Italiya. Gabatarwar wannan kofen ta nuna cewa wani ɗan zuhudu mai suna Marino, wanda yake kurkusa da Papa Sixtus na V, ya ziyarci ɗakin karatun Papa Roma wata rana cikin 1585, sai ya sami wata wasiƙa ta St. Irenaeus yana sèkar manzo Bulus yana kafa tushen sèkarsa a kan Bishara ta hannun Barnaba. Daga nan ne sai Marino ya yi sha’awar samun wannan Bishara ƙwarai da gaske. Wata rana ya sadu da Papa Sixtus na V cikin ɗakin karatun, da suna hira, sai Papa Sixtus na V ya kama barci. Sai ɗan zuhudun ya sami zarafin neman littafin, ya kuwa same shi, ya ɓoye shi a haɓar rigarsa. Ya jira sai da Papan ya farka sa’an nan ya tafi da littafin. Duk dai wanda ya karanta rubuce-rubucen St. Irenaeus ba zai ga inda aka ambaci Bishara ta hannun Barnaba ba, babu kuma sèkar da aka yi wa manzo Bulus.

Duk da haka, akwai wani batu da kowa zai iya sani, yana a rubuce cikin Ayyukan Manzanni cewa, Barnaba da Kansa abokin tafiyar Bulus ne lokacin da ya yi wa’azi Cikin Urushalima, da Antakiya, da Ikoniya, da Listra, da Darba. Barnaba kuma ya yi wa’azin bishara tare da ɗan ɗan’uwansa a Kubrus. Wannan yana nuna cewa, Barnaba Mai gaskata bisharar gicciye ne wadda Bulus da Markus, da sauran manzanni suka yi wa’azin ta, wadda akan iya taƙaicewa cikin sheɗara guda: Almasihu ya mutu a kan gicciye a matsayin kafara domin zunuban duniya, ya kuma tashi a rana ta uku domin baratarwar duk wanda yake ba da gaskiya. Tun da Bisharar Barnaba ta musunci wannan gaskiyar, tabbacin a fili yake cewa littafin ɗan jabu ne.

Wasu masana sun ɗauka lalle ɗan zuhudu Mario ne marubucin Bishara ta hannun Barnaba, bayan da ya karɓi Musulunci aka ba shi suna Mustafa Al-Arandi. Wasu sun so su yarda cewa kundin cikin Italiya ba shi ne kofen farko ba, amma an juya shi ne daga Larabci na asalin littafin. Dalili kuwa shi ne, duk mai karanta wannan Bisharar wai-wai ta Barnaba, zai iya ganin cewa marubucin yana da sani ƙwarai na Kur’ani, mafi yawa na matanin kusan an juya su ne dalla-dalla na ayoyin Kur’ani. Daga cikin na fari da suke da wannan ra’ayi shi ne shehin Malami Dr. White, cikin 1784.

MARUBUCI: SHI NE KIRISTAN DA YA RUNGUMI ADDININ ISLAMA

Ko me ra’ayoyin manyan masana zai zama, tabbatacce ne cewa, littafin nan ya ba da labarin Yesu Almasihu ta hanyar da ta yi karo da matanan Kur’ani, ya kuma rikitar da gaskiyar abin da Bishara ta ƙunsa. Wannan ya sa muka gaskata cewa, marubucin Kirista ne wanda ya rungumi addinin Islama. Mun Lura da wannan cikin faruwar waɗannan al’amura.

Ya fi ba da tagomashi ga Muhammadu a kan Yesu. Ya ba da labari cewa Yesu ya ce, “Lokacin da na gan shi, sai na ta’azantu na ce, ‘Ya Muhammadu, Allah ya kasance tare da kai, ya kuma sa ni in cancanci kwance maɗaurin takalmanka, don in na isa wannan, zan zama mai girma, kuma annabi mai tsarki’” (44:30, 31). An kuma ce, “Yesu kuma ya ce, ‘Ko da shike ban isa in kwance maɗaurin takalminka ba, duk da haka na sami alheri da jinƙai’” (97:10).

Littafin ya ƙunshi wasu sashin magana da suke daidai da tsofaffin rubuce-rubucen Musulmi. “Yesu ya amsa, ‘Sunan Masiha abin mamaki ne domin Allah kansa ya ba shi sunan a lokacin da ya halicci ransa, ya kuma ɗora sunan a kan ɗaukaka basamaniya, ya ce: ‘Ya Muhammadu, ka jira domin saboda kai nake so in halicci sama da ƙasa, da ɗumbin halittu da zan ba ka, don duk wanda ya albarkace ka, za a albarkace shi, duk kuwa wanda ya la’anta ka, za a la’anta shi. Lokacin da na aike ka duniya zan sa ka zama manzona domin ceto, maganarka kuma za ta zama gaskiya. Sama da ƙasa za su shuɗe amma bangaskiyarka ba za ta shuɗe ba daɗai. Sunansa mai albarka shi ne Muhammadu.’ Sai taron jama’a suka ɗaga murya suna cewa, ‘Ya Allah, ka aiko mana da manzonka. Ya Muhammadu, ka zo maza-maza domin ceton duniya’” (79:14-18).

“Da Adamu ya miƙe kan ƙafafunsa, ya ga haske kamar na rana a sararin sama, da wani rubutu, ga abin da ke a rubutun, ‘Babu wani Allah, sai Allah kaɗai. Muhammadu kuma manzon Allah ne.’ Sai Adamu ya ce, ‘Na gode maka, Ya Ubangiji Allahna, domin Ka yi alheri, ka halicce ni, Amma ina roƙon Ka, ka gaya mini ma’anar kalmomin nan, ‘Muhammadu manzon Allah ne?’ Allah ya amsa, ‘Maraba bawana Adamu. Hakika, ina gaya maka cewa, kai ne mutum na fari da na halitta. Wannan da ka gani kuwa ɗanka ne, wanda zai zo cikin duniya shekaru masu yawa nan gaba. Zai zama manzona wanda dominsa ne na halicci dukan abu. In ya zo zai zama haske ga duniya, wanda aka ɗora ransa cikin samaniya har shekara dubu sittin kafin in halicci wani abu.’ Adamu ya roƙi Allah yana cewa: ‘Ya Ubangiji, ka ba ni rubutun nan a ƙumbar yatsotsin hannuna.’ Sai Allah ya ba da rubutun nan ga mutum na fari – a ƙumbar babban yatsa na hannun dama, ga abin da aka rubuta, ‘Babu wani Allah sai Allah kaɗai’ a ƙumbar babban yatsan hannun hagu aka rubuta, ‘Muhammadu manzon Allah ne’” (39:14-26).

“Daganan sai Allah ya ɓace wa ganinsa, mala’ika Mika’ilu kuma ya kori dukansu biyu (Adamu da Hauwa’u) daga firdausi. Da Adamu ya komo, ya kuma ga an rubuta a kan daɓe: ‘Babu wani Allah sai Allah kaɗai. Muhammadu kuma manzon Allah,’ sai ya koma ya ce: ‘Mai yiwuwa ne Allah yana so ya zo da wuri (Ya Muhammadu) ka kuma cece mu daga wannan taɓarɓarewa’” (41:29-31).

Waɗannan batutuwa sun yi karo cikin kalma da ruhu, tare da tsofaffin rubuce-rubucen Musulmi, kamar su “Al-Ithafat Al-Saniyya bil Ahadith Al-Kudusiyyah” da “Al-Anwar Al-Muhammadiyyah min al Mawahib Al-Laduniyyah” da “Al-Isra Mu’jiza Kubra,” da sauransu.

RIKITARWA GA BISHARA MAI TSARKI

Akwai ɗumbin tabbaci masu nuna cewa marubucin ba shi da wata ma’amala ta kowace iri da manzannin Almasihu, ko almajiransa da suka rubuta littattafan ta wurin izawar Ruhu Mai Tsarki. Wasu daga cikin fitattun tabbas sun haɗa da waɗannan:

Na fari dai shi ne, jahilcin marubucin a game da labarin ƙasar Falisɗinu da ƙasar da take dakalin labarun addini. Ya ce, “Yesu kuma ya tafi tekun Galili ya shiga jirgi zuwa Nazarat, garinsa. Sai aka yi hadiri mai ƙarfi, kamar jirgin zai nutse” (20:1, 2). Sanin kowa ne, Nazarat a kan tuda take ba a gāɓar teku ba, kamar yadda marubucin ya ce. A wani wuri kuma ya ce, “Ka tuna cewa Allah ya yi shirin ya hallaka Nineba saboda babu ko mutum guda da ke tsoronsa. Yunusa ya yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish don yana jin tsoron mutane, amma Allah ya jefar da shi cikin teku, kifi kuma ya haɗiye shi, ya je ya amayar da shi kusa da Nineba” (63:4-7). Sananne ne cewar Nineba ita ce babban birnin sarautar Assuriya, an kuma gina birnin a gāɓar gabas ta Kogin Yufiretis a sashin makwararin da aka sani da suna Al-Khisr. Saboda haka, ba a yankin Tekun Bahar Rum yake ba kamar yadda marubucin ya faɗa.

Abu na biyu, marubucin bai san tarihin Yesu Almasihu ba. Cikin sura ta uku ta wannan jabun bishara, an rubuta cewa, “Lokacin da aka haifi Yesu, Bilatus ne Gwamna a zamanin shugabancin firistancin Hanana da Kayafas” (3:2). Wannan ba gaskiya ba ne, domin Bilatus ya zama gwamna daga A. D. 26 zuwa A.D. 36. Hanana kuwa ya zama babban firist daga A.D. 6; Kayafas kuma daga A.D. 8 zuwa A.D.36. Cikin sura ta 142 an rubuta cewa Masiha ba zai fito daga zuruyar Dawuda ba, amma daga zuriyar Isma’ilu, ba kuma ta Ishaku ba (124:14). Wannan ƙaton kuskare ne, domin duk mai karanta tarihin asalin Almasihu cikin Bishara ta gaskiya, zai ga cewa, bisa ga jiki, shi daga gidan Dawuda ne, daga kabilar Yahuza.

Abu na uku, marubucin ya haɗa da wasu labarun da ba su da tushe cikin Kristanci. Ga misalin irin waɗannan labarun: “Lokacin da Allah ya ce wa mabiya Shaiɗan, ‘Ku tuba, ku kuma sani Ni ne Mahaliccinku.’ Sai suka amsa: “Mun juya daga bauta maka, domin Kai ba mai adalci ba ne, amma Shaiɗan mai gaskiya ne kuma salihi, shi ne kuma Ubangijinmu.” Daganan sai Shaiɗan, da zai tafi sai ya yi tofi a kan wani ɗan tarin ƙasa, Jibra’ilu kuma ya ɗaga tofin tare da ɓarɓashin ƙasar, a sakamakon haka sai mutum ya zama da mayaƙan ruwa a cikinsa” (35:25-27).

“Yesu ya amsa yana ce musu, ‘Hakika, na tausaya wa Shaiɗan da na san fāɗuwarsa, na kuma tausaya wa mutum wanda ya jarabtu cikin zunubi. Saboda haka na yi azumi da addu’a ga Allahnmu Wanda ya yi mini magana ta wurin mala’ikansa Jibra’ilu yana cewa, ‘Me kake so, Yesu, menene roƙonka?’ Na amsa, ‘Ya Ubangiji, Ka san muguntar da Shaiɗan ya haddasa, shi kuma da yake halittarka ne, ya lalatar da mutane da yawa da ruɗinsa. Ka yi masa jinƙai ya Ubangiji.’ Allah ya amsa, ‘Yesu, duba, na gafarta masa. Bari kaɗai ya ce, ‘Ubangiji, Allahna, na yi zunubi, ka yi mini jinƙai’ daga nan zan gafarta masa, in komo da shi a matsayinsa, na asali.’ Yesu ya ce, ‘Da na ji wannan, na yi murna, na gaskata ni na kawo wannan sulhu. Sai na kira Shaiɗan, ya kuwa zo yana tambaya, ‘Me zan yi maka, ya Yesu?’ Na amsa cewa, ‘Kana yi don kanka ne, domin ba na muradin aikinka, amma na kira ka don amfanin kanka.’ Shaiɗan ya amsa, ‘In ba ka son aikina, ba na son naka ni ma, don na fi ka daraja. Ba ka isa ka hidimta mini ba. Kai daga turɓaya ne, amma ni daga ruhu’” (51:4-20).

Ba mutum mai cikakken hankali da zai gaskata cewa irin wannan labari ya fito daga Bishara hurarriya daga Allah. Da fari dai, Allah bai ji daɗin Shaiɗan ba ko kaɗan lokacin da ya fāɗi, aka kuma koro shi daga gaban Allah. Bai dace da tsarkin Allah ba a ce yana neman shiri da Shaiɗan har ya yi sulhu da shi. Na biyu, tun da farko Almasihu ya shiga yaƙi da Shaiɗan ba ji ba gani. Littafi Mai Tsarki yana cewa, “Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Åan Allah shi ne domin ya rushe aikin Iblis” (1 Yahaya 3:8). Na uku, cikin yaƙinsa, Shaiɗan bai taɓa kuskura ya ce ya fi Almasihu daraja ba. A akasin wannan, cikin taron mutane a Kafurnahum, lokacin da Yesu ya umarce shi ya fita daga cikin mutumin, sai ya yi ihu da ƙarfi yana cewa, “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san kowanene kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah” (Luka 4:34).

abbatacce ne cewa marubucin Musulmi ne. Duk wanda ya karanta bisharan nan ta wai-wai, Bisharar Barnaba a hankali zai sami ɓarɓashin Islama a ciki. Na fari, littafin nan ya ƙunshi labarin kamannin Almasihu. Cikin sura ta 112 ta ce: “Saboda haka, sai ka sani Barnaba, cewa a kan wannan dole in yi yaƙi. Åaya daga cikin almajiraina zai bashe ni a kan azurfa talatin. Bugu da ƙari, Na tabbata, wanda ya ke bashe ni za a kashe shi da sunana, domin Allah zai ɗauke ni daga duniya ya sāke kamannin mai bashe ni, don duk wanda ya gani zai ɗauka ni ne shi. Sa’ad da zai mutu, mutuwar takaici, zan kasance cikin wannan siffa har lokaci mai tsawo a duniya. Amma in Muhammadu ya zo, manzo mai tsarki na Allah, za a kawar da wannan wulakanci daga gare ni” (112:13-17). Labarin nan ya zo daidai da irin koyarwar zamanin da ya kama daga ƙarni na biyar zuwa na goma sha biyar.

Na biyu, akwai zargin cewa an daddagular da maganar Allah. Cikin sura ta 12 an faɗo Almasihu yana cewa: “Hakika, ina ce muku, in ba a kawar da gaskiya ba daga Littafin Musa, da Allah bai ba Dawuda ubanmu Littafi na Biyu ba. In kuma littafin Dawuda ba a daddagular da shi ba, da Allah bai danƙa amanar Bishararsa gare ni ba, domin Ubangiji Allahnmu ba mai sākewa ba ne, ya kuma furta saƙo guda ga ’yan Adam duka... Sa’ad da manzon Allah ya zo, zai zo ya tsarkake littafin nan nawa wanda fasiƙai suka lalatar” (124:8-10).

Wannan magana jafa’i ne gāba da ainihin dukanin Tsarkin Maganar Allah, ba kuma zai taɓa yiwuwa ba irin wannan magana ta fito daga Almasihu, wanda ya ce, “Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba” (Matiyu 24:35).

BISHARA TA HANNUN BARNABA JABUN SHAIDA CE Gāba Da KUR’ANI

Tun da fari na ce littafin da aka liƙa wa Barnaba jabun shaida ce gāba da bishara, domin kuwa mafi yawan mataninta birkita gaskiyar bishara ne. A nan ƙasa na ba da wasu matani da suke ƙunshe cikin jabun Bishara, wadda a ƙashin gaskiya, su ma shaidar ƙarya ce gāba da Kur’ani:

1. “Yusufu ya tafi daga Nazarat zuwa, wani gari cikin Galili, tare da matarsa mai juna biyu... don a rubuta sunansu bisa ga dokar Kaisar. Da ya isa Baitalami, bai sami masauki ba, domin garin ƙarami ne, ya kuma cika da baƙi. Sai ya tafi wajen gari inda makiyaya suke. Sa’ad da suna a can, sai lokaci ya yi da Maryamu za ta haihu. Sai aka kewaye budurwar da wani haske, sai ta haifi ɗanta ba tare da shan wuyar naƙuda ba” (3:5-10).

Kur’ani ya tabbatar da cewa Maryamu ta yi naƙuda kamar kowace mace mai haihuwa, gama Kur’ani ya ce: “Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nisa. Sai naƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturun dabiniya, ta ce, ‘Kaitona, da dai na mutu a gabanin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta” (Suratu Maryam 19:22, 23).

2. “Ku ’yan Adam, ina misalin Miskinancinku, gama Allah ya zaɓe ka kamar ɗa ya kuma ba ka firdausi. Amma kai miskini ka fāɗa cikin fushin Allah ta wurin aikin Shaiɗan, an kuwa kore ka daga firdausi” (102:18, 19).

Kur’ani ya ɗauki gaskata cewa Allah yana da ɗa sāɓo ne, sāɓon da ya cancanci hukuncin gidan wuta. Kur’ani ya ce: “Kuma ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce, ‘Allah yana da ɗa” (Suratul Kahf 18:4, 5).

3. “Mutum zai wadatu da mace guda da Mahaliccinsa ya ba shi, zai manta da sauran mata duka” (116:18); Ku’arni kuwa yana koyar da auren mata fiye da ɗaya yana cewa, “Kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba a cikin marayu to, ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa’an nan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to, ku auri guda... ” (Suratun Nisa 4:3).

4. “Lokacin da Allah ya halicci mutum, ya halicce shi da ’yanci don ya san cewa Allah ba ya bukatar sa, kamar dai yadda sarkin da ya ba bayinsa ’yanci don ya nuna wadatarsa domin bayinsa su ƙara son sa” (155:13). Wannan ya rikitar da Kur’ani da ya ce: “Kuma kowane mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa... ” (Suratul Isra 17:13). Sharhin Al-Jalalaini, ya ɗauko faɗar Mujahid a Matsayin tushen da ya dogara, yana bayyana ayan nan kamar haka: “An haifi kowane mutum da takarda ɗaure a wuyansa inda aka rubuta cewa shi miskini ne, ko kuma mai farin ciki.”

5. “Sai manzon Allah ya ce, ‘Ya Ubangiji, akwai wasu masu bi Cikin Gidan Wuta, suna can har shekara dubu saba’in. Ina jinƙanka, Ya Ubangiji? Ina roƙon ka, ya Ubangiji, ka ’yantar da su daga wannan horo mai tsanani.’ Daga nan sai Allah ya umarci Mala’iku huɗu mafiya tagomashi su je gidan wuta su fito da dukan waɗanda suke na addinin manzon Allah, ku kai su firdausi, wato aljanna” (137:1-4). Wannan matani ya rikita gaskiyar Kur’ani, wanda gaba ɗaya ya musunci wannan roƙon ahuwa, gama ya ce: “Lalle, Allah ya la’ani kafirai, kuma Ya yi musu tattalin wata wuta mai ƙuna. Suna madawwama a cikinta har abada, ba su samun majiɓinci, kuma ba su samun mataimaki” (Suratul Ahzab 33:64, 65).

6. “Yesu ya yarda da ya ce, ‘Hakika, ina ce muku, Ni ba Masiha ba ne.’ Sai suka tambaye shi, ‘Ko kai Iliya ne, ko Irmiya, ko kuwa ɗaya daga cikin annabawan dā?’ Yesu ya amsa, ‘Babu.’ Sa’an nan suka ce masa, ‘Wanene Kai don mu shaida wa waɗanda suka aiko mu?’ Yesu ya ce, ‘Ni ne muryar mai kira cikin Yahudiya, ku daidaita hanyar manzon Ubangiji” (42:5-11).

A halin gaskiya, ko akwai mummunar jabun shaida mai gāba da Bishara da kuma Kur’ani fiye da wannan? Ko akwai Musulmin da zai gaskata wannan rikitarwa mai cewa “Masiha” shi ne Muhammadu ɗan Abdullah ba Yesu ɗan Maryamu ba?

ALBARKA Tā TABBATA

GA MASU

KWAÅAITA

GA ADALCI

domin za a biya

musu muradi


KIRAN BEGE
P.O. Box 14555
KANO
NIGERIA

Internet: http://www.the-good-way.com -