Littattaffen da muke da su

Murfi Taƙatchen bayani Yadda yake
ALHERINA YA ISHE KA
Na Ghulam Masih Naaman

Wannan Littafi shaida ne na wani Musulmi daga Pakistan wanda ya karbi Yesu Kristi ya zama mai cetonsa. Ya bauta wa Ubangiji tare da matarsa da iyalinsa, duk da wulakanci da wahalun day a sha chikin gida da kuma waje.

An kebe shi Fasto a karkashin Ekklisiyar Anglikan inda ya ci gaba da bauta wa Ubangiji har karshen rayuwan sa.

HTML
Almasihu Cikin Islama Da Kristanci
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Almasihu cikin Islama``. Littafi ne wanda aka yi nazari game da koyaswar Christa da koyaswar Musulmai akan mutantakar Yesu Christi. Marubucin ya tattauna abubuwa game da Maryamu a cikin Ku´rani da Littafi mai Tsarki, da kuma matsayin Yesu Kristi. Ya kuma yi bincike akan haifuwar Yesu da sauran battutuwa game Yesu Dan Allah da sauransu.
HTML
BISHARA TA HANNUN BARNABA <<SHAIDAR KARYA>>
Na Iskander Jadeed
Wannan dan littafi ya shaida cewa an karyata wannan Bishara ta hannun Barnaba. Bishara ta hannun Barnaba na cike da kurakure masu yawa. Marubucin yana zaton cewa wani dan kasar Italiya ne wanda ya shiga musulci ne ya rubuta Bishara ta Hannun Barnaba.
HTML
Dalilin Zamana Kirista
Na Sultan Muhammed Paul
Wannan littafi ya kunshi labarin wani Musulmi daga Afganistan wanda ya karbi Yesu Kristi ya zama mai cetonsa bayan da ya yi nazari akan irin koyaswanda ya taso da shi. Ma rubucin ya mayar da hankalin sa ne akan irin gardama day a yi da Krista kafin tubarsa. Ya nuna yadda ya samu ceto cikin Yesu Kristi.
HTML
GICCIYEN ALMASIHU GASKIYA NE, BA ALMARA BA
Na John Gilchrist
Da gaskiya ne wai an gicciye Yesu? Wannan muhimiyar tambaya ce, domin, an gina Kristanci akan gicciyewar Kristi da tashin sa daga Mattatu. Littafi mai Tsarki wanda ya zama tushen bangaskiyar Krista na tabbatar mana da cewa Yesu Kristi ya mutu akan Gicciye. Wannan littafi na kuma nuna cewa Yesu bai taba yin shiri domin ya hambarar dad a wata gwanati ba. Bai ma taba yin kokarin karekansa daga wani zargi ba.
HTML
KO ALLAH YA BAYYANA CIKIN JIKI?
Na Iskander Jadeed
Ko zai iya yi wu wa cewa Allah ya bayyana kansa cikin sifan mutum? Ma rubucin wannan littafi ya yi nazari da bayani akan yadda Maryamu ta haifi Yesu (an haife shi a kamanin mutum). Ya zauna a cikin wanan duniya, ya yi irin rayuwa na dan´adam. Ya ji yunwa, ya ji kishin ruwa, ya gaji da tafiya, har ma ya yi barci a cikin jirgin ruwa. An wulakanta shi ko da shike shi Allah ne cikin jikin mutum. Ko da shike ya zo cikin sifar mutum, ikonsa ya cika sama da kasa. Wannan shine asirin halayensa kamar yadda aka bayana a cikin littafin Matiyu 11:27 da kuma 1 Timatawus 3:16.
HTML
KU AUNA ABU DUKA KU RIƘE MAI KYAU
Na Iskander Jadeed

Wannan dan littafi yana bayana wadansu koyaswar Krista a saukake game da:-

- Gicciye a cikin Sabon Alkawari da Ku´ani

- Masu neman yaki

- Zunubi

- Buddha da Kristi

- Halayen Kristi

HTML
TIRNITI [MURHUNNIYA] DA ƊAYANTAKA
Na Laccar da Papa Shenuda III ya bada a Babbar Majami’ar Markus a Alƙahira
Wannan lacca ya nuna wadansu kurakure da Musulmai suke dashi cikin tununin su game da Triniti.
HTML
Ta YaYa Za Mu Iya Sanin Gaskiyar Linjila / Bishara?
Na Iskander Jadeed
Wannan littafi ya yi nazari akantushen bangaskiyar Krista. Marubucin yak are martabar Littafi mai Tsarki, da martabar Dan Allah, da gicciye, da wadansu battutuwa da ba mutane wahala.
HTML
Tarihin Matanin Kur’ani Da Na Littafi Mai Tsarki
Na John Gilchrist
Wannan littafi ya mai da martani ne ga littafin Deedat mai suna ``Littafi mai Tsarki Kalmar Allah ne?``. Ya kuma yi nazari akan wadansu shaidu daga cikin Kur`ani da Littafi mai Tsarki. Marubucin littafin ya kuma tattauna wadansu irin shaidu uku. Shaidu daga Littafe masu Tsarki, daga littafin Apokrifa da``Babbar nakasa``, kurakure dubu hamsin, da abubuwan da ke lalata Littafi mai Tsarki. Akwai kuma tarihin Yesu Kristi.
HTML
YA UBANGIJI KA KOYA MINI HANYARKA!
Na Iskander Jadeed

Mutane da yawa na son saninhanyar gaskiya ta sanin Allah. Kamar yadda akwai Allah daya kawai, hakannan kuma akwai hanya daya kadai zuwa wurinsa. Wani hanya ce?

Musulmai sun bada gaskiya cewar ``Islama ne addinin Allah``; Gaskiya cewa Islama ce hanya zuwa ga Allah. Yesu ya ce, ``Nine hanya``(Yohanna 14;6. Shine hanya? Kana iya samun amsar wannan tambayar a cikin wannan littafin.

HTML